BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL
* * *
Na samu masu kitso na yawan zuwa neman kitso a wurina da kuma sayen kayan sanyi da nake sayarwa a gidan.
Haka ya hana ni shiga damuwa da halin da nake ciki don yanzu takai bai bani abinci sai dai inyi dabara inci wa cikina.
Dan neman kudin da nakeyi Allah yai ma abin albarka sai gashi ina samu sosai duk abin da na taba da sunan kudi sai Allah ya sama abin albarka .
Ga anty maman biyu yanzu ta mayar dani kamar wata yar uwata na jiki nakan dauki lakaci naje nai mata gyaran gida da sauran aikin da shafi na mata dai.
Wanan ya kara kawo muna shakuwa a tsakanin mu har yakai ta tutube da zancen karo karatu tunda taga takarduna suna da kyau.
Murmushi nayi kawai nake cewa Anty nasan ko nai mashi magana ba bari zai yi ba koma ya bari ita mahaifiyar shi ba bari zatayi ba.
Don haka na hakkura da wanan zance zan tsaya inda Allah ya ajeni Allah bai manta da kowa ba ina ji ina gani na koma dani da wanda baiyi karatu ba duk daya.
Tai shiru tana kallona can ta nisa take cewa yanzu idan zaki iya sana,a sai mu duba muga yadda za a yi don dai wanan kitso Safiya bazai fishe ki ba.
Nai murshi nake cewa zan iya mana anty tunda ba wani abu nake yi ba tace to za a diba a ga binda ya dace dani.
Nai shirin komawa gida don karfe biyu ya wuce ta hada min goma na arziki kamar kullun na nufi hanyar gida ina sauri don in koma inyi abinci.
Bai bani kuma indan bayin ba fada ne idan na dafa kuma ya lashe, sai dai ashe na makara don na samu ya dawo gidan ko.
Ina kokarin shiga ne naji an shako ni ta baya sai da idanuwa suka firfito don wahala yana fadin yar iska ina kika fito kin fito wurin biyar mazan ki.
Gaba na ya fadi don jin sabon sherin da ya kulla min kuma nai karfin halin fadin Allah yai min tsari ga shiga halaka da duk wani muslimi mai imani.
Nace ni wurin maman biyu na fito don ina mata aiki tana dan bani abinda zanci yanzu can na fito zaka iya binkawa kaji gaskiyan abin.
Yana huci yakai idon shi ga dan jakar kayan da na shigo dashi gidan sai ya fisge jakar ya shiga bincike nasan dama kudi yake nema ba wani abu ba yana ganin dubu biyar ya saurin dauka yana huce yana muzurai da idanuwan shi ya hankadani gefe daya ya fice gidan.
Nakai kallona ga kayan da ya wawatsar min a kasa na duka na fara kwashewa tare da ajiya zuciya idanuwa na zubar da hawaye.
A hankali na zare hijjab din dake jikina na shiga adana kaya inda ya dace da komai a cikin shinkafa naga wani leda an dukule abu ina budewa na ga kudani da takarda a ciki da sauri na dauka ina karantawa kamar haka.
Nasan mijin ki ba zai barki da kudin motan dana baki ba shiyasa na saka maki wanan a cikin nan don in kin gani ki boye ki samu na amfani dashi.
Safiya ki ci abincin da na baki idan ya kare kada kiji kunyan dawowa ki fada min a shirye nake da in taimaki don rayuwan ki na bukatan taimako.
Ina hawaye nake karantawa nagama ina mata addua nasan Allah ne ya turo wanan matan a rayuwa na don ta taimaka min.
Idan badon Allah da ita ba da ban san yadda rayuna zai kasan ce ba a garin da bani da kowa sai Allah amma gashi ta rike ni tankar jinin ta tana taimaka min.
Da safe da wanki na tashi a gidan da gyaran gida komai na gyara na dora girki dayake ina da komai a hannu na girki nayi lafiyayye na zauna naci.
Na shiga wanka na fito ina shiryawa naji shigowan shi sai dai kamar ba shi kadai bane tashi nayi na leka tare yake da wata mace mai siffan kabila da dan riga karmi ajikin ta wata yankwamama da ita ta sa gashin doki akan ta.
