BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

 Yace kin san may ?

Na ce aa yallabai yace yau yayan ki ya fama min wani ciwo a zuciyata sai nayi sauri cewa subbahanallahi.
Yace dakata mana kiji ai ba wani abu yace min ba illar cewar da yayi Allah ya bamu tagwaye da munyi aure.
Sai nayi murmushi yace ban taba jin ina son haihuwa ba nima sai yau daya fada min haka naji nima ina son in ga zuria na a duniya koda kuwa bazan rayu tare da su ba.
Nace balle zamu rayu tare dasu insha Allahu ai Allah shi ya fimu sanin daidai ga rayuwan mu ni dai mu bar wanan zancen ba yanzu ba tukun.
Yace saboda may ?
Ko ba kya son haihuwa ne ke nace wai kuwa kasan sunan yarinya Safiya ?
Kin kawar da zancen ke nan ko?
Safiya yaya yasa wa babyn namu nace wallahi ina zuwa yace ga takwara nan yayi min ya ce Allah ya raya muna ita a tafarkin addinin musulunci nace amin.
Yanzu yaushe zaki dawo lagos ba wasa nake yi ba fa ina son in sani ne ?
Nace kaida baka ko kasan kake tambayana yaushe zan dawo bafa a gari daya muke zaune ba balle kuma baka ma kasar baki daya.
Murmushi yayi yace ina son in san lokacin da zaki dawo idan yayi daidai da dawowa na Nigeria don ta lagos zan sauka.
Nace gaskiya ban sani ba tukun sai dai idan anyi suna naga yadda yanayin ya ke zan saka ranan dawowa na.
Munyi sallama dashi naci gaba da aikina na fito inda na samu su yaya sun gama cin abinci sun cinye duka sai kwano.
Na kwashe zuwa kitchen tare da kokarin dora girkin yamma don inyi in gama da wuri in huta ina aiki yan barka suna shigowa jefi jefi kamar yadda ake zaune a bariki.
Na gama na gyara wurin na koma ciki nayi wanka sai lokacin na samu zama da samira muka fara hira wanda hiran namu akan yanayin garin nasu take min da kuma bani tarihin ta.
Da yadda suka hadu da yaya saadu yan uwanta suka so su hana auren su wai ba a san asalin shi ba sai da kyat aka yarda ta aure shi don suna son junar su.
Nace ai yanzu aure babu inda bai kai mace gashi ban taba zuwa bauchi ba amma aure yana shirin kaini can din.
Tace wanda zaki aura dan bauchi ne shi nace mata dan bauchi ne tace a can yake zaune nace da ita a a .
Sai nayi dariya nace shi wanan ai baida takamaimai zurin zama dan kasuwa ne baya zama sosai sai dai ina ganin abuja zai aje ni amma dai ban sani ba dai.
Waya na jawo na kira anty don nasan yanzu ta dawo gida kira uku ta daga wayan tana fadin mutanen kalaba kun sauka lafiya yaya baby da maman ta.
Nace lafiya lau anty baby safiya tana gaida ke tace a a safiya aka sama yarinyar nace eh anty .
Tace ashe gaskiya kika matsa da zaki kin san abinda kuka kulla da yayan na ki nace wallahi anty ban san safiya ya samata ba sai da nazo naji.
Tace sai yaushe zamu ganki nace anty sai anyi suna zamu zauna da yaya saadu don yanzu bai samun zama a gida.
Tace yana da buki yaushe zai zauna gida kuma Allah yasa a watse lafiya ki gyayar min dashi don Allah ina mashi barka idan ya shigo .
Mun gama ina cewa ta gyayar min dasu yan biyu tace kin sa sun zo sun damay ni da tambayan ina kika je nayi murmushi nace nasan dama zasu tambaya ai.
wayan nake aje wa sai naji samira na fadin itace wacce kike a wurin ta lagos halan ?
Nace eh wallahi mutumiyar arziki bata da matsalan komai wallahi ta rike ni tankar itace ta haife ni.
Tace kinyi dace da uwargijiya yar albarka samun irin su yanzu da duniya ya dauki zafi ai sai dace.
Yan barkan da suka shigo yasa ni tashi na basu wuri falon su na koma na kwanta ni kadai babu komai a raina sai tunanen rayuwa.
Maganar haihuwan da mukayi da shi dazun nake tunane a irin wanan halin da mutum yake ciki har zaiyi tunanen haihuwa wa a hakan.
