BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:12 PM – Ummi Tandama: BAHAGGON , , , , , , , ,

????????5️⃣4️⃣????????

NOVEL DINA NA KUDI NE WANDA YA SAN BAI IYA RIKON AMANA TA FADA MIN IN BATA KUDIN TA , , ,

Shirye shiryen buki aketayi amma ni hankalina baya gare su cike yake da damuwa don ban san yadda zai kwashe da mahaifiyar shi ba.
Na kwanta zuwa dare naji kiran wayan shi ya shigo min a sanyayye na daga wayan gami da sallama a bakina.
Yace kin fara barci ne nace ina naga barci ban san hukuncin da baaba zata yanke a kaina ba kuma ma ai yanzu barci bai ga idona ba tunda nace aure nake so.
Dariya yayi sosai har yana lyalkyatawa yace fada min may zai hana ki barci don Allah ?
Na abubuwa da yawa mana Uncle yace kamar su mai nace wayan san iyaka sai dai ranan da na tare a gidan ka.
Don kullun cikin kawo kudi ayi kaza nake yace look nafa fada maki bana son tarkace daga ke sai boxes din ki za a kawo min na fada maki .
Nace naji uncle amma dai ai za ayi abinda zan ba yan yinin buki ko ?
Yace kai mata ho wanan kuma kina son ki sawa kan ki nauyi ne nace ki bari inzo in dauke ki daga ni sai ke sai gida na amma kin ki.
Nace wani gidan uncle yace gidana na Abuja mana ba anan zaki zauna ba ?
Nace haba uncle kai ka ga haka ya dace ga hajiya baaba da ranta da lafiyan ta a dauke akaini gidan ka na Abuja ?
Ai ka bata damarta na mahaifiya ta sa muna albarkan aure dariya yayi yace Safiya wanan halin ya kara sa ina son ki wallahi yanzun dai sai an kaiki bauchi ke nan wurin hajiya baaba ko ?
Nace a wani irin murya mai sanyi shiya yafi mutunci uncle yace to shike nan hakan yayi kyau zan fada mata su shirya nan za a kawo ki direct idan an dauko ki.
Muka dan taba hira yana fada min yadda suka kwashe da mahaifiyar tashi nace uncle dama bata san halin da kake ciki ba duk wanan dadewan yace bata sani ba.
Kuma ko yanzu na fada mata ne don kada daga baya tazo ta zargeki ga abinda ba laifin ki ba ya kawar da zancen da fadin zan turo maki da sako gobe sai ki kara kiyi hidimar bukin dashi yan uwa na zasu zo ranan alhamis da kayan lefen ki wanda naso ace madam ne zata zo dashi.
Amma wanan matsalar yasa baaba tace daga wurin ta za a kawo komai yadda ya kamata nace Allah ya kaimu lafiya amma ni da an bar lefen don baaba ta riga ta aiko min da akwati biyu yace ta fada min wanan ai mun gani muna so ta hada maki wanan kuma ni na hado maki shiya kaini Dubai dama.
Mukayi sallama ina mai kara yi mashi godiya ya kashe wayan na sauke ajiyan zuciya.
Ina mai ci gaba da tinanen wanan baiwa da ubangiji yai min amma ma kuma baiwan sai yazo min a bahaggon rayuwa.
Washe gari ya shiga gaida mahaifiyar tashi nan yake fada mata yadda mukayi akan nafi son in tare anan bauchi don ta sa muna albarka.
Murmushin nuna jin dadi tayi tace mashi shiya har kullun bani dana sani da zaben ka don nasan bakayin abinda za a yi da an sani cikin sa.
Ko wanan auren kaddaran na Samira da kayi don yan uwanka ne da sukai hadin ba bincike yanzu gashi an bar mu ciki.
Daren jiya banyi barci mai dadi ba a rayuwa na amma da nai tunane sai naga bawa bai wuce kaddaran sa mutuwa kuma tana iya riskuwan bawa a ko wani lokaci.
