BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

Kuyi hakkuri please kadan kuka samu
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:10 PM – Ummi Tandama: BAHAGON , , , , ,
????????5️⃣????????
DON ALLAH YAR UWA IDAN BAKI IYA HAKKURI DA YANAYI, NA ROKEKI KI AMSHI KUDIN KI TUN RAYUKAN MU BAI BACI BA DA JUNA , KOMAI NA RAYUWA ALLAH KE BADA IKON YIN SA DON HAKA MUYI HAKKURI DA JUNA, , , , ,
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON BA A YAFE BA.
IDAN KIN FITAR MIN DA NOVEL ALLAH ZAI KARBAN MIN BASHI NA A WURIN KI
Da asuba na fito tsakar gida ina shara don kasancewan ummi ca mai girki ranan.
Ummi na gani ta fito daga dakin ta cikin zumbulelen hijjabin ta na sallah idanuwanta na zubar da hawaye.
Kai tsaye ta nufi hanyar kofar gida tsatsiyar dake hannuna na aje na nifi wurin ta da sauri tare da riko hijjabin ta nace.
Ummin mu ina zaki ?
Tajuyo hawaye na zuba a idon ta cikin raunaniyar murya tace dani.
Gidan mu zan tafi .
Take nawa idanuwan suka ciko da kwalla don nasan wannan tafiyan da zatayi bana lafiya bane cikin rudani nace mata.
Ummi may yasa zaki tafi kibarmu cikin gidan nan ?
Batayi magana ba sai hawayen daya karu a idon ta ta juya taci gaba da tafiya atake na fashe da kuka mai tsuma rai.
Na bita muka fita waje ina cewa ummi hakkuri zakiyi dan tafiya kibar mu a haka cikin wannan gida ba shine mafitaba.
Tace dani gidan mu zan tafi na gaji da wannan zaman na kunci da bakin ciki.
Na sake cewa da ita kiyi hakkuri ummi watarana sai labari, sai ta dan kalle ni tace dani .
Haba yarinya da ace za a daina ai da an daina shekara nawa ana bu daya shikenan mutum tsakanin ka da mutane babu zaman lafiya .
Duk gida an tsane ka har ku yashafe ku sai yaushe wanan halin zai kawu.
Ina shirin bata amsa baba ya fito don zuwa sallah yana ganin mu har yaso cewa su waye a nan ?
Ko ya gane mune sai yaja tsuki ya ce ai ki kyale ta tafi tunda har yanzo ita bata san tai hakkiri ba sai ya wuce.
Nace da ita ummi ki daure don darajan mu ki koma tace yaya basu hana na kwatar wa kaina yanci ba.
Dakyat ta yarda muka koma ciki munyi arziki mutanen gidan basu fito ba har ta koma ta shiga dakin ta.
Shi kan shi baba da yaga bata tafi ba da alama yaji dadin hakan don yasan abune mawuyaci ta tafi gidan su su kyale ta ta dawo din.
Hakana muka wuni agidan cikin bacin rai sai dai ina yi ina kara kwantar wa ummi din da rai.
Da dadare baba ya dawo baiga dan dakin mu a waje ba ya shigo dakin namu ganin ya shigo yasa mu fita dakin na shimfida mu tabarma a waje muka zauna.
Ummi na zaune a bakin gadon ta ya samu wuri ya zauna a kusa da ita yace Rabi niban san ina hakkirin ki yaje ba yan zu.
Har yarinya karama zatafiki tunane, ina iya hakkuri na gurin naga na kyautata maku amma hakan ya gaza samuwa.
Kiyi hakkuri don Allah ki yafe min ba laifina bane nakan rasa may ke yawan kawo maku wanna matsalan.
Ummi dai bata tanka shiba ta kawar da kan ta gefe daya don bata son ko kallon shi balle ganin shi.
Ganin haka yasa shi mikewa yabar mata dakin yana cewa a bani abinci na ci ya fice.
Ya nufi hanyan fita ta bishi da hararan tsana don kwata kwata ta gaji da shi zaman auren dai sukeyi ita bata ga wani amfanin hakan ba.
Ta mike tana jin wani tukukin bakin ciki a ranta ta rasa yaya zatayi ta magance matsalar dake damun ta a ranta batare da wani yaji ba.
