BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

* * *
Kwana uku shiru babu wani motsi a gidan kwakwara mama ta kara samun baba a kan zan cen.
Ta nuna mashi damuwar ta tana cewa malam ka dubi Allah kaje kadawo da matar ka ta dubi yaran ta yara sun koma kamar marayu a gidan.
Yace ina son zuwa sai dai ban san da wani ido zan kalli Rabi da shi ba don don iyayyen ta sun mani mutunci amma ni na kasa rike masu ya.
Gobe zan sami malam lawal ya rakani muje ko zata dawo in kuma ahi zai tafi wala ba a sa.
Mama cikin nuna damuwa sosai ta ce dashi da haka yafi don ace anyi buki yar ta bata gida gara dai ayi hakkuri.
Washe gari ana gama sallah asuba baba ya samu malam lawal da maganan yai mashi bayanin komai bai boye mashi ba.
Malam lawal yace a gaskiya baka kyauta ba da baka bincike a gidan ka ai yaron ka gaskiya ya fada a tare ake hade kai dakai ana cuta wa Rabi.
Sannan fa ka sani yanzu ba aiwa yaro dole samu da wayawan kai da aka samu ita yar uwar naka ta nuna dan ta tasani.
Gashi an fara samun haka tun ba a yi auren ba idan anyi akazo aka samu matsala wa aka cuta yar ka da uwarta.
Daga karshe dai baba ya nuna su tafi su kadai don shi yana jin nauyi da kunya zuwa ya tun kari iyayyen ta.
Sun isa garin da sanyin safiya sai dai basu samu mahaifin nata ba a gida amma yayan ta da kannen ta suna gida.
Bayan sun gaisa malam lawal yace dama mun biyo sawun Rabi ne don Allah ayi hakkuri ta koma tsakanin harshe da hakori ma ana samun matsala bare mutum da mutum balle zaman aure da ya gaji hakan.
Yayan nata yace haka ne amma naso ace shi malam Audu yazo da kan shi don ko mu a kauye mun daina wa yaran mu auren dole.
Bayan haka duk hakkurin da Rabi ke yi ita da yar ta baya gani sai da ya kora muna ita gida dom ya nuna muna ya gaji dasu.
To idan shi ya gaji dasu da ai har diyan nata ya koro muna mu bamu gazawa da su.
Malam lawal ya jijiga kai yace ai dai yi hakkuri a madadi na abokin sa ina bada hakkuri koma may nene ya hada su tsakanin miji da mata ne.
Hakan ba zai sake faruwa ba tunda idan mukayi laakari ai hakan bai taba faruwa tsakanin su ba tun suna zamanin kurciya yanzu da aka tara iyali.
Yayan ummi yace eh saboda hakkurin irin nata ba shine zaa ce bai taba faruwa ba amma ia duk halin da take ciki muna da labari.
Yanzu ko da anin ya isheta ai da kan ta ta ne may mu dama ranan muke jira don duk abin da yasa kaga Rabi ta bar diyan ta to abin yaya kamari.
Malam lawal bai gaji da bada hakkuri ba har mahaifin ummi din ya dawo gida ya samay su.
Nan su malam lawal aka shiga gaisuwa dashi nan dai malam lawal ya gabatar da bukatan su na bikon ummi din.
Tsohon yai shiru can yace a gaskiya Rabi bata taba yaji ba nasan halin Rabi da hakkuri abu daya zaisa na yarda na mayar da ita dakin ta shine.
Bukin yar ta da yataso amma idan ba haka ba Rabi bata komawa gida nan ya isa haka na.
Ya dubi dan shi daya yace shi ga ka kira min Rabi, kanin ummi ya shiga kiran ta ta shirya tafito don amsa kiran mahaifin nata.
Sai fitowanta ne ta ga su malam lawal ta durkusa a gaban mahaifin nata cikin ladabi tsoho ya dube ta yace.
Rabi ga abokin mijin ki sun zo bikon auren ki don haka maza ki shirya ki bisu.
