BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
9/22/20, 8:13 AM – Ummi Tandama: BAHAGGON RAYUWA, , , , , , , ,

????????8️⃣7️⃣????

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU

Bayan baaba ta shirya mu ne abin ya danyi sauki sosai tsakanin mu kwanan baaba biyu tare da mu a gidan bata tafi ko ina ba suka shirya komawa bauchi.
Ko gidan Aisha da kyat na samu ta tafi bamu dade ba muka dawo sai sahad store da muka shiga ta dan duba abinda take bukata ita da anty suwaiba da yan matan ta.
Kudin da uncle ya basu shi suka sawo yan kayayankin fashion dashi a cikin saukin farashi washe gari zasu tafi don haka bamuyi barci da wuri ba a gidan.
Da safe kuma na tashi nayi sakkon dora masu abin karayawa kafin su wuce saida suka karya suka dauki hanya anan suka barmu cike da kewan su a gidan.
Sai gidan ya koma muna tsit bayan wucewan su zuwa azahar na shiga kitchen na hado masan da nayi warming da miyar kassa na dawo falo na zauna kasa saman carpet ina ci.
Mommy ta shigo falon masan takai ma kallo daga inda nake zauna ina ci a hankali ina kallon tv take fadin wai ni na rasa yaya mutanen nan ke masan su yafi na ko ina dadi ?
Nace da ita suna tsaya su gyara ne ko ke a gidan ki mommy idan zaki tsaya ki gyara kamar yadda sukeyi zai koma ki.
Mommy ko na zubu maki ne na dago kai ina tambayan ta don nasan gwanace wurin cin masa nawa mai dalili ne cin da nakeyi don saboda ciki nake cin masa yanzu.
Zama tayi tana jawo Abba zuwa jikin ta na fadin Abba bazakaci masan nan mai miya ba don ruda ma ciki zaiyi nace bazan bashi bani idan kuna so ku debo naku ku dumama kuci.
Zan jira yan matana suzo ne sai mu dumama muci don suma suna son masan nan sosai nagani tace dama magana nazo muyi dake yanzu gaki kuma kina cin abinci.
Mommy may nene nace cikin dago kaina ina fuskantar ta ta ce ba wani magana bane dama gani nayi tunda an kai karshen matsalar ku da maigidan ki .
May zai sa har yanzu baki zuwa gare shi kike baya baya dashi bayan kisan kece mai laifi kuma an shirya maganan nan a tsakanin ku kuma kon kasa bashi hakkin shi har yanzu.
Jikina ne yayi sanyi sosai da maganan mommy saboda ban dauka ta fahinci ban shiga turakar incle ba dama don tana rigamu shigewa dakin ta.
Maganan ta yasani dagowa na sake kallon ta da tace indan kina haka kina cutar da mijin ki ne da kan ki zamana a cikin ku kima baida wani amfani ke nan.
Nasiha sosai tayi min akan abinda nakeyi akarshe nace na gode mommy in Allah yaso zan gyara mommy tace ki kulla don Allah diya ta.
Nace mommy ba wai ina share shi bane dama ban san may zai mun bane idan na kusanci ida yake kin san shi bai iya fishi ya sauka maza ba.
Komai zai maki dole ki shanye don shine gaba dake kece a kasa don haka ki maza ki shirya tsakanin ku komai ya wuce a tsakanin ku.
Mommy in sha Allahu komai ya wuce zan shanye duk wani abinda zai min kan hakan koda bai hakkura da hakkurin da mahafiyar shi ta bamu ba zan shaye duk wullakancin da zai min.
Allah yayi maki albarka da kika fahinci haka komai zai wuce da zaran yaga kin bishi kin kara bashi hakkuri.
Banki ta mommy ba da na gama na gyara mai daki tsab na feshe da room fresh na wanke ban dakin na rufo mai na dawo part dina.
Sai yama ya dawo gida lokacin muna falo zaune dukkan mu har mommy muna hira su kuma suna cin abinci.
