BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:12 PM – Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , ,

????????4️⃣1️⃣????????

Ummi ta nisa bayan ta gama sauraren magana na tana cewa dani anya yar nan baki iya tsaga fadi ba wanan mutumin bai fi karfin mu ba.
Na ce ummi nima abinda nake tunane kenan amma ita anty bata son ina fadin haka din tace yanzun dai ki dan kara nazari kafin ki kai ga gabatar dashi nan din.
Fadan inna da mukaji shiya dakatar damu daga maganan da mukeyi din da muka saurara muka fahinci da saadatu ne take fadan akan daura gidan sauron da muka sayo.
Fada sosai suke yi a tsakanin su nice na fito nayi wa saadatu magana sai take cewa wai inna tace bata yarda ta daura gidan sauron ba a dakin ta.
Nace haba inna tana da wani daki yanzu a gidan nan bayan naki don Allah ki yi hakkuri kibarta ta daura daidai inda take kwanci.
Nayi dana sanin fitowa raba fadan nan tsakanin inna da diyar ta don abin karshe a kaina ya dawo babu irin kazafin da inna bataimun ba ranan kowa najin ta a gari.
Dole naja kafana na koma dakin mu bisa umurnin mama har lokacin bata daina fadan da take yi ba ta hade mu ta zage tas tana cewa sai dai yawon banza amma badai aure ba gare ni.
Naje nayi fasikanci na nadawo ina wa mutane sallo sai inyi wa wa yanda basu san abinda nake yi ba .
Ummi tace da na hanaki fita zakiga kamar ban son zaman lafiya ne ai gashi kin jawo wa kanki kwana da bakin ciki a ran ki.
Nidai shirin kwanciya nake yi ina kara jimamay maganan Inna datake yawan fada min a koda yau she magana ya hada ta damu.
Ya zama min dole in yarda da bukatar Sulaiman akaina kamar yadda yace bai son abin ya dauki lokaci don shi yanzu bai ga abinda zamu tsaya jira ba .
Magana ummi keyi dani amma banji ba nayi nisa sai da ta kara daga murya na ji ta nai saurin cewa ummi kanin mijin anty na ne.
Kuma su suka hada ni dashi don shima irin matsalar mu guda dashi aure yayi matar ta rufe mai tana da lalura sai da akayi abin ya bayana mata.
Bacin rai yasa ya rabu da ita duka duka watan su shidda da aure suka rabu da ita tace amma ko bai kamata ya sake ta ba tunda ya dai riga da ya kamu da ciwon.
Nace ai nima abinda nagani ke nan amma sai anty tace dani dama ba sonta yakeyi ba itace ta like mashi.
Yanzu ke baki ganin akwai matsala idan kika bashi baki akan ya fito nifa ina tsoron masu kudin nan don da wuya suke rikon aure.
Nace ummi duk wanan tunanen nayi shi kuma na fada ma anty amma sai cewa tayi nasan dai ba zata kaini inda za a cuce ni ba kin ga banda ta cewa don darajan ta a gare ni.
Amma dai ni sanin da nai mai baida wani matsala rayuwa sai dai ba a san abinda ke boye ba kwai ne.
Tace yanzu dai kafin ki koma sai ki shirya kije can gida ki ga baba da yaya Adamu ki fada masu in ma mallam ya yarda sai mu tafi tare dake mu gan su.
Nace to ummi hakan ya kamata ayi nima dai hankali na bai gama kwatawa ba dashi amma babu yadda zanyi ne kawai sai ya zama kamar na watsa ma anty kasa a ido bisa kokarin da takeyi dani.
Haka na muka kwanta kowa da tunanen da yake yi a zuciyar shi sai asuba muka tashi bayan nayi sallah na fito na share gidan na tara kwanonin da akai amfani dasu.
Ina cikin wanke wanke ne na kusa gamawa sai ga inna ta fito sai cewa tayi dama ko acan abinda ke yi ke nan anzo nan za ai muna barkadon banza.
Nace inna ina kwana bata amsa min ba ta shiga daki sai gata tafito da kwanoni masu yawa ta zube min su ashe mama na daga kofan ta tana kallon mu.