Matsawan tana son kawa karshen auren nan sai dai idan nata auren zai tabo ne hakan kuma tonon asiri ne gurin yayanta
* *
A gurin mutanen gidan mu muke jin wai su gwago zasu zo ai maganan auren mu da dan ta .
Zan iya cewa kowa a gidan mu bai san wanan mijin da ake cewa anyi min ba a cikin yara don haka aka matsu da su zo din .
Ba wani yi gyara ba balle kwalliya don taron bakin da zasu zo, ranan weeken ne don haka kowa yana gida bamu fita ba.
Muna zaune a cikin dakin hira muke da ummi na ina dariya mukaji ana masu sannu da zuwa da bakin lagas.
Gwago ce ta fara shigowa gidan ita daya mutanen gidan mu sai raba ido suke suga mikin nawa.
Suka kwasa sukayi dakin mama a ca aka shiga zuwa gaida ita dakin na mama
Ummi ce ta fara zuwa cikin mu taron ta gidan yawa da gulma nan aka saka ido akan ta.
Ta gaida gwago bata tsaya ba ta dawo dakin ta ta umurceni da naje na gaida ita din , na saka wani tsohun hijjabi a jiki na fita.
Daga kofa na tsaya nake cewa gwago sannu da zuwa ta juyo da sauri tana cewa karaso mana ciki Safiya.
A hankali na taka na shiga dakin na tsugun na kasa take cewa dani a a baki san yau zamu zo bane banga kiyi kwalliyan taron mijin naki ba.
Na dukar da kai na kasa take cewa dani tare muke suna nan kofar gida kin san shi ba mai son shiga mutane bane.
Haka yake tun yana karami da gudun mutane amma yi saa ya yarda ya biyo mu ne.
Sai mama tace ai shi hali shi tun na kurciya yana nan mashi ke nan baya son hayaniyan nan dai kamar yadda na san shi ashe ?
Ina suke ban dago ba take cewa dani maza ki shirya ki samay su a kofar gida.
Na tashi simi simi na fita daga dakin na koma dakin mu na zauna ban fadawa ummi abin da tace dani ba.
Sun dade da mama daki sun kashe murya sai zuwa can mama ke cewa safiyan tana can waje ne har yanzu.
Yar wurin mama ta amshe da cewa bata fita ba tana nan gida sai mama din ta taso tazo har dakin mu da kan ta tana min fada.
Hijjab din ummi na salla na zura a jikina na fita idanuwan yan gidan mu caaa a kaina
Na samay su su biyu a waje na karasa wurin su da sallama a bakina ko wanin su ya kunna taba yana zuka.
Jin sallama na da sukayi dayan yai saurin kashe taban hannun shi shiko dayan ko a jikin shi bai masan na zo ba.
Sun saka kida na tashi kamar gidan dj mutum ya shiga da kyat na bude bakina saboda warin taban da yacika wurin ina jin kamar zan yi amai.
Na kara gaidasu cikin murya a sanyayye sai gudan ya amsa min dayan wanda nake ganin shine dan gwagon mu yana dai zaune.
Sai can gudan yace dani a, a ko ke ce Safiyan a hakalin na bashi amsa da eh da sauri ya dago kai ya kalle ni, na sake cewa kunzo lafiya.
Mai maganan ya bani ansa da lafiya kalau mun samay ku lafiya ya karatu nace Alhamdullahi sai nai shiru.
Jefi jefi can yace barin dan taka wurin mai shagon can na sayo abu nasan yayi haka ne don ya dan bamu wuri.
Tafiyan shi ke da wuya shiru ya biyo baya har na wani lokaci sai naji yace barka da fitowa.
Nace barka mu da wuni.
Yace ya kike lafiya na bashi amsa.
Na jingina jikina da motar su don na gaji da tsayuwa yace da fatan anyi maki bayani a gida.
Sai na girgiza kaina nace ba wanda yai min baya ni an dai ce nazo na gaishe ku.
Ya ce Ok in kin koma za suyi maki yace ina dai fatan kin san abu ga makaranta don naga kamar har yanzu da saura.
Ko da yake wannan matsalar gwagon ki ne nace dashi namu dai.
Yadda na fadi maganan sai ya fahinci ko ban gane dukkan abin da yake fadi ba.
Yace ina baki fahinci magana ba cewa nayi iyayyen mu sun yi cewa zasu hada a tsakanin mu sai dai ni a tsarin rayina nafison macen da ta mallaki hankalin ta .
