BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

* * *
Gidan mu ana kiran shi da gidan Jima don duk wani nau,in fata zaka samay shi a gun baba wanda yake sarafawa ya mayar dashi fata.
Mahaifin mu ya gaji wanan sanan ne a gun mahaifin shi shima mahaifina kamar yadda na fada maki a baya mata uku ke gareshi irin auren karfin hali na malam bahaushe.
Mama itace ta wanke shi suna da shekara uku da aure ya auri inna wacce dama da ita yai samartakan shi tana budurwa tai aure ta fito ya aureta.
Sai inna ta daya aura daga baya a wani kauye tazo gun yan uwan ta ya ganta ya shiga nema da yake Allah yayi dashi rabon zuria a tsakani kuma.
Don saida yan suka suka dinga suka amma ummi tace sai shi take so tun wannan lokacin da aka kawo ummi gidan matan gidan suka dauki tsana da tsangwana suka saka mata tun abin na dan dadi har takai zama ya koma zaman hakkuri kamar yadda matan hausawa da yawa suke zaman yi a gidajen su.
Idan ka dan yunkura daukan mataki sai ace kayi hakkuri don iyali sin taru suma matan abinda suke duba ke nan wani lokaci akan idan sun bar diyan su may yai makomar su kuma gidan gun matan dake gidan.
Suma kan su kishiyoyin ummi din ba barin junar su sukayi ba don zakaji fada ya gaure a tsakanin ko kan diya ko kuma kayan abinci idan wata zata karbi girki a cikin su.
Wanan halin da wuya ai kwana biyu cikakke basu samu baraka ba irin hakan wanda sai mutane sun shigo rabo daga waje.
Haka yasa gidan namu ya kara suna gun mutanen uguwar mu gashi yaran gidan ba tarbiya ko kadan komai girman mutum zasu iya ci masa mutunci don samun daurin gindi a gun uwayen su da sukayi.
Ba yabon kai ba don ina dakin ummi a gaskiya ko kwatance za a yi da dakin mu ake kwatancen masu daman gidan na mu a unguwa.
Da wanan rayuwan muke zama a unguwar mu hakana yau da dadi gobe ba dadi don dai an fimu karfi ta ko ina a gidan dole sai zama na hakkuri kawai a tsakani tunda Allah ya riga ya hada zaman mu a cikin su.
Bawai iya mu ba har wani wanda ya rabe mu haka nan suke hassada dashi da bakin ciki .
Yadda duk ake son tarbiya muna samun shi a gun uwar mu don duk da matsin kishiyoyin da take ciki batai sake dabawa diyan ta tarbiya ba wanan fannin sai dai kawai talaucin da rayuwa na kakanakayi da muke a gidan.
Allah ya taimake ni duk diyan dakin namu muna da dan kokarin mu a fannin karatun mu ba wanda baida kokari a cikin mu.
Wanan ne daman da muka samu zance na rayuwa don da wuya ai hutu wani cikin mu bai dan samu kyauta ba nabajin ta muna dan samun abin dan more rayuwa a hankali.
Ga irin dan kyaututukan da muke ciyowa a wurin musabika da kuma quzee din mukeyi a makarantar boko.
Maimakon a taya mu murna a gida sai tarin takaici ko a ce an dai bamu ne kawai don bakin iya yin mu.
A haka zamu wuni ranan cikin bacin rai a gidan saboda hattara da tsangwaman da zamu shiga gun mutanen gidan mu.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:10 PM – Ummi Tandama: BAHAGON, , , , , , ,

????????2⃣????????

FREE PAGE

SEENABU MAKAWA

MAISON WANNAN NOVEL ZATA IYA KIRANA DA WANNAN LAYIN DON YIN REGISTER 300 TA BANK KO RECHARGE CARD NA 400
ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENITH BANK 2253380105 SAINAJI KU MASOYA AI HAKKURI DA MU WRITERS YANAYI NE YA KAWO HAKAN DA FATAN ZAKU FAHINCE MU, , , , ,