Don haka yanzu kafin ka tafi sai a fara shiye shirye tunda buki ya dawo wurin mu don da ina dauka acan za a yi komai.
Bai baro bauchi ba sai da suka gama shirin komai da za ayi a nan ya san nan ya baro garin ina kwance naji waya alaman sako ya shigo min ina dubawa kudine wanda sai da ya sani kaduwa.
Na duba na kara dubawa naga milayan guda chur ya turo min tare da sakon da ya biyo baya na .
Nasan wanan zasu ishe ki komai da kuke son yi har da gyaran dakin ummi yadda ya dace asha buki lafiya.
Ummi na kira kurayan daki nake fada mata abinda ya turo min tsaye take sai da takai zaune tana fadin.
Yarinya wanan mutumin kuwa yasan ciwon kudi ashe nifa abin nasa yana ban tsoro wallahi.
Nace ummi samu kudin yake a lokacin su kuma nema akeyi ko yaushe wanan ai ba koma a wurin shi sai kin ga company da ya bude nasa na kan shi.
Tayi shiru tace duk dai da haka abi abin sannu dai yaya Sani na kira da ummi ta fita yazo nake neman shawara a wurin shi yace yanzu abinda za a yi shiryawa zakiyi mu samu Amina aminiyar ki can birni ita zata taimaka maki da sharan da ya dace tunda sune yan birni su suka san abinda ya dace ayi.
Banki ta nashi ba don shawara ne mai kyau ya bani ko banza ya kamata tun farko in neme ta amma na manta da ita.
Don haka shiryawa na yi muka nufi gidan su ni dashi da Rukaiya da tace zata bimu mun isa mun samu taro na arziki a wurin mummy din .
Bayan ta gabatar muna da abinsha cikin wanda takeyi na sana an ta sai na fito mata da maganan abinda ya kawo mu.
Taji dadi sosai tace bari ta kira Amin nan taji yaya za ayi nan ta buga mata waya ta dauka sun gaisa sai take fada mata gani a gidan ta ga kuma bukatan da ya kawo mu zamu zo wurin ta.
Ina jin yadda take murna tace ai ba sai na zo ba gobe ita zata shigo sai a san abin yi mun ji dadi sosai don haka muka koma gida.
Daga yaya sani har yaya Nura basu zauna ba don duk abinda ake so suke zuwa birni su sawo su dawo shafiu kani na ma ba abarshi baya ba.
Amina ta iso da kaunan mijin ta dake zawarci a wurin ta nan suka shiga shiri do ba lokaci issashe gare mu.
Komai an kamala don haka aka kai gidan gwago ana tarawa a can nima na bar gidan mu can gidan gwago din na koma.
Ranan da yan uwanshi zasu iso ana gobe zamuyi walima sai abin ya taru yai masu yawa nidai nawa ido sai dai ina kewan anty na don da yanzu itace zata shirya min komai.
Maimakon bakin da muke jira su iso yaya Saadu ne da iyalin shi suka iso da mahaifiyar Samira da yayanta mace da na miji sai Sadiyan shi da tace zata biyo su.
Nan aka shiga murnan ganin su sai dare bakin shi suka iso garin don haka aka kaisu gidan su Amina a can aka sauke su.
Su yaya Saadu kuma suka sauka wurin mama amma ita Samira da yarta dakin ummi na suka sauka don tace can ne dakin su.
Sai da safe suka gabatar da kayan lefen da suka zo dashi bisa jagorancin mahaifiyar Amina da ta zamay masu uwar daki anan don har sun saba da itako sabon mata baida wuya.
Ga ganin lefe ga shirin walima da za ayi wanda duk kusan matan karkaran mu mama ta aika masu da mintin gayyata wurin.
Inda Amina ta gyato malama khadija daga birni tazo ta wayyar ma mata da kai akan hakkin aure da na yayan su.
