BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

* * *
A can gida kuwa ummi da kanina shafiu sun rike sanaar da na bar masu dakyau don takar ina gari ne don yaron bai da wasa ko kadan.
Saadatu inna ta kwaso ciki tun ba a gane ba har mutanen gidan mu suka gane ana ta kumbiya kumbiyar zubarwa sai dai Saadatun taki ba Inna hadin kai a zubar da cikin tace tsoro take ji.
A wani dare basu san baba yana waje yana alwala ba rikici kan azubar da cikin ya hada ta da inna a dakin su tun bai sauraren su har takai baba ya saka kunne ga maganan su.
Nan yaji abinda ya tayar mashi da hankali ya koma dakin shi sai kuka koda gari ya waye bai fito ba har wani lokaci.
Mama ne ta shiga dakin shi don taga may ya samay shi ta samay shi a cikin wani hali take hankalin ta ya tashi.
Zata tara mashi jamma a yace taje dai ta kira mai inna da su ummi da yaya Sani su zo.
Kowa ya taru suna jiran suji may zai fada masu sai can yace ma mama yanzu har da ke ashe za a hada kai a cuta min gidan nan.
Abu na faruwa haka amma an rasa wanda zai iya fada min sai da Allah ya sanar dani jiya da dare nan ya kwashe abin da yaji tsakanin inna da Saadatu yake fada masu.
Nan Inna ta kama fadan karya wai baidai ji da kyau ba mama ne tace haba Rakiya ko makaho ya lalube saadatu ai yasan halin da take ciki.
Don baki samu bane shiyasa muka kawo ido muka saka maku kawai amma batu duk ya gama bin gari ai.
Shiru wurin yayi sai yaya Sani ne ya kawar da shirun da cewa Inna kin kai ga yadda kike so ba abin da baki fada akan matsalan Safiya agidan nan.
Yanzu gashi ke Allah ya nuna maki nashi isharan sai ku san yadda zakuyi da ciki ai maza basu son ta da aure amma suna son ta da lalata.
Baba yai magana karo na biyu yace ba mai zubar da cikin nan a gidan nan don bani kunya biyu abarshi ta haifi abinta kuma duk wanda yace zai yi yunkurin zubar da cikin nan sharia ce zata raba mu dashi.
Nan ko inna ta aza hannu akai wai dama ta sani baba bai kaunar ta da diyan ta ai yafi son yaga sun lalace a gidan.
Yace yadai ji amma ba mai zubar mai da ciki a gidan shi sai inna tace zata kaita wurin yan uwanta a wani kauye a zubar can.
Amma ba yace bai yarda ba da kuyan lahira ya kwmmace yai na lahira don zunubin shi bai kona shiba na yar shi ba zai kona shi ba.
Haka dai aka watse baram baram a wurin inna ta shige dakin ta tana kuka diyan ta ma suka bita kukan sukeyi suma.
Gidan dai ya koma masu ba dadi na kira ummi da safe don inji lafiyan su take fada min halin da ake ciki nan ko na tausaya masu sosai.
Ummi tace min abinta ne Allah ya mayar mata ta gani ko tafiyan nan ba abinda bata fada ba wai karuwanci kika je yi acan.
Yanzu gashi taga abinta har a kuryan dakin ta ta koma mujiya a gidan don ko fitowa bata son yi tsakar gida.
Abin su na kishi a yadda ummi ke magana sam bata tausaya ma inna da Saadatun ba sai nine nace ummi wanan abin fa ba inna kadai ya shafa ba har daku dake da diya a gidan.
Don suna gidan mu ne zai lalace ga banza sai ai muna bugun dan kadanya gaba dayan mu ba wai za a ware ta ita kadai bane a zaga.
Sai naji tayi lau shi tace abin tane ai da ban haushi wallahi nace hakkuri za a yi a rungumi kaddara tun da baba yace ba a taba cikin.
Nan dai na bata shawara nakuma ga ta dauka san nan mukai sallama na kashe wayan cike da jimay abunda naji din.
Banyi niyan kiran saadatun a yanzu ba sai hankali ya kwanta zan kirata in kwantar mata da hankali don nasan bayin ta bane sherin uwar ta ne Allah yake nuna mata abin ta tun a duniya.
