BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
9/15/20, 7:06 AM – Ummi Tandama: BAHAGGON RAYUWA, , , , , , , ,

????????8️⃣1️⃣????

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU

Bayan tafiyan su samira da basu dade ba na shige daki nayi laasar na fito muka fara gyara kaya da Nura su maimu suna taya mu.
Kafin wani lokaci muyi ma komai muhalin shi mu aje a inda ya dace kuma na nuna masu wanda zasu ci inda suna bukatan ci din.
Falo na dawo inda kanne na suke suna kallon na zauna sai dai ni ba kallon nake yiba waya nake amsawa daga mutanen gidan mu suna tambaya na mun sauka lafiya .
Abincin dare suka ci ina zaune a kasa idan na sallamay sallah ishai wayana yayi kara uncle ne ya kirana a lokacin na dauka da sallama tare da karawa a kunne na.
Uncle ina wuni na fara fadi ya sauke a jiyan zuciya kadan yace madam kun dawo ko kuna can har yanzu nace uncle gani daki na muna ta kewan ka, gidan ya koma ba dadi da baka nan.
Murmushi yayi tare da fadin I miss you to my wife ina Abba dasu mummy nace ga Abban nan hannun maimu mummy kuma bata dawo ba.
Maimu ya maimaita sunan da na fada nace eh tare da su nazo ita da hindatu sin zo muna hutun kwana biyu ne .
Yace bana ce ki samu yarinya kizo da ita ba idan zaki dawo don ki samu abokiyar hira a gida nace ko yanzu ga su suna debe min kewa a gidan.
Bai kara yin magana sai cewan da yayi kara ma Abba waya inji muryan shi sai na manna ma yaron waya a kunnen shi nan ya fara yin gwalanci kamar ya san abinda ake nufi mika ma maimu wayan nayi tace ina wuni yaya yace a a ke yar kauye ashe kun shigo gari sai yarinyar tace eh.
Amshe wayan nayi ina fadin kin yarda ke nan ke yar kauye ce ko na kara ma hindatu tace cikin muryan ta mai sanyi ina wuni yaya ya amsa mata tare da tambayan da wa nake magana tace hindu ce.
Sun jima yana masu tambayoyi wani su bashi amsa daidai wani kuma su fada mashi ba daidai ba
Mukai sallama dashi yana fada min kada in rufe gida yanzu zaa kawo min sako in kar ba godiya nayi mai tare da tambayan shi yaushe zai dawo ?
Yace kin damu in dawo ne ko wani abin kike so madam nace babu komai sai dai kewan ka da mukeyi na rashinka a kusa damu.
Kararawa kofa yayi kara ni da kaina na tashi na bude gidan malam musa driver ne da ledoji da kwalaye ya shigo dasu ya koma ya dauko sauran sai leda daya miko min hannu da hannu na karba .
Bayan na karba na fahinci maye a cikin ledan don jin zafi danayi daga cikin ledan yana tashi da kamshi.
Yayi muna sallama nace ya tsaya ina zuwa yace a a hajiya nima maigida ya saya min nawa na gode wallahi sai da safen ku yana dan dukar da kai kasa alaman girmamawa gare ni .
Yana fita na koma wurin kayan daya shigo dasu ina duba inda naga kayan tea ne mayan gwangoni madara biyu sai na milo da nescafe da ovoltin sai katon din sugar na kwali.
Dayan kuma fruit ne a ciki iri iri masu kyau fresh one murmushi nayi don akwai wanan abin daduk aka sayo muna a gidan.
Ledan da kamshi ke tashi a cikin sa wanda tun ban bude ba na fahinci may ye a cikin wanan ledan kaji ne gassasu guda uku kosassu sun gasu dakyau irin gasuwan resturant din nan da albasa da kabeji da sauran tarkace wanda yakan sawo muci a gidan.
Yaran dake satan kallo nace hindatu ta dauko plate a kitchen guda uku kowa ya dauki kazan daya yaci maimu tace anty duka nace eh duka maimu.
Ban koma ta kansu ba ina faman dakilan wayana suna ci suna dan magana kasa kasa danaji maganan yayi yawa na dago ina cewa dasu wai may kuke fadi ne kasa kasa.
Wai cewa tayi kada mu cinye duka mu rage gobe muci saura nace akan may zaku rage idan kuna iya ci duka kuci mana.