Macen data waye tasan duniya ya nunani yace dube ki ina ganin duk baki fi shekar sha hudu ba in ma kin kai.
Na yi wani gajeren murmushi nace to yaya na iya da zabin a kaina babu komai sai dai nima in son samu na samu yaro sauriyi mai shekaru kalilan wanda zai rike ni tsakani da Allah.
Amma tunda iyayye suka sani babu komai Allah ya tabbatar da alheri a tsakani.
Yaji haushin amsan da na bashi yace ba laifi nima hakan zan daure nai maneji dake kafin kan ki ya waye.
Nace abin na da sauki tunda kaima da wayewar iyayye kake kuri tunda sun sani nasan da sannu zai waye din kaga ba maganar na waye ko ban waye ba dole ne nayi biyyaya ga magabata na.
Tun da sune masu iko dani banice ke da ikon kaina ba zanyi biyyaya a gare su.
Ya sake jin haushin magana na amma a fili yacewa yayi ashe ra, ayin mu yazo daya kenan kan biyyaya ga magaba tan mu sai ki shirya zaman ukuba a tare dani.
Nace insha Allahu in yin hakan shine farin cikin mahaifi na a shirye nake da na rugumi duk wani ukuba da zan sama a gidan ka.
Sai ki shirya ke nan yarinya don ba zan yi renon banza a rayuwa na nace dashi Allah ya shige muna gaba.
Nace idan ka gama zan koma ciki hanya a bude take maki zaki iya tafiya sai dai kina da daman fadawa iyayyen naki irin ra,ayin .
Na dan yi jim na wani lokaci sannan nace dashi idan son samu ne kaine babba kai ya kamata ka tun kare su da zancen.
Saboda kai zasu fi daukan zancen ka da muhinmanci ya ce yin hakan ba zai yuyu a gare ni ba amma ba matsala.
Ya fara dube dube a cikin motan nidai duk warin taba ya ishe ne a wurin gani nake kamar a kamfanin taba na shiga.
Sai naji yace dani ga wannan kya kara kisai littafi da biro, sai na girgiza kaina ba tare da nakarba ba nace ka barsu na gode ina da wadatar littafi da biron.
Ya langabar da kai tare da karya harshe acikin turanci yace you will regret later sai kuma a harshen hausa yace ai ba cewa nayi kina da matsalar su ba,
Nace to na gode ban karba ba na fara tafiya yace to shike nan, na soma takawa a hankali shi kuma ya bini da kallon tsana.
Bayan na ahiga gida dakin mu na nufa yayin da masu gulma an zuba ido a ga abin da zan shigo dashi.
Tun shigana gida san bani da natsuwa ziciya ta kwata kwata bata natsu da wanan hadin ba ko banza bai a cikin tsarin mazan da nake so.
Wayewan shi yayi yawa bai laifi yana da tsarin maza amma dai tsarin dan maciji don farine dogo ga iya gaye komai nasa karfafa ne amma ziciyan sa da jikin shi babu tarbiya a ciki.
Sai dai ban da zabi akan haka don bani da ikon bijirewa maganan mahaifina don haka naci alwashin tursasa zuciya na da hakkuri koda kuwa yin hakan zai rasa farin cikina.
Sai da gwago ta gama abin da takeyi ta fita zuwa waje zuwa can ta dawo ciki da wasu ledaji a hannun ta.
Ta nacewa ga wannan na sarakkuwa nane kayan mun gani muna sone muka zo dashi zan dawo idan yaya ya dawo gida mu gana kafin mu tafi.
Har suka tafi ban sake ganin shi ba nadai ji labari cewa sun tafi an tsaida bukin mu da zaran na gama karatuna wanda yazo saura wata uku mu kanmala.
Ba waya ke gare ni ba balle ya dinga kirana haka yasa ban ji daga gare shi shima baiji a wurina.
Na dan kwatar da hankalina don na fuskaci jerabawan dake tafe min na final exam da zamuyi duk da ban sa rai ga cewa zan samu ci gaban karatun nawa.
Kulliyomin ba wani kwaciyan hankali a tare dani gashi duk biyayya da nake keyi ba gani akeyi ba don saida yakai an hada gwago fada da baba na da ummi wanda nasan bakowa yai wanan hadin ba sai mutanen gidan mu.
