BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/25/20, 10:38 PM – Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , , , , , ,

????????6️⃣4️⃣????????

NOVEL DINA NA KUDI NE IDAN KIN FITAR ALLAH ZAI FITAR MIN DA HAKKINA AKAN KI IDAN KUMA KIN KARANTA KI SAN HAKKINA NA KAN KI.

Yar uwa na fadi zan sake fada ban yafe ba idan kin fitar min da novel waje Allah yabi min hakkina akan ki don bayan yafe ba.
Idan kin karanta min novel baki biya ba ubangiji ya kwato min hakkina a gunki cikin gagawa.
Bakin mu sun tafi cikin dadin rai muka rabu dasu lafiya suna ta farin alherin da dan uwan su yai masu da zasu tafi koni nayi mamaki don a yanda uncle yake bakacewa yana da tarin arziki irin haka a rayuwan shi.
Kyaunta yamun dadi har cikin raina don yadda ya dauko yiwa yan uwa alheri ba karamin alheri bane agare ni don na fita zargi daga bakuna su.
Yadda nake jin suna zagin anty kan ta kakace komai da karshe akaina zagin zai dawo sai gashi ya sauya gaba daya wanda suke ganin wai nice na sauya shi hakan.
Ko yan uwana bai bari ba don kullun aiken shi na hanya zuwa wirin yan uwana da iyayyena sai dai inji sun bugo waya suna min godiya abinda ya aika masu din.
Gashi dana fara mai godiya zai daga min hannu alaman ya isa haka na sai da yayi dana gode mai bani fasawa.
Ba abinda ke mun dadi kamar yadda mahaifan mu ke sa mashi albarka har nima abin ya shafe ni don da hajiya baaba da babana ida sun fara mai addua idan ina kusa sai na lumshe idona don jin dadi.
Sai dai halin shi na fushi yanzu ya rage don baya wuce kwana daya yana fushi dani ko don cikin dake jikina ne yake raga min ban sani ba.
Don Uncle akwaishi da saurin fushi abinda baka dauka abin fada ba yanzu zakaji ya juye ya koma fada gare shi.
Sanin halin shi da nayi yanzu na gane bai son kana magana yana yi sai in ja bakina inyi shiru sai ya gaji ya kyale don kan shi.
Abin da kan yawan hada mu shine fita a dade duk da ba fita nake yi ba don bai bari na mami kowa a garin ba sai yan uwa tsiraru da muke dasu ko nafita sayen wani abu da zaran ya kira nace ban koma gida ba ya ishe shi jidali har wani lokaci.
Ya hana mummy komawa gidan yaya Saadu wai ta zauna dani har in kara jin karfin jikina don acewar shi ban gama warwarewa ba har yanzu.
Ina jin dadin zaman mummy don mace mai dadin zama ga sa mutum hanyan daya dace yabi na alheri ga kuma bata jin kiuya ko kadan aiki ba sha mata kai ga tsabata gidan nan ko yaushe kwal yake don tsabtan ta.
Hakan yasa ya yanke sharan bata albashi duk wata da farko taki karba wai ai an zama daya don yaya saadu yana kokari dasu.
Sai uncle yake cewa ta karba ai duk wanda ke karkashin shi haka yake masu shine dalilin karban kudin ta duk wata.
Yaya Saadu da matar shi samira sunzo kan hakan da yake yi sai cewa yayi shi in son samune ma mummy ta zauna damu tunda ba komai take yi ba acan.
Idan tana son zuwa ganin yaranta ba zai hana ba taje tayi kwanakin da zatayi ta dawo don shi hankalin shi ya kwanta da ita don ko na haihu dole ne ya nemo wanda zai kula da baby din.
Yaya Saadu yai mata magana kuma ta amince mashi din da hakan tunda dama zaman hakkuri takeyi can yara kowa ya kama gaban shi.
Muna waya da anty don dawowan nan namu na tura mata kudi wanda yake bani duk wata na hada dari biyar na tura mata don dai a zuna lafiya ni da ita don kawai na fitar da komai a ranta mu zauna lafiya.
Ranan nasha yabo a gunta take cewa in dan hada da dabara ina rika amsan kudi idan sun taro sai ta san abinda zatayi min dasu nace anty na gode.
Wanan yasa ko yaushe yanzu muna waya akai akai da ita ba kamar baya ba can da ta share ni din haka yasa han kalina ya kwanta yanzu don da ina cikin damuwa idan na tuna halin da muke ciki da ita na rashin shi.
Yau tun safe uncle bai fito ba yana dakin shi bayan na gama karyawa na nufi dakin shi don in duba shi sai na samu yana rufe yana barci haka yasa nayi zaton hutu yake yi kawai.
