BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

Mun isa lafiya motaci biyu suka zo daukan mu zuwa gidan shi harda Aisha duka muka tafi gidan nasa.
Mun samu an kara gyara gidan anyi abinda ban san gidan dashi ba ya kara wani kyau da daukan ido na juyo na kalleshi da mamaki ya gyada min kai kawai yana lumshe idanuwan shi.
Gwago da mummy sun kasa boye farin cikin su na ganin gida sai yaba kyawon gidan suke yi har muka zauna nan mai aikin shi ya fara gabatar muna da abinci.
Mun ci mun sha a tare dasu mummy da Aisha don shi ana sauke mu ya shiga ya canza kaya ya fito bayan ya nuna muna dakuna ya fita.
Tare da Aisha da mummy muka gyara dakin da ke zaman nawa tana da sakewa sosai don tana jana da hira sai dai nine ban sake jiki da ita ba.
Take fada min yaran ta uku yanzu duka mata ta barsu nan Abuja ne a wurin kishiyar ta nace Anty Aisha kina da kishiya ne?
Tayi murmushi tace mu uku ne ai dayar tana can bauchi don a can take aiki ita kuma dayar da suke nan dama anan ya aure ta.
Sauke ajiyan zuciya nayi batare da na kara magana ba sai naji tayi dariya tace kwantar da hankalin ki yaya na mai son yawan tara iyali bane.
Idan kika dubi yanayin shi rayuwan shi kaf na turawa ne don dan kaida ne shi sai kinyi da gaske kafin ki fahince shi amma idan kin fahince shi zaku zauna lafiya.
Ina son ki jajirce wurin hakkuri da kawar da idon ki a alamuran shi bai faye son mamuwar mutane ba don Allah Safiya ki taimaka muna ya ja mu a jiki dan yazo kice kadai hope din mu.
Murmushi nayi kawai nace a fili Allah yasa tace yayana yana da saurin fushi amma kuma yana hucewa a dan lokaci musasnman idan kai mashi laifi ka bashi hakkuri.
Tace ina fada maki halin shi ne don ki kiyayye don naga kamar ba wani sanin juna kukayi sosai ba.
A raina nace ashe akwai aiki kuwa ashe ganin kitse saman ruwa nake mashi ke nan sai naji tace idan kin ga ya tashi bai son magana kada ki damu kanki kidan nisance shi sai ya nemo ki don kada ku samu matsala tace bani wayan ki in saka maki layi na don mu ringa waya dake.
Na mika mata tasa layin ta ta kira ya shiga tayi adding dina a contact din ta isowan driver da kayan mune yasa mu fitowa daga dakin muna taron su.
Nan dai Aishan ta taimaka min muka kawar da kayan komai mukai mai mazauni munyi sallah la,asar mijinta yazo ya dauke ta tana mai ce min baya sati zata shigo ta duba mu.
Bayan tafiyan ta na sauke ajiyan zuciya naga yanzu may abin yi nan na fara shawaran ko girki zan dora muna amma sai na samu har mai aiki ya gama ko yana shirin wuce wa gida.
Wuein su mummy na koma na zauna nan muka fara hira dasu mummy ke cewa dani taji abinda kaunar mijina le fada min dazu don haka take son fada min .
Inyi amfani da baiwar da Allah yai min na mace wurin canza mashi halayen da suka ce yana da musali idan yai fushin ba kaucewa zan yi ba kokari zanyi in jawo shi a jiki ta hanyan yin kwalliya da girki mai dadi da nasan yana so.
In kuma tabbatar da na hada da addua da yaiwata sadaka din ganin haske ga alamarina in kuma yi kokari in koya mashi bin yan uwan shi ya saba dasu amma indinga boye sirina dana mijina tsakani na dasu .
Do ba komai nai ya kamata su sani ba tace kinga wanan yarinya da aka hadoki da ita to itace ido da kunnuwar uwar mijin ku.
Don haka koda zaki sake mata ba irin sosai din nan ba kada ki dingayin abu a gabanta do shine zai sa ta dinga kwasa tana fadi a gida.
