BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ban da lafiya da fatan zakuyi hakuri da mistake din kuka gani anan kwana uku ina typing ban iya hadawa ba.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:10 PM – Ummi Tandama: BAHAGON, , , , ,

????????4️⃣ ????????

SEENABU MAKAWA

DON ALLAH NAMIJI KAYA SHIGA DON MATAN MUTANE MUKA KA TARA ANAN INKA KA SHIGA ALLAH YA SAKA MU NA
DON ALLAH YAR UWA ABIN DUNIYA KAR YA JAKI GA HALAKA IN KI BIYA KADA KI TURAWA WANDA BAI BIYABA DON BAZAN YAFE MAKI HAKKI NABA, , , ,

Dare ne kowa na zaune a tsakar gida saboda zafi da duhu da akwai yaro ya shigo yana kwala sallama a kofa.
Baba na gida ya amsa yaron yace wai ana sallama a waje sai baba yace yaya Nura ya duba yagani.
Zuwa can ya dawo yace wai wani wai wurin Safiya yazo amma ya ba son ganin ka.
Inna tai caraf tace Safiya kodai Ainau, Safiya ina taga saurayin da zai mata sallama, ga wayannen ta tanan wake maganan ta.
Yace nidai abinda ya fada min kenan na fada yasamu wuri ya zauna yaci gaba dacin abincin sa.
Inna tace tashi maza Ainau jeki ki gani wake sallama dacewan Ainau yar wurin Mama taje ta ga ba wurin ta bane tadawo kafin Ainau ta dawo ta shige da yar ta mairo daki.
Sukayi ku ku ku da ita saiga Aina tadawo tana fadin Inna ba wurina bane wannan fa dangaye ne ke sallama a waje.
Saiga Mairo ta fito zata har takai kofa taji ance ke dakata wurin ki aka zo ko kuwa tace zan duba na gani ne.
Maza koma ki zauna yaya sani ne ke wannan maganan da mairo daga dakin Inna ta daka mashi tsawa tace kabari tafita ta duba mana ko ita akewa sallama.
Ya ce yaushe mairo ta koma Safiya a gidan nan ne ke bana son rainin woyo maza kidawo wurin nan tun ranki bai baci ba.
Sanin hali yasa ta juwoyo simi simi ta da dawo cikin gida ta zauna ya mike ya fita zuwa kofan gida wurin bakon da kansa.
Duk wanan kace nacen magana da suke faman yi kunnen mu nida ummi sukeyin sa, kallo daya zai kayi min kagane a rikice nake.
Ummi dai batai min magana ba don tsaban tsoro duk jikina ya dauki rawa a lokaci daya can najiyo muryan yaya sani yana kwala min kira.
A rikice na fito daga dakin na rabe gefe guda a tsugunne lokaci guda yake cewa dani, akwai wanda kukai magana dashi zai zo gida ne ?
Gaba daya hankalin yan gidan mu ya dawo gare mu suna sauraren mu a hankali na bude bakina zanyi magana .
Naji Inna tace dani ke yan zuwa har da masu mota kike tsayawa don tsaban miskilan da munafunci irin naki na gado.
Nasoma rantsuwa baki na rawa ina fadi wallahi tallahi na rantse da Allah inna bantaba magana dakowa waye ba
Ji nayi yaya sani yace Safiya na amsa da sauri da naam ya ce tashi kije inda ake maki sallama waje.
Ai gara dake daza ki jawa mai mata kika jawo muna su diyan su da kara da doki duk zuwa yake wurin su fa.
Maza tashi tafi kada yaga an tsaida shi kin dade baki fito ba ya dauka bakya nan ne.
Na mike gwaiwa da sanyi da ce tau yaya nufi kofar gidan wurin wanda aka ce din yana min sallama wanda yaja min zagi da zargi agida uwurin mutanen gidan mu.
A kofan gida nahango shi tsaye ya jingina jiki da mota hannu daya kuma ya dafa motar shi dashi ya tsura wa kofar gidan mu ido.
Yana gani na ya dan muskuta tsayin shi yagyara da kyau har na iso kusa dashi.