Sai dai kwana biyu na shiga damuwa sosai har anty ta fahinci haka ranan ta kirani dakin ta dama nasan kira dakin ta magana ne na muhinmanci.
Nan ta shiga tsoratani da nasihohi iri iri na ban tsoro don ita tana zaton halin da nake ciki ne nasa damuwa akan shi.
Nan dai nace mata anty bashine ke damuna ba yar uwata ce ta shiga wani hali abin yake damuna arai.
Ba abin da zan iya boye mata yanzu sai na kwashe komai dake faruwa na fada mata sai da ta bari na gama fada mata komai sai tace dani.
Lallai Safiya kina da imani a zuciyar ki in bashi ba matar da take son taga bayanki zaki dauki damuwar ta ki saka a ranki karfa ki jawa kan ki wani sabon lalura gaki yarinya karama dake.
Addua zakiyi mata kawai shiya fi nace anty ban taba jin tsanar diyan Inna araina ba don itace maisa suke min abinda sukeyi din tace ai shi nace kiwa yar uwar ki addua Allah ya rabata lafiya don aikin gama ya gama ko.
Nai mata godiya zan fita tacevin dakata ledan dake gefen ta ta miko min nasa hannu biyu na karba ina godiya tace bani zaki godewa Sulaiman ne ya saya maku.
Yaji ina maganan saya maki waya yace in bari zai kawo maku waya yau ina office sai gashi dasu guda uku shi na zaba maki wanan farin ga sauran nan zan ba su faiza nasu ita da fati .
Nan shiga mashi godiya da addua ita ko sai dariya ta min tace ai wanan karamin aikin shine wallahi .
Ranan haka muka kwana da murna tare da mu kowa yana farin cikin rike babban waya a cikin mu wanda kudin shi zai iya kai dari da hamsi.
Ranan ina kwace falo saman doguwar kujera kasalance sanyi da iskan dake fitowa daga naoran sanyayya falon na barazanan saukar min da barcin marance.
Sai ga Fati ta fito falon daga dakin ta take cewa dani wai dama dakina zata ashe ina nan zama tayi gap da kaina tace .
Dama wani abu nake son kin min Safiya sai na dago ina kallon ta don jin may take so na dashi.
Ta dan nisa take cewa ba wani abu bane nake so sai ki dauko min lamban mutumi na a wayan anty idan kin samu hali don bata yarda in dauki wayan ta sam.
Ke naga kuna dasawa da ita don jiya naga ta baki wai ki tura abubuwa a cikin wayan ki.
Ban kai ga bata amsa ba sai muka ji sallaman shi a kofan falo ya karasa shigowa yana rike da brief case din shi tare da su yan biyu a bayan shi ga katuwan leda da ya riko a dayan hannun shi wanda nasan tsaraban su yan biyu ne a ciki.
Daga inda nake kwance mukayi arba dashi ban riga na kai ga tashi zaune ba.
Har suka karaso inda nake yaran suka fado min suna cewa yau uncle ya kaisu yawo birch sun ga ruwa da kifi .
Na yun kura na tashi zaune ina kamo dan kwalin kaina da ya zamay min don a kwance nake.
Ita ko Fati duk ta rude da ganin shi zuciyar ta ya rinka saka mata tunane daban daban ba gaira ba dalili na samu na kai zaune ina mashi sannu da zuwa.
Bai dago ya kalle ni ba sai dai a ranshi yana nasawa tabbas yarinyar kyakyawa ce mai cike da kwarjini da kamala ya fadi a zuciyar shi.
Sai naji Fati cikin rudewa tana cewa gashi ko anty ta fita har yanzu bata dawo ba kamar bai son magana naji ya bata amsa da tana tafe sunyi waya da ita ai.
Mikewa nayi zuwa kicthen na hado mai abin sha da ruwa na kawo mashi sai ga anty ta dawo har fati ta zauna tana mashi zuba a gaban shi.
Nan mukai mata sannu da dawowa nikan na bar wurin sai yaran suka biyu ni suna bani labarin fitan su da uncle din.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:12 PM – Ummi Tandama: BAHAGGON , , , , , ,
????????3️⃣4️⃣????????