Ga kayan kwalliya ga sutura Allah ya wadataki dasu don ha ki daure da yaiwata kwalliya ajikin kina lamshi da saurar su zurfin karatu ba shiba ba indan akwai kudi babu abinda mutum ba zai iya ba sai ki dan more ma wanda kika samu a baya.
Sai dai mijin nan naki naga mai wayayyen kai ne mai yuwa ya barki ki koma makaranta ki kara ilimi.
Nan dai muke sai biyar da wani abu ya dawo gidan lokacin naci kwalliya da wani English wear a jikina ina tsaye ina magana da zarah a falo yashigo gidan.
Sannu da zuwa mukai mashi nida Zarah bai amsa ba sai kallon zarah da yayi bat ta bar wurin kai tsaye yanufo inda nake tsaye.
Kai tsaye ya hada bakin sa da nawa ya manna min ragowar lemon plus din dake cikin bakin shi na rufe bakina da sweet din ina ce mai thanks.
Yace kin ga irin gaisuwar da nake so daga gare ki daga yau sai ki saba dashi murshi na sauke mai laushi.
Ya koma saman kujera ya zauna na wuce na dauko mai ruwa mai sanyi na kawo mai tare da kokarin zubawa a kofi ya dagakatar dani da amsan goran ya kwankwade ruwan roban gaba daya.
Yana sauke numfashi nace bakaci komai ba tun karyan safe ko?
Ido ya lumshe min na koma kitchen na hado mai kayan bukin da muka zo dashi na da alkaki da goran juice ya karba yana min godiya.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/15/20, 7:51 AM – Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , , ,

????????5️⃣6️⃣????????

NOVEL DINA NA KUDINE KADA KI KARANTA IDAN BAKI BIYA NA SAUKE HAKKINA A KAN KU MAI FITARWA KUMA UBANGIJI YA BI MIN HAKKINA AKANTA KO WACECE.

Bazan gaji da jan Allah ya isa ba a kanki mara tsoron Allah don ki gyara masu kike daukan nauyi a kan ki don baki san nauyin Allah ya isa ba zaki fadi ranan da nadama zata riske ki ko zata riskeka yadda baka/ki fasa fitar min ba nima ban gajiya da bin hakkina a kan ku dabara ta saura gyaraka/ki mara zuciya da gudun goben ta
Duk da gajiyan dayake tare da shi bai hanashi mike wa yana ce min sorry na barki ba bayanin komai a gidan.
Kamoni yayi ya mikar yana fadin muje kiga tsarin gidan naki ko ban musa ba na bishi yana rike dani yake nuna min ko ina na gidan.
Sai naga ashe kallon tsoro nakewa gidan dama duk ban san komao ba a tsorace nake kallon gidan ashe yace da fatan komai yayi maki yadda kike so.
Murmushin da yake so nayi masa daidai lokacin da muke komawa falon don zama yace yanzu may kike son a karo maki a gidan koda na nauin kayan kitchen ne nace komai yayi a yanzu daga baya idan ina so zanma magana.
Hannu na ya kamo ya danka min mamullaiyan da alama na gidan ne sai wani wanda ban fahinci ko na maye ba.
Kallon mamaki nake mai sai naji yace makulin motar ki ce tana waje aje sai ki shirya koyon mota yanzu sauran kuma na sauran dakunan gidan ne don ni ba zaunin gida ba ne koda bukatan shiga ya taso maki.
Ban iya magana sai mikewa da nayi na durkusa a gaban shi gwiwoyi na biyu na saman carpet din falon hannaye na biyu na dora a kan cinyan shi na fara zanbga mashi godiya.
Yace No no stop it safiya do you know how much i care for you?
Na gyada mashi kai hawaye na zuba min a idona bayana naji ya fara shafawa a hankali tare da share min hawayen dake zuba min a fuska da hannunshi na dama.
Cikin raunin murya na craking nace uncle dole in yi kuka ka nuna min kaunar da ban taba zaton samu ba a rayuwa na.
