BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

* *
Hai huwana da wata uku na dan fara ciwon kai sakuma yawan zazzabi da yake biyowa akai akai.
Ranan ina kwance yaya saadu ya bugo min waya na mike da kyat na dauki wayan tare da sallama yanayin murya na da yaji yasa yace baki da lafiya ne Safiya.
A hankali na bashi amsa da wallahi yaya kwanan nan duk kai da zazzabi ke yawan damu na na rasa gane kan jikin nawa.
Yace subbahanallahi kin kuwa je asibiti nace ban je asobiti ba ina dai shan magani a gida ne yana min sauki in na sha magani ai.
Yace No kije asibiti a duba lafiyan ki asan may ke damuwan ki yafi sauki da shan maganin nan da kike yi nace naji yaya zan tafi.
Mukai sallama yace dama ya bugo ne yaji lafiyana tunda suka koma bai samu kirana ba sai yau nayi hakkuri nace nagode kwara muka sallama yana kara jaddada min akan in tafi asibiti fa nace zan tafi ai.
Kwana biyu na ji sauki nikan na manta da zuwa asibitin da mukayi dashi naci gaba da harkokina kawai.
Kamar naji sauki da jikin zai tashi mun sai yakaini kwace kasa nai ta faman jiya a gida ina zuwa chemist ina karbo magani na dan ji sauki.
Ban san yaya akayi yaya saadu ya samu lanban yaya Sani ba ya buga mai yana cewa ya kirani wayana a kashe.
Sai yaya sani yake ce mai ai banda lafiya ne kwana biyu kila na kashe wayan ne .
Yace subbahanal lahi kon ka kaita asibiti andubata yace dashi a a ina ganin bataje asibiti ba yace da yaya sani don Allah akaini a dubani.
Shi zai turo da kudin zuwa asibitin haka ko akayi amma da yaya sani yai magana gida akace mai dahuwan kassa nakeyi tunda banyi ba da na haihu sai yanzu nakeyi.
Sunyi waya dashi yaya sani ke fada mai abinda akace ya matsa wa yaya sani aka ya kaini asibiti fa yanzu ba a wasa da ciwo gida.
Har na dan ji sauki kwana biyu kuma sai jikin nawa dawo fiye da farko dole muka kwasa sai asibiti.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:11 PM – Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , ,

????????2️⃣6️⃣????????

YAR UWA NOVEL DIN NA KUDI NE IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLESASE, , , , , , , , , ,

Mun yanki kati muka bi layin ganin likita a tare da sauran jamma a da muka samu a wurin.
Sannu sannu har layi ya kawo gare mu muka shiga wurin likitan bayan yan tambayoyi sai ya tura mu wurin yin test.
A can ma mun dan bata lokacin mu a wurin don mutane da sukai yawa masu son ai masu test din.
Mundan jira suka bamu sakamakon mu koma wurin likita dashi muna zaune a gaban likita dani da baban mu da yaya sani.
Munyi zaune shiru ya gama rubutun da zai yi ya dago kai yace baba wanan yar kace ?
Baba ya gyara zama yace kwarai kuwa yata ce wanan kuma wan ta, sai likitan ya sake tambaya tana da aure ?
Baba ya dan kara gyara zaman shi yace eh to ta dai taba auren yanzu wata hudu kenan da mijin ya sakota da ciki ta dawo gida wata uku kenan da ta haihu goyon ta koma.
Sai likitan ya girgiza kanshi alaman tausayawa gare ni ya sake tambayan baba yanzu ina mijin nata yake muna son ganin shi, shi mijin nata.
Baba yace ayya ai ba nan yake ba can Lagos yake da zama da iyayyen shi shiru likitan yayi yasa biro da yake rubutu a bakin shi kamar mai nazari.
Ya dago yace baba indan ba damuwa su fita waje muyi magana dakai sai baba yace ai ba damuwa likita duk diyana ne indan kaga wani matsala ne kafadi muji.
Sai likitan yai shiru can kuma ya dan dago kai ya kalli baba din yace a gaskiya ba yar ka tana dauke da cutan tsida mai karya garkuwan jikin dan adam.
Baba yace ban fahince kaba hawanjini komay kace likitan ya girgiza kai yace gwaji ya nuna muna tana dauke da cuta mai karya garkuwa jikin dan adam watau HIV.
Ban san lokacin da na yanka ihu ba baba yace ke may ye haka kuma daga bayani ki yanka muna ihu tashin hankali.
Likita yace tana da right din yin haka don ba karamin masifa bane ya samay ta.
