BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
9/13/20, 7:47 AM – Ummi Tandama: BAHAGGON RAYUWA, , , , , , ,

????????7️⃣9️⃣????

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU

Shigowan yaya sani ya katse muna maganan da muke akan khadija din don ko ba komai baza mu so yaji muna sukan dan uwan mahaifiyar shi ba a fili.
Ya shigo yana fadin yanzu maimu da hindu suka tare ni a hanya suna fadin wai dasu zaki tafi idan zaki koma ?
Nace a sanyaye haka nake so indan zan samu baba ya yarde min don gidan yana min girma ba kowa a kusa dani.
Yace ai ba wani matsala bane idan mijin ki zai yarda da hakan sai dai kin san wasu baza basu son haka sam a rayuwan su.
Nace shi ya bani shawaran hakan ma sai dai bai san da zancen maimu ba hindu dai mukayi magana a kanta da zan zo saboda ita khadija taki zama can.
Yace khadija kan ai tafi son nan tana gudun kada a kwace mata guy din ta sanusi sai dai kuma ni naga sanusi baida alkibila don da batan yar gidan hakimi ya koma nema.
But khadija ta fito daga daki tace yaya sani may kace yace au ashe kina ciki takara tambayan shi yace mata bai sani ba tace uhumm ummm ai naji abinda ka fada dama shafiu ya fara fada min yace kinji shine kike kara tambayana kuma.
Nace yaya sani kaga muyi maganan abinda yasa na kira ka don Allah bar wanan zancen nata na shirmay ko a gidan shi kike da ke kadai zaki zauna balle bakuyi aure ba yana saurayi zai zauna dake ke kadai.
Yaya sani ni kaga shawara na kiraka muyi don Allah yace to anty ina jin ki da sauri nace kai yaya sani nine kuma antyn naka kuma ?
Bakiji abinda na fada maki ranan ba ne Safiya yanzu ai kin zama antyn mu gidan nan don ko maishi a yanzu shine babba don shawaran komai shike kawowa kin ga ko dole ne mu girmamaki ai.
Ummi tace kai kaidai sani baka rabuwa da barkwanci wallahi yace ummi wallahi gaskiyan ke na ai anty ina jin ki.
Dariya ya bamu sosai gaba dayan mu dakin sai da muka dara mai nace dama shawara nakiraka muyi akan Saade da Ainau.
Yace bakaji magana na yafito ba ummi yanzu ni da ke nan ai ban taba shawara akan su ba ko yanzu ita gata tazo da shawara kuma nasan wanda zai amfane su ne.
Murmushi nayi wanan karon ban dara ba don abin na yaya sani ya wuce sani na yanzu ya juyo yana fadin ina jinki anty safiya ?
Nace yau naje dakunan su ziyara naga halin da kowacen su take ciki to ina dan son inyi wani abu akai ne a halin da suke ciki din na farko dai shin gyara masu daki zamuyi ko abin sana,a zamu ba ko wacen su ta kama sana,a kanta.
Yana fadin a a ummi ma tana fadin ummu ummm kudai yi shawara don ko kun basu kudi mazajen su zasu karbe kudin nan ne.
Yaya sani yace abinda zan fadi ke nan ummi kika rigani fadi yanzu wallahi nace to yanzu idan na saiya wa kowacen su freezer yayi da kayan kallo a daki don debe masu kewa da kira masu kasuwan sana, an su hakan zaiyi yaya ?
Kwarai kuwa ummi ta fada da sauri shiko yaya sani kai ya fara girgiza yana fadin Allahu akbar lalai safiya samun mai irin zuciyar ki yanzu sai antona wallahi.
Yanzu har kin manta da irin wullakancin da suka dinga maki a baya a gidan nan da sauri ummi ta tare shi da fadin ummm umm sani idan ana tuna baya ba, a zumunci yanzu.
Don Allah ku bar tuna wanan magana ya wuce sai dai zumunci tsakanin ta da yan uwanta irin haka ai Allah bai maja fada ka tsaya kuma ranawa.
Sai ga hawaye a idon yaya sani din ya fito har yana sharewa da bayan hannun shi nace haba yaya sani may ye haka kuma ashe ba godiya yakamata kayi wa Allah ba da ta buda muna ta hanyar dabu zata ba yanzu.