YAR UWA NOVEL DIN NAN NA KUDI NE IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU DON BA A YAFE BA, , , ,
Anty ce ta shigo gida da karfe shidda na yammaci duk muna a falo zaune sannu da zuwa muke faman yima ta tana amsawa a gajiye takai saman kujara ta zauna tare da fadi wassh Allah yau na gaji sosai ga shi kuma gobe zan bi hanya da safe.
Gaba dayan mu maida mata hankali mukayi don jin ina zata tafi kuma da safe da tace din, mike kafa tayi saman dan stole din da ke gaban ta tana gyara zama take fadin .
Gobe tafiya zamuyi da uncle Sulaiman zuwa abuja zamu tafi muga wurin da yake son saya ya matsa sai baban su yan biyu yaje yaga wurin dani kafin ya saya.
Faiza ne tace ai hakan nada kyau mutum ya dinga sa ba gabatan shi gaba kafin yaya abu sai anty tace wanan ai halin Sulaiman ne.
Har sukaci suka sude ban saka masu baki ba ina daga kwance ina sauraren hiran tasu anan na dan fahinci wani abu a tsakanin su.
Tun da asuba ta shirya wai ashe ta jirgi zasuyi tafiyan bakwai yai masu a airport jirgin su bai dade ba ya daga zuwa abuja.
Muna gida zaune ni da faiza ita kuma fati tun tafiyan su ta fita daga sunan baza ta dade ba sai gashi har hudu na yamma yanzu.
Hudu ya gwauta sai gata hurjanjan ta shigo gidan bata ko kalle mu ba ta shige dakin ta Faiza ta kalle ta ta tabe baki.
Nidai na mayar da hankali ga tv don karamin aikin faiza ne yanzu ta dauko topic din fati aduniya taki jinin Fati da komai nata.
Itama fatin na kula da haka bata kaunar Faiza don takance min munafukace wai don haka zama a taka tsantsan ya kamani a cikin su sai bani yarda daya yayi da daya a bayan shi.
Ban jima ba a wurin na mike na shige daki da yan biyu don bada su aka tafi ba na zata kwana zasuyi sai gashi sun dawo da yamma .
Tana da gajiya don haka bata zauna da mu ba tayi dakin ta don sauke gajiya a jikinta lokacin ne fati ra samu daman shigowa dakina.
Ni sai da naji tsoro lokacin dana ganta tace ke matsoraciya nice na sauke ajiyan zuciya .
Nace may ke faruwa ne Fati na ganki da daren nan haka, ta dai ce uhumm kawai ba tare da tai magana ba takai zaune a wurin .
Tace aike dai baki sani ba yau naje wurin wani mai magani ne a wani kauye wani irin kallo nai mata na dafe kirjina nace maigani kuma ?
May kika tafi nema gun mai magani ko baki da lafiya ne ban sani ba sai naga ta girgiza kai tana cewa haba dai kamar ba mace kike ba .
Zuwa nayi a samo min kan madam din gida da kuma mutumin nawa gaba nane ya fadi ras taci gaba da yi min bayanin abinda ya kaita .
Ban iya karasa sauraren ta ba sakamakon fadawa tunanen danayi mai zurfi a raina nace tabas inda akwai abinda na tsana shine inga mace tana biyan bokaye da malamai a rayuwanta.
Balle fati da ko aure batayi ba ta fada wanan akidar sanan babu kunya babu tsoron Allah ko nauyi bata ji har tana fada min inda ta tafi da yadda akayi.
Wanan abin ba karamin tashin hankali bane musanman ma da tace takai har da anty gun mai magani to aima yar uwar nata may can.
Ida babu kuya babu tsoron Allah take fada muna yadda suka kwashe da boka a take na suma jin hawaye masu dumi na bin kuncina bata farga da hankan ba sai daga baya.
Maganan da tai min ne ya dawo dani hayaci na kallona take yi da wani irin mamaki baiyyane a fuskan ta ta ce dani Safiya may ke faruwa ne naga kina kuka daga ina baki labari.
Girgiza kai nayi cikin takaici nace Fati waya baki wanan shawaran na zuwa wurin boka at dis age da kike har kin san hanya bin bokaye.
Abin haushi da takaici kuma kirasa wacce zaki kai sai yar uwar haihuwar ki wace ta zamay maki uwa da uba ga komai naki.