Sai naji ya sunkuya ya rungumoni zuwa jikin shi ya na zaunar danu saman kujera yake fadin you deserve morethan this a wurina kin dawo min da farin cikin da na cire tsanmanin zan sake samu a rayuwa na.
Yan zuma haka in bakiyi hankali ba ina dap da in baki kaina gaba daya ji nayi kamar dariya zai kubce min a hankali na zare jikina daga nasa na zauna kusa dashi.
Gaba daya rikewa bayi wai yau nice a cikin wanan rayuwan da na dade ina mafalkin samu wanda sai dai inga anayi a tv ko wani gida gani yau na tsinci kaina ciki tsundon.
Sai nake ganin abin kamar yar koyau na koma don ban saba da irin wanan rayuwan ba tun daga farko ji nayi yana tsiyaya lemon dake gaban mu a cup ya dan kurba sai ya miko min sauran gaba daya na zuke.
Naji muryan shi yana fadin baki ce min komai ba batun kara karatun ki ko da yake idan son samuna ne ki zauna gida as a house wife zai fi min dadi naki jinin mace mai yawan fita a rayuwa na sha fada maki hakan a baya.
Zan maki kokarin da duk wani abin da zaki bukata na rayuwa idan kin yi laakari da irin halin da muke ciki na rayuwa rayuwan ma har nawa take a gare mu yanzu ?
Na dago idanu na dan kalle shi kadan sai naga ya zuba min idanun shi yana yana sauraren amsan da zan bashi.
Haka yasa nayi saurin sauke idanuna kasa ina wasa da yan yatsun mu dake hade a hankali na iya furta mashi uncle na hakkura da karatu.
Kin hakkura fa kika ce da karatun na kada mashi kai alaman eh yanisa yace saboda may ke fa kika ce min kina sha, awan karatu a baya .
Na nisa nace yanzu na fasa a hankali.
But why , ?
Ko dan abinda na fada yanzu ne kika fasa cika burin ki ?
Nace a hankali eh to duk mai hankali yayi tunane haka din ne don may kuma nake bukata ga karatu yanzu banda in zauna dakina in nemi ladan aure.
Don maganan ka gaskiya ne har wani rayuwa zai ba ni shawa yanzu kuma bayan wanan da nake ciki indan nayi duba da dafin mutuwan da ke a jiki na karatun ma karshen inyi ban mora ba gara kawai in zauna in rugumi kaddarata da hannu biyu yafi.
Yace hakan yayi maki don ban son daga baya ki koka dani ko kadan duk da zanyi iya kokari na wajen kare maki hakkin ki dana bukatun ki.
Na na insha Allah yayi min zan zauna in kula da gida da bukatun ka na lura kaima hakan yafi maka don dai kaga ina sha, awan karatun ne ka mara min baya akai.
Guntun Murmushi naji yayi mai alaman da magana na dago kai na kalle shi sai yace hakan na dakyau don kin fara cinye jerabawan da nake gwadawa akan ki.
Saboda haka nayi maki alkawarin zaki rika amsan albashi kamar yadda nake ba sauran maikatana duk wata.
Katse shi nayi da fadin a a Uncle gaskiya ni hakan ya, , , , ji nayi yarufe min bakina da hannun shi tare da fadin Shhhh, , , , .
A hankali yace min shine magana na don may ake aiki ba saboda neman kudi da tallafa ma kaiba don haka shawaran da na yanke ke nan a kan rashin karatun ki.
Duk kuma lokacin da naga kin samo sallon batani da irin takon ku na mata sai in canza raayina zuwa wani nauin don kin san mace bata da wuyan bata namiji da halin ta don gashi kwana nawa da auren mu har kin koya min rasgin zama gurin aiki gashi yanzu sai da na dawo gida don ki.
Mikewa nayi tsaye ina kokarin gudu cike da jin kunyan shi amma sai ya kamoni zuwa jikin shi yana fadin.
Where do you think you are going ?
Yana sakin dariya yana kokarin janyoni jikin shi ina fadi kada mummy tafito fa ta samay mu haka yace may zai kawo mummy nan part dina.
