BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

* * *
Ko da muka shiga school ranan mun makara sosai nasha bulala na na wuce aji raina a bace ba don bugu ba sai dai abinda na bari a gidan mu na cin kashin da akewa mahaifiyan mu.
Don ni a iya sani na banga wani hslin rashi biyayyan da take nuna masu ba a gidan don ko aiki yai masu yawa watarana sai ta taya su idan kuma diyan su ko sune basu da lafiya zakace wani nata ne ba lafiya ta shiga sintiri gaida mashi ke nan a cikin su.
Ita ranan da duk wani yaron ta zai kwanta ciwo babu mai lekashi har ya ji sauki ya mike ba su gaida mutum.
Don Allah maijin kan bawan sa ne da wuya dan dakin mu ya kwanta ciwo a gidan mu sai can ba a rasa ba zakaji wani cikin mu ba lafiya.
Zan dai iya cewa ummin mu mace da bata da kyashi ko hassada kuma mu kan mu ta koya muna wanan akidar nata na matukar hakkuri tare da sanin ya kamata .
Ba don halin nan nata ba na irin rayuwan da kishiyoyi da miji suke mata a gidan na wullakanci amma daidai da rana daya bata mayar da martani irin wanda bai dace ba a kan su.
Ni na rasa may ke jawo wanan kiyayyan haka akan mu da uwar mu sai yanzu da wayo ya fara zo min ne na fahinci ba komai bane illa zalar kishi irin na macen bahaushe kawai.
Don ummin mu yarinya ce a cikin su kuma har yawan haihuwar da tayi bai sa kyaun ta da dirin ta ya gushe ba gare ta wanda su sauran sai dai kawai zaman rayuwa.
Zan iya cewa a gun mahaifiyan mu yan dakin mu maka kwaso dirin mu mazan mu da matan mu ba laifi uban mu ma dogo ne sai dai shi baki ne amma baya ga tsayin nashi komai na mahaifiyar mu muke debowa.
Daga hasken fata tsayin don itama tana dashi zuwa suma hanci da idanuwa manya masu fari kal dasu.
Don idan zagi ya tashi dashi matan gidan mu ke zagin mu ko yaushe sai suce damu shegu masu zubin uwar su.
Sai kaji guda ta karbe da cewa ba dole ba tunda tafi miji jaraba dama ai ance wanda yafi jaraba a wurin saduwa shi da ke biyowa a duniya.
Tun ban san kallaman ba har na fara fahintar ma anan shi idan sun fadi na turo baki ina maijin haushin kalamin su gare mu.
Ranan dai sunan naje makaran ta ne amma babu wani abinda na iya tsinanawa a karatuna na dawo gida da bacin rai na samu ummi ta dan gyagiji tana aiyukan ta a tsakar gida.
Uniform din kannena kwaso duk da tsofi ne amma bana taba barin su da dauda kullun na dawo sai na wanke muna su na sha idan sun bushe na buge nakai daki kafin mu wuce islamiya.
Do ba halin na barsu nazo na iske an masu ba daidai ba ko tukunya za a sauke dasu ake saukewa idan an tashi aiki in suna shanye a waje.
Mun gama shirin mu muka shirya zuwa islamiya mun fito ke nan yaya sani yana zaune a daban su na yan matasa yace dani ke Safiya zo nan.
Jiki na min bari na nufe shi sai naji yace dani kunci abinci nace eh yaya munci yace to ki saurareni kiji daga yau duk wanda kika ga zai daki ummin ki ki nemo sanda kema ki buga mashi ninace a mutu har liman.
Da sauri na dago kai ina mamakin kalamin shi yace eh don abin yai yawa daga magana sai duka irin haka itama Rabin na fada mata ta daina zama ana mata wanan cin fuskan tun bakuyi wayo ba har gashi kun tasa ana bu daya a gidan.
Yace baki ji may Nura ya fada bane kowa ma ai uwarshi ya sani don haka ninace ki rotsa mutum koma waye.
Yace maza ku tafi kada ku makara zance a gun yaya sani muka samu sauki dakin mu don yafi kowa zama tantiri a gidan mu.
Sai gashi kuma Allah ya dora mu a kan shi yana jin mu a gidan ko dan ladabin da muke mashi ne oho ?
Don zamu ganshi komai yawan abokan shi sai mun duka mun gaida shi idan kaya muka gani a hannun shi zamu karba a hannun shi mukai dakin su.
Shima idan yar dahuwar shi ya samo ni zai nema na dafa mai kuma ko ya bani bana karba nace ya bar shi, sai idan ya zare min ido zan karba naci ko na bawa kan ne na suci.
Tun wanan fadan da akayi gidsn mu ummin mu ta dan samu baki idan ana mata wanin abin cin fuska zata zage ta mayar da martani kamar yadda akai mata ba dadi din itama.
Abin dake ci mun rai shine irin yadda gamu da yawa a gidan mu amma kowa a ware yake ba mai hurda da wanin shi dan dama tsakanin yaran dakin mama dana Inna akwai dan shiri a tsakanin su.
Nice dai babu halin idan suna zaune ko suna wanin abin da ya shafe yara mata nace zanzo wurin yanzu zakaji sun fara hattarana.
Suna fadin ke kuma may kika zo yi nan munafuka kawai sai wata tace muguwa mai irin halin uwar ta kawai in ba gulma ba may kika zo saurare nan.