May kike nema wanda wanan boyar Allah batai maki ba a rayuwan ki muma da ba uba daya muke ba may ta rage mu dashi a rayuwan mu.
Kafin in fadi wani abu sai ta katseni da cewa bafa wani abu nake so gare ta ba kawai yardan ta nake so ga bukata na akan sulaiman kawai.
Na girgiza kai har wanan lokacin fuskana yana dauke da guntun hawaye wani irin kallo nake binta da shi mai nuna tsanan abinda ta fada min.
Sai ta hau cewa ni fa yarda da amincewa yasa na fada maki da ace nasan ke ba yar hannu bace ga wanan harkan ba abinda zai kaini fada maki .
Nisawa nayi nace wallahi zan fada maki gaskiya tun wuri ki daina wanan halin tun bai zama maki jiki ba ko.
Ta mike tana cewa yau hiran namu dake ba zai yi ba do bani son mutum mai kara min zuciya akan abin da na saka gabana.
Tamike tare da nuna ni da yatsa tace i hope wanan maganan ya tsaya iya ni dake kawai a gidan nan idan naji shi a waje zamu samu matsala dani dake sai ta fice.
Kallon mamaki na rakata da shi ta buga min kofan daki garau ta fita na sauke ajiyan zuciya ina mamaki halin matan yanzu har da macen da batai aure ba ta iya zuwa gurin boka don kawai a asirirce mata yar uwar ta ina ga in ta samu kishiya kuma ?
Tun wanan lokacin mukai sanyi ni da Fati Faiza tayi tayi tasan may ya hada mu bamu kaman da amma naki fada mata sai ce mata nake yi kila ta samu wata kawar ne a waje.
Yanzu anty bata faye zama a gida ba suna aiki sosai a wurin aikin su don haka sai kula da gidan ya dawo hannun mu.
Duk da dai sauran ba wani abu sukeyi ba sai ni da mai aiki zamu aiwatar da komai kafin masu gidab su dawo Faiza irin mutanen ne masu fuska biyu.
Amma bayan haka ta na da kirki sosai amma sai na fahinci akwaita da aikin ganin ido abinda bata sani komai da muke a gidan yana kunnen anty.
Ta san yadda kowa ke rayuwan shi a gidan ido kawai ta saka muna tana kallon kowa da halin sa ranan da rana anty tai muna dawowan bazata a gidan .
Ina daga ni sai mai aiki dake wankin kayan ta nikuma ina muna girki da zamuci ga yaran ta zaune suna kallo a falo na dafa masu indomie kafin an gama hada abincin gida.
Su ko faiza tana barci a dakin ta tayi dadaya a saman gadon ta Fati kuma ta fita yawan ta sai in yai mata dadi kafin yar ta dawo aiki take dawowa gida.
Tana shigowa ta samu yaran na cin abincin da na aje masu suke ci take tambayan su suka ce anty safiya ne ta dafa muna.
Jin motsi yasani fitowa ina yarfe ruwan da na daureye hannu a hankali naga itace ashe ta dawo nake mata sannu da zuwa.
Tace sannu da aiki safiya shiya yanzu sai in fita gidan nan hankalina kwace ba tare da fargaban wani abu ba ga yaran nan dako ban da kwanciya hankali idan na barsu a gida don kamar ban barsu da kowa bane saboda basu samun kulawa yadda ya dace..
Har na gama girki na kawo ma anty nata sai mai aiki ta shigo ta samay ta a zaune falo ta fara gaisheta da dawowa.
Tace yanzu na gane zuwan safiya gidan nan yai maki dadi don duk kin tatara aiki kin bar matayi daidai ina kawowa anty ruwan sha naji tana fadin haka sai nace a a anty tare, , , ,
Hannu ta daga mi alaman in shiru naja bakina naci gaba da jera mata abincin tana may ci gaba da fadan da takewa funke mai aikin ta.
Sai ga Fati ta dawo nan tabita da harara simi simi ta shigo tana kamay kamay fada tai mata sosai ranan har ni din bata bari ba.
Bayan kamar kwana hudu dayin haka kowa a cikin mu ya shiga taitayin shi don gudun laife gare ta daga ni sai Faiza dake charting a wayan ta.