Ya shigo da alaman a gajiye yake na mike nabi bayan shi zuwa dakin bayan na kara gaida shi na wuce ban daki hada mai ruwan wanka na fito ina fada mai na hada mai ruwa ok kawai yace min yana duban wasu takarda a hannun shi.
Ban tsaya ba na fice a dakin na koma falo na zauna ya gama ya fito cikin kayan da yake zama dasu a gida da alaman ya rufe fita ke nan yau din.
Gurin cin abinci ya nufa ya ja kujera ya zauna isowa nayi gurin ina kokarin bude kukolin abincin da aka aje don shi a wurin.
Sai da ja zuba mai tuwon semo da miyar yauki Nura tayi muna na abincin dare ya wanke hannun domin fara ci .
Daya daga cikin kujerun na jawo na zauna nima a wurin abincin shi yake ci hankali kwance kamar bai san ina wurin zaune ba a lokacin .
Sai zuwa Abba ne wurin namu ya fara magana yana fadin babana kaci abincin kuwa banga cikin ka ya cika ba shiko yaron kokarin daukan goran ruwan dake gaban shi yake yi.
Yace zuba mai ruwa kila kishin ruwa yake ji baida bakin fada na zuba zan ba yaron ya karba daga hannuna yana kokarin bashi yaron na kawar da kai sai goran yake son dauka kawai.
Daukan yaron yayi zuwa jikin shi ya dibi abincin ya fara kai mashi a baki tare da balle goran ruwan dake gefen shi ya kafa mai a baki sosai ya zuki ruwan daga cikin goran ya cire bakin shi yana mai da numfashi sama sama .
Ina zaune gefe na harde hanayena ina kallon su hankali kance yadda suke yi ba karamin son yara uncle keyi ba dole ya yi min masifa kan barar da cikin da nake shirin yi din don ko banza ya kamata ace yana da yaran da suka kai biyar yanzu a shekarun shi.
Ban ankara ba ashe ya dago yana fadin kin kuwa fara bashi maganin da hajiya ta kawo mai nace cikin kada kai tun tana nan aka fara bashi sai dai bai son sha idan an bashi sai da dare idan zai kwanta ake bashi.
Ke maimu dauko mai biscuit din shi ko zai ci nace biscuit kuma uncle da daren nan zai iya saka shi kashi don ruda ciki yake yi.
Ba tare da ya kalle ni ba yace ke ke wankewa idan yayi ko ba za a bashi idan yana so shiru nayi kawai ina kallon su mommy har ta mike ta shige tun fitowanshi nasan kallo take a dakin ta.
Ganin ya gama na hada kayan zuwa kitchen sai hindatu ta taso tana tayani kwashe kayan a wurin anan yake mata ba a tana murmshi.
Yau bai dade a falon ba ya shige sai dana dauki lokaci na gama hada mai blact tea din shi na ganyen na,ana na samay shi a dakin.
Kamshi ke tashi a jikina sosai a lokacin yana zaune yana aiki a laptop din shi tsab na gyara komai kafin in kwanta a bayan shi.
Bai daina abinda yakeyi din ba har wani lokaci ya rufe tare da mikewa ya nufi bayi can ya fito ya zauna yana shan tea da na aje mai a bakin gado.
Sannu a hankali na dago daga inda nake nakai zaune ina fadin Uncle don Allah kayi hakkuri ga abinda ya faru a baya ba munafata ke nan ba ga abinda kake tuhuma na dashi.
Har tsawon wani lokaci bai mun magana ba nima ban sake magana ba ina zaune shiru a inda nake a bayan shi cikin fargaba.
Sai can naji yace yanzu may kike son in ce tunda ke baki son haihuwa dani ni kuma ina son haihuwa a rayuwana baki min adalci ba Safiya ban cancanci haka a gare ki.
Baka yarda dani ba ke nan uncle nace akan may zan yarda dake yanzu bayan ba wani ya fada min ba ni nagani da ido na a lokacin da baki zata ba.
Murmushi nayi nace to shi ke nan na dauki laifina tunda haka kake son ji a bakina ko nayi kuskure a yafe min daidai yana kaiwa kwance yace min .
