BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:12 PM – Ummi Tandama: BAHAGGO, , , , , , ,
????????3️⃣9️⃣????????
INA MAKU FATAN ALHERI ACIKIN WANNAN TAKIN DA MUKA SHIGA UBANGIJI ALLAH YASA MU DACE DA RAHAMOMISA AMIN YA ALLAH YAR UWA, , , , , , ,
Har ya juya ya tafi motar shi ta fita get din gidan tana tsaye tana daga mashi hannu tana murmushi a fuskan ta ta sauke ajiyan zuciya ta juya zuwa cikin gida.
Still su Faiza na falon ta shiga tana fadin aaah lafiya baku ga lokacin sallah yayi bane kuna zaune kuna kallo .
Nan suka bata rai sai anty tace may nene haka wai ina kuma safiyan ta shiga kuma bata zuwa ta dauke kayan nan a nan tashiga da su .
Faiza ce tai karfin halin fadin baza a bude muga abinda aka sayo ba shi muke jira mu watse dama wani kallon banza anty tai mata har ya sata natsuwa .
Tace don Allah baku jin kunyan hakan da kuke yarinyar nan bata saka maku ido amma ku kokarin ganin kwakwaf dinta kike yi ko yaushe.
Dan malama taya ni kwashe kayan nan mukai mata ciki kafin mu watse haka nan cikin bacin rai suka taya ta daukan kayan zuwa daki na sun shiga ga dakin tas sai kamshi ke tashi na gyara gado kamar wadda keda mijin aure a dakin.
Ina bandaki koda suka shigo sai maganan anty naji tana cewa ga kayan ki nan mun shigo maki dashi kafin fito ta face daga dakin don haka na tsaya nayi alwala nai sallah.
Sai da na idar da sallah duk suna falo sun fito na dauko kayan zuwa wurin anty da su buda tashiga yi tana yabawa da kyan abubuwan tace wanan irin kyauta haka Safiya ?
Na dan marairaici nace wallahi anty ni har abin yaban tsoro don haka yau ta diban kayan duk abinda yai mashi dadi a rai.
Wani irin dariya ta kwashe dashi tace ina ruwan sabon shiga dake dashi yanzu duk kun zama kamar yan koyo Faiza ce ta dakatar da duban wani ruba da ta dauka tana dubawa don bata san ko may ye a ciki ba.
Tai saurin aje roban a hannun ta tana kallon anty gami da cewa ko dai da walaki ne wanan sayayyan haka nikan nayi mamaki haka kawai zikau mutum zai yi hidama haka.
Ashe zamu sha buki kenan ta fada a cikin gatse wa mu biyun duka sai anty tace inda rai da lafiya mun kusa cassawa.
Tsukin da Fati taje ne ya katse hiranda faiza da anty keyi kan kaya tamike but ta shige tana ambatan munafunci shi kadai na iya ji cikin maganan ta.
Bayan shigewan tane anty tace wawiya kawai mara hankali don rashin wayyo wai ke ke gwada ma namiji kina son shi baza ki jira ya furta maki ba da bakin shi.
Sai faiza tace wanan shi ne son maso wani anty ta karasa da koshin wahala ba tana daki tana hauka shi hankalin shi na inda yake so.
Ashe bata karasa shiga ba tana jin duk abinda suke fadi sai dai bata ga bakin su sai ni da banyi magana ba taji haushi na.
Wai dama mu yan kyauye mun iya shige da fice wurin kwantan maza an raba kayan bayan anty ta fitar min da masu amfani naci din ne kawai tace a raba.
Bayan na koma daki wayana dake cikin jakkata yai kara da sauri najawo jakar ina daukan wayan wani irin firgita nayi don ganin kudi a jakar nawa.
Har wayan ya katse ban samu dauka ba don kudin ya firgitani kara waya ya kara yi sai na dauka a firgice ina sauke ajiyan zuciya.