Da kyat na samu ya sake ni koshi don an fara kiran sallah ne a lokacin don haka muka watse zuwa sallah.
Da dare har dakin da su gwago ke ciki ya samay su akan yana son su fito muci abinci tare dasu basu so ba amma haka suka fito yana jan su da fira har suka sake jiki da shi suna cin abincin.
Bayan mun gama na kwashe kayan ya zauna dasu suna mashi hira anan yake fahintar yaya Saadu company da yake aiki dasu yanzu sun durkushe.
Ni dai daki na koma na fada wanka don naga sabon angon nawa ba na wasa bane wurin son tsabta da lalubar mace bayan na shirya waya na dauko muna magana da Amina don wani ruwa da ta bani ina son tai min bayani akan shi.
Nan muka tsaya tana min hira bayan komawan su gida yadda suka kwasa wirin rabon kudin da aka basu tukwaici acan.
Kofa naji an turo ko ban duba ba nasan cewa shine ya turo kofan dakin ya shigo yana tsaye da jallabiya baka mara hannu.
Ya rike cup yana shan abu a ciki sai dai bani iya cewa ga abinda yake sha a cup din kai tsaye ya nufo ni sai da ya zuke abinda yake shan ya tambaye ni da kin sha maganin ki kuwa ?
Kai na girgiza mashi alamar a a zama yayi yana fadin dauko tare da fadin kina wasa da shan magani ko safiya baki san in kin kiyi kwana daya baki sha ba zai iya tambayan ki ba.
Mikewa nayi na bude wardrobe dina na dauko kwalin maganin ina barewa sai yace miko min in gani ya karba ya dan duba sai ya miko min tare da fadin akwai wanda na anso a italy zan baki ki gwada sai dai yana da matukar karfi sosai idan kin sha zai sa ki cin abinci sosai amma yana aiki sosai a jiki.
Kofa na nufa don in dauko ruwan da zan hade maganin dashi sai naji yace dani no barshi in munje daki kya hade.
Kallon shi nayi da sauri yace yes dakina zamu yau ko kin fison kullun dan kwali ya jawo hula har a saka muna ido a gidan.
Don ni gaskiya ba yanzu nake son gwago ta koma ba so nake ta dan zauna damu na dan wani lokacin kafin a maida ta in son samu ne har da mummy din don matar na da dadin zama.
Murmushi nayi nace uncle ai sai kasa a zage mu daga kawo amarya sai su samu wuri su zauna.
Ina fadi kamar zanyi kuka yace common wa zai san ma suna gidan nan balle a fadi haka ko baki son zaman su ne sun takura maki keda angon ki.
Wani kallo nayi mai na ba haka bane sai naji ya sukkuce ni bai tsaya dani ko ina ba sai tsakiyar gadon dakin shi.
Da kyat ya barni na sha maganin nawa duk rokon da nake mai baijini ba sai da yayi abinda yake son yi ya samu natsuwa.
Washe gari su yaya Saadu suka iso Abujan don daukan mummy su tafi amma sai Uncle ya dinga masu delay da tafiyan sai da suka share kwana hudu tare da mu.
Ranan da zasu tafine yaya ke gaya min Uncle ya dauke shi aiki a company shi tare da bashi wuri zama da iyalin shi kuma yaya sani zai zo don shima an sama mashi aiki anan.
Nayi murna kwarai ko banza nima na samu dan uwa a kusa dani yanzu abokin shawara ga matar shi Samira akwai shiri sosai a tsakanin mu da ita.
A ranan na biyar suka kama hanya nan suka barni cike da kewan su don dan zaman da mukayi ba karamin jin dadin hakan nayi ba.
Gidan ya rage daga ni sai gwago wace da kyat a rana ta fito falo sau biyu ko yaushe ta daki daga sallah sai lazimi tana kallo.
Sai in dare yayi ya dawo gida zai dan je gunta su dan taba hira wani lokaci har da ni sai Zarah da har yanzu bata gama sake jiki dani ba sai dai akwaita da son kallo ko yau a cikin kallo take ita.