Yaya taran zasu taso suji halin da iyayyen su ke ciki a duniya kuma ba wani dadewa zasu iya yi da iyayye su a raya sam wanan tunanen na sulaiman ban kwanta mi ba arai nikan.
Mu dai samu mu raka da rayuwan mu a hakana batare da mun jefo wasu a cikin matsalar mu ba yara su taso a wahalce babu iyayyen su a duniya.
Shigowan mahaifiyar samira da ba sai an fada ma mutum ita ta haife ta ba don kamar da sukayi da ita.
Sannu da zuwa nake masu tace a a lalai kuwa ga gwagon baby na gani sukeyi min sannu da zuwa na amsa masu a sake tare da masu jagora zuwa daki.
Bayan na gama wadatasu da abin sha saina koma falo ida nake zaune da farko na kwanta ina jiyo hiran su daga inda nake zaune samira na fada mata abin arzikin da na kawo masu.
Tunanen ummi na ya fado min a raina din haka na ja waya ina laluban ta nayi saa wayan ya shiga muka gaisa nake fada mata ai ina kabala tun jiya na iso.
Tayi ta samin albarka da na samu zuwa nake tambayan mutanen gida tace duk suna lafiya aiki dai yayi nisa jiya da yayan ki sani yazo.
Yake fada min wai yanzu window za a sa sai kuma aci gaba da sauran aiki nace yaya sani ana nan dai ana ta fama tace bari kedai.
Ai kina shan albarka a wurin shi kullun yazo maganan ke nan a bakin shi nayi dariya nace yaya sani ho yana nan dai da halin nasa
Tace may zai fasa take bani labarin harkan sana a ta nace ummi ai yanzu ya zama naki sai dai ku kula kada kudin ya karye .
Mun gama waya na sauke ajiyan zuciya ina mai ci gaba da tunanen duniya a raina har har mahaifiyar samira suka fito daga daki suka dawo wurina muka zauna muna dan fira jefi jefi basu dade ba sukai muna sallama.
Ban shiga ba anan nake zaune don akwai kawarta a dakin bata fita ba don haka na basu wuri su dan tatauna a tsakanin su.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:12 PM – Ummi Tandama: BAHAGGON , , , , , , , ,

????????4️⃣8️⃣????????

Daf da magariba yaya saadu ya shigo ya iskani zaune a falo nayi zugum cike da tunanen zucci muryan shi naji daga sama yana fadin.
Safiya haba zaki bata min rai fa idan kina zama ke kadai kina saka damuwa a ranki da tunane tunanen banza marasa amfani gare ki.
Nisawa nayi nace duk abu mace mai rai da lafiya in tana da hankali dole tayi tunane a rayuwan ta.
Zama yayi a kujera da ke fuskantana na sake cewa dashi yaya ke nan ai dole mutum yayi tunanen rayuwa din ni yanzu kaina ya daure don ban san makoma na ba.
Yace come on, wace irin magana kike fadi haka?
Wace irin magana kike fada safiya may yasa kikace hakan ?
Ta dukar dakai na kasa nai shiru da alaman tunane nakeyi abinda zan fada mashi.
Yaya wai ba za a kara ma auren nan lokaci ba don ni kwata kwata ba wai na shirya mayin aure bane yanzu.
Abu ne mai wuya yan uwanshi su yarda dani ko su soni far daya don dukkan su fa masu kudine family su cap yaya, yaya za a yi inyi daraja a wurin su.
Ya kalle ni kafin yace shi zaki aura ko yan uwan shi na ce shine yaya.
Sai naji ya kyalkyale da dariya yana mikewa yace kai amma ku mata wani lokaci sai mutum ya rasa ina tunanen ku ya tafi ne wai.
A daidai lokacin Samira ta fito daga dakin ta tana ce min tare da miko yar ta naga yamma yayi a goya ta ko ?
Karban yarinyar nayi nake mata kirari ina kokarin goya ta a bayana yaya yake cewa zai tafi masallaci yai sallah.
Yana fita Samira ta kalle ni tana cewa kin ko ci abinci safiya don ni banga kin ci komai ba tunda safe ?
Nace dazun da safe na karya ai ni dama haka nake abinci bai damay ni ba tace ko wani abin kike son ci baki magana ba.