Ummi na ce muka gaisa da ita na tambayi mutanen gida take cewa kowa lafiya sai dai mahaifin ki ne baiji dadi ba kwanan nan.
A firgice nake tambayan abinda ya samay shi take cewa dai je asibiti an bashi magani amma bin sai gaba yake yi kuma.
Na dauki salati nace ummi zan zo ko gobe ko zuwa jibi in Allah ya yarda mukai sallama hankali na bai kwanta ba ga zancen kudi ga maganan baba da ya tsaya min a rai.
Don haka na kasa bari sai da safe na saka hijjab a firgice tare da daukan kudin da wasu kaya daga cikin na dazun na hari dakin anty din.
Nayi sa a tana dakin bata nufi dakin daddy ba lokacin tana gani na ta mayar da hankalinta gare ni tare da fadin Safiya lafiya kuwa.
Karasawa nayi bakin gadon ta na zube kasa sai ta mayar da hankalinta gare ni na fitar da kudin ina mika mata nace anty yanzu nagan su a cikin jakkata ba san da su ba kuma.
Murmushi tayi ta karbi kudin a hannuna tana dan juya kudin tare da yi murmushi tace wa zai saka maki in ba Sulaiman ba don yasan in ya baki ba karba zakiyi ba don ya fada min kin ki ki saki jiki ku fahinci juna .
Dukar da kai nayi kasa ina tunanen yaushe ya zuba min su ban sani ba to wai ma ni ina zan kai wanan kudin haka masu uban yawa.
Ita ce ta katse ni da cewa indan kina tambaba ne bari yanzu in kirshi muji sai ta shi ga lalavan wayan ta dake bayan ta, alokacin nake fada mata cewa mun yi waya da ummi yanzu take fada min jikin baba ba dadi .
Sun je asibiti wai amma abin bai ja baya ba na karasa fadin ina son inje gida anty don in ga halin da yake ciki.
Ashe har ya dauki wayan ban sani ba yaji may nake fadi yake cewa tare kuke da mutumiyar ke nan tace eh wallahi gata nan tazo min a firgice wai taga kudi a cikin jakkanta.
Murmushi yayi yace rabon ta ne ya shiga jakkan ta kila tace ai dama nasan aikin kane amma dai ka ruda min kauna ka sani.
Dariya yayi yace ina son ta saba da halina ne tun yanzu idan zan ba mutum abu bana bashi ya sani sai baya na.
Tace kabi mun kauna a sannu ko muce mun fasa kaje gaba ka samu daidai da kai yace tuba nake babban yaya kin san kaunar taki sai a hankali.
Nan take fada mai zancen mahaifina da nazo mata dashi ya kama fadin subbahanallahi yazu yaya ke nan tace wallahi fa daddy nake son ya shigo musan yaya za a yi don tace zata tafi.
Yace OK kuyi magana dashi muji yaya za a tsara mata tafiyan don ba abin da za a tsaya bane wasa saboda ba a san halin da yake ciki ba.
Nan dai su kai sallama ta kashe wayan tare da mayar da kallon ta a kaina tana fadin dama yakanyi ciwo haka ne na girgiza kai tare da fadin gaskiya bai taba yin haka ba sai wanan karon.
Turo kofan da akayi ne muka mayar da hankalin mu ga may shigowa daddy ne yace a a kuna meeting ne haka komay ?
Tace dashi uhumm wallahi mahaifin ta ne aka bugo waya yanzu baida lafiya shi ka gan mu haka.
Subbahanallahi shi ma ya ambata yana cewa tunda suka bugo jikin ya matsa mashi ke nan kwarai tace ai itama maganan da takeyi yanzu ke nan hankalin ta ya koma can.
Yace dolle ne amm yazu dai abari zuwa safe sai inga yadda ya dace ayi ta tafi har ya juya zai fita daga dakin sai ya juyo yace shi sulaiman din yasan da zancen ?