Baba tace likita may kace yace ina nufin ciwon da ya samay ta yana da wuyan sha ani sai ya fara yiwa baba bayani yace.
Sai da ya kawo wiri aure ya ce mace na dauka ta mijin ta idan mijin ba mai tsayawa ga matar sa bane yana neman mata a waje shine dalili daya na tambaye ku mijin nata yana ina?
Da sai mu ga gwada shi mugani shike da ciwon ko ita anan zamu fahinci wanda ya sawa wani ciwon a cikin su.
Baba ya miki yace ke tashi muje kin ji ai ba nan kawai bane asibiti akwai wasu guraren zuwa bayan nan.
Da kyat na miki don duk illahirin jikina yai sanyi baba na ta faman fada niko tunane nake yi ko shiyasa yaya saadu ya matsa in je asibiti.
Yasan dan uwan shi nada ciwon ne yasa ya damu da zancen azo dani asibiti a duna dai aga may ke damuna ne.
Mun shiga gida ana fadin kun dawo baba ya na fada kaji min dan iskan likita kawai ka rasa abin dafa mata sai mugun ciwon da kowa ke guda.
Nan da nan aka firfito waje don saure inna ce tace may akace yana damun tane wai ?
Yace bar mugun liki wai wai Safiya na dauke da wani ciwo ko tsida ko may tace badai kanjamau ba yace wai shi .
Nan da nan Inna ta dafe gaban ta munshiga uku mun lalace a gidan nan muke zaune da mai kanjamau sai ya dakata fadan yana kallon inna din da ta rikice.
Yace ke kuma may nene duk kin bi kin wani rude dake ?
Tace malam kanjamau fa akace irin ciwon da ya kashe dan gidan malam sahabi kwana ki har akaki taba gawan sa.
Nan jikin baba ya fara sanyi yace don Allah ki bari ke ma kin yarda ke nan tana da wanan ciwon ?
Tace bani yarda tunda mijin ta karuwai ne abokan hurdan shi ko yaushe cikin su yake yana like a gidin su yaya bazan yarda da maganan likita ba.
Ummi na tasaka kuka mai tsuma zuciya mai sauren ta tana cewa na shiga uku na lalace yau ni Rabi may zan gani a rayauwa.
Tayi dakin ta tana kuka cikin dakin ta samay ni nima kukan nakeyi in cewa ummi yaya Ahmed ya cuci rayuwa na.
Ummina na mutuwa zanyi in barki in barki da yan uwana da kowa naki ni safiya na shiga uku.
Yar nan Ahmed bai cuce ki ba malam ya cuce ki shida ya bashike duk da yasan halin yaron ya kuma amince da ya hadaku.
Kuka muke yi nida ummi da kanne na adakin baji ba gani sai baba ya tsaya daga kofa yana cewa wai baku barin kukan nan ba a fa sheda cewa shine abinda ke damun ki ba kun aza ma mutane kuka haka a gida.
Dole mukai shiru irin yadda yake ta faman fada sai dai ummi bata tsagaita nata kukan ba da take yi gwanin van tausayi ance uwa uwace bakowa ke karba sunan ba.
Baba ta samu an tsagaita kukan ya kwantar masu da hankali dan kwana biyu ga damuwa ga ciwo naci na baba ya ki kwantar da hankali ya fahinci komai.
Wanan karon an jijigani sosai Yaya sani sukai waya da yaya saadu yana tambayan shi yaya jikin nawa ?
Ya fada mashi ina jin jiki anje asibiti ga abinda likita ya fada innalillahi yake maimaitawa yace dama ina tuhumar haka ya faru .
Don shima Ahmed din tun fitan Safiya baida cikakan lafiya tare dashi yace a kaiwa baba waya su yi magana.
Bayan ankai sun gaisa da baba yake cewa baba naji ance kun kai Safiya asibiti likita ya fadi abinda ke damun ta kun karyata.
Baba yace gaskiya ne haka akayi wani likitane mai mugun nufi ya zarga mata wanan sherin don kazafi irin na likitoci.
Yaya Saadu yace baba ka saurare ni kaji yace ina jinka yace don Allah don Allah kukai yarinyar nan asibiti ta karbi magani in ba so kuke mu rasata ba gaba daya.
Abinda likita ya fada ba karya bane haka ne don na dade ina zargin haka shi ya da ita don mijin ta ma nemin mata ne ga shan giya idan ya sha baya laakari da irin matan da yake hurda dasu.
Baba kukai ta asibiti a san abinda ake ciki su dora ta ga maganin da ya dace tasha tin bai mata nisa ba.
Baba yai mashi godiya sama sama sukai sallama ya dukar dakai yana kukan nadama ya cuce ni ya cuci mahaifiya ta dashi kan shi.