Wa ya dauka zan rayu har na kai wanan lokacin da Allah ya kawo mu har ya bani daman taimakawa yan uwana da iyayyena.
Yace wallahi ummi jiya ni kadai a daki sai da nayi ta kuka in na tuna irin abinda inna tayiwa safiya a gidan nan sai in kama jin kunyan kaina duk da bani nayi abin ba amma uwatace fa tayi dole inji kuyan kaina.
Yanzu badon zuwan safiya da ta bata kulawa ba ai mu nan duk ido muka sa mata a gidan don bamu da hankalin fahintar haka gare ta.
Ummi tace sani abar tuna baya don Allah don tuna bayan baida amfani sai yasa mutum ya sare yaji bai iya aikata wa dan uwanshi alheri.
Nan dai muka tsayar da magana nace gobe sai ku shiga birni kaida su malam musa ku sayo masu abinda ya dace a saya masu ko wace zan bada duba dari dari a kashe mata sauran canji a basu abinsu idan ya rage dama kudin da yake bani ne duk wata.
Ban yin komai dasu ba don idan nazo gida inyi amfani dasu yadda ya dace kaga su sunci nasu rabon ke nan yanzu.
Wani irin dadi ummi taji har cikin ranta nan ta shiga samin albarka yata sani na fadin amin ummi ya mike zuwa dakin inna wai zai dubata nasan kuma zancen zai kyankyasa mata taji.
Don har zuciyar shi yake magana don bazance ga wani rana da yaya sani ya taba kuntata min ko ummi na a gidan mu tun tasowa na ahaka yake damu kamar dan ummi da ta haifa.
Shiya mahaifiyar shi ke fadin wai ummi ce uwar dakin shi tabi boka tabi malam ta mallake mata da ta hana shi hurda da ita da yan uwanshi sai mu.
A can dakin inna nan yaya sani yasa ta gaba yana fadin inna kin gani kin ga kunyan da kika ja muna agidan kirikiri kin san kina cin zalun din wanan boyar Allah a lokacin.
Amma kika rufe ido kuka dinga cusguna mata a gidan nan ita da diyar ta da mama ta gane hakan ba daidai bane sai ta zamay jiki ta barki ke kadai kina masu cin fuska yadda kike so.
Yanzu gashi dama irin haka ne akarshe irin mutanen da akaci zalum din shi suna hadiyewa suna hakkuri suna shayewa Allah bai bari su tabe banza.
Yau gashi ina ciwon safiya baika yadda ke ake gudun ki ba a gidan wanda har diyan cikin ki suna gudun su shigo dakin nan wurin ki.
Wanda ita alokacin ba a gujeta ba haka kamar naki ni nasan duk wanan abin ishara ne kawai Allah ke nuna maki abinki da zaki roki yarinyar nan safiya tun wuri ta yafe maki da zaifi sauki wallahi inna ga wanan halin da kike ciki.
Da kyat inna ta iya dago kai ta kalleshi tana share hawayen dake fuskanta tace sani na dade yin wanan tunanen a raina nasan na zulunci yarinyar nan sosai a rayuwana.
Ba kowane sillar auren ta da yaron wurin gwagon kuba sai ni jin dani yaran basu da tarbiya, ni na je nabata gwogon ku shawara mai zai hana ta nemawa danta safiya tunda gashi ta kusa gama boko.
Nayi hakane don inga rayuwan safiya ya tarwatse ban tuna da cewa ba ayiwa Allah wayo ba sai yanzu na fahinci hakan.
Da farko har ina murna naga bayan su ita da uwar ta a gidan nan sai kuma gashi ubangiji ya kawo mata miji ta sanadin ciwon da ta dauko wurin dan uwar ku.
Sai yan, , , , , katse ta yayi inna mai sukai maki haka mai zafi har kika bisu da wanan mugun nufi haka a rayuwan su.
Kishi ne kawai sani kishi tun ranan da malam ya auro uwar safiya a gidan nan na dauki karar tsana na dora a kan Rabi ba don komai ba sai don ganin tafini kurciya da kyau .
Wanda zai sa malam ya dauke hankalin shi a gare mu da diyan mu gashi kuma ta dage ta saka diyan ta a makarantan boko wanda ku diyan mu talla yafi muhinmaci a wurin mu duk bakuyi karatu ba sai nata diya.