Basu iya cinyewa dukka ba duk zalaman su anan suka barshi nace suje su saka a fridge ban ci nawa sai fruit din naci kawai bamu dade ba nace suje su kwanta su huta.
Sai da na tabbatar sunyi barci na dauki Abba zuws dakina na kashe wutan falon komai daya kamata in kashe na kashe na shiga na kwanta asuba ta gari.
Da safe muna tashi bayan munyi sallah nace suje suyi wanka kuma kullun da sunyi sallah haka zasu dinga yi suka shige daki don yin wankan dana ce suyi.
Abba nayiwa wanka na shirya shi na dauke shi nakai masu dakin shi na dawo nayi nawa wankan na shirya.
Nura ta iso ta fara aikin hada muna breakfast din safe a lokacin na shiga kitchen din nace kada tayi wani mai yawa don ba a ci sosai.
Bayan mun karya ne muka zauna su kallo ya dauke masu hankali waya na na dauko na kira samira muka dan taba hira da ita nace idan ta samu lokaci ta shigo don Allah ina son tayiwa su maimu sayayya kayan sawa don ni ba dama in fita uncle bai gari.
Tace zata shigo zuwa rana asan abinyi din akai nan muka kashe wayan nima kallon na kama yi don shine aikina kawai tunda ba fita nakeyi ko wani abuba.
Sai idan uncle yana gari ne watarana nakan shiga in muna abincin garagajiya don yana so ita kuma Nura bata iya ba sosai.
Hajiya baaba na kira don mu gaisa tace na dawo ko ina gida har yanzu nace hajiya mun dawo jiya muna Abuja yanzu.
Tace yaya muka baro su nace suna lafiya suna gaida ku baaba tace to yanzun dai kinje gida hankali ya kwanta ko ?
Don Allah safiya ki bi mijiki a yadda yake so ku zauna lafiya don Allah yanzu tunda kin san halin shi kibishi a yadda yake ban son yawan fitin da kuke wayan yi ko yaushe din nan.
Insha Allahu baaba zanyi yadda kikace din tace nasan komai safiya nasan kina hakuri sosai dashi shima din halin shine kawai haka bawai yana yi cikin son ranshi bane.
Godiya nayi mata na kashe wayan ina tunanen maganan da mukayi da hajiya din shigowan samira gidan ya kawar min da tunanen da nakeyi.
Samira ta shigo na bata kudi nace taje dasu don kada a samu akasi tace bata zuwa da kauyawa ko ina nace watarana kina ganin su nan sai sun fiki wayewa.
Tana masu sheri suka fita taja motan yaya tabar gidan tare dasu haka yasa na samu kwaciya nayi barci sosai dani da Abba kadai a gidan.
Zuwa rana suka dawo da kayan da ta sawo masu din kayan sunyi kyau sosai na bata atamfofi a cikin kayana da zata kai masu dinki.
Nace ina son yaran nan suyi clean ne samira su din rabin jikina ne da komai nawa watarana sune wa yanda zasu tallafa min a lokacin da nawa kadfin ya kare.
Tace gaskiya ne Safiya da har ina ganin wautar ki na dauko su sai yanzu na gane hikimar yin hakan da kikayi akan su.
Zasu taimaka maki kwarai a rayuwa ki don naka sai naka haka abin yake wallahi Allah ya taya ki rokon su nace amin samira.
Sannu a hankali nake koya masu komai kuma suna ganewa sosai don sun sauya kamar basu ba don da gani sun saurari fadan da akai masu da zasu zo.
Sai da uncle ya kara sati biyu ranan alhamis ya dawo da dare ni dai ina barci naji wayana yana ruri na dauka muryan shi naji yana fadin bude min gida don Allah.
Da sauri na mike tare da daukan key na fita daga dakin na bude gida da sauri yana tsaye yadan jigina jikin shi a bango suith din shi na sagale a kafadan shi.
Mirmushi na sake a fuskana tare da fadin sannu da zuwa uncle hannuwan shi ya bude da sauri na shige ciki .
Yana rike dani muka shiga gidan bai nufi dakin shi ba sai da ya tafi yaga Abba dake barci na wuce na bude mai daki tare da kunna naurorin dakin na hada mai ruwan wanka.