Har yakai ummi na ta kasa hakkuri tai tafiyan ta gidan su sai suka koma fadin cewa don tagacewa buki na ya taso ne ba ta aje komai ba yasa ta tafi gidan su wai.
Wanan tafiyan na ummi shi ya rage muna walwala sosai dani da kan ne na a gidan ko yaushe ina daki ina barzan kuka.
Yan kane na sukan damay ni da tambayan yaushe ummi zata dawo idan nace ta tafi gidan su kila ba zata dawo ba sai su fashe da kuka.
Na rasa mai ke mun dadi gashi nima dake dan kula dasu ana ahirin yi min aure a lokacin duk da ba wani alaman shirin aure da akeyi a gidan namu .
Don ban gani a kasa ba kamar yadda idan za ai buki ake ta faman shirye shiryen buki agidan namu.
Ban san may mama tagani ba ta sako dama sherin na wurin inna don ita ce tace wai ummi na na fadin sai da gwago tasan cewa dan ta bai da tarbiya zata ce a hada shi da diyar ta.
Ta fadi maganan wurin yan uwan su mama da suka kawo kaya gidan mu su kuma suka kwasa suka je suka fadawa gwago maganan .
Nan gwago ta shiga fada tana zagin ummi wai damay diyan ummi sukafi diyan ta don ma za a rufa mata asiri a auri yar ta.
Ta aikowa baba magana akan cewa ya ja wa ummi kune ga baganan da take sake mata shi kuma baba bai tsaya binke ba yai cikin ummi da masifa har yana cewa tana bakin ciki da hurdan da yake yi da yan uwan shi.
Shine akan wawiyar yar ta take son hada shi da yan uwan shi ta bata isa ba wallahi idan bata iya ganin auren haya a bude yake mata ta tafi gidan su.
Ita kuma ummi ta kasa hakkuri ta mayar mashi da ansa cewa ba tai bakin ciki da su ba sai yan zu inma tayi bakin cikin ai dole ne don ba aiwa yar ta adalci ba ai ga yannan ta agidan abadasu mana.
Rikici yai rikici don itama ummi ba raga masu ba wannan karon ta rufi idon tamayar masu da mai zafi.
A karshe sika kwasa da baba har yakai tabar gidan cikin dare duk magiyan da nake mata bata tsaya ba.
Mama ta sulce jiki ta samu wani wan baba ta fada mashi halin da ake ciki ta kuma ce a gaskiya ita bata taba jin ummi tai wannan maganan ba.
Baba musa ya samu babana sai cewa baba yayi dashi ta tafi mana idan hakan yafi mata alheri.
Baba musa yace dashi matsala gidan ka baka bincike baka kuma son a fada maka gaskiya kun samu boyar Allah kuna cuta mata ita da diya ta cikin gida.
An tabbatar min da cewa bata fadi wanan maganan ba yau kake da Rabi a gidan nan ya kamata kasan abida zata iya aikatawa da wanda bata iyawa.
Nan dai suka rabu da shi babu dadi ranan da yamma da baba ya dawo gida yana ta fada da baba musa.
Mama tace dashi ai bai fadi karya ba gaskiya ya fada wa ya taba ji a gidan nan lokacin da Raba ta fadi hakan.
Sai inna ta caraf tace kina nufin ke nan karya ne sheri akai mata ai idan bata fada anji ba alama ya nuna hakan.
Yace kin ga idan ke zaki je ki dawo da ita ban hanaki ba ai bani na kore ta ba sherin ta ne yakore ta balle ku matsa min.
Yaya sani na gida zaune yana cin abinci yace baba a gaskiya maganan gaskiya kuna cin amanan boyar Allah nan ga mama ta fadi gaskiya tace bata ce ba ai shike nan .
Ke inna in kina rage sheri ki rage don ke ma diya mata ke gare ki gasu nan har guda biyar maki.
Tace to ubana baki zakai muna ko may yace ni gaskiya nake fada maki tace bako haka ba.
Ya mike yabar abincin da yake ci yace to tabar maku gidan sai kuyi yadda zakuyi da diyan nata.
Ya shura takalman shi ya bar gidan.
Sai fada ya koma tsakanin inna da mama tonon asiri ya tashi baba yana zaune yana jin komai.
Dole gidan ya koma babu armashi kowa na cikin damuwaidan ka cire inna da diyan ta suke an shuwa a gidan kawai.