Tun wanan lokacin ya koma kamar baida lafiya a gidan washe gari ma bai tafi wurin bidan kudin shi ba.
Ina daki mun bana fitowa don da na fito yanzu kowa zai kama kan shi babu mai zama dani balle idan na taba abu wani ya taba.
Daga ni sai yan dakimu nake hurda kawai a gidan suma kamar ana kyanaman su din kamar ni.
Abinda yasa na fara ganewa yadda mama ta dauke kafanta ga sha,ani na agidan ba ruwanta dani yanzu.
Ba may son ace yana hurda dani kamar zan lika masu cutan a jikin su koda yaushe ina daki ga jikin ba dadi min.
Shi baba har lokacin bai yarda ba saidai nadama ya shige shi sosai na yadda yaba da ni ga dan gwago duk da yasan bana kwarai bane shi.
Ya dinga tuna irin badakalar da suka kwasa da ummi a gidan kan aure na , ashe tafishi gaskiya da ta nuna rashin yardan ta da aure.
Ashe mafalkin da tace tayi dani mara dadi nada na saba da abinda zai faru da nine gaskiya idan haka ne gwago taci amanan zumunci.
Ga ciwo ga saki ga haihuwa ba yar tazo a wani irin yanayi takoma ni ina zan kai alhakin wanan yarinyar a kaina.
Sai hawayen nadama da dana sani suka fara zubo mai yana fadin Safiya ni na cuce ki da kaina da na tursasa maki auren wanan yaro akan ki.
Kwana biyu baba yayi cikin wani irin yana yi ga ummi na kullun tana faman kuka a daki gwagon ma haka.
Kwana bakwai da faruwan wanan maganan sai ga yaya saadu ya dira garin da dare mun dai ji zuwan shi amma bai shigo ba don dare yayi lokacin.
Da safe ya shigo gidan ba wani taron arzikin da ya samu gun mutanen gidan mu sai a wurina da ummi na da bata gwada mashi komai ba.
Don ni nasan irin taimakon dayai wa rayuwa na a likacin da nake bukatan taimako ba kowa a kusa dani.
Ya gaisa dasu ya shigo har dakin mu ina kwance na mike da kyat da kwance da nake ina mashi sannu da zuwa.
Yace dani sannu Safiya ashe kuma haka abin ya kasance ban iya bashi amsa ba sai hawayen da ke zuba min a idon .
Ummina ma kukan takeyi yana share hawaye yace dani bari kuka Allah na sane dake safiya kowani mai rai da irin tashi jerabawan.
Allah yasa mu iya cinye jerabawan mu ummi tace dashi amin mun gode da kulawan ka gare mu yace nazo ne mu kaiki babban asibiti ki karbi magani da ya dace.
In Allah ya yarda zaki samu lafiya in dai kina shan magani Allah da yai cuta shi keda maganin sa.
Sai ga baba ya shigo dakin namu ya kalle ni yace sannu safiya yaya jikin na amsa dakyat da da sauki baba.
Daga inda yake tsaye hawaye ya fara zuba mishi yace haka Allah ya nufa dake zumunci nai wa suka ci amanan ki.
Yaya yace ayi hakkuri baba in Allah yaso zata samu lafiya indai tana shan magani ai yanzu an samu maganin cutar.
Yanzu baba asibitin birni zamu da ita inda zamu ji mafanin da ya dace a bata tana amfani da shi.
Ikon Allah kana ganin zata samu lafiya idan ana shan maganin yace kwarai kuwa don ai mutane da yawa na dashi amma saboda suna amfani da maganin ba a ganewa.
Yace a shirya ta sai in san da suwa zamu tafi mota na nan da nazo dashi dashi zamu tafi.
Abin mamaki da baba ya fita ya lalubo mama don tafiyan sai cewa tayi gaskiya bazata samu zuwa ba adaije da wani.
Muna jin ta daga dakin mu ina kuka ummi na kuka tace oh Allah mutum da ranshi ya koma abin gudu.
Yaya saadu yace babu komai mama insha Allahu zata samu lafiya tace baka san halin mutanen gidan nan ba.
Tun yanzu sin tsane mu sun tsagwamay ta kyama da tsoron mu suke ji wai zamu saka masu cuta mu halakasu.
Yace babu komai mama a dai bari ta fara sha maganin a gani suda kansu zasu daina ai sai dai ta kiyayye rezan da take amfani dashi kada ta bari jinin ta ya fita wani ya taba.