Kuka ne yaci karfin yaya sani yake fadi wallahi inna kin cuci kan ki kin cuce ba komai ki bibiyar mu ba sai alhakin wa yan nan bayin Allah dake kan ki.
Mikewa yayi yabar dakin cikin bacin rai ya fita daga gidan can ya koma waje ya samu wuri yana kuka har yagaji sai da abokin shi shamsu yazo ya bashi hakkuri ya samu yayi shiru.
Washe gari kamar yadda mukayi magana da yaya sani hakan ne ya kasance don yaya sani sun kama hanyar birni shida su malam musa da shamsu abokin shi suka tafi sayayya.
Sai laasar suka dawo gidan mun fito mun ga kayan ba a sauke su ba mukace a wuce masu dashi gidan su .
Sai tambaya su mutane ke yi kayan waye haka yaya sani din ke fadin nasu Ainau ne da Saadatu safiya ta bada kudi a sawo masu a birni.
Murna ya cika yan gidan mu sai shewa suke da murna nan yaya sani suka wuce da kayan zuwa gidajen su saadatu din.
Ranan ba a kwana ba saida su suka zo gidan Ainau da sarakuwar ta ita kuma saadatu da kishiryata da suke shiri suka zo godiya.
Kullun ina waye da uncle sai dare yake kirana ko da safe haka yasa na samu daman fita wurin yan uwa duk inda nake so yau zan shiga birni wurin Amina ida can zan kwana wurin ta.
Da khadija zamu tafi don tana son zuwa sayen abu acan sai sha biyu muka bar gida inda muka kama hanya da su malam musa driver da yaya sani zamu tafi.
Mun isa lafiya sun sauke mu suka shiga gari wai zasu diba masauki inda zasu sauka mun shiga wanda yake orin ginan quaters din nan ne mai daki biyu da falo sai ban daki da kitchen.
Muna zaue a falon ta ida take ina aka saka damu a gidan tasan da zuwan mu don mummy ta bugo mata tun ranan dana je wurinta nace ranan monday zan tafi wurin Amina din.
Zzaune muke ta cika muna gaba da abinci sai hira mukeyi da ita ga jaririn da ta haifa nan bayan haihuwana har ya dan yi wayo shima.
Bayan mun yi sallah mun huta khadija ta fita zuwa kasuwa sayo abinda ta shigo saye ni kuma Amina ta jani zuwa gidan kawayen ta tana nuna masu ni.
Yaya sani ne yakirani a waya wai gasu sun dawo yasa muka bar gidan kawarta na uku da muka shiga muka dawo gida.
Nan ta basu abinci sukaci muka dan taba hira dashi mijin ta ya dawo nan suka fita waje suka hade dasu malam musa sai hira.
Sai yamma khadija ta dawo da kaya niki niki data sayo tana cewa ai na fada maki anty garin ku yafi nan tsada wallahi.
Amina ce ta tare da fadin ke ko khadija ina zaki hada tsadan birni da na nan ai ba daya suke ba, zama tayi tana cewa garin nan akwai zafi Anty Amina mun fiku sanyi a gida.
Nace ba yanzu kika shigo ba ai dole kiji zafi Amina tace tadai saba zama a cikin AC can abuja amma ai kusan sanyin mu dayane da gida .
Magariba akayi muka tafi zuwa sallah tunda nayi sallah nake zaune a daki ban fito ba don naga mijin ta na gida a loikaci khadija na kwance saman gado tana sauraren waka a waya ta ni kuma ina kasa zaune saman sallaya da casbi a hannu na ina ja.
Amina ta shigo dakin ta zauna tana cewa Abba yayi barci ne ashe kallon inda yaron yake kwance tare da khadija nayi naga yana barci.
Tace ku fito muci abinci mana kun zauna a daki nace gani nayi kada mu takura ma maigidan ne yasa muka zauna a daki tace ai ya fita sai goma ko sha daya yake dawowa gida.
Kasa boye mamaki na nayi nace Amina sai sha daya yake dawowa fa kika ce tace watarana har yakan wuce sha daya wurin hira.
Addua na nayi tare daa aje tasbahan cikin handbag dina nace Amina ke kuma kika kyale shi a hakan kinaa kallon shi.
Kin san fa irin abinda ya ci ni ke nan a baya da yaya Ahmed ke irin wanan rayuwa bani da wayon da yancin da zan hana shi fitan dare har yazo ya zama min ja iba daga baya.