Tako zo din don ta wayar dakan mata a wurin da sanyaya masu zuciya da nasihohin ta daga niimar da Allah yaba mace ta gari da jin tsoron Allah a cikin rayuwan airen ta bawa yaya hakkin da ya dace na fanin kula da hakkin su daya rataya akan uwaye mata.
Alamarin ya kayatar sosai don bazaka fahinci haka ba sai kaga yadda mata suka natsu a wurin har da mazaje a can baya da suka zo don saurare.
Ko wace mace a wurin ta natsu ta kama kan ta alokacin kalaman malama na shiga jikin ta nan aka kai karshe su Amina dasu samira suna ta faman raba masu abinda aka tana don waliman buta da dabino sai abinci a cikin take away.
Taro ya watse lafiya kowa sai sam barka akewa juna inda mafi yawan mata basu koma gidajen su ba suka shigo yinin bukin da ake yi a gidan mu.
Sai da dare ne mahaifiyar Samira da su mama suka kaini wurin baba don muyi sallama saboda da safe sammako zamuyi a tafi.
Ina sungun ne a gaban baba yayi gyaran murya ya fara da fadin ikon Allah Safiya kin ga yadda rayuwa ya koma muna a dalilin ki.
Ni banda abin cewa dake sai fatan alheri da gamawa da duniya lafiya Allah ya baku zuria masu albarka.
Ki rike hakkin aure ki rike mijin ki amana don ko shi din ba makyataci bane irin wancan na farko da mukayi maki jeki ubangiji ya kara sa maki albarka.
Kuka ne yaci karfi na lokacin da naji baba yace don Allah ki gafarce ni Safiya dani da duk wani wanda ke gidan nan.
Shima baba kuka ne ya kumbce mashi don haka da sauri mahaifiyar samira ta jani mukabar dakin nashi zuwa dakin mama sai dakin inna.
Tana uwar dakan ta muka shigo Saadatu ne ta shiga kiranta tace tazo ga Safiya nan an kawo ta wurin ta neman gafara.
Muna jin ta tana cewa ni may zan mata su tafi dai Allah ya sa mu sheda sai mama Jummai da dake tare da mu ta bata amsa da cewa ai mun riga mun sheda sai dai muce gwamma da akayi ba wani abu muka kawota yi ba wurin ki don zama tare a sahirce ma junane.
Ta fito don bata dauka anji maganan ta ba sai cewa take naga dai yanzu Safiya ai ba yarinya bace don duk abinda zamu fada mata ta sanshi Allah ya bada zaman lafiya.
Suka mike dajin abinda ta fada suna fadin amin tare da ja hannu na da uwar Samira tayi muka bar dakin ina sa takalma na naji Saadatu na fadin kai Inna sai yaushe zaki ja muna farin jini gun yan uwan mu ne ?
Ni dai mun tafi banji amsan da zata ba yar nata ba don jasan ba mai dadi zataji ba ga bakin inna.
Mun koma wurin ummi na can suka tasa ta gaba wai tayi min fada nasan ba abinda ummi zata iya fadi a gaban su dama sai cewa tati Allah ya albarkaci aure ku yarinya.
Bayan shi bata ce komai ba sai sharan hawayen da takeyi nima kukan nakeyi a lokacin wanda dagani har ummi bamu san ko kukan may mukeyi ba.
Sai mahifiyar Samira ce ta iya cewa haba ai bai kamata ace kuna kuka ba don abin farin ciki ne ya samay mu bana kuka ba mama jummai tace kuka dole ne gare su ai.
Haka dai aka watse ina jin suna hiran lefen da aka kawo wanda mama tasa akai dakin baba wai akwati har set biyu babu ne kawai babu a cikin sa.
Nan suka shiryasu tun cikin daren da za a tafi na kira mama nace a rabawa yan uwa da abokan arziki da sukayi tsaye a wurin sha anin nan suka zaba daga cikin wanda baaba ta turo dashi akabawa wa yanda suka dace aba.
