BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

Idan zaki fitar min da novel na barki da raddin ubangijin mu je ki tayi tunda baki san hakkin amana ba zaki fada ranan da baki baya magana sai hali.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:12 PM – Ummi Tandama: BAHAGGON , , , , ,

????????4️⃣7️⃣????????

Ni safiya ace mutum bai tsoron Allah shi dole ne karatun nan ance ba a yafe ba an hada ki/ka da Allah an hada ku da darajan annabi amma kuna wasa dashi ku sani fa hada mutum da Allah ba karamar kalma bace akwai ranan haduwa dashi ranan nadama ranan da baka da abin bayar sai ladan da ka tara ma kan ka.
Mutuna ko yanzu ko anjima koyau ko gobe ko ko ko ko zamu koma ga Allah koda ciwo ko babu ciwo may zamu fada wa Allah.
Dabara ya rage ga mai shiga rami shi kadai ni dai tun da asuba na mike batare da samira ta sani ba nayiwa gidan ta kwal ga ruwan zafi da na sa masu na wanka ya ya tafasa na sauke na fara hada mata abin karyawa.
Sai da naje daukan baby dake barci a gefen tane ta bude idanun ta tana fadin subbahanallahi gari ya waye ne ?
Murmushi nayi nace madam ki tashi ruwan zafin ki na jiran ki a bayi ban saurara mata ba na fara cirewa baby kayan jikin ta na nufi bayin da ita inda maga kayan wankan ta aje a gefe.
Wanka nayi mata na gasa mata jiki dama na iya tun ina gida idan ummina ta haihu nakan taimaka mata da wankan yara.
Na fito na fara shirya baby sai lokacin Samira ta samu ta mike zuwa wanka tana cewa yau wata rana zamuyi wanka da safe haka yadda ya dace.
Nikan naji dadin ziwan nan naki Safiya wannan kokari haka ta mike take bin dakin da kallo tace wai ko kin yi barci safiya wanan irin aikin haka ?
Kafin ta fito na saka wa yarinyar kaya cikin kayan da nazo mata dasu uwar ta fito wanka tana kallon mu da sha a wa tare da fadin aa lalai takwara tazo wanan kaya ai da ki bari sai ranan suna ki saka mata.
Murmushi nayi kawai na goya yarinyar na na fita daga dakin sai gani na dawo da cup cike da shayi mai kauri dana hado mata.
Na aje a gefen ta dago kai tayi ta kalle ni nace madam sai a sakai a shanye kafin ya huce nace za a daukan maki kaya ne ki saka ?
Tace gaskiya Safiya zaki shagwaba ni da yawa ki wuce ki barni da kewan ki nace kada ki damu madam dama shi nazo yi yanzu aiki na ne nakeyi.
Batai sanya ba ta kafa kai ta shanye shayin duka sai ga zufa ya karyo mata nan ta mike ta dauko kayanta tana sawa.
Na fito falo naji ana bude karamin dakin nan dake rufe ashe yaya ne anan ya shige ya kwana na juyo don ganin ko waye mukayi tozali dashi.
Nace yaya barka da kwana yace an tashi lafiya Safiya nace Alhamdu lillahi yaya yace yau takwaranki ne ta samu goyo haka ?
Gaskiya banji kukanta ba yau da safe don kullun itace ke tayar damu da safe da kukan ta nace yau tasan gwagon ta na gari batayi kuka ba tun da nai mata wanka takoma barci.
Yace kai har wanka ta samu yau da wuri haka nace gwago tazo fa yaya zanbar diyana takai wani lokaci bata gasa jikin ta ba.
Nan ya fara bin gidan da kallo yaga gyaran da ya sha yace keko kinyi barci kuwa nace may ka gani yaya yace wanan irin aiki haka tun da farar safiya haka ?
Nace shiya kawo ni may zan kwata wa inyi ga aikin madam a gaba na yanzu lokaci ne da take sin hutu a jikin ta don haka ta kwanta ta huta jikin ta ya watsake.
Na shige kitchen na barshi yana mamaki ya raya a ranshi da haka uwar shi ta rike zumuncin da mahaifina yaso su kulla da abin yazo da sauki.
Ya shiga daki nan ya samu samira tana ninke kayan da ta cire ta juyo tana kallon shi tace kaga aikin kanwaka ko sai yau na karkare yarda da abinda kake fadi nata.
Na shiga dakin na samay su suna magana nace yauwa bari ma in baku sakon ku tunda gaka a dakin nan na jawo akwatin kayan da nazo dashi zuwa gaban shi na juya wirin hand bag dina na ciro kudin da na ware mashi tun a gida na bashi.
Sai bina yake da kallo yana neman karin bayani nace yaya kana kallona mana yace ban fahinta bane safiya nace to kaya da na takwara nane da uwar ta gashinan akwati guda sai kudi kai kuma ka kara kai hidiman buki da su.
Tsaye yake dama zai shiga bayi sai naga ya kai zaune a wurin yayi shiru can ya dago kai yace Safiya duka wanan dawainiyar ani kika yi shi bayan zuwan da kikayi kuma ga wanan wahalar.
Ba wahala bane idan duk abinda nake dashi zanyi maka bazan taba yin da na sani ba yaya kai kaja in maka hakan da nayi.
Samira kan kallo na take da mamaki da kyat ta samu bakin magana tace wai safiya kin wanke ni ga bakin jamma a kin gama muna komai a duniyan nan.
Kin san yayan ki aikin company yake yi gashi wata uku ba a biya su jiya jiyan nan muka gama magana dashi na yaya zaiyi ko zamu daga sunan nan har zuwa gaba.
