BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/18/20, 10:16 PM – Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , , ,

????????5️⃣9️⃣????????

NOVEL DIN NAN NA KUDI NE IDAN KIN FITAR UBANGIJI YABI MIN HAKKINA A KAN KI/KA DON BAN YAFE BA, , , ,

Kamar yadda yaya Saadu ya fada haka ne ya faru don yayo kaura daga kalaba zuwa abuja da iyalin shi inda suka zo da yar uwan Samira da mijinta ya rasu zata dan kwana biyu a wurin su.
Sai bayan kwana biyu suka zo gidan mu don bamu da wani nisa sosai dasu dasu ban san da zuwan su ranan ba sai ganin su nayi kawai a gidan.
Sun shigo ina daki Zarah ce tazo tana fada min zuwan su cewa tayi nayi baki suna falo azatona ko anty uwace suka sake dawowa gidan.
Amma kuma sai nayi tunanen mai zai kawo su kuma in ba rashin zuciya ba yadda aka kwasa dasu din nan ya nuna shi sam bai san su ba.
Wanda kuma nasan yayi hakane don ya kakabe su daga gidan namu gaba daya da zuwa don zuwan nasu babu alheri a cikin sa.
Fitowa nayi sai mukayi arba da sister kamar yadda suke kiran safiya karama dashi.
Nace Lah bakin kalaba ne a gidan namu baku tsaya munzo taron ku ba har kun tula min nauyi na aka ?
Samira tace a, a mun huttar dake aikin san ke amarya ce ba a matsamaki yanzu na samu wuri na zauna ina mikawa sister hannu tazo wuri na sai yarinyar ta make hannun ta bata zuwa.
Gaisawa mukayi ina tambayan su mutanen gida da sauran yan uwanta tare da fadin ai na dauka zaku zo min da mummy ne wallahi.
Tace mun so mu zo da ita kodan azumi dake tafe takine sai da gabaya zata biyo mu in dan ta shirya.
Nace kai mummy ho har wanu shiri zata yi kuma makin ta biyo ku kawai kuzo tare samira ne tace wai Safiya kin ko ga yadda kika canza gaba daya.
Nace kai samira dashi kuma zaki tare ni tace wallahi safiya kin canza gaba daya komai naki ya canza kamar ba Safiyan yaya saadu ba.
Dariya muka ka kwashe dashi gaba dayan mu falon nace aikin Uncle tace aina gani wallahi gaskiya aure ya karbe ki sosai wallahi.
Nayi murmushi dadi har cikin rai na nace bakomai bane Samira sai kwanciyan hankalin da na samu yanzu.
Nura na kira sabuwar mai aikina yar kabilar yarbawa ce ita ta shigo nake cewa ta kawo ma bakina abin sha ta kuma hada abinci dasu don da mu zasu wuni.
Samira ne ta dakatar da ita da cewa wallahi a koshe muke don bamu dade da karyawa ba muka fito gidan.
Gaba daya Samira sai yabawa da yadda aure ya sake ni take yi nan take fada min ai jiya yayan ki yayi waya gida ashe ita yar uwar ki ta haihu ne kuma mijin yaki aurar ta ?
Nace wallahi ai yanzu takai wata biyu da haihuwa kyale dan iska so yake sai anbiyu mai ta bayan gida akan zancen zaimai da hankali ayi.
Tace ai naji yayan ki na fadin karshen mako zai tafi abinda ya hana Sani zuwa kenan cikin satin nan yace ya jirashi sai ya zo.
Nace kai mutane sai sannu baison ta yayi mata ciki dan iska kawai tace ai haka yayan ku ya fada shima yace dole ya aure ta don bai baro garin nan sai an daura auren su.
Nace haka yagi wallahi don idan anyi mai sakwa sakwa tsarewa zai yi ya barta da yaron tana wallaha ita kadai.