Bari yayan ki ya dawo sai ai mashi magana ya dan samo maki wani abin marmari ko zaki iya ci amma kan kya zauna da yunwa hakana.
Nace ai banjin yunwa ne da zanci abincin baidawo ba sai taimai waya da zai dawo gida sai gashi da drinks mai sanyi da gasassan kaji biyu ya dawo dasu.
Gaba ya sani dani dashi da samira sai da yaga na ci kaza guda daya aje min amma rabi banyi ba na dan kora da drinks din na ji nauyi a cikina.
Sai dai cikan da cikina yayi ya hana ni barci da dadi da dare sai da na sha magani na samu shakkat a rayuwana.
Ana gobe suna ban zauna ba don aiki yai yawa a gidan bani na samu kaina ba sai dare shima ba wani barci na samu nayi sosai ba.
Asuban farko na tashi kafin gari ya waye na gama ayukan daya dace duk wacce tazo sai dai in debo mata abinci da abin sha in bata.
Anyi suna lafiya aka watse kuma lafiya sai mu da wasu yan uwan Samira aka bari muna gyara gida anan muka kwana tare da su.
Washe gari muka kara gyara gida sai suka fara tafiya dama su uku ne bayan tafiyan su ne na samu wuri na kwanta don duk na gaji sosai a lokacin.
Barci nayi sosai a ranan sai karfe hudu na tashi ina duban lokaci samira tace ai taki tasheni ne don taga na gaji.
Sallah nayi nazo na hada masu ruwan wanka sukai wanka muka zauna hira da ita yaya bai dawo gida ba sai da dare.
Nan ya zauna muka sha hira dashi har yaci abinci ban dade ba na basu wuri zuwa ciki nan barci ya dauke ni koda Samira ta dawo dakin ta samu har munyi barci nida safiya karama.
A kwana uku da suna muka zagaya gidanjen yan uwa da abokan arziki da suka zo mata suna da barka.
Duk gidan da muka shiga zanga sun kira samira a gefe suna tambyan ta ni wacece a gare su ?
Wasu su fadi alheri akaina wasu kuma suce tayi hankali dani tunda ba uwar mu daya uban mu daya ba zan iya aure mata miji.
Ita dai dariya take masu kawai a gidan su muka dawo muka ya da zango anan don sai dare muka koma gida don uguwar su guda sai dai da dan nisa da gidan su.
Ina cika sati daya da zuwa na fara zancen komawa don kullun na kira anty sai ta tambaye ni yaushe zan dawo ne.
Shiyasa nake son komawa yaya yaso yai min sayayya amma na hana shi sai mun komai sai cake da akai masu wanda zanje dashi a matsayin kayan buki da sauran tarkace na kwalam din yara.
Munyi waya da sulaiman na fada mashi ranan da zan taso sai yace inba yaya nombashi ya kira shi nabawa yaya ya kirashi ashe zai turo da kudi sai min ticket ne yakuma bawa yaya din wasu kudi.
Ranan monday na dawo lagos da karfe goma na safe muka sauka lagos din bansan wazai zo daukana ba don da niya ta in shiga taxi a kaini har gida.
Amma sai ganin Sulaiman nayi shida kanshi yazo dauka na ban ma san yadawo kasar ba sai dai yanzu da na ganshi.
Bayan an gama saka kaya a motar shi ya dauki hanya dagani sai shi a motan sai da ya fara tuki ya dan kalle ni a daidai lokacin da nike mashi sannu da zuwa.
Yace ai yanzu ke keda sannu da zuwa bani ba yace yaya ki ka barsu acan nace lafiya kalau suke sun ce ai masu godiya a gun ka.
Yace namay fa nace daiwaniyan da kasha na bari na in zo masu buki har kwana goma sha hudu.
Murmushi yayi yace wanan sakon yaya saadu ne ko don shine namiji dan uwana shiya san irin halin da na shiga don ba karamin hakkuri nayi ba da na barki kika tafi.
Dan kallon shi nayi nace kai uncle kamar a gidan ka nake zaune zaka fadi haka.
Ba tare da ya kalle ni ba yace in a gidana kike ai bazaki tafi ko ina ba saar ki guda yanzu baki zo gidana ba tukun.
Ban iya magana ba nayi shiru yace zan so ace kin fara koyon nisa da mutane don na fada maki matata bata yau yana daya daga cikin abinda ya dani da mata ta tafarko.