Fuskana kamar zanyi kuka a lokacin nazo na tsaya sai yace dani ba gaisuwa yan mata kamar baki na na ciwo nace dashi Ina wuni ?
Shima cike da yanga yace min lafiya lau yan mata,
Wai halan ba ke kadai bane Safiya a gidan naku sai naga wasu yan mata nata fitowa da sunan safiya mana.
Saida na dan bata lokaci kafin nace ni kadai ne mana kawai da sun fito ne sun dauka wiri su aka zo yaron yai matuwa yace safiya don sun ga ba wanda ke aikowa kirana sai yau.
Ya nisa tare da cewa “kai, kice ni din nazo a sa, a ke nan nine zan bude fage in bar tarihi.
To amma naso naga baba ne da kaina koda yake ai naga yayan mu ya bani go ahead naci gaba da zuwa .
Kallon sa nakeyi ta gefen ido ya yagyara tsayuwar shi da kya yace na samu goyon baya kai tsaye ke na kinga duk lokacin da nake son ganin ki ina iya zuwa.
Na turo baki ina cewa indai na amince da hakan ko nifa na fada maka karatu nake son yi ban da lokacin tsayawa soyayya.
Ba zabin ki nake son ba illa yaka ki bani hadin kai shikaratu nufi ne na Allah.
Don haka ki bar Allah yai maki zabi kar ki raja, a a bangare daya don kinfi son karatu kice gareshi zaki tsaya.
Kunya bakin ciki da takaici suka sauka min a lokaci daya na rasa amsa da zanbashi kawai sai hawaye suka dinga zubo min .
Ganim ina kuka yasa shi cewa subbahanallahi ko ban fadi daidai bane ga magana na kike kuka.
Ganin bazan yi shiru yace Allah ya naki hankuri idan kin huce na dawo mu gaisa watarana dama yan yanzu zuwa nayi wurin baba don neman izini ban samay shi ba naga yayan ki.
Ya bude motar shi ya dauko leda cike dakaya ya miko min nace yabarsu na gade yake cewa Safiya nadai gane bakiyi naam dani ba ne.
Nace ba hakana bane in son samu ne nafison saina gama karatuna tukun yace wanan baida matsala mudai samu fahintar juna tukun shi yafi.
Nan nabarshi da kayan naki karba ashe ya samu dan makwabtan mu yace ya biyo ni da kayan ciki.
A Cikin gida kuwa tun fitana mutan gidan suka kasa suka tsare suga yadda za a yi yayin da inna take ta masifa da yaya sani akan wai nata mata shiga hanci da kudundune kan ala, amarin ta inda take shiga ba nan take fita ba.
Shigowa na kenan yaron da ya biyo ni da kaya ya shigo gidan shima inda na nufa can yaron ya nufa da kaya niki niki.
Yaya Nura ne yake tambayan yaron maynene yadauko a hannu shi haka sai yaron kewa Safiya ace nadauko mawa .
Gaba daya suka sako ido suga kamay nene a cikin ledan saidai bazasu iya ganin ko may a ciki ba saboda duhun dakeyi.
Inda da hali dazasuce akawo ledan suka abinda ke cikin sa sai dai hakan bazai yuyu ba don yaya sani na gida alokacin.
Dole da ido suka koma yin magana ba halin su maganta yai cikin su da rashin kunya.
Har washe gari kayan na nan a jiye ba a taba ba ba a kuma bude ba a cewar umma in yazo na mayar mai da kayan sa kada na nadauko mata wahala tana zaune kalau.
Daga ni jar ummi tsoron taba kayan muke ja agidan bamu yarda nun taba komai ba daga ciki Ummi tai mashi dogon ajiya.
Abim duniya ya isheni a raina ga kayan mutumi a je a gidan mu ina tsoron tabawa a tsakar gidan mu sai habaici ake min cewa a samu a hanawa dangi.
Amina na samu a school nake fada mata halin da nake ciki don dai gaskiya ni sulaiman yafi karfina da soyyaya.
Dariya Amina ta soma yi min tana cewa safiya kenan ina kika taba jin haka kedai kawai kice matsayin ku ba guda ba.
