BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:11 PM – Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , ,

????????2️⃣5️⃣????????

YAR UWA NOVEL DIN NAN NA KUDINE IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, , , , ,

Cikin wata daya da nayi a gidan mu cikina ya karasa shiga wata na tara duk da nace ma ummi da mama bansan ko wata nawa cikin yake ba.
Amma su daya ke manya ne sun gane na shiga watan tara nan aka shiga min jikile jike ana bani.
Don samun saukin haihuwa wai idan haihuwa yazo vazan wahala ba sosai indan ina shan abin karya zaki.
Watarana da dadare ina cikin barci na farka da matsanacin ciwon mara da ban taba jin irin sa ba, wai ashe nakuda ya kamani .
Cikin barci na dinga tada ummi na daga barci ina fadi wayyo ummi bayana marata ciwo kamar zai fashe min nake jin shi.
Ummi ta tashi a rude take tambayana ya nake ji na fada mata, fita tayi daga dakin taje ta tada mama sai gasu sun dawo a tare da mama din dakin.
Nan suka fara bani abinda ya dace da akewa mai na kuda da fada min yadda zanyi abin yazo min da sauki.
Abu wasa wasa har wuraren karfe sha biyu na rana ba labarin haihuwa gashi ina dan banzan wahala.
Don haka suka yanke shawaran su kaini asibiti don ina wahala sosai na gala baita matuka na wahala a gida.
Mun isa asibiti aka duba ni suka ce haihuwa ne sai dai bazan iya da kaina ba don haka za ai min theater ne.
Bani dake wahala ba harda su mama da suka kawoni sai da hankalin su yai matukar tashi, aka rubuta masu abinda za a sayo kafin theater din.
Baba ya fara fadi tashin neman kudi don ya sayo maganin da sauran kayan aikin don baida kudin a hannunshi.
A cikin karfin hali na daure nace baba akwai kudi a hannuna a tambayi ummi na agida ta duba zata gansu.
Allah da ikon shi anshiga dani dakin theater sai Allah ya kawo min saukin haihuwa na nisa sai abin cikin cikin nawa ya fito.
Ashe abin da matsala ne shiya sa na wahala diya ce mace sai dai tazo da wani irin halitta na daban likitoci suka taru akan mu suna dibata.
Daga karshe dai hakana dai aka sallamay mu muka koma gida da ita cikin yanayin da tazo.
Sai dai mama ta hana abawa kowa yar ya gani tana dunkule a raggan zani duk wanda yaga abinda yarinyar keyi dole ya tausaya mata.
Karamar yarinya da bata dauki alhakin kowa ba a kanta tana bautar Allah cikin wani yanayi na ban tausayi.
Amma ita inna har kiran mutane take su zo su aga abinda na haifa mutane ko sai suka fara tururuwan zuwa ganin halittan yar.
Kwana daya da haihuwa Baba ya shigo gida da dadare yake ce min yaya za a yi a samu su gwago can lagos a fada masu zancen haihuwan nawa.
Na lumshe ido nace baba aida a kyale su kawai, yace aa baki da hankaline yarsu ce fa suna da hakkin a fada masu ai.
Sai nace sai dai yaya saadu don shi kawai nake da nomban shi wayan shi cikin su bayan shi ban da lanban kowa cikin su.
Ko shi da yazo ne yaban wayan da zo dashi shine har na samu namban shi din, da ban da layin kowa a cikin su.
Yaya sani ne yakirashi sai baba ya karba yana fadama mashi zancen haihuwan yayi murna sosai dajin na haihu lafiya da Allah ya saukeni lafiya ba tare da anmin aiki ba.
Sun gama da baba yace a bani wayan yai min barka na karba cikin jin kuya nake karba mai yace da ya kashe zai kira mummy da Ahmed ya fada masu na sauka lafiya.
Hakan ko akayi nan ya kirsu ya sheda masu zancen haihuwan nawa sai dai ba wanda yai farin ciki da jin haihuwan daga cikin su.
Shima gogan daya kira shi cewa yayi and so what idan ta haihu may kake son nayi mata yanzu kuma ?
Ashe lokacin suna tare da Liliya ne ya kirashi don haka baida halin nuna farin ciki da haihuwan nawa.