Da wanan masullan kitson naku na mata idan an kiyayye hakan ba abin da zai faru da kowa duk fadan mutane ne kawai amma banda haka ana mua mullar komai da mutum kamar kowa.
Tace kayya yarinya dai ai ta nakasa yanzu ba zancen aure a gare ta ke nan har abada ko samun zuria a gare ta.
Yace aa mama duk dai wanan a barshi har Allah ya bata lafiya yace mama ki shirya mu tafi dake kawai ina jin rikicin wanda zai tafi akeyi a waje da baba.
Mama ki rungumi yar ki kar ki yarda ki biyewa mutane ki kyamace ta sai kowa ya ji dadin kayamatar ta a gidan.
Ummi ta share hawaye tace babu komai ai idan na kyamace ta wa zai duba min ita ya riga da ya cuce ta yariyar nan ta bisa bakin ta da cewa baida tarbiya .
Amma malam ya rufe ido yaci muna mutunci a gidan nan har yana ikirarin korana a gidan.
Yazu da haka ya cika da ita wake wahala dani da ita a daki kawai ke wahala ba wanda ya damu da mu a gidan nan har da wa yanda ke zuga shi kan zancen.
Baba ne ya shigo rai a bace yace duk sun ce bazasu tafi ba sai ummi tace ni zan kai ta da kaina barin tashi na shirya.
Suka fita shida yaya saadu suka bar mu ummi na shirin tafiya sai ga gwagon ta ta shigo gidan nan ta samu ummi na shiri take fada mata abin dake faruwa a gidan.
Gwagon tace baki zuwa zauna ki fake yaran ki ni aiki may nake da sai kin je da kan ki kamar baki da kowa duniya.
Ta juya zuwa gida din ta shirya tai sallama da yan uwan ta bata dauki lokaci ba ta dawo dama yaya yana waje suna jiran a fito dani.
Ummi na da gwago suka tallaboni zuwa wajen mota duk yan gidan mu sun zubo muna ido wasu na ce muna sannu wasu kuma sai kallon tsoro suke min.
Mama ne take tambaya dawa zamu tafi gwago tace da ita za ai tafiyan sukai mata Allah ya bada lafiya.
Aka kamani na shiga mota na zauna da kyat gwago ta shiga suna tsatsaye suna kallon mu yaya sani yai magana da cewa
A a bada mama za a tafi bane gwago tace ai sun gama nasu ranan wuya sai naka ai sai kawai yace ina zuwa barin zo dani za a tafi.
Ya shiga gida da sauri sai gashi ya fito da shirin shi uwarshi na kwala mashi kira yace sai ta dawo zan raka safiya asibiti ne.
Nan tashiga da fada wai sai yaje an halaka shi ya mai she ta baya amma una baiji ba mota ya daga yaya saadu yaja babana yana gaba mu muna baya muka tafi.
Mun bar ummi da jin bakar magana a gidan mussanman inna da ke ta zage zage dan ta daya bi.
Har saida ummi ta gaji ta bata amsa tace ai itama ba saye tayi ba kuma ba qurin yawon banza ta kwaso shi ba.
Yanzu kuce haka amma lokacin da kuke zuga baba a kan auren baku nuna bacin rai ba sai yanzu da ta baci kowa ya zamau jikin shi ya na nuna mata kyama.
Allah da ya jarebeta dashi bai manta da ita ba yana sane da halin da take ciki kuma kowan ku bai wuce nan ba ai.
Sai mama tace Rabi bai kamata ki fadi haka ba kuwa yaya zamu kyamace ta ai mun san ba ita ta dorawa kanta ba.
Sun dai cuce ta kuma sai Allah ya saka mata don Rakiya da danta ba suyi ba wallahi abaku yarinya da lafiyan ta ku illanta yar mutane ko waiwaye babu.
Yadda sukai wa yarinyan nan sai ubangiji ya saka mata ummi tace ai ba Rakiya kawai da duk wanda ke da hannu a ciki ubangiji ba zai barshi ba da yarda Allah.
Mama ta shiga damuwa da maganan ummi ummi ta shiga daki tana kuka tabi ta tana bata hakkuri ummi tace wallahi ba zan taba yafe wa ba yaya.
Kiyi hakkuri Rabi komai da kika gani ya faru da bawa Allah na sane dashi ummi tace amna yaya ya dace yadda kuke kyamatar yarinyar nan abin har mu ya shafa.
Wanan maganan na ummi shi ya kawo laushi ga mama har ta tsawaci yayan ta a daki kan su daina guduna haka bai da kyau su kyale inna dama haka take son gani fa kowa a gida burin tane taga an koma baya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92Next page

Leave a Reply

Back to top button