Kayan shi ake shigowa dasu gidan daya dawo dasu sun gama na rufe gida tare da yi masu sai da safe.
Ya dauko yaron ya nufi dakin shi dashi a kafadan shi nan na gama komai nabi bayan su nima tari naji yana yi sai muryan shi daya dan shake bai fita sosai.
Uncle baka jin dadi ne dan murmushi yayi yana kara gyara ma yaron shi kwanciya da kyau ya juyo gareni yana fadin .
Mura ne ya kamani kin san yanayin sanyi da ake yi yanzu acan ya fara kokarin cire kayan jikin shi na juya na fita zuwa kitchen inda na hada mashi shayi da cita da kanunfari na kowo mai dakin har lokacin bai fito daga wanka ba.
Bakin gado na zauna ina jiran shi koda ya fito yana goge ruwan dake jikin shi tari ya kama yi a lokacin tashi nayi na fara tsiyaya mashi ruwan tea din dana hada mashi a kofi.
Ya gama yasa kaya a jikin shi ya nufo inda nake jiran shi da cup din tea din da nake dan motsawa a hankali cup din na miko mai bayan naga ya zauna a saman gadon.
Karba yayi yana tari sosai hankali na ya daga sosai ya dan kurba kusan sau biyu yace na kwana biyu ina tarin nan tun acan.
Sannu nayi mai nace yi kokari ka shanye tea din zai taimaka maka ka samu barci da sauki don wanan tarin dake damun ka.
Ido ya dan lumshe kadan yace yaya kibaro mutanen gida nace duk suna lafiya suna gaida ku sun ce kuma ai masu godiya sosai.
Da akai may yana miko min kofin daya shanye tea din na aje a saman dan drower dake gefe na hawayayi saman godon ya dan dukule a wuri daya kamar mai jin sanyi.
Hankali ya tashi ga yanayi da naga yake ciki sai dai yana kokarin kwantar min da hakali da fadin ai murna ne kawai ke damun shi a lokacin.
Ki kwanta yace dani haka na kwanta a sanyayye tare da tausayin kan mu ga halin da muke ciki na rashin lafiya a jikin mu .
Ni yanzu in uncle ya mutu ya barni yaya zanyi da rayuwana jamma, a da sauri na kawar da wanan tunanen a raina tare da kai hannu na na dan shafa Abba dake barci a gefe na.
Ina sauke ajiyan zuciya hannu na guda nakai a saman goshin uncle wanda idon shi ke a lumshe a lokacin.
A haka barci ya dauke mu dama karfe uku na dare yayi ko haka yasa mu makara da safe ba laifi ya samu barci kamar yadda nace mashi din zai samu.
Washe gari ban fito daga dakin uncle da wuri ba don makaran da mukayi yan matana har sun fito sun zauna falo kin san dan kauye bai barcin safe shi.
Sai raba ido suke suga inda zan fito a gidan har Nura ta shigo ta fara aikin ta sacen na fito ganin inda na fito ina sabale da Abba daya tashi daga barci nayi mai wanka acan.
Da sauri suka taso suna gaida ni da kwana na amsa masu cikin dadin rai ina fada masu baban Abba ya dawo jiya da dare .
Sun nuna farin cikin su a hakan daki na shiga tare da kiran su muje dakin nawa a lokacin a saman gado na aje Abba na juya dauko mashi kaya in saka mashi.
Hindatu ta dauke shi tana mashi wasa maimu tace anty na zata kin fita ne da ban ganki ba nace aini maimu ban faye fita unguwa ba sai idan ya kama.
Mun gama muka fito falo bayan na shirya suna zaune suna jirana a dakin sai da nagama tsab muka fito lokacin had Nura ta hada abinci a table na dan duba nake fada mata dawowan uncle tea din jiya na kara hada mai tare da bude fridge na dauko hadin tsoho na zuba a cup na nufi dakin shi.
Na samu ya tashi yana zaune yana duban wasu takardu a hannun shi nace uncle ina kwana yaya jiki da gajiyan hanya.
Na aje kayan kafin ya amsa na juyo na dan kai mai kiss a saman goshin shi yace da sauki madam yaya gida yaya bakin ki kuma ?