Sai gata ta shigo gidan sun dawo unguwa da yaran zaune nake zugun nayi tagumi nayi zurfi acikin tunanen duniya.
Sai muryan ta naji daga sama a kaina tana fadin Safiya wallahi zamu bata dake a gidan nan matukar baki daina damun rayuwanki da tune tunen marasa tushe ba ke kadai ke gidan nan ne da kika kasa sake ranki cikin yan uwa kiyi walwala.
Na dago kai da sauri ina kallon ta a lokacin ya shigo da kaya niki niki da suka sayo ashe tare dashi suka fita unguwan .
Nisawa nayi ina mata sannu da zuwa sai dai bata amsa ba sai ci gaba da fadan da takeyi min kamar ba magana yake yi ba don hausa shi da baya fita da kyau yace.
Bata da lafiya ne ko may ke damun ta haka din ?
May kuwa uncle na rasa gane hankalin yarinyar nan tun da tazo gidan nan taki ta sake jikin ta kamar kowa sai zama tana yawan tunanen banza da wofi ita kadai.
Zaune yakai saman kujeran da fuskantar mu tare da aje kayan da suka shigo dashi din tace kamar wanan yarinyar da bata wuce 19 years ba zata saka ma kanta tune haka.
Jinayi yace keko may yasa kike haka din tunda antyn ki bata son yadda take ganin ki ba kamar kowa ba a gidan yana magana yana kallo na .
Yaci gaba da cewa don Allah ki kwantar da hankalin ki ki daina damun kanki koma may ye a ranki ki fitar dashi don tunane yana iya kawo maki illa a lafiyar ki.
Ya maida kallon shi ga anty yace bata dade da zuwa nan din bane ko may ko gida take tunane haka ?
Tsaki tayi tace wani irin dadewa kuma ai duk ta rigasu zuwa nan halintane hakana din kawai dason shiga damuwa.
Shi ya kawar da maganan da dauko maganan bude gidan shi da suke shirin yi yace sai in an gama tsarawa zai zo mata da yadda akayi ya mike yana shirin wucewa sai lokacin tace dashi ba zaka tsaya ta hada maka fruit din ba.
Yace no barshi kawai zan tafi don naga mai hadawan bata cikin hayacin ta mikewa nayi da sauri nace barin hada zan iya ai.
Ban dauki lokaci ba na hado mai nakawo yace dashi zai tafi don baida lokacin tsayawa yasha a nan din, har waje suka fita da anty sun dade sai gata ta dawo ciki.
Lokacin muna zaune da diyan ta da Faiza tace in bude ledan da suka shigo dashi gidan in fitar da kayan dake ciki.
Nan Faiza ta tayani fitarwa muka fitar da kayan wanda yawanci duk na twins din tane tufafi da kayan makulashen yara tace mu diba in kai saura dakin su.
Bata barni haka ba dana dawo na zauna sai da ta bini da nasiha kan in cire damuwa a raina Faiza ke cewa ta rasa may nake wa yawan tunane hakana.
Ba laifi nayi korin ganin na fitar da komai a raina sai dai ba abinda zan iya fitarwa kai tsaye bane yadda take nufi amma na dan rage yawan sa ma kaina damuwan da nakeyi din.
Mako biyu tsakani ranan muna zaune dukkan a falo sai ga ta ta sauko daga sama ta zauna take cewa Fati ta shirya mata kayan su yan biyu zata Abuja gobe tafiya ya kamata.
Sai ta juya gareni tana cewa ke ma Safiya ki shirya don dake zan tafi saboda yaran nan ba zasu barni ba inyi abinda ya kaimu da sauri Fati tace anty nima in shirya ina sin zuwa Abuja wallahi.
Tace da Safiya zan tafi ko ita don yara zan tafi da ita Sulaiman zai yi bukin bude company a can da gidan da ya saya a take fati ta shiga rokon ta wai taje da ita.
Tace karatun ki fa fati kina fa wasa da karatu gashi kun kusa rubuta jerabawan fita ke bakiyi ma kanki fada ne wai kamarki har yanzu a secondry school ?
Nan ta turo baki gaba tana fadin na dai gane kin fi son safiya damu a gidan nan komai sai kice safiya ita kadai.