Tace ga uwar su wata kala ita kuma naji sani ya bugo ma yayan ku waya yana fada mashi rashin mutuncin da tayi ma mama ranan.
Nace kai inna ai sai a hankali ta tare da fadin akan makkan da su baba zasu tafi ne wai mama na maula gashi an biya wa mahaifiyar ki anbarta nan.
Wanan matar ai halin ta sai ita Samira ni ban taba ganin mace irin ta ba wallahi diyan ta tun suna bayan ta har sun gaji sun gane ta yanzu.
Tace wai itama ko yadda minjin nan naki ya rike Sani bata ko jin kunya ta rage wani abin amma sam bata san wanan nace wa inna aima yanzu ta rage wani abu don baba ya fita bayan ta yanzu.
Nan dai muke ta hira har muka shiga hiran gidan su yaya Saadu take fada min kwanaki sun tafi gaida gwago sun samu jikin yaya Ahmed yayi mai tsanani yana kwance yana jiya a gida.
Allah ya bashi lafiya nace da ita don dan uwana ne ko banja Allah ya isa ba Allah zai isar min da cin amanan zumuci da suka.
Murmushi nayi ina tambayan wai su habiba fa ko sun yi aure ne yanzu tace ke dai bari sadiya ce kadai a gida wai ita habiban ta tare gidan wani saurayin ta.
Sadiyan ce ta bugo waya kwanaki tana fada ma yayan yace zai zo har muka taho kuma bai je ba ko ta dawo gida ban sani ba.
Sadiya din ai da tace wai zata biyo mu ta dawo nan shine yaki yarda yace ta zauna ta kula da uwa don yanzu ba wani karfi ne gare ta ba.
Nifa Safiya ba wani shiri nake yi da mutanen nan ba tun zuwan da nayi na farko uwar da habiba ke cewa wai ya auro masu kwatakwalin ghana.
Na lah kece wai kwatakwalin ghana tace wallahi ko ai nace masu ni uwana da ubana yan katsina ne aiki dai ya kaimu kalaba baba kuma yayi ritaya bai koma gida damu ba amma har yanzu muna zuwa garin mu.
Dariya nayi kawai ina tunanen rayuwan da ya wuce baya irin cin fuskan da gwago da habiba suke min sai sadiya ce mai kula ni a garin da ban san kowa ba.
Su kuma sauran mazan biyu yanzu duk sun kama gaban su kowa ya watse dama haihuwan bariki ke nan.
Mun dade muna hira sai da muka mike zuwa sallah muka dawo muka zauna cin abinci tare muka gyara gidan dasu kafin su wuce sai yamma yaya Saadu yazo ya kwashe su.
Kafin su tafi mun dan tsaya da yaya saadu munyi magana akan matsalar saadatu dashi in da nace kafin ya wuce gida ya biyo ta wurin tukun.
Mukai sallama suka tafi lokacin shima mai gidan ya dawo wurin aiki ya samay su a gidan mintsila naji yakai min gefe na na dafe wurin da sauri ina kallon shi.
Yace yau don kin ga yan uwanki shine ko hugging ban dan samu ba nace afuwan yallabai kasan dan uwa aikwai dadi wallahi.
Ya riko min hannu muka shiga ciki yana fadin tafiyan mu fa yana matsowa don haka nake son muje ai maki pasphot din ki.
Naji dadi nace uncle ashe da gaske kakeyi batun tafiyan dani zaka tafi kai ya gyada min tare da fadin kin dauka wasa nake yi baza mu dawo ba sai mun tsaya umura daga don watan azumi da zai kama.
Don ni ban azumi a kasan nan a can saudiya nake azumina don haka nake son mu samu lokaci muyi list din mutanen da za a taimakawa.
Nisawa nayi alokacin da muka iso wurin kujerun falon tare da zaunawa sama har lokacin bai sake min hannu ba.