Baka ce bata da wani kyau na ga ya rungumo ta yana tsotson sassan jikin ta da sauri na sake labulen ina runtse idona.
Wani irin kuna nake ji a raina har na koma na zauna sai wata zuciya tace dani na fita na yi masu magana.
Koda nafito sun shagala a cikin abinda suke yi basuji fitowa na ba daga dakin har naje gurin fridge na dauko goran ruwa mai sanyi ban tsaya jiran komai ba na bude goran na kwarara masu ruwan akai.
Wani irin zabura sukayi da karfi yace kina hauka ne zuciyana ya dake nace yanzu dai na fara haukan .
Zan kara zuba masu ruwan ya daga hannu ya sharara min mari sai da na gigice na dako nai kan yankwamaman da duka sai shi kuma ya shiga duka na sai da yai min lis .
Da kyat na kwaci kaina a hannun shi na bude kofa a gigice na fito gidan haka nabi hanya ba komai a jikina sai gidan gwagon mu.
Na isa da kukana tana gani na ta zabura tsaye tana fadin ke lafiya may ya faru da Amadun ne yayi hatsari ne komay ?
Duk suna tsaye a kaina sai faman rusa ihu nake yi da kyat na tsagaita kukan da nake yi nake cewa duka na yayi gwago don ya shigo da mace gidan nai magana.
Sai bude baki tayi tace ke mai ya kaiki yi mashi magana gidan shi ko naki har wani dadi ki yaji da zaki ce kar ya nemi matan da yake so.
Dakatar da kukan da nakeyi nayi ina kallon ta cikin mama tace kin ga bazan hana shi jin dadin rayuwan shi a kan ki ke ma in kina iyawa jiki kiyi shaanin gaban ki lagos bariki ne kazo na zo ba mai shiga shanin wani anan.
Yo wanan wani abu ne da kullun zai zama abin masifa a kanki kin hana yaro shakat a ruyuwan shi.
Habiba tace mummy ai duk laifin ki ne da kika hada shi da wanan kucakar yarin sam bata dace da zama matar shi mutum kamar doluwa gata nan.
Sukai min kaca kaca suka korani haka na fito ina kuka na nufi gidan don ban son in tafi gidan mama biyu saboda gidan zumu ba kasuwa bane.
Na dawo na samu sunyi shaye shayen su a gidan sun bar baje kwalaben giya sun shige daki sai kida ke tashi daga ciki.
Hakana na shige tare da bakin ciki a raina ranan dai yadda naga dare haka naga safiya.
* * *
Yaya sani yazo ya sallami ummi da dare da cewa zai yi tafiya kamar yadda ya sallamay ta haka ma ya sallami kowa a gida ba tare da wani yasan idan zai tafi ba.
A cikin daren nan yabi mota sai garin lagos shigan safe yai wa lagos din bai sha wahala ya samu motar zuwa unguwar mu.
Gidan gwago ya nema ya samu suna cinikin safiya mutane da yawa a wurin ta masu karya wa sai ganin shi tayi kwatsan.
Da mamaki take maimaita sunan shi tana cewa sanu kaine a garin namu injin dai lafiya yace lafiya lau ta saka a kawo mai abin karyawa ya karya dama tun abincin da yaci a gida bai sake karya ba har lokacin.
Bayan ya karya ya bukaci a kaishi wuri na sai ta fara yi mai kwana kwana don tasan cewa daren jiya nasha duka wata kila ina can ina jinya jiki na.
Da dai ya matsa Sadiya tace bari ta kai shi gwagon bata so haka ba tare da Sadiyan suka zo gidan mu,
Daidai lokacin ya tsaye yana surfa min zagi wai naki fitowa in dafa masu abin karyawa yana cewa don ubanki ki fito nace dakin nan tun ban biyo ki na kara maki ba.
Aka turo kofan shigowa gidan na fito karuwan ta fito daga ita sai dan tawul iya cinyan ta tana cewa wai may ke faruwa ne sai ma a lokacin nasan wai bahausa ne ita don hausan da tayi.
Kallon kallon akeyi wa juna kamar daga sama na ga yaya sani a gidan ban san lokacin da nayi ihun murna ba na rugumay shi sai kuma na fashe da kuka don murna .