Inna ta wuce tana maganganun ta sai mama tace kai wanan balain da may yai kama don Allah ba a barin mutane suji da abinda ya damay su sai bakin fitina tun da farin safiya haka.
Wa na hana yadda yake so a gidan nan idan kuma kin saka kan ki ne sai a sayar maki ba abune mai wuya ba ehhy.
Mama tace in ma zaki iya nan da shekara sai ki tayi bama sayar ba ko kwasa ne sai ki yi gaki ga wuri ai.
Wanan abu damay yai kama kin kwana fitina kin tashi dashi duk yarinyar nan bata kula ki ba ba sai kiba kanki lafiya ba wanan ai zubar da mutunci ne gare ki.
Nan dai sukai dan cacan baki tsakanin su ba wanda ya kula ta ni dai na gama na shige dakina na barsu nan.
Wanka na fito nayi ina cikin gyara jikina sai ga Saadatu ta shigo dakin ummi din ta samay ni muka gaisa.
Nake tambayan ta yaya jikin ta sai tai murmushi tace jiya na samu barci sosai wallahi Safiya na gode kwarai wallahi banda abinda zan fada maki sai dai kuma kiyi hakkuri da halin inna don Allah.
Na yi murmushi nace ai inna uwane fadan su gare mu taki wata rana zai muna amfani a gare mu dariya ta dan yi tace kayya ke dai kiyi hakkuri kawai.
Muna nan muna dan hira sai jin muryan inna mukayi tana kwala ma saadatu kira share uwar tayi kamar bata jita ba.
Sai da ta kara kiranta tace tana zuwa ta ci gaba da maganan ta sai da nace taje taji kiran da inna ke mata ta dawo.
Bayan fitan ta ne na ci gaba da shiri na nace ma ummi gidan gwagon ta zan tafi in gaida ita tace dani aiko kin kyauta.
Nace a debi tsaraba abawa kowa har da makwabta tace kidai diba sai ki ba mutanen gidan abasu sai na makwabtan duk ki diban masu.
Dole na tsaya nayi kamar yadda tace inyi din tace haka yayi bayan na raba na dauki na fanin su gwago aka fita min dashi waje inda zan samu mashin din da zai kai mu gidan gwago din.
Mu kafito ni da kauna na da zata rakani gidajen uwayen mu muka hau mashin sai gidan gwago anan muka shiririce da ita har lokaci yayi mun fito.
Mun tashi muna batun zuwa gida maman mu bayan muyi sallah azahar ta dafa muna taliyan hausa da manja munci mun fito sai ga kani na saman keke ya biyo mu.
Nace lafiya ka biyo mu haka yace anty wai kizo wasu mutane suka zo wurin ki a wata irin katuwar mota.
Anty baki gansu ba kamar bature dayan mutumin suna nan sun shiga gida gaida baba shine ummi tace in zo in kiraki.
Na ce ni fa kace shafiu yace wallahi anty don Allah kiyi sauri don da ganin su masu kudi ne baki ga motan da suka zo da ita ba fa.
Gwago tace yi maza ki je tunda an aiko kiranki Allah dai yasa muji alheri dariya nayi kawai sai nace bari mu aje maki sakon su mama anan mi tafi.
Juyawa mukayi zuwa gida tun da muka karyo kwana na hango motan take naji gabana ya fadi nace to waye yazo har nan wuri na ?
Haka dai muka shiga gidan da fargaba ko waye yazo a kofan ummi muka hango takalman su ga awakin ina sun zo suna hawan takalmin nasu mama tana korewa muka shigo.
Wurin mama na nufa ina tambayan ta ko su waye tace haba Safiya ashe abin arziki muka samu baki sanar da kowa ba sai yanzu da bakin ki suka shigo gaida mahaifin ku suke sanar damu.
Na danji kunya nace kai mama ho baga shi kun sani ba yanzu ai sai yace cikin shake muryanta ai baki sani ba tun shigowan su mutumiyar ta shige daki bata fito ba nace wake nan mama.
Tace wa kika sani banda innar ku uwar yan hassada kuwa ake dai bari shiga dakin baban ku kiga abin arzikin da suka zo muna dashi.