Nace uncle, , in uncle dama akan maganan su Aisha ne har yanzu naji shiru akan zancen shine nake maka tuni na fada tare da dukar da kaina kasa.
Tallabo habana yayi yana fadin ban manta ba ai akwai abinda nake shiryawa a kan su su ukun duka har ma da sauran yan nasu.
Sai dai da farko tunda kin matsa sai ku shiga da ita Niima house decoretion ku zabi abinda ya dace da ita sai a gyara mata part din nata ni inda mijin zai yarda sai in bata gidan da zata zauna da ga ita sai yaranta kawai.
Dadin maganan shi naji kamar yan uwa na za aiwa hakan sai nakai mashi runguma tare da bashi kiss gefen fuskan shi.
Murmushi ya sauke yace ashe kin iya nokewa kawai kikeyi yanzu da nayi maganan masoyiyar ki aikin bani ba tare da na nema ba.
Nan dai muka zauna har lokacin sallah yayi muka mike zuwa sallah ina maijin dadi sosai a raina bayan na idar da sallah ne na jawo wayana dake jone a caji ina kiran Aisha din.
Ta dauka tana fadin matar yaya dazun fa nake maganan ki a raina nace na zama yar halas ke na kin ki ambato tayi dariya kawai.
Nace kin samay tace a a matar yaya sai kin fada nan dai na kora mata albishir din dayayi mata akan gyaran wurin ta da kuma zancen mijin ta ko zai yarda a bata wurin zama ta zauna daga ita sai yaran ta kawai.
Tace cikin sauke ajiyan zuciya wallahi da yaya yaimin haka da ya kyauta min wallahi ni ko bai yarda ba komawa zan yi idan ya bani wurin zama.
Nace ki dai lalabashi ko zai yarda da hakan tace wallahi ba wanda yasan halin da nake ciki a gidan nan ne da yaya ba zai fadi haka.
Daga maigidan har abokiyar zaman nawa hakkuri kawai nakeyi a zaman mu don dai kada in koma gida ne aimun dariya da kuma yara da suke samun karatu a nan.
Nan dai mukayi ta hira tana fada min irin kuntatawan da suke fuskanta ita da yaran ta a gidan wurin kishiyar ta da mijin ta.
Shigowan shi dakin nawa ne ya katse muna hiran mu sai da ya zauna bayan mun gama wayan naji yana tambayana ke da wakuke wayane haka tun dazun.
Nace anty Aishan kace yace ok nan dai nake fada mai halin da take fuskanta a gidan har na gama baiyi magana ba dama kuma ni ban tsanmaci yayi din ba yana dai iya bani lokaci wurin saurare na.
Da safe Aisha tayi sakkon samun shi gida kafin ya fita nan dai na basu wuri suka kebe da dan uwan nata karshe dai da ya fita na shigo na samu tana share hawaye.
Ruwa na koma na dauko mata na kawo mata ina fadin tasha ko zataji sanyi take ce ai bata ko karya ba ta fito Nura na kira nace ta hada masu breakfast a daning.
Sai da taci ta koshi har yaran nace Anty Aisha kiyi hakkuri don Allah komai na duniya mai wucewa ne ga bawa.
Tace matan yaya ban san abinda yasa yaya ya kasa fahinta na ba har yanzu maganan shi guda koda yaushe akan miji nima inda nasan haka tun farko aida ban aure shi ba.
Hakkuri nake ta ba ta tare da fadin ki shirya driver zai dawo ya kaimu mu duba kayan yanzu na juya wurin yaranta ina tambayar su ko sun koshi.
Kada kai sukayi alaman sun koshi din nace to ku tashi kutafi wurin anty Zarah tana dakin ta kuyi mata fira sai lokacin take cewa zarah na gidan nan ne ?
Nace tana nan dakin ta bata fito bane sai bayan fitan yaran ne na samu magana da ita inda mukayi magana na fahinta nake kara bata hakkuri tabar bari yaran suna jin damuwan ta da mijin nata ko yaushe.