Take idanuwan ummi ya ciko da hawaye zata yi magana tsohon ya daga mata hannun tare da cewa.
Haba Rabi ban sanki da mussu ba, ita rayuwa hakkuri akeyi da komai ki yi hakkuri ki koma daki mijinki ko domin yayan ki .
Tabude baki zatai magana tace baba amma, , , , ,
Ya koma katseta cikin tsawa yace kin san ni sarai bani son mussu aiko ?
Tashi ki je ki shiryo ku tafi.
Badon ummi ta soba haka ta shiga ta shirya tana shiri tana kuka ta fito da lulubin ta suka nufi tasha da su baba lawal.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:10 PM – Ummi Tandama: BAHAGGON , , , , ,
????????6️⃣????????
INDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON BA A YAFE BA ONLINE NOVEL NE, , ,
Lokacin da suka dawa bata zo gida ba wurin gwago ta nufa malam lawal ya je ya dauko baba yazo dashi gidan gwago.
Gwago da malam lawal suka su gaba da nasiha akan a zauna lafiya arike hakkin iyalin abawa kowa hakkin ta yadda ya dace.
Baba yace insha Allahu komai ya wuce zaa gyara da yarddan Allah zai kulla da hakkin iyalin shi
Da daddare su gwago suka rakota gida ta dawo dakin ta tare da kara mata nasiha a zauna lafiya ta kyale kowa da halin sa.
Lokacin da suka shigo gidan mutanen gidan suna waje zaune mu kuma muna daga cikin dakin mu sai naji murya kamar na yar uwar mama na sallama.
Hakan yasa ni mikewa in leka aikuwa nahango tafe da ummi na buga tsale ina cewa lah ga ummi mu ta dawo.
Mukayo kanta da murna suka shiga dakin komai yana nan tsab yadda ta barshi dakin ba laifi suka samu wuri suka zauna.
Zauna na durkusa ina gaida su kaunan ummi ke cewa dani wanan wata irin amaryane ba kwalliya ko kadan.
Na turo baki gaba take cewa ai ko bakya son mijin a dan yi maki gyaran irin na amare ko ?
Wannan wani gyara zata samu babu kwaciyan hankali ahaka suke ahirin kai ta gashiko ance mijin nata dan duniya ne inji kaunan ummi gudan.
Aiko ba komai a dan gyara ta in ba haka suke so su kwashe ta sukai ba akara samun abin fada masu nan gaba.
Take cewa dani washe gari ki same ni gidana da safe da dan abin da zan maki koda yake ma an makara duk da haka dai hakan za a yi.
Sun dan zauna nan nake basu labarin irin yadda mama tai ta matsa mashi akan ya dawo da ummi dakin ta da kuma yadda tai ta dan taimaka muna da ummi bata gidan.
Nan da zasu fita suke gaida mama din suna fadin ga Rabi nan ta dawo Allah kauda tautsayi tsakani.
Mama tace ba komai zama tare ke kawo wani abin amma in an ciza aka hura sai ya wuce.
Har suna shirin fita daga gidan sai inna tace muda ba a gayar wa sai ace mu mutu.
Baku duk mutuwa ai amma dai baku so ganin hakan ba anso ace bata dawo ba sai gashi ta dawo din bakin cikin haka zai kashe mutum.
Inna tace bakin ciki ya kashe wa matar da baa bi bayan ta ba ta wanke kafa ta dawo don kwakwa irin naku.
Tace wa ke nan zaune gida kamar kayan wanki tun yaushe mijin naki ke bin sawo har kauye.
Abun da yaba inna haushi ke nan tace ke kinyi kadan ki shigo kice zaki zage ni har dakina.
Mama lami tayi zaton dukan ta inna zatayi kafin inna ta karasa daga hannu taji an kwashe ta da mari tajuyo a cikin mamaki taji an sake sauke mata wani marin .