Yaya sani ne ya shigo da kwalaben abinsha gidan a cikin leda yana sauri ya nufi dakin ummi dashi nace Allah sarki dan uwa ko ina ya samu kudin da ya karma min bakin dashi oho ?
Ya fito dakin ya ganni yace a, a ashema kin dawo ga baki mun samu daga abuja sin zo wurin ki kin kuma zo nan kin tsaya jin na dawo yasa ummi dake zaune a takure dakin fitowa ta bamu wuri.
Nan na shiga da kunya dakin da sallama na suna zaune saman tabarman da aka shimfida masu hankali kwance ga dan wake a gaban su da akayi gidan suna dan cokala suna ci.
Hamza ne ya amsa min sallama na yana dauko dan wake a kwano yace a a amaryan mu ina kika je bamu baki izzini ba haka.
Dan dariya nayi nace gidan kakata naje don tun da nazo ban je na gaida ita ba sai yau sai kuma akace min nayi baki.
Nan na dan dago kai na kalle shi bai ko dago kai ba sai cin dan wanken shi yakeyi kamar bai san ina wurin ba ma.
Yace dama ai ba ita mukazo gani ba mun dai ga wanda muka zo dubawa gashi har ummin mu ta bamu wanan abincin da na dade ban ciba muna ci.
Nace aiko abu yayi kyau amma sai dai kaci kadan kasan a gidan sarakkai kake yace ina nan ai yanzu nima na zama dan gida baki ganina a kuryan dakin uwana zaune.
Kara shiga dakin nayi yayin da na dan rakube a gefen dan gadon katakon ummi sai hamza ke cewa dashi a gara ki fada mai don naga yana batun mubar kwanon kawai.
Nace yaya hanya suka amsa da lafiya nace amma uncle shine da mukai waya dakai dazun baka fada min kuna haya ba a shirya ma zuwan ku.
Sai yace akwai shirin da yafi wanan ne a gare mu munzo munga mai jiki kima mun gabatar da kan mu an kuma ce ambamu abinda muke so gaya min akwai abinda yafi wanan farin ciki .
Sai ya samay hannushi daga kwanon tare da aje fork din da suke cin danwaken dashi yace naji dadin da ummi tace kin fada mata komai a kaina shi kuma baba ya amince dani albarkacin madam.
So ni yanzu banda wani shaku na neman ki don naga inda kika fito dakuma yan uwanki na kuma yaba da abinda idona ya ganan min.
Karya da rashin asalin shine ba a son a cikin zance naga komai kuma na gamsu da hakan yazu idan na koma munyi waya da madam da mijin ta za a zo a nema min auren ki kamar yadda sharia da alada ya tana da don na fada maki ban son wanan abin ya dauki lokaci mai tsawo .
Ina bukatan azumin bana inyi shi da matata a dakin ta don ban son a sakani cikin gwauraye kuma.
Kaina na kasa duk kunya da nauyi sun cika ni suka ce in kira masu ummi suyi sallama da ita don zasu kama hanya saboda nisa.
Na daga tsam zuwa kiran ummi din na samu tana dakin mama can na samayta na fada mata zasu wuce ta taso sunyi sallama da ita bayan godiya suka aje mata kudi suka mike.
Sai ta bukaci da su je su gaisa dasu mama sukace sun gode nan akai masu iso suka shiga wurin su kowacen su ya aje mata daurin yan dari biyar biyar a gaban ta.
Yaran gidan mu sai binsu suke yi suna kallo wasu na fadin wai batare ne shi saboda farin shi suma uncle bai barsu hakana ba sai da yai masu nasu alherinl.
Mun fito muka samu yaya Sani da driver a waje suna ganin mu suka taso nace yaya sani bakin ka zasu wuce don naga kaine mai ma saukin baki agidan.
Yace ai dole safiya ance min bakin kauna na ai banda zama don murna murmushi nayi don jin abinda ya fada nace yayana nakaina ke nan Allah barmin yayan mu.
Amin sukace muka karasa wurin mota sai shi hamza yace barin dan ga nan baya yaya garin yake ne sai ya wuce ya barmu mu kadai daga ni sai shi su yaya sani sin mara ma hamza baya.