A karshe dai driver yazo na muka fita gidan bayan na rufe ko ina na gidan Nura kawai muka bari a gidan tana aikinta.
Mun tafi wurin mun kuma duba suna da kaya sosai a wurin mun zabi mai kyau cikin mafi tsada da daraja har labulen da za a saka mun zaba bayan mun gama muka kirashi mukai mai bayani.
Yace mu bashi shugaban wurin suyi magana dashi nan na bashi matar sukai magana ta fada mai kudin kayan sun tasan ma milayan daya da dari biyar yace ta bashi account din su.
Mun dawo gida a gajiye don dan zakayawan da mukayi a wurin akarshe falo muka zube duk mun kwaso gaji a tare damu sai Nura ce ta kawo muna ruwa da abinsha muka dan sha ga abinci ta gama mukaci muka tafi sallah.
Aisha ganin abin takeyi kamar a mafalki sai maganan takeyi duk zaman da mukayi daki na bude mata don ta shiga da yaranta su huta a ciki inda nima na wuce nawa dakin don yin sallah.
Bayan na idar da sallah na zauna ina tunanen ratuwan Uncle da yan uwanshi na rasa gane may ye matsalan shi da su haka.
Gashi ni yana iya yiwa yan uwa na dama wasu lalura ba tare da jin kyashin komai ba a ranshi amma nasa kafin yayi sai ya ja masu rai zaiyi.
Koma may watarana tunda ina cikin su zan ji ko may ye matsala da inda abin nasu ya samo asalin faruwa.
Ita ko Aisha tana shiga dakin dana bude masu wanda yake gyare komai akwai a cikin sa gashi kuma kullun a gyare yake duk da ba kowa a dakunan.
Wayan ta tadauko a cikin jakkan ta ida ta kira mahaifiyar ta bayan sun gaisa take cewa hajiya maganan ki ya fara tabbata gaskiya.
Yau yaya yasa mun fita da matar shi muje in zabi kayan dakin da nake so a wani shago nan dai take fada mata duk yadda akayi a wurin da kuma fadan da yayi mata kafin ya fita.
Murmushi mahaifiyar tayi tace kamar yadda nake fada maku wanan yarinyar zata zamay muna alheri a cikin mu sannu a hankali zamu samu ta canza muna shi amma fa sai kin bita a sannu komai zai daidaita.
A hankali tace kwarai hajiya aina ga alaman hakan tun yanzu gashi yaya har da zuwa gida na yayi ta dalilin ta nan dai take fada mata son canza mata wurin zaman da yake son yi ma,ana ya raba masu gida da kishiyar ta.
Wanan maganan mahaifiyar taji dadin din shi sosai inda tace Allah yasa Aisha su kuma Allah ya saka masu da alherin sa.
Ki barshi da mijin naki ai kar tasan kar shi da shi, shi yasan ta inda zai fito mashi da maganan a tsakanin su har ya yarda da maganan a saukake.
Bayan la,asar muka fito nan falo muka zauna muna hira sai gashi ya dawo gidan yaranta dake waje suna wasa ya shigo dasu rike a hannun shi.
Sannu da zuwa mukeyi mashi amma hankalinshi na ga hiran da yaran suke yi mashi sai dai da kai yake iya amsa muna gaisuwan da muke yi mashi.
Ina zaune rakube ina kallon yadda yakewa yaran tausayi ya bani don nasan yadda yake tsananin son haihuwa a wanan lokacin.
Ido na zuba masu sosai daga inda nake zaune tashin hankali na da uncle yanzu shine haihu wata shidda kenan cur a gidan shi ba bu wani labari ciki a gare ni shiko yanzu ba abinda zai farauta mashi rai kamar ya ganni da ciki.