Bayan wanan magana babu wanda ya kara furta wani abu daga cikin mu har muka kawo gida ya shiga da mota ya tsaya bai barni na shiga ciki.
Mun tsaya yana kara min korafi dadewan da nayi ban dawo ba na ce in sha Allahu zan kiyayye a gaba ya lumshe ido yana bude min motar na fito da sauri kamar wacce za a kama.
Ina shiga Faiza ne kawao zaune a falo tana karyawa tana gani na ta tare ni da fara,a a fuskan ta tare da tambayana yaya gajiyan buki.
Ban dade wurin ta ba na kwashi kayana da security din gidan ya shigo min dashi zuwa dakina ba bata lokaci na fada saman gado ina tunanen tsaurin ra,ayi irin na sulaiman daya fara nuna min tun ban shiga gidan shi ba.
Barci ya dauke ni maitsawo ban falka ba sai biyu da rabi koshi don sallah na tashi bayan nayi sallah na dan gyara kayana sai na fito falin gida.
Babu kowa a falin sai tv dake aiki shikadai a falon nan na samu wuri na zauna tare da kokarin bude wayana miscall din yaya Saadune a wayan har kira biyar yai min.
Kiran shi nayi ya dauka da korafin ina na shiga tun dazun yake kiran wayana ban daga ba har hankalinshi ya tashi sai da ya kira Uncle yace mashi na iso lafiya.
Nace wallahi yaya barci ne ya dauke ni sai yanzu na tashi naga miscall din ka yace har kin daga muna hankali kin isa lafiya ?
Nace nace lafiya na isa yaya yaya safiya da mamanta yace gasu zaune suna gaida ke mun dan taba hira yace bari na barki ki huta sai mun sake waya nagode kwarai safiya da zumuncin da kika raya.
Nace ba komai yaya ai yiwa kai ne kamar yadda shima yake yawan fada min idan yayi min wani abin alheri ina mai godiya.
Bayan mun gama waya dashi ummina na kira ina sheda mata na dawo lagos yau take tambayana lafiyan su?
Mun dade muna hira nayi mata sallama na kashe wayan tare kwantawa a daya daga kujerun falon.
Sai uku da rabi anty ta dawo gidan tashigo falon ina jin muryanta na dago mukai arba tace a a mutanen kalaba ne aka dawo ?
Namike zaune ina mata sannu da zuwa bata amsa min ba takai zaune tana cewa yaya kika barsu nace lafiya anty suna gaida ke kuma suna godiya.
Tace ina sauran mutanen gidan suke bayan ta dan bi wurin da kallo, nace da ita suna dakin su bata kara magana ba sai ta mike zuwa dakin ta kawai.
Bin ta nayi da kallo ta shige na sauke ajiyan zuciya tare da komawa saman kujera na kwanta lokacin sallah yayi na shige nima ciki.
Tunda nayi sallah ban fito ba don banji kowa a falon ba don haka nima na zauna a dakina sai bayan sallah isha,i Faiza ce ta fara fitowa sai anty.
Can na fito dauke da tsaraban da na dawo dashi a hannu na su yan biyu na gani na suka nufo ni da sauri suna murnan gani na.
A gaban ta na aje kayan ina ce mata ga tsaraban suna nan anty tace cikin nuna jin dadi wanan duka namu kice dai mu muka haihu din.
Ballan cake din tayi takai a bakin ta sai yaran suka nufuta suna fadin suma a basu suci nan suka far ma cake din da ci tana fadin yayi dadi sosai wallahi.
Fira muke yi jefi jefi sai ta jefo min tambaya da cewa Sulaiman ko yazo ya ci abinci kai na kada mata tare da fadin ban sani ba anty .
Ta juya wurin Faiza tana tambayan ta ko ya zo gidan nan itama take cewa barci tayi wayan ta ta dauko tana lalaban layin shi amma bai shiga ba.
Taji tsuki tace wayan nashi ma a kashe yake tace Fati wai ba zata fito bane komay takeyi a dakin ne har yanzu ?
Aika yara tayi su kira Fatin sai gasu sun dawo wai ta koro su daga dakin basu gama fada mata ba sai gata ta fito tana wani shan kamshi ta daure fuska.
Nan take tambayan ta ko uncle ya shigo da rana tace tun dazu ina daki ban fito ba kawar da kai tayi daga gare ta.