A hankali na jawo mai kofa na rufe sai naji muryan shi yana kirana don haka na tura kofan na koma ciki karasawa nayi bakin gadon da yake.
Murya ta alaman rashin lafiya yake magana da cewa don Allah hado min tea ki kawo min nan zan sha magani da sauri na duka ina fadin Uncle baka da lafiya ne?
Kai ya gyada min alaman eh sai nakai hannuna saman laulausar kan shi dako yaushe bai rabuwa da gashi irin na fulani yayi kwance lup a saman kan shi.
Zafi naji jikin nashi yayi nace subbahanallahi Uncle kuma kake kwance jiki ba dadi haka a gida gyara kwanciya yayi yace jeki hado min tea din don Allah.
Fita nayi da sauri nan dai na hada mai komai na dauka zuwa dakin har lokacin da na dawo dakin yana kwance a yadda na barshi na fita.
Bayan na aje ne na dan taba shi ina fadin ga tea din na hado maka Uncle ya dan yi mika tare da bude idanuwan shi ya sauke a kaina.
Ina tsaye akan shi cikin damuwa na kura mashi ido sai da ya dan jima ya mike zaune tare don son yunkurawa ya tafi ban daki nasan kewaya yake son yi amma ya kasa.
Tsoro naji sosai a lokacin nace in taimaka maka ne ka tashi ya dago kai yadan kallene sai ya girgiza kan shi yace hada min ruwa dai a ban dakin .
Na shiga na hada mai na dawo wurin shi har lokacin yana zaune a yadda na barshi hannunwan shi na rike sai ya dafa ni ya tashi tsaye da taimoko na ya je ban dakin ganin ya shiga ya fara tubewa na barshi na fito.
Wayana na dauko na kira yaya Saadu nake fada mai yau Uncle ba lafiya da sauri yace gashi nan zuwa yanzu ya dan jima ciki ya fito bai ko tsaya share jikin shi ya dawo saman gadon dana gyara bayan tashin shi.
Kurban tea din yayi bai sha wani abu ya koma ya kwanta tare da dan yin nishi nace maganin fa yace barin dan huta zan sha ai.
Ina tsaye a kan shi ina kura mai ido idanuwan shi a lumshe ina tunanen lokacin da yaya Ahmed yayi jinya ina gidan shi yadda yayi tayi mun a lokacin da yadda hankalina ya tashi gani ni kadai a gida dagani sai shi haka nayi ta jiyar shi har ya samu lafiya.
Nace kilama lokacin duk yana dauke da cutan yake jiya hakana ni ban sani ba saboda kurciya da nake dashi.
Wayana yai kara ne yasa nasan yaya Saadu ya iso ke nan da sauri na juya na fita zuwa wurin shi yana tsaye falo ko zama baiyi ba.
Ina fitowa ya tare ni yana fadin yana ina nace yana dakin shi bai tsaya ta kaina ba ya nufi dakin nashi da sauri ina biye dashi a baya nima da sauri nake mara mai baya hankali na yayi kololuwar tashi da yadda yake kwance sharaf.
Muna isa kofan ya shiga da sallaman shi uncle yana kwance a yadda na barshi ciki jin muryan yaya daji yasa shi dan dagowa kadan yana amsa sallaman da kyat.
Yaya ya karasa gun shi yana fadin yallabai yau jikin ba dadi ne haka yadan dago yana dan yake yace Saadu ta taso da kaine kuma ?
Yace wallahi fa na kirata mu gaisa sai take fada min jikin naka yau bakajin dadin sa sosai ya dan kara gyarawa yace wallahi ai duk kwanan nan karfin hali nake bana jin dadi.
Nabishi da ido da mamaki cike a fuskana sai naji yaya Saadu na tambayan shi ko zasu tafi asibiti ne sai yace kasan matsalan ciwon mu da zaran mutum yayi dan ganganci yanzu ciwon zai bugar dashi ne.
Akwai wani yaro dake zuwa nan gida ya kara min ruwa shima yana da irin matsalan tare dashi yana kokarin jawo wayan shi dake karshin filon da yake kwance akai.
Yace amma kafin yaron yazo barin in hade magani da zai saukar min da zazzabin don baa shan maganin sai aci abinci sosai.
Cikin marairai ce murya nace dashi a kawo ma wani abu kaci ne yanzu kai girgiza min ya bude baki da kyat yana cewa tea dana sha is ok for me.
Drower ya nuna min da hannu yace jawo wancan zaki ga wani dogon roba fari ki dauko min na isa wurin da sauri na tare da jawo drower din na dauko mai maganin.
Yaya ya karba naje dauko mai goran ruwa mara sanyi ko da na shigo na samu yana kiran mai kara mai ruwa din a wayan shi.