Magana daya ne yanzu inga kin haife cikin nan lafiya shine kawai zai sa hankali ya kwanta dake nace har yanzu kana zargina kenan bai yi magana ba sai kashe muna wuta da yayi yana gyara kwanciyan shi da kyau.
Nima komawa nayi na kwanta tare da lumshe idanuwa ina tunanen wanan hali na uncle duk abinda ya kamata nayi dai nayi mai a yanzu.
Ban tsamanin jin hannun daya kai jikina ba a lokacin amma sai tunane na ya kwance a lokacin may yasa maza suke hakane a wurin wanan fannin basu jin kunyan yin haka ko wani lokaci suke da bukata.
Washe gari ban koma barci ba don yace yana da tafiya zuwa Niger state sayen wasu kaya don haka na wuce kitchen don hada mai abinci da wuri kafin Nura tazo aiki.
Ina tsaka ga aiki sai gashi ya biyo ni da wayana a hannun shi da na baro dakin yace yaya Saadu ne ke kirana a lokacin .
Nayi mamakin kiran yaya Saadu haka da safen nan na karba daidai lokacin daya kara kirana din na dana wayan ina fadin ina kwana yaya .
Yace lafiya Safiya kin ga na kiraki da safe haka ko wallahi waya aka bugo min daga gida da dare Allah ya karbi ran Ahmed jiya da daren.
Innalillahi wa inna alaihim rajiun ya rasu yaya yace wallahi safiya da dare jiya suka bugo min waya yana tsaye daga kofa yana saurare na.
Na dago kaina na kalle shi ya tsure ni da idanuwan shi cikin son jin abinda ke faru a lokaci a sanyayye nace wai yaya Ahmed ne ya rasu jiya da dare.
Waye haka na yace dani a sanyaye nace yayan yaya Saadu dana taba aura a lagas Allah yai mai rahama yace yana wucewa zuwa dakin shi.
Jikina yayi sanyi na bishi da kallo dakin mommy na nufa a lokacin don fada mata abinda ke faruwa damu duk ta rude dataji maganan.
Na dan dade muna maganan na koma kitchen na karasa aikina hakana a dadafe sai tunanen zaman da mukayi dashi a gidan shi nakeyi.
Nashiga dakin bayan na gama komai na samu yana tsaye yana shiri har yayi wanka a lokacin ga abin karyawavcan nace mashi sai kuma naja na zauna bakin gado har ya gama shiri ban yi magana.
Tare muka fito a dakin nashi a lokacin zama yayi yake cewa mommy bata fito bane har yanzu nace ina ga shiryawa take zata gidan su yaya Saadu tace .
Baiyi magana sai jawo plate dayayi a gaban shi ganin duk a sabule nake a lokacin sai lokacin na natsu na mike na fara zuba mai arish din a plate.
Sai da ya fara cin abincin yace zasu tafi can lagas din ke nan yau da sauri nace ban sani ba don bamuyi maganan haka dashi ba.
Wayan shi ne yayi kara yaya saadu dine yakirashi a lokacin yake fada mai rasuwan dan uwan nashi yace eh ai daka bugo mata muna tare Allah ya jikan shi yasa ya huta.
Zaka tafi lagas din ke nan yace eh da yau nake son mu shirya mutafi da iyalina mota zaku bi ko jirgi yace ina ganin mota zamu bi don mu uku ne.
Bari kubi jirgi zaifi ku isa da wuri zan fito yanzu zan biyo ta gurin ku kafin in wuce ni dai sauraren maganan su nake yi banyi magana ba.
Sai dai zuciya ta ba dadi a lokacin don mutuwa ko na wanda baka sani ba yana shiga ranka balle ga wanda ka sani din.
Har ya gama yana min sai ya dawo ban iya cewa dashi zan tafi gidan yaya Saadu in mai gaisuwa ba don kada ya fassara min magana da wata manufa kuma.