Dole zan bar wurin don zagi da hattara irin haka yasa ko suna abin su bana shiga shirgin su ina daki da ummi na ko ina wani aikin a waje sai dai abinka da yaro inayi ina sauraren su sai na manta na saka baki wata rana su kyale ni wata rana kuma nasha ba dadi garesu.
In kaji dariya na ko farin cikina muna tare da kanne na ko kuma na fita zuwa makaranta ne.
Idan baba ya shigo yaga bana cikin su yanzu zai fara fada dani wai ina tsabbare kaina a cikin yan uwana.
Sai kaji Inna tace mugun hali ya ci may idan batai hakan ba ko uwarta baka ganin komai nata a makidance takeyi shi don dai kawai duniya ta zage mu.
Ace muna gallaza mata ita da uwarta a gidan kasan mutum baida gadon ka amma yana da na maganan ka yanzu.
Sai kaji baba ya amsa da naga alama ai an koya mata halin tsiya ta iya itama.
To ba dole ba kullun suna daki ana mata hudubar tsiya a kai dabiar da ba zai amfane ka ba ko yau tana tsabbare sun hada kai da uwar ta a daki suna wance tayi min abu kaza don may bazata tashi da mugun hali ba kuwa ?
Abin yana ban mamaki don sai inga ai komai a baiyyane yake ai a gidan ni dai a iya sani wani fitina bai tasowa ace da Safiya a cikin sa.
Ko wani ya kawo kara daga waje yace ai Safiya tai mun wani abin suko ko yaushe cikin sallama mashi ake ana kawo karan su gun shi.
Sai dai abin mamaki wanan bai sa yayyena maza su kini ba a gidan namu don su basu matsa min kuma ba su yarda ai min sheri a gaban su yanzu zasu ce zasu daki yarinya idan tai masu tsiya tun dai yaya sani.
Kuma duk wanan abin idan sun dan samo kudin su gun Ummina zasu nufo dashi ta baye masu har ya kare.
Da haka har ummi ke dan samu tana basu shawaran abinda zasu yi wanda zai amfane su a rayuwan su, sai kuma iyayyen nasu suka koma cewa.
Wani sallon yaudara ne don ta raba su da yayan su ummi ta dauko sukai mata ahir da yaran su shikan yaya sani da ya samu labari tun a nan yau zaune tsakar gida yana fadin.
Oho wai ni za aiwa yau don a raba ni da mai taimaka min a dinga kwace min kudi to ban yarda ba babu wanda zai hanani bawa maman safiya a jiyan kudi na a gidan nan.
Ke mama da kike fadin haka ba nan Nura ya sayo akuya ba ku kai masa sheri aka sayar da akuyan akace mai ya bata.
Cikin tsawa mama tace dashi kai kada ka kawo min diban albarka idan kaje kayo shaye shayen kane kake son saukewa a kaina bazaka sha da dadi ba yanzu na saka yara na suyi maka tsinanen duka a gidan nan.
Wuf daya yayi ya yanko reshen darbejiyan dake baya gidan mu yana fadin yau naga shegen dan ki daya isa ya tabani a gidan nan idan ba a kwashi gawan shi ba shege nake.
Yau kuwa zan gwada maki halin mashayan da kika kira min aiko yai cikin su a kofan dakin ta da take tsaye da diyan ta a take suka watse.
Suna rige rigen shiga daki wani na ture wani daga kofan dakin wurin shiga dakin don yai masu mai ka uwa da wabi baki daya.
Ashe fadan bai kare ba sai ga Inna ta na cewa idan har yaron na yana shaye shaye ke ko diyan ki barayin kororo ne da karuwai, waye bai san abin da suke a gari ba har akuyan da kike fadin an sace dake da diyan ki kuka sace shi ai.
Nan fada ya kaure tsakanin ranan dai gidan mu babu dadi tonon asiri zalla suka dinga yiwa junan su har abin dake a boye saida kowa yaji shi gare su.
Baba na kasuwa dole aka kirashi shi yazo ya kashe wanan wutar fitinar da ya ruru a gidan don gaba daya yaya Sani ya haukace masu a gidan.
Iyakarmu kallo da saure sai washe gari da baba ya kira sulhu da safe kuma suka so su dora laifin gun ummi na mai farin jini a gare su.
A nan ma yaya Sani baiyi shiru ba yace may ye laifin ta a ciki kudi dai ne har gobe ko kaya ita zanbawa a jiya ni babu ruwa na da zancen kishin ku.
Dole inna tana ji tana gani suka saka mashi ido don ya riga da ya kangare ba mai iya lankwasa shi a halin yanzu.
Idan ya shigo gida har da gaiyya yake jan ummi na da hira a cewan shi haushin mama yake ji don itace ke kulla duk wani makirci a gidan.
Ita ko Inna bata tsayawa saurare sai ta hau ta zauna a kai daga baya kuma mama ta zamay jikin ta ta nuna bada ita akayi zancen ba ta bar Inna a ciki.
Mu dai a gun mu har gobe gaba dayan su a yan uwa muka dauke su ba mu banbanta a tsakanin mu dukkan su a yan uwa muke daukan su.
Sai dai su a gun su ba wani canji a gare mu dasu har gobe halin yana nan na yan ubanci da suke nuna muna a gidan.
Mun zama su shanun ware ko bare da suke kyankyamin mu daga cikin su suna bakin ciki su bude ido su ga dan dakin mu na wani abin ci gaban rayuwa yanzu sheri zai tashi a tsakani sai anga bayan abin an durkusa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92Next page

Leave a Reply

Back to top button