BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ina zaune bayan na gama gyan gida tare da dan dafa abin da zanci tunda shi ba damuwa yayi da abincin dare ba sai dare sosai yake dawa kuma a buge.
Kofa naji a na murdawa sai na tashi na bude ban yi tsan manin shi bane a lokacin.
Shine tsaye bakin kofan ya kara daure rain shi naja baya tare da mashi sannu da zuwa tun da yau ya shigo cikin dan hankalin shi gidan.
Bai ko kalleni ba ya shige ciki da hanzarin shi nikan na koma na zauna inda nake da farko .
Sai zuwa can ya fito yana saye da gajeren wando da yar faran singlet ajikin shi ya samu kujera ya haye yana kokarin kuna taba.
A kawo ma abincine nagama nace dashi sai yai wani dagowa ya kalle ni a hankade yaci gaba da abin da yakeyi.
Na ja gafe daya na kama kaina na natsu ga kallon tv da nakeyi saboda yin hakan shine alheri a gare ni tunda naga yana jin tsiya yau din.
Haka muka zauna zugun zugun sai busar taban shi yake yi wanda warin ya cika falon ya hana ni sukuni gaba daya a wurin.
Nake zan shige ciki naji yana cewa ke kawo min abinci in ci zan fita , koda na kawo mai abincin ko cibi uku baiyi ba dan dama yaci dan doyan da na hada wurin girkin dashi.
Ya tsamay hannuwan shi ya ture plate din gefe daya kasa daurewa nayi nace cikin damuwa abincin bai maka bane in dafa ma wani.
Kamar dama jira yake tsutsayi yaja ni nai mai magana sai ko ya mike da sababi kamar wanda naiwa bakar magana yana cewa.
Ke kada ki kuskura ki nemi takura min da tambayan banza da wofi ke zaki sani cin abincin dole ne kokuwa da zaki damay ni da nacin tsiya.
Jikina yai sanyi na tsaya kawai ina kallon shi a cikin mamaki karo na biyu na sake tambayan shi cikin girmamawa may kuma nai maka daga tambaya kawai .
A fusace ya jefamin wani irin harara tare da cewa ke wai baki da hankaline ki barni mana kon zauna kina damuwa na kawai da bakin nacin ki.
Na dago idona cike da damuwa ina kallon shi daga abin arziki kawai sai hattara irin haka sai dai a fili fadi nayi Allah baka hakkuri na ga bakaci abincin bane.
Sai ya zubo min wani irin kallo na fushi yace a hasale ke don Allah ki wuce dakin ki, ki bani wuri kaganin ki ma kara tada min da hankali yake yi.
Zanyi magana yace waike wata irin yarinya ne mara hankali sai ya dakatar dani da hannun shi na dama cikin wani irin murya mai cike da tsawa yace nace ki wuce ki bani wuri in ba haka ba zan yi maganin ki yanzu nan.
Na juya zuwa ciki hawaye na zuba min na fada saman gado na ina bakin ciki da dana sanin wanan zaman kaddaran da na samu kaina a cikin sa zama da mashayi mara tarbiya.
Zuwa can naji ya fita yabar gidan na sauke a jiyan zuciya a hankali na mike na fito do in yi sallah.
Bai shigo gidan ba sai wajajen karfe goma lokacin har na kwanta sai dai ban yi barci ba ko da alama yau baya a cikin maye do banji yana haukan nashi ba.
Ban fito ba shi ma bai nemay ni ba don haka sai da gari ya waye na fito a falo naga ledan daya shigo na kayan break fast da su sabulu da omo da maclean da sauran su.
Ban taba nadai kaqar na fara gyaran gidan ina tsaka da gyaran falon gidan ya fito da jallabiya a jikin shi.
Tsaida abin da nakeyi nay na gaida shi da ina kwana yaya ?
Sai ya jefe ni da kallon nan da na tsana bai ce uffan ba ya dauke kan shi gefe guda.
Dukawa nayi naci gaba da aiki na sai da na gama naje na duba abinci na samu ya dahu na zuzuba a cikin plate nadawo na sama shi falon nace.
Ga abin karyawa nan na gama a saman table bani bukata ya bani amsa dashi a fusace .
Da mamaki nake kallon shi idona ya ciko da hawaye nadake nace don Allah yaya idan laifi nai maka laifine ka fada min abin da nayi sai in gyara don gaba.
Wai ke wata irin yarinyace idan gidan kike son na bar maki zan iya bar maki kin isheni nida gidana kin hana ni shakat wallahi.
Wanan ai takurawa rayuwa ne an daukoki kin zo kin zauna wa mutum a gida kin hanani shakat dani da gidana .
Da mamaki nake kallon shi nace nima bayin kaina bane zama a gidan ka umurnin iyayyene nake bi hakana.
Ya fadi a fusace da cewa very good dama zaman umurnin naki iyayyen kike bi , ni sai kiyi kokarin hadani da nawa yan uwan da iyayye ko ?.
Da sauri na kalle shi ina cewa ai iyayyen ka da yan uwanka duk nawa ne hannu ya daga min yana cewa ba yan uwanki bane kan, don da basu zo gidan nan kin yi masu wullakanci ba sun koma rai bace.