A dawo lafiya nake yi mashi har yakai kofa yace idan mommy ta shirya sai ku tafi tare ki sauke ta ki masu gaisuwa.
Na gode nace mashi ya fice gidan na sauke ajiyan zuciya mikewa nayi zuwa dakina ko kayan ban ita kwashe wa na soma shiri nima.
Sai da na sauke kannena a makaranta muka wuce gidan mun samay su har sun shirya da ganin yaya Saadu kasan yayi rashin dan uwa a lokacin .
Don ya fita hayacin shi sosai kan mutuwan da akai mashi din samira ke fada muna ai Uncle yazo yanzu ya wuce shine ma ya biya muna kudin jirgi zuwa lagos din.
Nayi ma yaya Saadu gaisu nace idan sun je ya mika min gaisuwa ga sauran yan uwa yace zasu ji safiya .
Yace Ahmed dai ya rasu bai samu rokon ki gafaran abinda yayi maki ba har ya mutu nace babu komai yaya na gafarta mai.
Allah dai yayi mai rahama yasa mutuwa hutu ne gare shi yace amin safiya muna gidan har suka shirya muka raka su zuwa airport muka sauke su a can muka dawo gida.
Ranan dai haka na wuni jiki ba dadi zuwa rana samira ta kirani tana fada min sun isa lafiya yanzu haka suna gidan ma ana batun kauda shi ne.
Wani iri naji a raina na kara mata gaisuwa tace ga sadiya mu gaisa sai da na gyara na fara amsa mata gaisuwan tana kuka sosai a lokacin ni dai hakkuri na basu nace ta gaida min da gwago ina mata gaisuwan rashin da akayi din.
Sai yamma ya dawo a daki na samay shi muka gaisa na hada mai ruwan wanka na fita bayan ya fito falo ne yana cin abincin dare nake mai godiyan abin da yayiwa su yaya Saadu din.
Yace halin shine yasa nai mashi hakan din don yana da rikon gaskiya da amana a tare dashi banda abinda zan saka mai dashi in ba haka din ba.
Shiru nayi shima bai kara magana ba ya gama ya mike yana tambaya na mommy nace suna daki basu fito ba yau.
Bamu dade ba muka shige ciki nikan kwanciya nayi don har lokacin jiki na ba karfe don mutuwan ya shige ni sosai ranan.
Sai dai ina kokarin ganin bai fahinci hakan ba don gudun zargina zai sa yace na damu aiko ban tsira ba sai jin muryan shi nayi yana fadin yau dai kamar kina cikin damuwa ko ?
Da sauri nace damuwa kuma uncle akan may kuma zan damu an maki mutuwa yau mana uban diyar ki ya rasu.
Naji zafin maganan nashi amma a fili cewa nayi mutuwa ko na wanda baka sani ba kana tausayawa mamaci ai balle wanda ka zauna dashi a baya .
Ko ba komai kuma ai dan uwana ne shi kaga dole inji mutuwar a raina wanda nima ba komai nake tunane ba sai tawa makomar a yanzu.
Naga alama yace yana gyara kwanci ba tare da ya kara magana ba muka kwanta hakana ba wani abu daya shiga a tsakanin mu ranan.
Da safe ne yaya Saadu ya kirani wai zamu gaisa da gwago na dan jim nayi na karbi wayan muryan ta na rawa cikin gurbatacen hausan ta da ya gauraye yanzu tace Safiya ke ce yaya gida yaya maigidan naki.
Nace muna lafiya gwago yaya akaji da hakkuri tace hakkuri ya zama dole Safiya Ahmed ya rasu yana fadin a rokar mashike ki yafe mashi don Allah.
Nace gwago ni na yafe mashi tun tuni ai dan uwana ne sai naji ta kama kuka dole na kashe wayan don ban iya jimirin sauraren kukan nata a lokacin.
Nima kukan na kama a wirin sai dai nayi saurin share hawaye na kafin kuka yayi min yawa don ta bani tausayi sosai sai dai shedan na rudina ina tuna irin cutar da sukai min a lokacin.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92Next page

Leave a Reply

Back to top button