Suna lafiya na bashi amsa ina zama kusa dashi nace yaya jikin naka don yanzu na kulla a raina duk fushin shi ko shirun shi zanyi kokari inaga na kara kawo kusanci a tsakanin mu.
Ko zan samu in rage mai yawan saurin fushi a rayuwan shi wanda ni kadai ne a yanzu zan iya kawar mashi da hakan.
Na fada masu ka dawo suna can suna murna na barsu suna karyawa a falo yanzun haka.
Yace akwai kaya cikin kayan da na dawo dashi ki duba ban samu wani lokacin tsaya yi maku tsaraba sosai ba don yanayin jiki na.
Uncle aimu kullun cikin tsara ba muke ina kai hannu na saman cup din maganin tsoho daya bamu musha.
Dauka nayi na kurba na kara kurbawa sosai sai na mika mashi don kawar da zargin wani abu a ranshi duban cup din yayi yace wanan kuma may nene haka ?
Magani ne kasha uncle yana da kyau sosai wallahi tsoho ne danaje ya sama muna don yanayin jkkin mu sai dai ban fada mai ko may ye ba don kada yaji kazantar sha.
Amsa yayi ya kurbe duk ya aje cup din tea din na mika mai yasha nace irin na jiya ne na hada ma naga ka samu saukin tarin jiya da dare.
Kwana kikayi ke nan gadina ashe naji ya fada nace ba dole ba baban mu ya dawo gida ba lafiya ina naga kwanciyan hakalina.
Murshi yayi ya karba ya fara dan spping din tea din a hankali yana lumshe ido har ya shanye ya dan yi gyaran murya nasan cittan ne ke aikin shi a lokacin.
Tashi muje in gaisa da bakin nawa yace min bayan tea din ya dan fada mai wurin na dan gyara kafin mu fito na kwaso kayan da na kai mashi tea din zuwa kitchen.
Suna zaune sai wasa suke ma abba yana dariya suka ji muryan shi a bayan su yana cewa wasu kauyawa ne haka a gidan namu ?
Juyowa sukayi suna gaishe shi ban fito kitchen din ba sai dana dauraye kayan dana shiga dasu din don rage ma Nura aiki.
Na fito na samu yana hira dasu cikin natsuwa yana tambayan su aji nawa kuke yanzu aji uku maimu ta fadi yace kaji ba kauya ba haka zaki ce ba .
Sai hindatu tace primary three yace a a ashe hundatun dai ta waye tafi maimuna jin turan ci ke nan nace ko go and come back ba wanda ya sani cikin su.
Anty munaji fa ana koya muna maimu tace nace makarantan da sai an kora ku kuke zuwa yaushe kuka tafi har ku iya wani abu.
Shigowan yaya saadu ne ya katse muna hiran ya shigo yanayi mai sannu da zuwa sun dan gaisa yace da cashiar suke haka yasa uncle fita.
Don bai yarda a shigo mashi gida kamar yadda sauran maza suke amincewa da kowa ya shiga masu gida kai tsaye.
Haka a kidojin shi suke kamar mutumin da shi yawan tsare iyali da sa ido akan mace ga komai da takeyi fitan su falon mukaci gaba da hiran makaranta da yan kanne na .
Yaya Saadune ya dawo yana fadin ashe maigida baijin dadin jikin shi ne ko da ya dawo yanzun naji yace likitan shi yazo ya duba shi.
Nace yace sanyi ke damun shi mura ya kamashi yace yadai boye maki amma ai ke ma kinga ya ramay sosai ciwo yayi sosai acan fa.
Wani iri naji a raina sosai a lokacin nace nima nayi zargin haka yaya yadda naga ya ramay sosai wallahi.
Yace kafin in gama tunane yace ki bani takardu a saman gado daya aje tashi nayi zuwa kwaso mashi takardun a dakin shi.
Bayan na dauko na kai mashi na koma dakin don hada sauran takarcen daya dawo dasu daga tafiyan nan naga takardan asibiti a ciki na dauka na duba abinda na dan fahinta ciwon nashi ne ya tashi mai acan har ya kwanta asibiti.
Shine kuma uncle zai boye min hakan idan wani abu ya faru dashi fa fiye da funanen shi sai banji dadin yin hakan da yayi min ba ai ba a boye ciwo ga masoyi nace wa kaina.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92Next page

Leave a Reply

Back to top button