Mutocin tafiya sun iso da dare nan suka kwana inda yaya Saadu da yaya Sani suka zabi masu zuwa kai ni.
Don dogon luxuries aka zo da ita sai karama don daukan amarya ni dai ban san masu zuwa ba na dai san Amina da Samira da yar uwar ta ne.
Daya daga cikin kayan da hajiya baaba ta aiko dashi nasa wanda Amina ta bayar aka dinka min a birni.
Sai da akazo shiga mota na ke jin yadda suke ta hayaniya nadan bude fuska na ina kallon su nace a raina wai ni Safiya yau akema gardaman rakiya gidan miji haka abinda irun su inna basu so gani ba gare nu gashi yau Allah ya nufa anayi akaina.
Yaya saadu ne a gaban motar da na shiga sai gwagon ummi da mahaifiyar Samira matar shi su samira karamar mota suka shiga da su Amina.
inda yaya Sani da yaya Nura suka jegoranci doguwar motar da mutanen dake cikin ta don shiya bugo yace a cika motar azo da mutane.
Mun sha hanya don duk da sammakon da mukayi sai bakwai na yamma muka isa garin bauchi nan naji abinda uwar Samira take cewa shi yasa ni dan bude fuskana nima in gani.
Acan lagos kuma sai faman zage zage anty ke durawa da taji ance mahaifiyar shi ta tura akai kaya ta wurin ta don har kiranshi tayi din ta fada mai bakar magana sai bai daga kiran nata ba.
Da daren nan maigidan ta ya dawo garin nan ya samay ta tana cika tana batsewa sai da ya huta yake tambayan ta abinda da ke faruwa.
Nan ta shiga labarta mashi karya da gaskiya yana sauraren ta sai da ta gama yace amma ban taba sanin baki da wayo haka ba maimuna.
Jin ya kira sunan ta kai tsaye yasata natsuwa yaci gaba da fadin yan zu ke uwa ce zaki bari har ta saki a gaba ki yarda da bukatan ta bayan kin fi kowa sanin halin ta dana yaranta.
Waima tsaya don Allah idan uwa ta juyaki zata iya juya Sulaiman ne kai tsaye ke kin fi kowa sanin ko waye sulaiman don shi dan kaifi guda na kuma ya nuna maki koshi waye.
Ya nuna maki in dake ayi in ma babu ke zai iya gashi sunyi bukin su hankali kwance yace amma ko da labari za a bani cewa zaki iya yin haka bazan taba yarda ba.
Sai gashi keda bakin ki ba kunya ba tsoron Allah kike labarta min shirin ku na shirmay kin dauka kowa baida hankali ne irin ki.
Jikin ta yai sanyi don ganin daddy bai goyi bayan ta ba dama dashi ta dogara ya dawo suyi ma sulaiman din sheri sai gashi ya dawo bakin su daya da sulaiman din.
Bata san cewa da daddy ake kulla komai ba akan bukin nan yayi mata tas yace yanzu dabara ya rage gareta ta gyara tsakanin ta da sulaiman din da ni.
Nan ya shige ya barta tana tunane tare da yin na daman abinda ta aikata gashi anty uwa taja mata hasara da tasan ita zai ba hadin lefen da yaje da yar uwan shi suka yi.
Don ba karya ba ne anty tana da son abin duniya dama maishi akace abu bai isan shi su ko yan uwan Sulaiman sai murna sukeyi yana yi dasu yanzu.
Don dama hurda da ita ya hana shi ya kula da yan uwanshi amma yanzu gashi su yaba su aiwatar mai da komai yadda ya kamata su yi.
Gida ne mai kyau na zamani wadda ya tsaru iya tsaruwa wurin haduwa wata da gani tobashiyan shi ne ita tazo tana muna jagora zuwa ciki sai zolaya take yi.
Maman Samira ta sani karanta wasu ayoyi daga cikin kurani tare da wasu adduoi na neman tsarin ubangiji.