Nayi saurin cewa a uzubillahi a daga suna kuma yaya Allah ya rufa muna asiri ashe gwama da na daure nazo don da anty ta so hanani zuwa na nace nace sai nazo.
Tace Allah ne ya kawo ki yar uwa ta fara jawo kayan tana bude zip din jakkan don na karshen ne babban duka duka nazo kasu dashi.
Shiko yayi mutuwar zaune ya kasa fadin komai har lokacin tana budewa ta sake karamin ihu da fadin wai Safiya ?
Shago ke nan ta fara budan kayan tana azawa a saman gado karshe rufe akwatin tayi tai tagumi kawai sai can ta nisa tace dear ka ga ikon Allah.
Sai lokacin ya nisa a sanyaye yace na gani samira ban san may zance bane kawai imani da tsoron Allah sun cika min zuciya samira.
Kawar da zancen nayi da fadin ni kaga malam kai wanka ka shirya kazo ka karya in ka gama ka fita ka sayo muna abinci azo a aje a gidan na ciro kudi ina mika mai.
Ido ya zaro yace na may ye kuma wannan kudin nace abinci zaka sayo mana dashi wanan ba na hidimar suna na baka kayi ba sai naji yace haba kai safiya haba dai.
Tare shi nayi da fadin ka gode ma Allah adduan ku gareni ya karbu ga ubangiji shi ya wadatani da wanan niimar idan ban gode nima na na rama maku ba may zanyi da kudi.
Kudine ina samu alhamdullahi don sulaiman yana wadatar dani dasu kuma yana fada min in yiwa yan uwana alheri daga niimar da Allah ya wadatar dani.
Yace Allahu akbar haka abun Allah yake safiya shiya sa idan kaga ubangiji ya yi ikon shi akan mutum kai dai kabishi da addua don baka san hikimar ubangiji ba a kansa.
Abinda nai maki a baya har ga Allah nayi maki ne a matsayin ki na yar uwata ta jini da kuma matar yayana da hadi na musulunci banyi don zaton wata rana zaki zama wani abu har ki rama min ba.
Nace na sani yaya nima kuma ba zan taba iya rama maka abunda kai min ba har abada duk wanda yai maka abu a lokacin da kake bukatan taimako a kan shi ai baka da kamar mai shi a duniya ba don kai ba da yanzu na wullakanta.
Yai saurin cewa Allah bai yoki wullakantata ba dama safiya ki godewa niimar da Allah yai maki tun farko tunda kin samu kiyi karatun boko.
Nan dai mukai ta hira dasu har ya gaji ya mike zuwa wanka yafito ya karya ya fice daga gidan baby Safiya ta tashi na kaita wurin uwarta na dawo na ci gaba da aiki na.
Tuwo na tuka mata na Semon da na gani a kitchen din da miyar yauki ina gamawa yaya ya dawo gidan da kaya niki niki tare da abokin shi.
Wai ya kirashi yazo yaga abinda na kawo masu abinci na gabatar masu bayan sun gama gani yaya yace safiya sai kina sa ina ganin gidan yau kamar ba nawa bane.
Muna tsaka ga magana Samira ta fito daki da wayana a hannu tana mika min ana kirana a lokacin.
Na karba naga Sulaiman ne da sallama na koma gefe daya ina amsa wayan yace gida yai maki dadi kin manta da kowa ko ?
Murmushi nayi nace yallabai an tashi lafiya yaya aiki yace lafiya kalau watau ke dai baki kiran mutum ko nace tsoro nakeji kada in kira ka kana cikin uzuri.
Yace don gani agogo sarkin aiki sai ba zan tsaya na saurari kiran mata na ba ko ?
Nace tuba nakeyi katse shi nayi da fadin ga yaya na ku gaisa yace af yana kusane nace yana nan yanzu ya shigo namika ma yaya Saadu wayan.
Sun gaisa yake ma yaya barka da samun karu sai yaya yace Allah ya mayar gare ku kuma da kunyi aure a sama mana tagwaye.
Murmushi yayi kawai yaya yake mashi godiya a bisa ga kokarin da yayi masu yace na komai ai anzama daya yanzu.
Yake tambayan yaya din wani aiki yake yi sai yace mashi a wani company yake aiki yanzu kuma company tai sanyi sai dai dan buga buga da suke yi sunyi hira sosai kafin yaya ya bani wayan mu ci gaba da magana dashi har yake tambayana da yaushe ne zan dawo ?
Nace jiya fa nazo har ake batun dawowa na yanzu sai nayi a kalla wata daya ko biyu kafin in dawo sai takwara na tayi kwari zan dawo.
Yace kina hauka ne nifa in badon madam ta fada min yadda kuke dashi ba kuma yanzu a wayan da mukayi na fahinci mutumin kwarai ne don gashi har yana min fatan samun tagwaye da auren mu.
Da hankalina bai kwata da zuwan ki garin nan ba sam nace sace ni za a yi komay ?
Yace yana da wuya ne nace ni ko kofan daki ban taka ba tun zuwa ina ciki kumshe ina za a gani har a dauke ni ?
Yace ki dai bi sannu don Allah ban son yawo please zan ma fada ma yaya don ya saka maki ido sai nace ai ka hutar da kan ka ni din kifin rijiya ce fita a guna sai ya kama dole nake fita.
Yace daya fi maki ashe ba zamu samu matsala ba ban son mace mai yawo a rayuwa na ko gadan.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92Next page

Leave a Reply

Back to top button