Aiko danbe ya kicimay masu take gida ya rude sai ga inna a kasa mama tabita ta haye da duka da yakusa.
Ganin inna bata diban komai a jikin mama lami yasa hausi yar inna dauko faskaren icce ta nufi mama dashi sauran ma suka dauko tadai samu mama dashi sau daya zata kara buga mata ne mama ta kauce iccen hau kan jikin inna.
Sai ga jini tarrrr yana zuba daga goshin inna din yaran suka kara fasa kururuwa mutane suka fara shigowa har da su yaya sani da abokan shi.
Yaya sani har ya dauko icce zai shiga dukan su dashi sai yaji mama na fadin yanzo kin ga abin da kika jawa kan ki in da suka shigo basu tan ka ki ba kin kyale sune sun tafi da baa kai ga haka ba.
Amma kin bisu da zagi da gori yanzu gashi har kin jawo yar ki tai maki rotse akai.
Sai jikin shi yayyai sanyi ya yarda iccen da ya dauka kasa yana cewa ashe inna ke kika ja wa kan ki gashi yanzu an barki da jinyan jiki.
Baba ya shigo gidan ya samu gidan a har gitse da kyat ya samu mama ta mayar mai da abin da ya faru yake cewa shi ba ruwan shi ta dauki mataki da kan ta in zata iya don shi bai sata ba.
Nan inna tashiga balle ballen bagana ida take shiga banan take fita ba wai baba an je an hada shi da boka da malam kan shi ya zare.
Baba ya shigo dakin mu don ya gaida ummi zamu fita yace mu zauna yake cewa ummi kin dawo lafiya ya mutanen gida.
Ta amsa shi da kyat da suna lafiya.
Yace don Allah Rabi kiyi hakkuri da halin inna kin saba da halin ta kiyi hakkuri a zauna lafiya.
Bata tankashi ba ta kawar da kai daga duban sa ma sam bata son ganin shi.
Shima yace da mu da ita sai da safen ku.
Allah yakai mu ta bashi amsa dashi.
Yana fita na sauke ajiyan zuciya nace ummi kiyi hakkiri tun da ya gane laifin sa abin ya wuce.
Ya gane ko yana shirin ganewa ai da sauran sa duk wanda yace ya karkata wuri daya a gidan sa ai kullun yana tare da tashin hankali.
Don dai yanzu in suyi min ba kyale su zanyi ba sai dai duk adauke mu masu fitinan don kyaluwa bai yi.
Abin da na lura dashi da baba da mama ke aiwatar da shirin bukin su sai ko gwagon ummi da suke dan jefawa ciki wani lakaci.
Mun kara jerabawan mu na karshe kowa na farin ciki da hakan a ban gare na bakin ciki ne tar ga zuciya na .
Sai dai ba wanda zan fadawa naji sanyi sallama muke da junan mu na samu Amina bakin get tana jira na mu tafi.
A kasa muke tafiya don bamu son mu rabu Amina ke cewa mun yi barka da saka uniform yanzu muna da freedom din kan mu ba mai takurawa rayuwan mu.
Take naji wani iri a raina tace ni dai nursing school nake son zuwa idanuwana suka ciko da hawayen bakin ciki lokaci guda don a da tare muke wanan burin kowa ya fadi abin da rayuwan shi ke so.
Nin nayi shiru tana ta magana take cewa dani bakiji bane Safiya, cikin raunaniyar murya nake ce mata ina jin ki ni nasan wana daman ya wuce ni ke nan a rayuwa na.
Tace saboda may zakice hakan wanda zaki aura din ba dan birni bane zai iya barin ki kici gaba da karatun ki bayan kuyi aure.
Na hade wasu yawun bakin ciki nace da ita kayya Amina wanan auren da za ai min takar bauta zan tafi yi wanda yafi wanda nake yi a gidan mu.
Da sauri tace saboda may kika ce haka nan nake koro mata da yadda mukayi ranan da suka zo da mahaifiyar shi.