Part din din mu aka fara kaini ko zama banyi su gwago suka ce akaimu wurin uwar mijina.
Mutane suna biye damu inda har zuwa dakin sai dai yan uwana sun tsaya a part dina basu biyo mu ba sai gwago da mahaifiyar Samira da mama da su samira da amina su bakwai dai suka rufa min baya.
Ta idar da sallah ke nan aka ce mata ga amarya an kawo mata tace sun koyi sallah mahaifiyar Samira ne tace yanzu dai muke so a bamu wurin muyi mun kawo amarya masauki ta ne.
Dariya tadan yi tana mikewa daga inda take tare dafadin aiko na gode da wanan zumuntan da kuka nuna min iso inda nake rufe da fuskana ta rugumay ni tana kokarin zaunar dani saman kujera.
Sai na zamay na zube kasa tace a a taso ki hau kujera mana kai na girgiza mata tace Allah yai maki albarka tasa hannu tana bude rufin fuskana.
Naji tace tubarkallah masha Allahu tare da zubamin idanunta akaina ina duke da fuskana kasa ban yarda na dago kaina ba munyi ido biyu da ita.
Gaba sai faduwa yakeyi ta juya wurin sauran yan uwanta dake shake a dakin tace tubar kallah kunga baba na ya iya zaben mata Allah yasa yadda fuskan ki yake dakyau har da halin ki mai kyau ne inji wata daga cikin matan dake dakin tace.
Mahaifiyar Samira ta amshe dace insha Allah yadda take dakyau haka ma zuciyar ta yake farar belbelace wanan mai farin nama.
Sai suka sa guda dakin ya amsa da shewan su nan dai su gwago suka mike suna fadin a basu wuri suyi sallah.
Nima daga inda nake zaune a kasa rufe da fiska nace sallah sai wata daga cikin kan nen shi tazo tace may kike fada amaryan mu kasa kasa nace sallah zanyi.
Baaba wai amaryan mu zatayi sallah tace kaita daki don Allah suyi sai sukace wani abu sai amaryan Abbati baaba dako jikoki bata yarda su shiga mata bayi yau gashi tace amarya ta shiga nan na fahinci yawan tsabtan da tijuwar ashe a gunta ya gado tsabtan shi.
Ni da samira Amina da yaya Samira muka shiga dakin sai lokacin na bude rufin kaina ina jin Samira na fadin ikon Allah wai dakin tsohowa ke nan garin dadi na nisa.
Bayan munyi sallah an wadda tamu da abinci da sha zuwa takwasa akace in fito a kaini part dina mun fito tare da rakiyan matan da hajiya baaba tace su rakani wurina.
Nan muka shiga suka bude dakin dake rufe wanda nasan shike zamana a gidan muka shiga .
Nan suka fice suka barmu sai nida yan uwana a dakin wanda sai lokacin na bude rufin fuskana don in sha iska tare da bin dakin da kallo.
Nan kowa ya sake yana diban abin da yake so da aka wadata mu dashi a part din nawa sai hira ake kwasa sai jefi nake saka baki don zulmin da ya ke damuna a raina.
Yaya Saadune suka shigo wurin mu dasu yaya Sani nan akai ta bakwanci dasu suna biyewa gwago da take jan su.
Wurina ya nufa yana fadin amarya yaya dai na duk kinyi wani laushi dake ajiyan zuciya na sauke tare da kakaro murmushi a fuskana.
Nan muka zauna dashi yana kara yimun nasiha a kan sabon wurin da na shigo yake fafin in kwantar da hankali na in fahinci yanayin su.
In zauna lafiya da kowa a yadda ya fahinci family kamar Sulaiman bai shaku da su ba sosai don duk wanda yazi sai yaji suna mai korafin bai zuwa gida.
Yace kin ga yanzu sai kiyi amfani da wanan daman ki sakashi a hanya ta yadda zai mami yan uwanshi kan sashi kuna zuwa gida lokaci lokaci.