Nan dai dan uwan yai mashi tas yakuma ce indan baiyi hankali ba sai ya hada shi da hukuma akan wanan case din.
A haifa ma ya kace min and so what kai wani irin jahilin mutum ne wai kana koda inmani kuwa kai ?
A cikin fushi ya nufi gidan su yana fada ma mahaifiyar su yadda sukayi da saadu din wai ya kira shi da jahili.
Tace ai gaskiya ya fada maka dole ne ai a fada muna san nan ai wani abu daga nan wurin mu kuma ya zama dole mu tafi yace wa ?
Cikin hasala shi ba inda zan tafi indai ke zaki tafi ban hanaki ba amma nikan ba inda zan tafi tun wuri .
Don nasan a jirace suke damu yanzu kuma sun samu kafar samun mu ke nan don haka ni ba inda zan tafi final.
Saadu yazo yasa uwar a gaba son su hada abinda zasu sai mu na kayan suna suzo muna dashi, mahaifiyar nasu tace bata da kudi yanzu a dai tambayi Ahmed din.
Gogan da aka tambaye shi dubu goma kawai suka samu a wurin shi wai baida kudi duk karuwai sun cinye kudin shi da giya dole yaya saadin ne ya fitar da kudi ya sai muna abinda za a zo dashi din.
Sun saka ranan tafiya saura kwana biyu suna munyi waya dashi nai mashi kwatancen gidan maman biyu don yaje ya fada mata.
Ya ko je tayi murna dajin na haihu din ta karbi lanba na a wirin shi ta bashi abinda zai kawo min sai dai bai gwadawa mahaifiyar ta suba.
Da dare ina zaune a dakin mama don anan nake jegona sai naji wayana na tsuwa alaman kira ya shigo min .
Na dauka da sallama muryan wace najine ko a barci na falka ina sheda shi maman biyu ce ta kirani, na dan kwala ihu do jin muryan ta, tace dani.
Ai nayi fushi dake nace anty ba hakana bane wallahi kullun kina a raina ban san yadda zanyi in kiraki bane.
Don lanban da kika bani ya bata nan dai muka taba hira da ita take tambayana yadda muka kwasa da mahaifin mu da nazo gida ?
Ta fada mata komai harda zuwan yaya Saadu wurin mu da yadda ya wanke ni a gaban su baba da sauran yan uwana.
A karshe mukai sallama da ita tace zan ga sako wurin yaya saadu idan ya zo nai mata godiya na kashe wayan.
Idan na kalli yarinyar tausayi take ban don yadda take wahala matuka taita murde murde da hannu idanuwa warwaje tana wani irin numfashi a wahalce kace ko zaka je kadawo kasamu bata da rai.
Mama ce ke kwana wahalce da ita har safe sai a kama mata tadan kwanta da rana ta runtsa barcin ba wani barci ba take tashi.
Da aka ga wahalan yai ma yarinya yawa aka koma asibiti da ita likita ya tambaye ni idan na taba mugun faduwa da ciki.
Nace a a yace duka fa kowani buguwa mai karfi sai nai shiru mama tace mijin da ta aura yake dukan ta da ciki likita yace wanan abun ne ya taba yarinyan tun a cikin ciki yasa tazo kamar jujartata.
Hawaye na fara yi ina tausayin yarinyar da kaina, magani aka rubuta muna muka dawo gida rai baci tun a mota mama ke ta zabga fada tana cewa mutane ba imani haka ?.
Yanzu gashi ke ke wahala shi yana can yana barikin shi hankali kwance abinshi.
Mun iso gida mama tana kuka tana ma mutanen gida mu bayani komai da likita ya fadi.
Allah ya isa yaya sani suke ta ja baba baki ya mutu da har ya fara cewa in gwago tazo sai in hakkuri in koma dakina.
Wai kada yarinya ta tashi ba uba tare da ita maganin da likita ya bayar a bata shi ake bata kai da kai sai numfashin ya fara ragewa ya dan fara komawa nomal.
Su yaya Saadu sun taso kamar yadda suka shirya ba isoba sai da safe don tafiyan dare sukayi.
Tun da ya shigo yagga yadda yarinyar take hankalin shi yai matukar tashi sosai gwago tun taron da yan gidam mu sukai mata ta shiga tsarguwa.
Mama na kuka take fada masu abinda likita yace a gamay da yarinyar yaya yace komai akace ya faru ne ba a kyauta ba gaskiya amma ayi hakkuri.