Jefi jefi yake jefo ma yaya magana wanda nasan don ya kwantar muna da hankali yake yin haka amma ta yanayin maganan zaka gane yana jin jiki karfin hali ne kawai irin na maza.
Doctor ya iso idan ya kira wayan shi yaya saadune ya fita don ya shigo da likitan dakin shi bayan fitan yaya ne ya kalle ni sai yaga ina hawaye a lokacin.
May kike ma kuka madam baki son in mutu in barki ne kai na gyada mai tare da fadin don Allah uncle kabar wanan magana haka insha Allah bazaka mutu yanzu ba sai ka tsufa damu .
Murmushin karfin hali yayi yace kaiyya ko daina wanan tunanen daga ni har ke ko yaushe mutuwa ai zata riskan mu koda ciwo ko babu ciwo don haka addua kawai ya kamata ki muna shine mafita.
Shigowan su yaya Saadu ne dakin da likita wanda yanayin shi ya nuna kamar kabila ne shi yake cewa yaya ga kaunar ka nan kuka takeyi wai bata son in mutu in barta.
Murmushi yaya yayi wanda nasan na karfin hali ne shima yace ki kwantar da hankalin ki Safiya in sha Allahu zai ji sauki.
Jikin dai ne nashi ya dan motsa mai kin san sha anin yau da kullun dole haka ya kasance ga bawa ko yaya ne don haka ki koma dakin ki kiba likita wuri yayi aikin shi.
Dagawa nayi jiki a sabule zan fita a dakin Uncle ya kirani yake cewa don Allah kada ki bugawa kowa waya banda lafiya har Aisha .
Kai na gyada mai na fice daga dakin raina ba dadi don duk na tsarace da ciwon nashi wanda dan lokacin kadan duk ya ramay kamar ya dade yana jinya akwance.
Ina fito sai ga mummy ganin yanayi yasa take tambayana ko lafiya taga Saadu yazo gidan ya shiga dakin maigida kuma.
Nace yau baya jin dadin jikin shi ne shine yaya saadu ya dauko mai likita da sauri tace subbahanallahi da sauki dai ko ?
Ta tambaya cikin son karin bayani nace jikin da sauki mummy nan muka zauna tana kwantar min da hankali har likitan ya fito dashi da yaya.
Yaya yace in je yana kirana sai dai kafin in isa dakin ya samu barci a lokacin nan dai na zauna wurin shi ina kallon yadda ruwan da ake kara mai yake shiga jikin shi.
Yaya Saadu bai dawo wurin shi ba haka yasa na dauka ko ya wuce office din sune ashe yaje ya sawo wani magani ne da fruit da dai wasu abubuwa.
Da ido yaya saadu yayi min magana na biyo shi muka fito daga dakin a falo muka tsaya ya juyo yana fuskanta na tare da cewa ki kwantar da hankalin ki.
Insha Allahu zai samu lafiya zazzabi ne mai karfi yadan bugeshi kin san mijikin baya hutu sai irin haka ya kasance dashi.
Kamata yayi ace ya ware wasu ranaku da zai rika zama gida ya huta don jikin nashi bai maison wahala bane ko kadan don Allah ki san yadda zaki kawo mai wanan shawara nima zanyi nawa kokari inga na fahintar dashi.
Nace na gode yaya yace shi zai tafi don suna da aiki akwai kayan da zasu shigo masu daga waje zai je yaga komai ya kammala a wurin.
Na sake mai godiya yace ba komai wanan ai duk ya shafe mu har zai tafi sai ya juyo yana fadin don Allah kada a tasheshi idan ba shi ya falka da kansa ba.
Mummy tafito jin muryan yaya tana fadin zaka tafi ke nan yace eh zai koma wurin aiki sai dai an jima zai dawo ya duba jikin nashi.
Bayan mun dayi magana da mummy na koma dakin wanda har lokacin ya sharar barci sai dai dan hannushi da ya dan karkace mai na gyara mashi a hankali hakan bai sa ya falka ba daga barcin da ya samu din.
Zaune nake na kura mai ido daga saman kujeran da nake zaune zuciya sai faman sake sake take min a kan shi ban sani ba har barci ya dauke ni a wurin mai nauyi nima.
Ban san tsawon lokacin da na dauka ina barcin ba shi ya fara falkawa ya hangoni zaune nake barci tausayi na bashi.
Don yasan wai gadin shi nake a haka barci ya dauke ni a gurin ya dade kwance yana kallon yadda nake barci a wahalce daga zaune.
Ga ruwan dake makale a hannun shi saura kiris ya kare a ledan jin kamar motsi yasa na zabura shi na gani a zaune yana cire roban ruwan a hannun shi.
Da sauri na mike na isa wurin shi ina fadin ka tashi yaya jikin na ka ina kokarin taimaka mai da ledan ta hanyar rataye ledan da allura sama.