Na tambaye ta karatu fa take ce min ta gama secondry bana jiran jerabawa take yi yanzu ina kula dashi da duk yazo ya samay mu da ita zaune sai in ga ya daure fuskan shi har yarinyar ta dan shiga tsarguwa da taga lokacin dawowan shi gida yayi zata shige daki bata kara fitowa kuma.
Ranan ina tambayan shi may sa yake mata haka sai cewa yayi dani cikin tsawa gada ki kara yi min maganan wanan yarinyar don ba zamana takeyi ba a gidan nan .
Da sauri nace Uncle in ba zaman ka takeyi ba zamanwa take a gidan ina kai hajiya taba ita muzo da ita don debe kewa bai yi magana ba sai mikewan da yayi ya fice dakin ya koma dakin karatun shi ya zauna.
Nikan abin ya daure min kai sai na ja baki na nayi shiru har naje gun gwago na zauna muna hira hankali na yana gurin shi don haka nace ma gwago ina zuwa.
Kitchen na shiga na hado mai snack da drinks na nufi dakin da yake da sallama na tura kofa ban tsanmani ya amsa min ba sai dai dan juyowa da yayi ya mayar da kanshi ga abinda yake yi cikin laptop din shi.
Sannu da aiki uncle sai da ya sauke ajiyan ziciya ya iya amsa min da yauwa sannu madam nace ga abin motsa baki nan na kawo maka kadan jika makoshin ka.
Na aje na juya zan fice daga dakin sai naji ya riko min hannu yana cewa ba tare da ya bar abinda yake yi ba bazaki karasa ladan ki ba kin kawo min abin sha baki zuba min ba zaki wuce.
Dawowa nayi na tsaya ba tare danayi magana na fara zuba mashi acin cup din dake saman tire din, mika mashi nayi tare da dan rusunawa.
Sai lokacin naga ya dauke kan shi saman sytem din yana fadin thanks nace aiki nane hakan ya zuke yana lumshe idanuwan shi.
Ya mayar da cup din cikin tire din yana maida kan shi saman laptop din jiki a sanyaye na fita daga dakin yana aiki yana cin dabun naman daya ji curry da kayan kamshi ya lumshe idanuwan shi.
Ban koma ta kan shiba na tsaya kitchen da falo na gyara ina gap da karasawa naga fitowan shi daga dakin har yanzu fuskan shi babu walwala a cikin sa.
Da gefen ido ya kallo ni ya shige part din shi tare da rufo kofan da karfi araina nace ga maganan Aisha ya fito take maganan mummy ya fado min a rai.
Idan yayi fushi ke ki kwantar da fushin ki ki bishi sai zama yayi dadi amma kin hau namiji ya hau wazai kwantar ma wani da fishin shi wata kila ma fushin da dalili yake yin sa.
Dakin gwago na leka na gaishe ta nake gaya mata lokacin sallah ya gabato tace ai har na dauro alwala wanan gida naku ba ajin kiran sallah.
Dariya nayi mata nace baga agogo nan ya sayo maki ba don ya dinga kira maki sallah kina ji tace kaiya ban faye amincewa da wanan abin nasaran ba ai.
Nace yanzu dai da kinji ya kira sallah sai ki mike lokaci ne yayi baya karya sai idan batir din da yake aiki dashi ne ya kare tace bakaji ba.
Ina dariya nace gwago kafin ya kare fa sai nan da kusan wata biyu tace wata biyu ni ina, ina yar nan ai kisa a dauke mu mutanen banza nifa har na fara yiwa maigidan ki tunin gida don naga so kuke sai kinyi ciki ina gidan nan kulle kamar kurkuku.
Fita nayi na barta ina dariya kada in makara da dauro alwala a lokacin naga gittawan shi zai fita zuwa sallah don ko yaushe sallah jam,i bai wuce shi.
Bayan isha,i na gama komai har abincin shi yana saman table na koma daki na shirya tsaba a cikin wani dogon riga baki mai hanuwa shara shara yaji kwalliya har kasa da kananan duwatsu an dan buda kasan shi kadan.