Koda yake ma baridai zan sam abin yi akai adai bari har Allah ya kaimu gobe din tukun na ya fice daga dakin ta dawo da hankalin ta gare ni.
Tace yanzu dai ki kwantar da hankalin ki sai da safe din in Allah ya kai mu jeki ki kwanta har da safe.
Haka na mike gwiwa na yayi sanyi nace sai da safe anty tace Allah ya tashe mu lafiya ki dai kwantar da hankalin ki kinji na fada maki.
Nace tau anty na gode na fice tare da rufo mata kofan dakin ta bini da kallon tausayawa gare ni ta sauke ajiyan zuciya.
Tun da na tun karo dakin na fahinci an shiga min dakin na karasa shiga aiko nan naga kayana a hargitse alaman an tone min kaya ana neman abu.
Bandai san may aka dauka ba na gyara kayan tare da hayewa gado ina ci gaba da tunane a raina dole ne baba yai ciwo abu yai mashi yawa a zuciya yanzu.
Ga nawa matsalan ga na Saadatu sanan kuma ga na gida mazan gidan mu duk ba wanda ya mayar da kan shi abin kwarai.
Dole abu yai mai yawa a zuciya tausayin halin da gidan mu ke ciki ya kamani na kalli kayan da sulaiman ya kashe min kudi a kan su nace a raina ai wanan da kudin ya bani na sai wa yan gidan mu abinci dashi zai kai su har tsawon wani lokaci suna ci.
A haka har barci ya dauke ni sai asuba na falka na yi sallah ina idarwa kuwa na kira ummi ina tambayan ta yaya suka kwana.
Tace gaskiya kan jiya ba ai barci dashi da dadi ba yanzu ma yaya Sani yashigo yana shirin su koma dashi asibiti.
Nace a bashi waya mu gaisa in ji may ake ciki yake fada min wallahi kan baba yana jin jiki yanzu asibitin zasu koma.
Babu kudi da asibitin birni zasu tafi dashi aje can a duba shi a san may yake damun shi nace yaya ko yanzu can zaku tafi.
A ari kudi ko nawa ne idan nazo zan biya yace ai an nema ba asamu aro ba sai nace yaba ummi wayan muyi magana da ita.
Ya bata wayan nake ce wa tabada kudin da zasu sarin kaya tace jiya suka saro kaya dasu nace a je wurin gwagon ta duk inda zasu samo kudi a samu kafin in zo.
A haka muka rabu sunje sun samu kudi kudin dan gidan mama ne kaunar ummi na sadakin shi aka ara nace ba matsala insha Allahu idan nazo zan biya.
Ban fito ba yadda na saba sai ga anty dakin a lokacin nayi kuka idona yai ja ta zauna a kusa dani tana cewa kuka kikayi ne Safiya.
Na dukar da kai ina zubar da hawaye nace anty jikin na baba ya matsa mai jiya wai basuyi barci ba dashi.
Subbahanallahi suko sai su zauna da mutum gida haka yana jin jiki ba zasu kaishi asibiti sai su zura mai ido.
A sanyayye nace da ita wai ba kudin da zasu kai shi asibitin ne suka ce ikon Allah toh Allah ya sauwaka.
Yanzu dai ina gani sulaiman zaki bi yau ku bi jirgi idan kun isa Abuja sai ya saka ki mota da za a kai ki gida yau zasu tafi da shi da daddy can.
Jin tace da daddy zamu tafi yasa hankalina kwanci don da zance mata ta bari in tafi a mota yafi don gudun zargi amma jin da daddy zamu tafi sai hankali na ya dan kwanta.
Yanzu dai ki tashi ki shirya zan fita inga abinda ya dace ayi kafin ki wuce ta fita nikuma na tashi na shiga shirin tafiya.
Su faiza basu san da zancen tafiyana ba sai da na fito don daddy yace ace na fito shine suke tambaya anty ke fada masu mahaifina ne baida lafiya.