Don Allah kiyi kokari kisan yadda zaki hana mijin ki fitan dare duk wani hiran da zaiyi yayi shi agida tare dake da yaran ki.
Yawon namiji kada ya wuce takwas na dare zuwa tara indan yakai goma abin yakan baci ne sai dai idan da uzuri ki daga mai kafa akan haka.
Tace niko ban dauke shi komai ba wallahi nace Amina shine komai kuwa don nasan illan yin haka a baya kokari zakiyi cikin hikima da basiran ki irin tamu na mata zaki hanashi wanan yawon daren ba a cikin haukan kishi ba.
Amma ai duk wani magidanci na gari marancen farko ya kasance yana a cikin gidan sa sai dai idan wani uzuri ya fitar dashi waje.
Tace kin ga yanzu kaina ya kawo wuta wallahi don idan za a fita din sai anyi kwaliya an fesa tura da sauran su ake fitan.
Nace ba zugaki nake yi Amina amma ke da sauran mata yan uwa na yakama mu gyara ko da neman matan mijin ki keyi to ya zama may tsaba yake yi.
Da yawa mu mata muke bada gudunmawar haka ga mazajen mu don bamu tsayawa muyi masu abindaya dace mu jawo hankalin su gare mu.
Sai kiga mace da kayan da wuni dashi a jikin ta dashi kuma zata tari miji dashi daa dare ba wani kamshi a gidan kamar mai taron wanda yayi tafiya ya dawo.
Ko wani canza na,uin girki zuwa kalar da yake so a koyaushe ki canza nauin abincin ki ki gyara kanki da yaran ki gidan ki ya kasance a gyara har shimfidan ki zuwa bandaki da tsakar gida da sauran su.
Ajiyan zuciya ta sauke tace wallahi ni wanan duk bai damay ni ba, a dade da nake wanan shirin na gyara gida inyi komai da kika fadi yanzu.
Amma yanzu tunda na fara aje yara na tatara nabar komai wahalaan aiki dana yara sun isheni a gida safiya ga zuwa wurin aiki kuma.
Amina nace cikin wani irin murya yasa ta natsu ta daina maganan da takeyi tace safiya .
Nace don Allah ki mai da hankali ga mijin ki yanzu ba ai ma maza hakan ke da kan ki kike shirin rusa gidan ki tayaya bazaki ja mijin ki a jiki ba.
Har zaki ba wasu matan waje kafan ashe maki miji daga hannun ki wallahi ki mayar da hankalin ki kishiga karatun na natsu ga maza.
Mazan yanzu ma kayi masu ba tsira kake yi ba balle kaba su lasisin fita bariki suyi don Allah mu mayar da hankali mata shike sa matan waje suke shigo su raina ta gida don yin sakaci tundaga farko musanman mace da take ita kadai bata da kishi idan kinayi sai kikara akan wanda kike yi din.
Kamar yadda tace hakan ne kuwa sai sha daya da rabi naji dawowan mijin nata lokacin munyi sallama da ita ina kwance barci bai dauke ni ba.
Godiya nayiwa Allah da ya fitar dani cikin wanan rayuwa ina tuna lokacin da nake gidan Ahmed da yake dawowa cikin dare a buge ko da karuwa .
Sai dai dayake nan arewa ne fitsaran su baikai na mazau na kudu ba da basu da nauyin kowa a ransu abinda suka ga dama sukeyi sai wanda ke da tsoron Allah a zuciyar shine Allah ke tsarewa.
Amma nan arewa a cikin tako suke alamarin na yadda kafin a gane halin na miji sai ta dade yana cutar da mutane wani kuma ba yadda za a gane halin sa sai Allah.
Da ire iren wanan tunanen barci ya dauke ni bamu falka ba sai asuba don abba tunda ya tashi kafin mu kwanta na bashi madara yasha ya koma barci bai kara falkawa da dare sai dana tashi zan yi alwala don yanzu ya fara wayau ya tashi yana ta kuka.
Saida khadija ta kamashi ta goya ta hada mai madara yasha ya koma barci ina zaune take cewa yanzu fa ya fara gane ki anty.
Don daga tadhin ki yasa kuka wai don may kika tashi nace bari zaiyi ai idan mun koma don dan tafiyan da mukayi bauchine gashi kuma bamu zauna ba mun taho nan.