Amma zancen yafi karfinki bai taso ba don dai sulaiman mijin da mata da yawa zasu so ne.
Balle mutumin daya nemi izzini ta gidan ku ai zance ya kare iyaka muyi fatan alherin ga hakan, nisawa nayi nace da ita Amina nifa in son samu ne nafi son sai na gama karatu kafin na fara zance da wani namiji .
Safiya kin kwantar da hankalin ki bafacewa akayi zaki aure shi ba dole, abune nufin Allah .
Nace haka ne amma ni sherin mutanen gidan mu nake jiwa don masheran tane na karshe sun sa yadda zasu kulla wa mutam sheri ya zama gaskiya .
Da dai zai jaye ya je gaba yane mi wata zai fi sauki don ina gudun jefa shi a cikin zargin mutamen gidan mu.
Ba tadai yarda sai bani karfin gwiwar da tayi akan na hakkura naga ya gudun shi in yasu sai nayanke hukunci akai.
Sulaiman mutumin kirki ne sosai a yadda na fahinci shi ba a garin yake zama ba zuwa yake duk karshen wata kokuma farkon wata.
Idan zaizo yakan yo muna sayayya yadda ya kamata ya zo muna dashi har kullun yazo bani sakewa dashi amma shi sai yake daukan hakan da kurciyane kawai.
Tun yana zuwa ban sauraren shi har yakai na fara sauraren shi ina dan bashi lokaci sannu sannu har kowa ya fara sanin shi a gidan mu.
Dan idan yazo zai ba da kudi da kayan rabo irin su sabulu da manshafi a rabawa mutanen gidan mu, inda ni kuma yakan kawo min kayan provition na amfanina.
Wannan abin shiya tsone idon mutanen gidan mu don walwalan da suke ganin mun samu a gidan.
Tsegumi da kazafi yaki karewa a gidan sai cewa suke wai babana yaga kudi shiyasa idon shi ya rufe bai iya magana wai har cewa sukeyi .
Sulaiman na dauka na da mota muna fita yana yawo a cikin gari maganganu dai marasa dadi suke kai da kawo akan zancen.
Sai dai ummi na hankalinta yakan tashi dajin wannan zancen sai da dare tan tayar dani daga barci ta sakani a gaba da cewa.
Yar nan kirufa min asiri ki kamaka kan ki karki tona min asiri a cikin abokan zama abin na da suke fada gamay dake Allah yasa ba gaskiya bane kodai daya ke nasan ki nasan halin ki.
Nasan abin da zaki iya da wanda bazaki iya ba amma dai dolene na kara tsawata maki akan hakan.
Don Allah ki kafa mutuncin ki ki rufa muna asiri yar nan bani kadai ba har da mahaifin ki nakan son rantse mata cewa ba gaskiya bane sai ta dakatar dani da cewa bar ni na fada maki yar nan.
Nice mai fada maki gaskiya duk duniyan nan ku nake da ku nake gani ina alfahari a duniyan.
Idan ummi tafadi haka nakan ji wani irin tausayin ta a raina wana abin yasa sulaiman ya rage zuwa gidan mu wanda
Hakan kuma suma ya shafe su don dan abin da suke samu ya daina zuwa yana basu sai kuma suka koma cewa .
Ya gama dani ya gudu suna dariya suna fadin na goga masu tsiya a ranan da sukai dariya a ranan kuma yan uwan sukaima suka zo wurin babana da kaya niki niki na nema wa sulaiman aure na.
Amsan da baba ya basu shine sai yayi shawara da matan shi don ina da yanne har hudu a gaba na ..
Yara suka shigo da kaya ciki niki niki kowa ya fito yana gani ana sake magana nidai muna daki da mahaifiya na ba wanda yaleko daga cikin mu.
Ana cikin wanan haya niyar gwago lagos ta bugowa mama waya ta layin Nura yana bawa mama ba, a jin abinda take fada sai da mama ta shiga daki.
Tace wai hayaniyar may kuke yi a gidan ku ne haka ina jin na hayaniya kamar mutane da yawa wurin.
Mama ta ba ta amsa da muna kallon kayan da aka kawowa Safiya ne shi meke ta surutu.