Fati tace shine kawai zata bi daddy da uncle don mahaifinta baida lafiya sai dai inda wata manufa zata tafi.
Da sauri anty tace may kike nufi ko may kika mayar damu ne kina nufin mu din mutanen banza ne komay ?
Shiru tayi don maganan itama haka yazo mata nan yar nata tai mata tas sai da ta raina kan ta Faiza cewa tayi zata rakani.
Anty tace da ita kema kin san yayan ki ba zai yarda ba ki tafi kar ma ki dauko wa kan ki wani magana a na zaune kalau.
Haka muka shirya muka fito motan daddy muka shiga zuwa airport din inda anty tai muna rakiya ita da Faiza .
Acan muka samu sulaiman nan sukai shige da fice har aka kira mu tafiya ya tashi ban san lokacin da kuka yazo min ba.
Anty tace dani a a kukan may kuma safiya kamar wacce ta tafi ke nan ashe akwai aiki randa zaki tafi gidan mijin ki.
Daddy yana muna sheri haka na barsu don anty itama ta karaya da kukan da taga ina yi din har sai da jirgin mu ya daga suka koma gida.
A jirgin kujeran su daya da daddy inda na samu wata mace tana da yawan surutu don har muka kawo hira take min a inda take ce min wai tazo ganin mahaifan ta ne a lagos.
Abuja take zaune ita da mijin ta sai dai mijin nata bayerabe ne ita kuma uwarta bayeraba ubanta bauhaushe.
Yaran ta biyu yanzu take tambayana ni a lagos nake zaune nake bata amsa da a wurin anty nake zaune zanje gida ne mahaifina baida lafiya.
Ta tausaya min har ta karbi lambana tace inda mun sauka zata kirani taji lafiyan mahaifin nawa.
Mun sauka duk a tsorace nake don ban taba ko ganin jirgi ba balle in shiga sai gani yau a cikin sa kuma mun sauka lafiya da kudirin ubangiji.
Mota yazo ya dauke mu muka tafi gidan daddy bamu dade ba suka fice suka barni ina zaune tunane ya cika min zuciya zuwa .
Zuwa sha biyu da rabi sai gasu sun dawo gidan sai dai sulaiman ne kawai bai ko son kallo na sosai ya zauna a kujeran yana fuskantana.
Yace sorry ko yanzu dai ki fara isa ga mota nan za a kaiki har gida sai kudi da zan baki ki yi duk yadda ya dace ayi.
Naso mutafi tare amma hakan ba zai yuyu ba don wasu yan matsalolin da nake dashi ki tabbatar anyi masa abinda ya dace dashi don Allah kudi ba matsala bane duk yadda ake ciki sai ki buggo min.
Nace a hankali na gode sai dai akwai kudi a hannu na don wanda ka bani anty ta bani kuma ta kara min wasu.
Yace bana son gardama kin san abunda zaki sama a can ne ya mike yana cewa ki kula da kanki kuma ai mashi duk abinda ya dace don Allah in akwai wani matsala a bugo min in sani .
Ki fito mota na jiranki a waje ku tafi daddy yace in maki sallama aiki ya rike shi bazai samu zuwa kuyi sallama ba.
Ban san lokacin da nakai har kasa ina mashi godiya irin wanan harcin da yai min ba dan haduwan mu dashi haka.
Murmushi yayi yace haba haba ba komai ki dai kula da kanki sai yai gaba na tashi a sanyayye nabi bayan shi.
A waje naga wata mota da driver naji yana cewa driver indan dare yai mashi goben in ban gama ba zai iya kwana ya bude min na shiga ina mashi godiya.
Muka wuce yana daga muna hannu sai lokacin na sauke ajiyan zuciya ina mika godiyana ga Allah da wanan baiwan da yai min dan lokaci guda.
Motar mu ta halba saman titi ina ta kallon yanayin garin zuciya fam da tunane kala kala muka nausa ga tafiya.