Ban fito ba sai da na ji motsin shi a falo ya na sauraren News hakan ya sani fitowa daga daki ture kusan kala uku na shafe jikina dasu yan saudiya.
Kamshi ya hade da sanyin da AC falon yake saukarwa ya bada wani inrin yanayi a falon tun fitowa ya dago ya kalleni ya kauda kai yaci gaba da kallon TV dake gaban shi.
Har na karaso gaban shi cikin daurewa na karaso gaban shi na dan duka daga bayan shi tare da sagala hannu na daga bayan shi nace sannu da hutawa Uncle.
Dan murmushi ya sake da bai sauka ciki ba yace barka da gida madam din Uncle zagayo dani yayi zuwa gaban shi ya zaunar dani saman kujerar daga gefen shi yana mai ci gaba dakallon shi sai dai har wanan lokacin bai sake min yatsun hannu na da yake wasa dasu ba.
Cikin daurewa nace Uncle abinci fa yace dauko min nan zan ci na mike cikin wani tako da ban san na iya irin sa ba na nufi dining din kwaso kayan da na jera akai.
Sai lokacin ya sauke wani iri ajiyan zuciya har ina jin shi don na kusa kawowa wurin shi a raina nace su zuciya manya.
Ashe akwai aiki a gabana dan wanan magana yake ta jawa rai haka anya kuwa zan iya sai da na gama jerawa nace bissimillah na samu wuri a kasa na zauna tare da jan plate zan fara zuba mai.
Ganin kayan tare a gaban shi kashi kashi yasa yace min may ye haka yau John ya girka muna?
Banyi magana ba sai ci gaba da bude warmer din nayi inda na fara ziba mai tuwon shikafa da miyar shawaka da yaji agusi da manja sai nama manyan yanka da nayi amfani dashi wurin hadawa da dan man gyada kadan.
Kamshi me ya kaure falon alokacin da na bude ferfesun kifin dana hada wanda nayi amfani da kayan yajin mu na gargajiya sai ruwa dana zuba da maggi.
Gani nayi ya sauko kasa abin wanke hannu na jawo tare da dauko ruwanda na tanada don wanke hannun nashi.
A hankali ya miko hannuwa fuskanshi akan tv ina zuba mai ruwan ya na wankewa a hankali na jaye ruwan gefe guda sai ya kallo ni yace ke ba zaki ci ba nace munci da gwago da Zarah tun dazun dana gama.
Naga ya kara hade rai yayi bissimilla ya fara ci har ya kare bai yi magana ba ni dai ina zaune na saka ma tv ido nima kamar mai saurare abinda ake fadi nan ko zuciya ta tambaya kanta take yi mai ya kawo wanan matsalar haka wai ?
Naji yace amma ba John yayi abincin nan ba eh kawai na bashi amsa dashi na fara hada kayan ina kwashewa na barshi dana ferfesun yana sha a hankali yana kallon tv.
Bayan ya gama na kwashe na dauko kamshi na bude falon dashi yadda ba za a ji karnin kifin ba idan an shigo falon.
Zama yayi a kasan tare da jingina bayan shi da kujerar daya sauka a kai tare da mike kafafuwan shi a kasa yana kadasu a hankali zaman naji shiru yayi yawa don haka na mike zan leka gwago a dakin ta.
Yace jimana sai na dawo na zauna cikin basarwa yace gwago tayi min maganan zuwa gida yau da safe don haka nake son ku fita ai mata tsaraba zuwa gobe.
Allah ya kaimu nace sai na juya na wuce bina yayi da kallo komay ya tuna a ranshi sai yaga bai kyauta min ba sauke ajiyan zuciya yayi may ye laifina a cikin wanan magana daga tambaya kawai ya dora min laifin dabashi ba.
Nasan nayi laifi na kuma dauka ina binshi don yayi hakkuri ya kasa cire laifin da bani nayi shi ba akaina.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92Next page

Leave a Reply

Back to top button