Na soma kallon shi baki bude ina fadi cikin mama ki da cewa ni har yaushe wani dan uwa na zai shigo na wullakan tashi ina nima su nake gani a matsayin nawa yan uwan a nan garin.
Kai ya girgiza min yana cewa ba gaskiya bane hakan don da basu gidan nan kin masu taron wullakanci ba.
Kin raina masu wayau ko bari su zauna bakiyi ba kike cewa wai bana gida kina kokarin rufe kofa su fita kullun suka shigo abinda kike masu ke nan.
Da sauri nake kallon shi cikin mamaki baki bude nace har yaushe suka shigo gidan nan in ba jiya ba kuma nan suke zaune suna tanbayan ka nace baka nan ruwan ma da na kawo masu basu sha ba nan suka tafi suka barni dashi basu ko sha ba.
Yace kenan dai sun zo din ko tabbacin cewa sun shigo kenan gidan kin masu wullakancin ko ?
Gabana yai mugun faduwa sosai ni?
Dama sherin da sukai min kenan to wallahi wallahi ban masu wullakanci ba a gidan nan yan uwana ne fa su dan may zanyi masu haka.
Wani harara ya watso min yace da yan uwanki ne aida baki wullakan ta su ba harkina fadin magana a kaina , nace ba haka bane ya daga min hannu yana fadin ya isa haka maganan ya isheni ji ki sani kuma ba zan dauki raini ga yan uwa na ba a gidan nan.
Ya juya ya shige dakin shi can ya fito ya dauki key din motar shi ya fice a hasale yabarni tsaye in da nike.
Kwana uku cur muka dauka bai damuwa da harkana a gidan haka muke zaune dashi ba dadi ta ko ina saukin abin yana barmin abinci inci wanda raina yake so.
Sai dai na fahinci akwai matsala a tsakanina da yan uwan shi ke nan amma na rasa gane ta ina wanan matsala ya ke tsakani da su.
Haka muke zama har na tsawon kwanaki ranan ko may ya gani oho sai naga ya fito yana bude kulan abincin da nayi da safe don yanzu yakai nabar gaidashi don ko na gaida shi baya karbawa tun ranan da na gaishe shi yace dani
Ke wata irin yariya ce wai mara zuciya gaisuwan na dole ne ko an baki ajiyana ne wai tun wanan ranan ban kara gigin gaida shi ba a gidan kowa harkan gaban shi yake yi.
Bayan ya gama ina saurare fita shi sai naji shiru alaman bai fita ba ke nan agidan.
Wuraren shadayan rana na fito a zotona yana dakin shi ne ashe yana falo kwance ban sani ba.
Gashi ba daman in koma yace dani munafuka sai na daure na wuce shi zuwa kitchen.
Dole hakana nake aiki duk na daburce na gama abin da nakeyi a kitchen nafito na nufi hanyan daki sai naji yace dani zo nan.
Gabana ya yanke ya fadi a sanyaye na iso gabanshi nace gani sai dai ban yarda na kalle shi ba shima din ta gefen ido yake kallona.
Yace dani ke baki iya gaisuwa bane ko may ?
Na nisa tare da cewa gaisuwan nawa ne naga baka so shiyasa tun da ba ajiyan ka aka bani ba.
Sai naga yayi tsam ya mike yayi amfani da hanayen shi biyu ya rike min hannu da karfin tsiya saida na sake kara.
Sai da yaga na jirkita don kan shi yadan sasauta rikon dayai min din yana kallon fuskana dake fitar da hawayen wahala.
Jinayi gaba daya jikina ya hau rawa don kusantan juna da mukayi a lokacin.
Hakanan gabana banda bugawa ba abin da yakeyi ba bata lokaci ya shiga kokarin manna bakin shi a nawa, nayi kokarin kwacewa shi kuma yai amfani da karfin shi ya hanani kwacewa .
Abin da ya kama daga bakina zuwa wuyana babu inda bai mana bakin shi ba da kiss ban yarda mun kalli juna ba sai ruwa hawaye dake zuba min nace cikin karfin hali don Allah yaya kayi hakkuri ka kyale ni.
Kamar hadiyeni zaiyi yace ina bakin naki mai fadar bakar magana ya shiga zan kyale ki amma ki sani duk kika kara min rashin kuya a gidan nan nasan maganin ki.
Don kawai ya kyale ni warin taba ya isheni tankar zan yi amai nake ji na amsa mashi da uhm mhm.
Ya sake ni da karfi har ina gauruwa da kushin da sauri na shige daki na na barshi wurin tsaye.
Jikina na rawa na fada daki ban daki na nufa naje kamar zanyi mai ina ta jakarjn amai bai fito ba na wanke bakina nafito duk jikina ya mutu..
Ban fito ba sai da naji yabar gidan na fito ina kallon wurin da yasha taba duk ga guntun taba a yashe a kasa.
Tsaki nayi na dauko perker na kwashe tare da gyara falon ina jan tsuki hawayen ta kaici na zuba min ko nace zan ja Allah ya isa gawa zan ja shi.
Ga mahaifina daya sani dole ko ga gwagona ta jawo min haka gashi har yau ban saka ta a idona ba.
Ban may su sadiya suka ce ainihin nai masu ba a gidan wanda har ya hasala ta da diyan ta gaba ki daya sun dauke kafan su da zuwa wurina.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92Next page

Leave a Reply

Back to top button