Sauri nake ina shirin tafiya makaranta kasancewa yau monday don nasan akwai dogon assembly da wasu bayanai a irin wanan ranan.
Socks na jawo na fara sakawa a kafana daya yayin da na ji an fara kwala min kira a tsakar gida.
Haushi da takaici ne ya rufe ni a lokaci daya don nasan wani sabon fitina ina zata dora min duk wanan saurin da nakeyi zai tashi a zero ke nan bazan samu assemby din da nakewa kwadayin samu ba kuma wata kila aike ne ko wani aikin zanyi.
Na aje socks din ban saka ba don karba kiran inna din samun ta nayi tana kokarin dama kunun koko take cewa dani na kwaso kayan zuba kunun ko wani daki na kawo mata.
Na juya rai bace naje karbo kayan na kawo ina kokarin ajewa ne takai idon ta akan roban dakin mu sai kawai naga tai cilli dashi a gefe daya.
Ni dai ina tsaye ina kallon ikon Allah ta fara zubawa sai data gama zubawa kowa ta jawo roban ta dan yafuta ta dan zuba muna rabin abinda take awo dashi ta dangwara mun sai na dauka na nufi daki ina juyawa a hankali ina kallon kunun da rai bakwai zasu sha su rayu a gidan.
Ina kokarin rufe roban ne naji ummina tana cewa babu kunun ne ko don naga kin dawo da roban hakana ba komai a cikin sa.
A sanyaye na ce akwai ima anzuba muna ta mike ta jawo roban tana kdllon kunnun dake a cikin sa sai naga ta dauki roban zata fita.
Da sauri na tare ta nace ummi kiyi hakkuri kusha hakana may duniya don Allah bata saurare ni ba ranta ya baci tafita.
Ba wai wanan ne karo na farko da Inna ke muna haka ba a gidan koda yaushe in dai ita zata raba abinci to na dakin mu kan kankare ne kuma ko mutum biyu baya isa a dakin namu.
Ina ga yau ta gaji ne gashi kuma mun kwana babu ko kwandala a dakin balle ta dan sai garin kwaki ko kanzo tabawa yara dan abin dake gare mu munyi kitso da wanki dashi a cikin sati.
Muryan Ummi naji tana fadin haba yaya wanan koko aiko su shaibu ba zai isa ba balle sauran yaran har akai ni.
Sai naji Inna tace da ita au da kika fito kikai min tsaye a kai zikau dake tsoron ki zanji na kara maku babu ko may ?
Ummi tace kawowa nayi ki duba ki gani ga sauran roban nagani duk a cike amma ki duba abinda kika zuba muna don Allsh dai.
Tabe baki tayi tare da fadin yanzu aike akeji kunu ne shi naga daman zubawa idan kin isa ki diba ki kara maku tunda keda diyan ki kune yan gwal a gidan ku kadai akaiwa bakin cin abinci cikin mu.
Ummi tace ba sai na diba ba ai idan bazaki kara ba abarshi don ban san wa zanbawa ba wazan hanawa ba, cikin yaran.
Eyye lalai ma Rabi wuyan ki ya isa yan ka wallahi to bara kiji ke din nan dai da nake gani baki kai min can ba kunu ne ba zan kara ba sai kiyi abinda zakiyi dama naga tun da na zuba munafukar yar ki take bin kunnun da kallo tana min wani tsiwa a kai.
Nifa din nan kujera ce daidai da zaman kowa idan wani abu kike ji da safe nan daidai nake dake yanzin nan don ban daukan raini da wullakancin kowa.
Don idan mutum yai min tsiya yanzun nan na nada mai dukan tsiya inbuge shi in bugi banza naga wanda zai rama mai kuma.
Ummi dai bata tanka taba ta duka tana kokarin juye kunun a roba da sauri inna ta tare tana fadin kada ki lalata muna kunu da wanan kazamin roban naku daya dafe don tsufa.
Muryan babana naji ya fito daga dakin inna yana fadin wai may nene ya akayi ne kuma da farar safiyan nan haka ?
Wani irin harara ta watso mashi tace wanan yar kauyen matar taka ke son shiga mun hanci da kudundune da safen nan akan kunun dana dama na basu.
Niko idan ta kawo rainin da sukewa mutane kaina yanzu zata sha na jaki wanan iskancin ta tsaya iya kai tai maka shi can bani ba.
Baba yace muga kunun sai ummi ta nuna mai ya kada kai yace haba Rakiya yanzu wanan dan kunun ace rai bakwai zasu sha shi ai babu gaskiya ga wannan zance yakai ido ga sauran robobin da aka cika yake cewa wanan nasu waye haka shi ?
Tace ko zaka shigar mata ne naga daga jin muna zancen mu na mata kayi wuf kafito kana kokarin saka bakin ka ciki.
Fitowan ka ba zai hana ni yin abinda nai niyar yi ba akai don ba wani yai wahalan dama min ba.
Ita har waye da zata fito tace min wai banyi daidai ba ko iskancin nasu ne zai kawo gare ni yau kuma ?
Ummi ta wufta da kunun a roban dake gaban inna ta juye tace ga kunun ki nan ki barshi Allah da ya halice mu ba zai barmu da yunwa ba yana sama yana ganin mu.