Nace oh safiya wai haihuwa bai zuwa a inda ake neman sa ne ga gidan Ahmed da bai son haihuwan a can Allah ya bani gashi a gidan uncle wanda yasan daraja da kimar haihuwa shiru kake ji.
Jin yana magana dani yasani dawowa cikin hayaci inda yake fadin may yasa baku sayo wa boy abinda yake so kuka sayawa amira ?
Murmushi nayi tare da sauke ajiyan zuciya nace uncle rabuda boy din nan rikici yake ji dai shifa yace a saya masu wanan din da yake ma fushi tun dazu bayan an sayo kuma wai shi bai so a canza mai.
Ya rugumo yaron zuwa jikin shi yana fadin kyalesu zamu fita in sayo maka wanda kake so yanzu barin in ci abinci sai mu fita dakai bada su Amira ba.
Abinci na gabatar mashi da kaina ya zauna tare da yaran sukaci suna ta zuba mai surutu har suka gama suka fice gidan shida yaran.
Aisha ta kalle ni tace ashe yaya yana so yara haka wallahi ban taba sanin yana kula yara ba ke kuma gaki shiru har yanzu babu labari kodai kina planning ne safiya.
Ajiyan zuciya na sauke nace nawa na aje da zanyi planning anty wallahi nima nasan haihuwa yake so Allah dai ne bai kawo ba har yanzu.
Take cewa ki dinga shan miyan kuka tun da safe haka ma idan zaki kwanta barci in Allah ya nufa zaki iya samu da wuri ki haihu.
Nace aiki na gode kice in samo kuka ke nan in dinga sha don nasan idan hakkurin uncle ya kure zai kai ga yi min magana nima kuma ina son in ga na haihu wallahi na kare ina lumshe idanuwa na.
Sai dare ya dawo da yaran idan kafin ya dawo ya kira wayana in fada mata ta shirya gashi nan zuwa zai maida ta gida na fada mata tare da hada mata tsaraba ya iso bai ko shigo ba muka fita .
Inda muka samay shi da yaran a mota nan mukayi sallama suka wuce gidan Aishan dashi koda ya je gidan bai shiga sai cewa yayi ta sallamo mashi maigidan nata.
Tana shiga shiko ya hau ya zugo a wurin kishiyar ta tana sa kafa tana fadin gidan uban wa kuka tafi har dare haka uban wa zai dafa maki abincin dare a gidan.
Sai dai ku kwana da yunwa ke da yaranki don ba zan bata kudina wurin sayen wani abu don ku ci.
Shi mai kudin gidan naku da baida moriya kije ya baki abinda zakuci da diyan naki kishiryarta na zaune gefe da diyan ta suna shan cornflake tace ta aje jaka a gida mana to ban dafa ba in an dawo acine.
Wani kallo tayi masu tace kaje yana waje yana sallama da kai yace wa cikin zaro idanuwan shi tace yaya Sulaiman da sauri ya zura sillifas din shi a kafa ya fice a hanya ya hadu da yaron gidan yana shigo da manyan kwalayen da ya sayo masu tsaraba wanda dagani har Aishan bamu san ya saye ba.
Kishiyar kuma baki ya mutu ganin kwalayen da ake shigowa dasu gidan ana dire su kofan Aisha din wani irin kishi ne ya kamata a lokacin.
Ya fita sun gana dashi ban san yadda sukayi ba dai da mijin Aishan can ya dawo ciki bayan sun dauki lokaci da uncle a waje yana cewa boy yau uncle ya kaiku shopping ne haka ?
Yana ta faman washe baki namiji dama baida kunya nan yabar kishiryar zaune tana kallon mamaki shine har da yiwa yara wasa a lokacin.
Uncle bai dawo ba sai tara da rabi ya shigo da ledan kajin da ya sayo wanka ya shiga sai bayan ya fito wankan ya fito falo yana fadin in bude mai kajin su zai iyaci kawai yau.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92Next page

Leave a Reply

Back to top button