Ki kuma sa ya danga masu alheri yadda ya kamata ke ma dai kin san sauran ba sai na gaya maki ba.
Dagowa nayi idona yana zubar da hawaye nace na gode yaya insha Allahu zanyi kokari inyi yadda ka koya min din.
Nan su yaya Sani suka shigo suma mun dauki lokaci dasu muna hira a wurin sanan sukai muna sallama suka fice.
Amina ta dawo wuri na tana kara haska min rayuwa abinda ya dace in daga yi da yadda zanyi in sa sabo a tsakanimu daidai sauran su.
Naji dadin shawaran ta duk da dama nasan wasu a dan zamana da anty danayi sai dai karin da tayi min na wasu da nake ganin kamar ba masu amfani bane a lokaci.
Sai dare sosai muka samu muka kwanta inda suka ce da safe zasu fita zuwa cikin gari don su bada labarin garin bauchi idan sun koma gida.
Washe gari akai haddaden walima a gidan aka watse lafiya nan mutanen mu suka shiga zaga gari ya rage saura ni da gwago da mama a dakin.
Sulaiman ne ya shigo don ganin fitan su da yayi yana saye da babban riga da yar ciki na farin voile sai dan dinkin da akaimai ba mai yawa ba can.
Ganin su gwago yasa shi jin kunya zai koma gwago tace mukan bari mu fice wurin hajiya mu barku ku gaisa yana fadin su zauna amma sai suka fice.
Acan suka samu su hajiya na al,ajabin kayan garan da muks kawo masu sukace kuko wanan dawai niya haka babu iyaka don roban guguru har bakwai da ruban nama biyu na ragon da aka soya sai zabin da ya sha gyara da hadi biyu alkaki roba biyu kwan zabbi an cika roba biyu sai jarkan man shanu da na nono da sauran tarkace masu muhinmanci.
Bai iya tsayawa ba a dakin don kunya yace barin in fita na dauka ai ke kadai ne a dakin na shigo yana magana yana min wani irin shuumin kallo har sai da gabana ya fadi.
Bai iya tsaya ba juya zuwa wurin baaba nan ya samu suna kallon kayan da aka baza a kofan dakin hajiya baaba ana kallo.
Lumshe ido yayi dayaji baaba da yan uwanshi na ta yabon karanmacin da muka nuna masu da kawo wanan kayan haka a matsayin gara.
Nima kuma a nawa bangare sai yabo sulaiman din da yan uwanshi ke sha wurin yan kawo ni don irin karamcin da aka gwada masu a gidan.
Washe gari suka kama hanya sai dai an bar gwago da mahaifiyar Samira su zasuyi min rakiya Abuja sauran aka tafi dasu mun dade da Amina muna tataunawa.
Gidan ya rage daga ni sai su mummy kamar yadda naji samira na kiran mahaifiyar nata.
Babu kowa a dakin nawa ya shigo ina tsaye gaban mirrow dakin ina kokarin tubke kaina da ya sha kitso ya zubo min a fuska.
Kamshi turaren shi ne ya fara sanar min da shigowan shi dakin nawa sai kuma na gashi ta cikin mirrow tsaye ya soka hannayen shi a cikin aljihun wandon shi tare da kare min kallo don bai taba ganina haka ba hijjabi ajikina ko gyale duk sai na daburce na rasa natsuwana a lokaci guda.
Daidai baya na yazo ya tsaya daidai inda nake a hankali ya ciro hannun shi daga aljihun da suke ya sauke su saman kun kuruna ban san lokacin da na lumshe idanuwa na ba.
A hankali ya dora kanshi saman bayana ban daina abinda nakeyi ba amma na kasa yi masa magana a lokacin saboda kunyan shi da nake ji.
Wai nice yau gani ga uncle a karkashin inuwa daya a matsayin ma aurata nauyi da kunya sun hanani juyowa gare shi in fuskance shi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92Next page

Leave a Reply

Back to top button