Shikan Ahmed shiru yayi don ya san duk banbamin da yake a kaina yaya Sani yaji shi ga kuma karuwan shi a tsaye da dan tawul tana cewa wai bazata dafa muna bane komay ko lalatsa muna yar iska.
Wani tsawa ya daka mata sai da ta zabura ta kama kanta tare da mashi wani irin kallon ko ta fahinci abinda yake nufi ne sai tai shiru.
Yaya Sani yace bari kuka Safiya yau Allah ya gwada min abin da ummin ki kata mafalki a kai.
Lalai ba gidan uban ta bane ashe kai baka da mutunci baka da kima ga kwalaben giyan su nan a zube da suka sha daren a jiya ba a kawar ba.
Na shiga rawan jiki da yaya na ina ce mashi ya zauna a baude nake tafiya ga kumburi a fuska na baki ya sundule min.
Shigewa yayi baya yagama hararn Sadiya da ta kawo shi gidan yaya Sani bai iya kara furta komai ba yai shiru yana bin gidan da kallo.
Nace yaya bari na hada ma abinci kaci yace ki barshi kawai na ci a wurin gwago zama nayi a kusa dashi ina tambayan mutanem gida.
Sai ga su sun fito daga dakin suka fice gidan sadiya ma tace ita zata tafi tabar aikin ta ne a gida yana jiran ta.
Bayan fitan su ne duka na fashe da kuka mai tsuma zuciya tamayoyi yake mim iin bashi amsa a hankali.
Ya nisa tare da fadi ashe dama haka yake kuma aka aura maki shi ba zan barki garin nan ba Safiya cikin wanan halin kafana kafan ki.
Naji dadi nace yaya sani ka taimake indan ka barni kashe ni zaiyi wallahi baya da imani ko kadan.
Muna nan har na gama shiri na kwatsam sai ga gwago na tashigo gidan tana wani haba haba da mutane,
Ya nuna mata ban fada mashi komao ba gamay da zama na a wurin su ta tafi tana cewa sai ya dawo akwai dakin su yaya saadu ta gyara mashi.
Yace ba zai dade ba zamu dawo gwogo na fita daga gidan ya dube ni yace akwai kudi hannunki da zai ishemu tafiya gida.
Nace eh yaya akwai yace don shima dakyat ya hada kudin da ya biyo babban mota yazo don ya ga ummi ta damu.
Mun tafi har gidan maman biyi dashi taji dadi tai murna taba lamban waya akan idan naje sai in kirata don yaji saukan mu.
Takawo kudin mota ta bamu harda na guzuri wanda zai ishemu nai mata godiya ta kaimu na dan yi tsara ba na saro lace da yan dogayen riguna takai mu garejin kananan motaci muka kama hanya sai arewa.
Tafe muke zuciya ta babu abin daka cikin sa sai yawan tunane fan ban san irin tarbon da zamu samu wurin mahaifin mu ba idan mun isa.
Can lagos shishiru gwago bata ga ya sani yazo gidan ta ba ta tayar da habiba taje tazo mata da shi.
Zuwan ta yayi daidai da dawowan shi gidan da dan ledan chefane a ciki don ya san yaya sani na gari yai wanan.
Sai dai babu kowa a gidan sai ga habiba yake tambayan ta tace bata san inda muka tafi ba itama zuanta kenan mummy ta turo ni in kira wanan bakon.
Dakyat ya bude gidan ya samu ya shiga sai bayan ya bude ne wata makwaciyar mu takawo mao key tace nace a bashi yace ni ina inane da zan bata key din gidan.
Taga dai na dauki jakkana da wasu kaya mun tafi idon ya fitar waje acikin mamaki yace What.
Eyyeh ta tafi tace damu har mun mata rakakiya yayi wani dan fito a bakin shi irin na yan daba ya shige ciki ita ko habiba komawa tayi gida ta fadawa mahaifiyar ai gwago naji tace dama ban yarda da zuwan dan iskan yaron nan ba.
Kana ganin shi kaga dan tantiri dan duniya ko ina babu mai zuwa daga ma yayi barka ya rabu da kaya gidan shi shegiya banda taulali mai aka kawo min dama su karata can.