Suka bayar da abinda suka zo dashi wanda ni nasan yaya saadu ne yayi shi don nidai duk zama na gidan bai taba yin min sutura ba.
An karba da godiya sai gwago tace adai yi hakkuri dashi mama tace ba a dai kyauta ba gaskiya malam ya bada yarinyar don zumunci ya dore gashi abin kuma baiyi dadi ba.
Baba sun zauna da gwago ya nuna mata bacin ran shi sosai ga irin rikon da dan ta yai min acan har da nata laifin ma, sai ta kama kukan munafunci wai yara zasu bata masu zumuncin su.
Baba yace basu bata muna zumunta don ba su suka hada mu ba balle su yanke muna zumuncin mu.
Nan ta danji sauki har ta fara aibanta ni wai ban da kirki banda tatali banda sanin ya kamata ko ita rashin kunya nake mata..
Sai da yaya saadu ya bari ta gama ya kawo matsalnta duk ya fada ma baba da yadda tabar tarbiyan su ya lalace komai ya fadi.
Sun dade suna magana baba ya san yi mata nasiha har da alkwarin wai zai mayar dani dakina yace dasu.
Ana gobe sunane sun zo washe gari da safe yarinyar ta koma Allah ya gani banji bacin rai da rashin ta ba don a halin da tazo da ta rayu wani gwamma ta koma yafi.
Nan dai aka kawar da ita yan uwana sun tausaya min sosai nidai abu ga kurciya ga bacin rai banji komai ba a lokacin.
Sai gwago ta kebe da yaya saadu da mama wai a rage abinda suka zo dashi tunda yarinya ta koma nan yaya saadu yai cikin ta.
Yace indon dubu goman da Ahmed ya bayar kike jin zafi ga dubu goma ki mayar mai da abinshi ban iya abin kunyan da kike shirin yi.
Mama tace wai ko Rakiya kan ki daya kuwa may yasa abin duniya yake rufe maki ido haka ita yarinyar da tai wahalan haihuwa fa ?
Nan dai suka yi shi baran baran sai da rayuka suka baci masu, washe gari suka daga suka koma inda suka fito.
Bayan wucewar sune mama ke mayar da yadda suka kwashe da gwago kan kayan nace mama aida kun mayar masu da abinsu ma.
Don ni bani son komai da ya fito daga wurin Ahmed sai mama tace ai ai a she shi dubu goma kawai ya basu su kara.
Duk kanin ne yai sauran kayan da kuka gani uwar bata sako komai ba ni bansan inda Rakiya zata kai son kudin ta ba wallahi.
Nan nake basu labari ai ko zuwa nayi gaida ita bata bani abinci sayarwan ta sai ansaya mun zan ci.
Kowa yai tir da irin hali nata na son kudi da rashin taimakawa uwan uwa kullun tazo sai kukan babu takeyi.
Maman biyu ta bugo min waya da dare tana min barka da taro ya watse lafiya ?
Murmushi nace anty ai yarinyar ta koma jiya nan dai nake fada mata yadda akayi da abinda likita ya fada akan ta.
Tace kin ma huta wallahi Allah ta baki lafiya yasa ita kuma ta huta nace amin nan dai mukai hira tana tambayana yadda aka kwashe da gwago tazo nake fada mata komai karshe nai mata godiyan sakon da ta aiko min mukai sallama da ita.
Tun da akai sati na dan watsake ina yin komai sannu a hankali ina mai da jiki na ina harkokina na yau da kullun sai dai ban fita ko ina ina gida koda yaushe.
Dan dama dama naka dan dauki lokaci in fita ziyaran yan uwa ban dadewa in dawo gida don ko na fita sai na tsargi kaina don ban son a dauko min maganan zama lagos.
Sana a nake gadan gadan kanena ke fita mun dashi don haka hankali na yadan kwanta har nakan manta da rayuwan gidan Ahmed din da nayi a baya.
Zan tura kudina wa maman biyu da kudi sai ta sayo kaya ta turo min dashi ta motar haya a kawo min.
Haka nake har na dan samu nawa sai kuma kyashi da hassada ya shiga zukatan Inna da wasu yaran gidan namu zaka ji ana sake magana akan sanaa nawa a tsakar gida koda yaushe.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92Next page

Leave a Reply

Back to top button