Gwago tace wacce safiya ba dai safoyan naku da nake son naiwa yaya magana ba a kanta.
Mama tace Safiya dai yar wirin Rabi na nan gidan nake maki magana sai gwago tace kaya kayan fa?.
Akwai matsala ne inji mama take tamabayan ta akwa matsala kan don dama ina son nemawa yaron nan auren ta ne yanzu kuma naji wani magana can.
A, a ta yaya za ayi gida bai koshiba akaiwa daji dole asan nayi dai akan haka amma dai zan fadawa malam di don ya sani a san abin yi.
Nan dai sukayi kulle kullen su da mama har suka gama mama ta kashe wayan tun da mama ta fito take anna shuwa da guda a tsakar gadan karshen ta suka shige daki da inna.
Shiru shiru basu fito ba sai wani lokaci mai tsawo suka fito suna murna suna dariya tun nan Ummi na tasha jinin jikin ta.
Washegari da safe magana ya fara fitowa a gidan mu cewa wai dan gwago na lagos za a bani da farko jin su mukeyi sai ranan da sulaiman yazo zan fita babana ya dakatar dani.
Ya tashi ya fita zuwa wurin shi bansan may ya fada mashi ba sai tashin motan sulaiman kawai naji ya tafi.
Baba yana dawowa cikin gida ya kwala min kira da sauri nafito daga dakin mu yake cewa dani .
Safiya wanan yaron dake zuwa wurin ki na dakatar dashi don zan hadaki da dan wurin gwogon ki na lagos ne.
Saboda haka daga yau bani sin jin zancen wanan yaron a gidan nan duk abin da kuka san kunci na shi ku tattara mashi a mayar mashi da abin shi.
Gaba na ne ya fadi na dago kai a razane na kalli babana zan yi magana sai hawaye ya hana ni fadin komai muryan baba ne ke cewa kin dai ji abanda na fada maki.
Nace a sanyayye naji baba ina mikewa ya kwala wa ummi kira yana cewa ina rabin take ne kizo kiji ke ma hukuncin da na yankewa yar ki.
Ummi ta fito duk jamaan gidan sukayi tsit suna sauraren shi yace yar daga yau ban son na kara ganin wani yazo gun ta.
Kuma ku hada nashi i nashi tun wuri ku mayar shi da kayan sa kinji magana na ya karasa kamar mai fada.
Daga kofan inna inda take zaune tace, hum,in a, she akwaita kuwa a gidan nan, yo wasu kaya kayan kayan da ake shigewa dasu daki muku,muku a cinye ina za a samay su ai yau ga ranan ta.
Ummi ta kada kai kawai ta wuce zuwa dakin ta koda ta shiga ta samu na kifa kai a gwiwa na ina kuka.
Cikin kuka nace ummi kin ji abinda baba yace,
Naji amma yaya zamuyi kin san halinsa baban naku sarai balle maganan da aka shirya yin shi akan mu.
Dom haka kar ma kisaka wa ranki damuwa akan abinda ki kasan bamai hanawa sai Allah
Tace dani ba kuka zakiyi ba don kuka bashine mafita ga wanan zancen ba samun mafita shine abin yi.
Da yake cewa dan gwagon ki zai hada ku dashi shidin ma ya san ki ne ko kuwa dai wani irin hadi zaiyi.
Nace ummi Allah yasa dai ba wanan mai shan taban bana yake nufi ba zai hada ni dashi aure.
Yanzu dai ki bari kisamu gwago da safe ki sanar da ita halin da ake ciki don mu san mafita.
Nace ummi kina ganin baba zai yarda da maganan gwago har ya yarda yajanye maganan shi .
Tace sai mun jeraba mun gani tukun don a gaskiya in dai yaran laraba ne ban ga mai tarbiyan da zace zaki aura a cikin su ba.
Yaran da idon su ya bude da duniya basu kallon kowa da daraja a idon su kowa a hankade suke ganin shi.
Kuka na saka wa ummi a cikin daki tu tana saurare na har tagaji ta kwanta ta bar ni nasan itama dai ta kwanta ne ba wai barci ta samu yi ba.