Hmmm aini idan na tuna badakal ku da uncle a bauchi abin dariya yake bani nace in dai uncle ne ai kadan ma kika gani don ban biye mashi ne kawai.
Yanzu baki ga dana nuna mashi ban damu ba dayace ban zuwa gida ban san abinda ya gani ba kuma yazo ya barni inzo da yaso ne fa da na zo mu koma tare dashi.
Tace hakan yana yuyuwa kuwa anty dz fa duk wanan ziyarar bakiyi shi kai koma a garin ba inda zaki ai.
Uncle ai halin shi sai shi wallahi wanda bai san halin shi ba sai yayi ta wahala da daki nakan shiga inta kuka daban gane haka yake ba.
Amma anty maganan da kika fada ma anty Amina daren jiya naga jikin ta yayi sanyi nace tayi sake ne tun farko ta saba mashi da hakan da tun farko ta koya mashi zama gida ba zai yi hajan ba koda zaiyi ba hakan da yawa ba dai.
Mazan mu na hausawa na da saukin kai idan mace ta san yadda zata bi dasu sai dai abinda basu so mace ta nuna masu kamar tana commading din su sai suce ka raina su.
Tun da mukayi sallah muke hira duniya dani da khadija anan na samu daman yi mata magana akan ta rabu da Sanusi dan uwar inna.
Na nuna mata illar abinda take shirin yi din dayin hakan nasan dai magana na batai wani tasiri a zuciyar ta ba sai dai a sanu zata gane abinda muke nufi gare ta.
Nayi mamakin ganin sai da rana ta take Amina ta tashi ida na fahinci ba wani dogon addini suke yi ba da ita da mijin nata don ta fito tana fadin wai sun makara ne.
Nace Amina ya kamata fa yanzu ki daina wasu abubuwa domin ke din uwace a yanzu kina kwaciya barci har asuba ta wuce bakuyi sallah ba ta yaya kike ganin zaki koya ma diyan ki ibada da hakan.
Shifa yaro anbinda kake yi yake koyi dashi mai kyau ko mara kyau don shi gani yake komai daidai kake yi.
Tace wai ni Safiya wanan mijin naki halan ustzune naga duk halaiyar ki sun kara canzawa yanzu ba a yanda na sanki ba duk da dama can babu ruwan ki baki kaimu rawan kai ba.
Dariya nayi kawai mun karya ban wani jin dadin zama a gidan ba don haka kamar yadda muka bar gida sha biyu haka muka baro gidan Amina zuwa gida bayan na masu alheri muka dawo gida.
Saboda gaba daya naga Aminan ta canza tabar halaiyan ta dana san ta dashi a baya sai wani nuna waye taki wanda bai dace da diyan musulmai ba da matan hausawa.
Abinda nake son mata su gane shine bawai sai mun nuna wayewa a fili za a san mun waye ba dabiun ki na diyar bahaushe musulma a ko ina ya rinjayi zuciyar ki.
Ako ina kika samu kan ki kada kiga kina zaman bariki ki watsar da tarbiyan da kika samu ki manta da rayuwan ki a yanzu yafi muhinmanci ga Allah.
Ki dinga fita yadda kika ga dama batare da kin rufe jikin ki ba wai ke zaman bariki kina daukan hakan a wayewa gare ki.
Kamata yayi yar musulma bahausa ta nuna a ko ina ta mai cikaken tarbiyane a duk inda ta riski rayuwan ta wanan rayuwan duniyan ba komai bane a gare mu.
Wataran kana gani anayi ba dakai ba lokacin ka makara ga gyaran dabi,un ka don yara sun taso sun dauki rayuwan da suka samu kanayi suna kanana.
Badon kan mu zamu daina wasu abubuwan ba sai don tunanen makomar yayan mu na yanzu da wanan tunanen na canzawan Amina a raina har muka iso gida a lokacin.
KUYI HAKKURI DA MAGANA NA YAN UWA MUNA CIKIN WANI HALI NA SAKACI DA ADDININ MU YANZU DON MUNA GANIN KAMAR WAYEWA NE.
MUN MANTA YAYAN MU NA TASOWA SUNA KOYI DA DABIUN MU MU CUSA ADDINI GA ZUKATAN YAYAN MU YAN UWA.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92Next page

Leave a Reply

Back to top button