Tace da baba kagani ko kaga irin cin kashin da tai min dai a gaban ka ko ita wacece da zanyi wahala dama kunu ta fito tai min wullakanci dashi.
Ummi ta juya bata ce da ita tak ba ta nufi dakin ta inna ke fadin samun wuri banza diyan masiyata yar kauye wanda bata da tarbiya ta uwa ta uba.
Ummi ta ce a, a yaya maganan nan iya ni dake ne baikai na iyayye ba fa don haka ki daina zaga min iyayyena da basu ji basu gani ba da safen nan.
Don ni iyayena ba mutanen banza bane ko da suke kauye ba wanda ya taba ganin su suna roko a wurin wani.
Dama mahaifin inna maroki ne ya tsufa amma har yanzu yana roko a cikin gari kowa yasan shi sai inna ta fusata da maganan ummi din.
Tai wuf ta kamo hijjabin dake wuyan ummi ta shake ta har idanuwan ta suka firfito waje tana fadin rokon sata ne ko maita da zaki min gori dashi.
Bata bata amsa ba ta sake sabon shake ta daga inda baba yake yana karasowa yana fadin sake ta mana Rakiya kasheta zakiyi ne ko may ?
Kafin ya karaso ta kaita kasa ta danne tana duka tana fadin gobe ki kara zagin ubana don yana roko roko ai ba sata bane duniya.
Jin sun kicimay yasani fitowa da sauri ga ummi a kasa inna ta haye tana duka mahaifin mu na kokarin banbareta daga saman ta.
Ihu na saka da karfi har yasa mutanen gidan gaba daya fitowa dama wanda bai tashi daga barci ba ya falka.
Ya banbareta saman ta shi da mama tana huci tana fafin gobe kice zaki kara zagina yar iska don an kyale ki har zaki kaiga zagin iyayye na.
Haka kawai don samun wuri yar kauyen banza a kauyen may kuke sha banda ruwan kasari da gwabe da safe.
Mama tace don dama sunyi hayaniya da yamman jiya a, a Rakiya baki da gsskiya ni kaina na san baki basu abinci yadda ya dace ba yau ba.
Ta juya kan mama tana fadin bani bayarwa kedin daban ne wurin basu wake kwashe abincin bakeda yara ki ba ku goma a daki daya katan banza kin tarasu ba moriya.
Daga can Nura dan mama daya taso daga barci ihu na ya tayar dasu yace kada kice zaki zagi maman mu yanzu rayuka su baci wallahi.
Su dai da kika raina don basu kawo karfi ba ki tsaya a kansu amma mu kan idan kokai wa maman mu yanzu zaki ji mu don kin dai san mun fiku karfi da yawa kuma.
Da sauri na karasa na daga ummi ina gurza kuka ina mata sannu ummi a cikin kuka itama din kukan take sharba a lokacin.
Tsawa baba ya daka min wai na raba su da ihu kada na tara mashi mutane a gida a dauka ko anyi mutuwa ne a gidan tun da safe haka.
Yaya Sani dan wurin Inna din ne mai dan dama a gidan mu yace a, a baba ai dole ne Safiya ta kuka irin wanan wullakancin haka a daki uwarta a gaban ta don basu da karfi kuma a hanata kuka ai cin zalun yayi yawa mana.
Ya juya gare ni yana fadin ke ba makaranta zaki ba maza kije ki shirya ki tafi kada ku makara bar su da Allah kowa ya zalunci wani Allah na gani ai don ba anan duniya zata tabbata ba ai.
Na dago kai nabi babana da kallo na sake kallon yaya sani din na juya nabi bayan ummi muka shiga daki.
Sai naji Inna na fadin kaikan sani anyi hasara wallahi yanzu akan kishiya da yan uba kake fafin wanan maganan haka to tunda kaji haushi sai kazo ka rama masu nasan ka isa wawa kawai wanda bai san ciwon kan shi ba.
Banji may ce da ita don rashin kunya a gidan mu ba sai na tsaya fadi ba ba abin kunya bane da yaci wa uwar shi mutunci a bainan jama, a.
Ina kokarin daukan dan tsunman jakan makaran ta ina goge hawaye ummi ke fadin kuyi hakkuri yar nan mu kuma namu rayun a haka yazo muna gidan nan Bahagon rayuwan Allah ya nufe mu da gani cikin su.
Yaya sani ne ya dago labulen dakin yana fadin ke Safiya miko min roban kunun naku naku nan ya dauke da katon roban da inna ta dama kunu a cikin sa gaba daya.
Uwar na daga wurin madafa tana fadin wai ko dan nan ka ka daya kuwa ko an hada dakaine an mallake min ban sani ba wai ?
Jikina na rawa na dauko roban dake gefe na mika mai ya raba kunun biyu ya juye muna a roban mu yana fadin maza ku sha ku tafi kada ku makara.
Da sauri na dauka na ciki na fara zubawa yan kanne na don ina gudun inna ta shigo ta hana mu sha kuma.
Har muka gama inna bata bar zagin Sani ba zagi irin wanda ba a son uwa taiwa diyan ta shi take faman zuba mashi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92Next page

Leave a Reply

Back to top button