Fati mun samay ku lafiya nace da ita bata amsa min cikin dadin rai ba wuce wa tayi kitchen ta hado abinci ta shige dakin ta dashi.
Ni dai ban dade ba na mike zan tafi daki sai take cewa da ni dan Allah kwashe min wanan kayan zuwa sama kafin in tashi.
Na kwasa nakai mata daki na dawo na gyara wirin a lokacin tana waya sai ga daya daga cin security din gidan ya shigo yana fadin oga ya kirana a waje.
Da sauri na dan juyo ina kallon anty da hankalinta yake ga wayan ta da take dakila sai ta dago take tambaya ko waye ?
Yace da ita Uncle ne daga Fati har Faiza suka kallo ni lokaci daya ban kulasu sauraren umarnin anty nakeyi a lokacin sai ta dago tace dani ba kiran ki ake a waje ba yau ban san may ya hana shi shigowa gidan ba.
Nidai na wuce daki don in shirya yayin da Fati taja dogon tsuki sai da suka kallo ta anty tace da ita wawiya kawai.
Nafito da shiri na nayi dan simple makeup sai dogon riga dana saka mai shara shara ligt green da takalma plat nace sai nadawo ban tsamani sun amsa ni ba na fita daga gidan zuwa wurin shi.
Yana cikin bai fito ba yana hango ni ya bude kofan motar ina karasowa wani kamshi ya daki hanci na a raina nace uncle ke nan badai kamshi ba kan.
Sannu da zuwa nace dashi ya sauke ajiyan zuciya tare da karasa fitowa daga cikin motar yana amsa min.
Ya gyara tsayi yana ce min yaya gajiyan hanya naga alaman baki gaji ba na katse shi da fadin yaya akayi yau baka shigo cin abinci ba ?
Ka bar anty tana tambaya yace nayi tunanen hakan sai dai idan na shiga ne ba zan samu ganin ki ba shiyasa nayi shawaran na fara kiran ki tukun.
Nace OK,
Tambayana yayi wasu kaya nafi sakawa sai kuma yace koda yake naga kin fi son irin wanan kayan da kika sa.
Murmushi kawai nayi batare da nayi magana ba yace ina son kafin nan da sati biyu a kammala komai daya kamata ayi sai a saka ranan buki.
Nidai har lokacin ban yi magana ba sai yace ko zancen bai maki dadi bane ina magana kin kyale ni ba amsa.
Uncle may zance ni yanzu duk abinda anty tayi daidai ne ni ba ruwana a zancen yace OK yanzu bari mu shiga sauran magana mukarasa a waya tunda baki iya magana a fili.
Na sake cewa uncle ba magana na bane don Allah ka bari mana na fada a tsigar shagwaba ya nuna min hanya alaman in wuce mu shiga.
Make kafada na nayi ya gane abinda nake nufi sai ya fara hanya na biyo shi a baya a tare muka shigo falon da sallama.
Tana shirin shigewa daki sai gamu ta dago tana kallon mu ba ita kadai ba duk wanda ke falon kallon mu yake yi a lokacin da muke shigowa gidan.
Ta bishi da dan hararan wasa tana cewa ai na dauka yau yajin shigowa gidan kake yi don ko da rana baka shigo ba akace.
Yace yana zama wallahi ban gama abinda nakeyi bane a bakin ruwa shi ya dauke min lokaci tace yau kuma abin yar tsayuwa kofan gida ne kawani aiko wai a kirama safiya ?
Yace No na kirata ne taimin iso in shigo kin san yanzu kin zama antyn mu ta harare shi tace waye antyn ?
Ni dai ban zauna shigewa nayi na barsu a nan suna wasan shammatan juna su ina kokarin cire gyale naji anty ta kwala min kira.
Da sauri na fito daga dakin tace ba mutumin abinci mana kin shige daki kuma kafin in juya yace No ta barshi kawai i am ok.
Yau ban jin cin komai tace yanzu naji magana amma da na dauka ko kana yajin cin abincin gidan namu ne yanzu.
Jin haka yasa najuya zan wuce tace kaga mutanen kalaba sai yau taga daman dawowa garin kallon ta kawai nayi na dan yi murmushi .
Yace na ganta har tana wani wai bata so ta dawo yanzu don ke ta dawo garin yau.
Tace ai da baki tafi kin barni ba kika je can kika zauna abinki hankali kwance.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92Next page

Leave a Reply

Back to top button