Tace dole ne in ce safiya don tafiku hankali da tunanen abinda ya kamata ko ruwa kuna iya ba mutum ne in ba ya kama maku dole ba.
Faiza ma ta marairaice mata saida tace duk su shirya mu tafi tare sannan aka samu lafiya don da Fati ta hau sosai ga maganan.
Kowa ya shiga shirin tafiya don tace sako zamuyi mu tafi kala uku kawai na dauka koshi dogayen riguna ne kawai na zaba.
Tun da safe muka kama hanyan abuja a mota mukai tafiyan don mijin ta baya nan suna ruwa wurin aikin shi basu fitowa sai bayan watanni a ruwan shiyasa ma bai faye zama a gidan ba.
Gidan su na abuja muka sauka wanda shi mijin tane wai yake dashi don harda funke mukayi tafiyan bamu bar kowa a gida ba.
Gidane mai dauke da dakuna hudu da falo daya na maigidan inda ta zauna a ciki sai dayan wanda fati da Faiza zasu zauna ni da yara tace mu shiga guda sai mu bar ma funke na farin shigowa wanda dama saboda masu aiki akayi shi.
Ba wani hira don kowa na da gajiya tare dashi wanka kawai mukayi sai abincin da aka kawo muna daga wani gidan abinci ina jin Faiza da fati na ta santin abincin don dadin shi niko takura bai bari naci sosai ba don na lura dukkan su biyu kamar yanzu sun tsane ni a gidan don yawan nuna mani kulan da maigidan namu takeyi ko a gaban kowa.
Na riga kowa shigewa ashe sulaiman din yazo gidan bayan na shiga barci nan Fati ta kama rawan kai saida anty ta tura ta ciki ta basu wuri.
Washe gari tun da safe da ta fita bata dawo ba sai wurare karfe hudu ta dawo gidan nan ma bata huta ba don wasu suka zo suna tsarare dasu.
Har na kwanta sai ga anty dakin na mu hannuta rike da tasbaha tana ja shiyasa nake son ta don wayen wata da tsabgogin gabanta bai hanata yin ibadan ta sam.
Mikewa nayi zaune daga kwanciyan da nake ta kalle ni tace wai ko kin dauko kayan kwarai kuwa Safiya don taro ne na masu hannu da shuni za a yi.
Nace anty na dauko wanan riga ne da kika sayo muna ranan na fadi tare da kallon ta don jin may zata fada gamay da shi.
Cike da tsukana tace min Safiya ai da kin tona min asiri a cikin taro da sai in nuna ba tare dani kike ba a wurin kawai kisa mutane su raina min da wayo ?
Dariya nayi itama abin ya bata dariya don jin nace anty wanan riga mai balain kyau.
Tace kin ga ni yanzu ma fita nazo kirakani muyi dama nayi tunanen hakan ki shirya ina fitowa yanzu zamu fita da faiza ba zan je da wanan mai rawan kan tsiya ba ta bani kunya.
Ashe harta fada ma Faiza ko koda na fito faiza na falo zaune tana kallo hijjab da dogon riga nasa ta kalleni ta wani kwashe da dariya .
Sai kuma tace min mutumiyar na ciki tana fushi wai za a fita damu bada itaba kafin in magana sai ga ta tafito tana saka ma kofa key tare da kiran Funke tana cewa ta kula mata da yara da sukai barci tun da magariba.
Na muka fita tare da rufo kofan gidan mukai ma Funke sai mun dawo wata mota baka muka samu waje a kunne yana jiran fitowan mu.
Baya muka zauna inda sai wani kamshi da ban taba ji ba ya daki hancina ga sanyi AC mota suka hade suna bada wani irin yanayi a motar, ita ta zauna gaba tare da driver muka kama hanya fita daga gidan kallon titi nakeyi inda naji Faiza tace ina wuni yaya Sulaiman .
Sai lokacin na dawo daga tunanena nace dashi ina wuni ya amsa muna a tare lokaci guda anty ke ta hira sai eh ko aa yake ce mata.
Tafiya mukayi mai nisa sai gamu bakin wani shago maigirma anan muka firfito inda muka barshi a cikin motar zaune muka fara shiga mu da anty.