Jin gina mukayi a jikin motar su yace safiya bazan boye maki ba naji dadin yadda iyayyenki suka tare mu sosai kuma mahaifinki na samay shi yadda nake so don ba masu kwadayi bane sai anbasu suke karba.
Yace shi wanan yayan naki yaya kuke dashi ne naga yana da kirki sosai sai dai alamu ya nuna min baiyi karatu mai zurfi ba ko ?
Nace yayana ne kuma mai kula dani sai na dan bashi labarin shi sama sama muna cikin hira ne hamza ya dawo yace kai muje inba son kake mu kwana garin nan ba dare fa yayi yanzu.
Yace ni ba bako bane kaine dai bako yanzu don ni in ta kama a kwana gida nazo hamza ya dan harare shi yace haka zakai min ko Safiya kin dai ji abinda ya fada murmushi nayi kawai.
Zai bani kudi nace a, a wanda ka bani da zanzo ban kashe ba duka sunanan su nake da amfani dasu yace to kara kikuma kashe su din don ki kashe wa yan uwa na baki kagin in godiya.
Ya juya wurin yaya sani sukayi magana da cewa ina fatan idan zata dawo zakai mata rakiya yaya sani ya washe bakin jin dadi yace ko yanzu ta tashi a shirye nake ni.
Sai naji yace ki tabbatar tare zaku dawo dashi don Abuja nake son ya tsaya ba sai ya biki lagos ba.
Nace angode indan kin shirya sai ku sanar dani driver zai zo ya daukeki nace mun gode baiyi magana ba suka shiga mota muna tsaye muna kallon su suka bace muna.
Sai naji wani irin ba dadi a raina nace may nake yi haka ne badai har son sulaiman ya kamani haka bane maganan yaya sani ta katse zuciyana da samo ansa da take so.
Don cewa yayi ikon Allah safiya ina kika samo wanan hadeden mutumin mai karamci diba fa kudin da ya bani bai ko kirga ba ya debo su ya jinka min.
Yaya Nura ne ya iso da sauri yace ina can wurin gina labari ya samay ni wani yazo gidan mu yana rabon kudi har da yan unguwa sun samu.
Yaya sani dake sa kudin shi a aljihu yace anshaka ai har sun tafi ko mukan muji dumus a aljhun mu naga yayi wani iri nace yaya Nura kar ka damu in kadawo sai muga juna.
Muka jera zuwa cikin gida tare inda muka samu suna ta farin ciki da zuwan bako suna ganina mama tace kaga yar albarka yar tohun lada haihuwan ki tankar da dubu .
Murmushi nayi tace Allah bai maka fada kayi hakkurin ki ya zama maki taki a rayuwa don yau mukan mun sheda kuma mun gani.
Dakin mu na shiga inda na samu ummi tayi tagumi zaune tana gani na ta wani nisawa tace sun tafi ko nace eh tace.
Kin ga irin alherin da yazo muna dashi kuwa yar nan ni abin ma na kasa gaskats shi a raina wai yau kece Allah yaiwa wanan budin haka a gidan nan.
Ga inna ku can harda ita wurin yabo ba kunya kamar ba ita ke tujara ba jiya a gidan nan nace kyale ta ummi ni bata gaba na fito mata da tulin kudin da ya bani nace gasu ya bani.
Zaro ido ummi tayi waje tace duka wanan kudin haka kodai sai tai shiru kuma sai ta kara cewa ni abin fa tsoro yake bani.
Nace ummi addua zamuyi don aikin gama ya gama tunda yace baba ya basu baki ko kiran da ake min a waje ne ya katse mu na fito da sauri nabar ummi da kidin a gaban ta.
Ina fitowa akace baba na kirana dakin shi na rude na koma daki na sako hijjab dina zuwa wurin amsa kiran baba din.
Ina shiga dakin baba idona yai tozali da kayan abinci a gefe guda tare nai mamakin yadda suka dauko kaya haka a motar su.
Na shiga da sallama na na samu baba ya dan dago daga kwaciyan dayayi nace baba ya karfin jikin naka ya amsa da lafiya lau safiya sai kuma ga baki mun gani da rana tsaka yau.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92Next page

Leave a Reply

Back to top button