Da safe ban shiga makaranta ba gidan gwagon ummi naje na saka ta gaba ina ta kuka da kallamai masu tsuma zuciya.
Gwago tai rarashin duniya ta ga ina batan shiga cikin wani hal dole ta aikwa diyan ta suzo tana neman su.
Sin zo sun samay ni take mayar masu da abin da ke faruwa kowan su yace gaskiya takuran yai yawa har da auren ma baza a bari inyi wanda nake so ba.
Sun yake magana cewa zasu je su sami babana akan zancen don su dauki matakin da ya dace.
Sai dai baba bai saurara masu ba ko kadan inda yake shiga ba nan yake fita ba yana cewa wa ya haifa mashi yar da zai fada mai yadda zai yi da ita.
Karshe dai aka tashi baran baran dasu da shi kowa na kunfan baki ran su ya baci suka tafi.
Bayan tafiyan su ya kira mahifiyana ya sauke mata kwadon balai har t
yake ikirarin cewa kan zancen nan sai ummi na tabar mashi gidan shi.
Ga zaton shi ummi zatai shi amma ga mamakin shi sai yaji tace da yafi nono fari wallahi indai kagani haka shi yafi maka to ka matsa.
Ta shige dakin ta tana bakar magana wanda sai yaune take mayar mashi da ansa a tsakar gida.
Su ko inna dadi suka ji yadda baba yake muzanta ummi dani a tsakar gida suna jin dadi sai cewa sukay mai abu ja mara abu ja.
Samun wurin mahaifi ya ya yanke sha wara kan diyar shi amma don karfin hali za a zo a ce ga yadda zai yi.
Bani ci bani sha nabi na ramay dana fito tsakar gida yanzu zakiji su inna na cewa yarinya an cuce ki an hadaki da tsoho wai a cewan su Ahmed ya tsufa baiyi aure ba za a daukeni yarinya karama a bashi.
Su dinga fadin wai ai karyan kilibibi ya kara min don ban ga wurin yi ba a gidan gwago don bazan kawo mata haka ba gida.
Daga ummi har ni bamu jin dadin mutanen gidan mu habaici da yaben magana bamu da shakat a gidan ko kadan.
Har takai rainin wayon yana son taba mutuncin ummi hakan yasa ranan nai magana wa mutan gidan .
Dan wurin inna ya dauki roban ummi yai wanki dashi maimakon ya mayar ida ya dauka sai ya barshi a tsakan gida ummi tai magana ya taso kamar zai duke ta uwar na gani bata tsawata mashi ba.
Bansan lokacin da nasa baki ba ga maganan fadan ya koma nawa duk da nasan ba iyawa zanyi ba.
Uwar tace ina na fito takama mu tai muna tas ni da ummi da sauran yaran dakin mu.
Baba ya dawo inna ta kwashi karya da gaskiya ta fada mashi inda yake shi banan yake fita ba a gidan.
Ga inna irin matan nan ne dabasu so a taba su diyan su amma suna iya yiwa dan wani ka mita magana daya sai anyi kwana barkatai ana maimaita shi.
Fitina ya ishi ummi tace kai yaya ina dai anyi wanan zancen ya wuce aiko ta hayayyako wa ummi da masifa da jidali .
Wanan abin ya kara jefa ummi cikin damuwa da kuci da takurawan ta kasance cikin tashin hankali haka yasa na kara shiga damuwa da halin da mahifiya na ke ciki.
Damuwa yayi min yawa ga auren da akeson min na dole a kaina ga halin da ummin mu take ciki da mutanen gidan.
Ranan itace da girkin gida girkin da ba komai ake kawo masu nahadi cikkake ba sai mutum yayi dabaran da kan sa.
Da taimakona ummi ta samu ta kammal aikin ta na dauka nakaiwa kowa nashi dakin su na koma dakin mu na zauna sai dai na kasa aiwata komi akaina na rasa manene abinyi don kawo sassuci na alamarin namu a gidan.
Haka na kwana da wanan damuwar a raina ban samu barcin kirki ba tara dani dama tun da wanan zancen ya fara bani barcin kirki a tare dani.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92Next page

Leave a Reply

Back to top button