Sai da ya dan dade zaune ba tare da yayi magana ba sai ya mike zuwa ban daki ya dan jima ya fito tare da dauro alwala zai yi sallah.
Nace dashi lokacin sallah yayi ne yace kina barci ina zaki san lokaci yayi anya haka ake jinya mai jinya barci mai ciwo barci ni dake wazai dubi wani a haka.
Murmushi nayi ina shimfida mai abin sallah tare da cewa wallahi ban san lokacin da barci ya daukd ni ba a haka zaune bai magana ba sai murmushi ganin ya tada sallah na nufi dakina don nima in gabatar da nawa sallah.
Na dade zaune bayan na idar ina kai kuka na ga Allah yabamu lafiya ni da mijina a wuri san nan na mike na fito abinci na fara hada mai nakai mashi.
Har lokacin yana zaune yadan kara jikin shi da bangon dakin kamar yana tunane na shigo dauke da abincin na zauna bayan na aje mai a gaban shi.
Ya dago kai yana kallona tare da da fadin zan ko iya cin abincin nan da dai fruit kika hado min watakila zan iya dan sha.
Nace uncle kayi ko two spoon ko three zaifi ka zauna bakaci komai duk yinin yau hakan zai iya jawo ma wani matsala kuma don Allah kadan daure kaci ko kadan ne.
Baiki ba na zuba mai ganin baya son ci yasa na karbi cibin a hannun shi ne debo nakai mai a bakin shi.
Murmushi yayi ya bude bakin ya karbi abincin yaci nima na debo nakai bakina don dai ya danci Alhamdullahi na samu yaci yakai cibi hudu yace ya koshi.
Mike nayi na kwashe kayan sai ya riko ni yana fadin ke ba zakici ba kin san fa kin finu lalura sosai kada kije ki haifa muna baby ba kosasshe ba.
Murmushi nayi nace nima fruit din zan sha idan na gyara hakan yasa shi ya kyale ni na fita da kayan nakai kitchen nan na tsaya na hada muna fruits salad.
Nan mummy tazo ta samay ni ina gap da gamawa take tambaya na yaya mai jikin nace da sauki mummy har ya danci abinci yanzu.
Tace a da sauki ke nan in dai ana cin abinci ai zai zo da sauki ciwon da ba a ci ba a sha ai yafi wahala ga mai jinya.
Nace muje ki duba shi mana mummy tace a bana shiga dakin mijin ki ba nace haba muje dai ai ba a kwance yake ba.
Ina gama mummy na bayana na shigo dauke da bowl din dana hada salad din daga kofa mummy ta tsaya take gaida shi ya amsa da mummy ne shigo mana.
Bata dai shigo har cikin dakin ba ta tsaya daga kofa tana mashi yaya jiki ya amsa da mummy naji sauki sosai tace Alaji ka dan dinga hutawa mana haba ga kunan kullun cikin aiki ba hutu.
Murmushi yayi yace mummy ai aikin nawa mai sauki ne da wanda ke yini a cikin rana ko yaushe jikin dai ne dama ba lafiya gare shi ba.
Tayi mashi sannu ta fita daga dakin ya mata godiya tana fita na zauna a kusa dashi tare da fara zuba mai yana zaune ya kura min ido kawai har nagama na miko mai.
Yakarba tare da fadin thanks gefe na koma na zauna tare da tsura mai ido da ido yayi min alaman in diba mana sai na kada mai kai tare da fadin ban jin sha.
Yau din baki shan fruits din nace na koshi ne sai naga ya debo ya mika min ba yadda na iya dole na bude baki ya zuba min amma sai naji yau abincin nawa ya koma min kamar madaci.
Da kyat na iya hade wanda ya rage min abaki na sai na samu kaina da tura kaina cikin kafafuna na dunkule a waje daya ina kuka.
Ji na ya kamoni zuwa jikin shi tare da dan bubuga min baya a hankali ba hana ni kukan ba sai da nayi may isa ta ya mika min ruwa in sha.
Ban ki na karba na dan kurba na aje kofin shidai yana zaune ya kukara min ido muryan shi naji ya katse min tunanen dana fara yi a lokacin wai may kike ma kuka ne haka.
Na bude baki nace Uncle bani son in rasaka cikin wanan halin da nake ciki kaine uwa da uba a gare mu idan na rasaka yaya rayuwa zata koma ?
Sai na fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciyan mai sauraron ta kamoni yayi zuwa jikin shi ya lalashi na wayan shine yayi kara a lokacin hakan ya dakatar damu da maganan da mukeyi.
Ji nayi bayan ya amsa wayan yana fada min ga yaya Saadu nan yadawo duba jikina yana falo.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92Next page

Leave a Reply

Back to top button