Na kara dace Amina ke kin taba ganin anyi aure mijin bai ma san da zaman matar da za a aura mashi ba.
Na kara sa cikin kuka da fadin zan yi biyayya ga mahaifina shi dake gurin yaganni cikin irin wannan rayuwa.
Zan zauna na rugumi kaddaran da ubangiji ya aiko min dashi amma ni nasan babu komai cikin yin hakan da suke son yi sai hada zumunci fada.
Tace matsalan Safiya shi baba yaki gane gaskiyan magana wa yan nan matan na zugashi in gaskiya ne ai suna da diya mata suba dasu ma ai sun fi kusa da gwago din.
Nace da ita ai fakewa sukayi da cewa wai ni nayi karatun boko suko saura basu yi ba don haka ni ce na dace dashi.
Tun ban da wayyo nake jin irin wayyewar su da kuma irin tarbiyan su ba daya ba da namu amma mama cewa tayi wai zaman birni ne kawai.
Har muka kai gidan su Amina maganan muke muna tafiya ganin yadda na bata fuska da kuka yasa ta cewa dani na shiga gidan su na wanke fuskana.
Mahaifiyar ta na tsakar gida taga shigowan mu take cewa damu yaudai kunyi barka sai kuma a fada wani.
Ganin yanayi na yasa ta katse maganan nata ta biyomu cikin dakin ta da muka shiga.
Ta samay ni zaune Amina a gefe na ina kuka wiwi tace may zan gani wai haka yau duk kukan karasa makaranta ne haka ?
Amina ne ta iya bata amsa da cewa mama matsalar auren ta ne take wa kuka.
Sai mahaifiyar ta tace yanzu yaushe raban naji an tursasawa yarinya auren dole can.
Irin wanan ma mijin ai ba zaiga darajan su ba bare kuma ke.
Cikin kuka nake sanar mata da yadda mukayi dashi din duk abin da ya fada min da suka zo.
Taja gwaron numfashi tace shi baban naki ne bamai saukin kai ba, bai san yanzu an bar irin wanan auren hadin ba ne.
Ai lokaci ya shude na irin haka sai dai kiyi hakkuri Allah yana sane dake yi addua idan akwai alheri ya tabbatar muna.
Nace Mama wallahi shima mutumin bai ko san suna yi ba don kwatakwata yace ni ba tsarin shi bane yadda na lura shima umurnin mahaifiyar shi yake bi don nagane so yake ni na fitar da rashin amincewa ga iyayyen mu a fili san nan gashi miti biyu yai yawa bai kuna taba ya zukaba.
Kaini ban ma taba ganin mai sha irisa ba wata kilama ba iya taba yake shaba.
Don ranan da na fara ganin sa tare fa suke da iyayyen shi amma babu kunya yanata zukar tabanshi in na tunashi a raina duk hankalina sai ya tashi.
Nayi hakkuri na jure wai don na farantawa baba rai amma na gaza sakewa a raina.
Ba wani soyayya tsakani na dashi saima munanan halayyanshi da yake nunawa a fili.
Nakara fadi cikin wani irin kuka saboda Allah mama ta ya ya zan samu natsuwa har nai farin ciki ga auren da na san bubu komai cikin sa sai tarin kaskanci.
Mama ta girgiza kai cikin damuwa tace kidaiyi hakkuri don bamu da wata zabbi sai abin da Allah yayi.
Ta dan tsagai ta tana mai matukar tausaya mani tace gaki yarinua mai hankali ace za a hada ki aure da mara tarbiya mara mutunci.
Da sun bar sulaiman ya ci gaba da neman ki aiko su da sun dara amma a kai bakin ciki da kasancewan ku tare.
Yanzu ina mutunci ga irin hakan da ake shirin yi nace mama don ma baki shiga gidan mu kin gani bane ummina fa bata dade da dawowa gidan ba duk akan maganan.
Maman Amina tai salati ta sanar da ubangij tace badai ta dawo gidan ba ko ?
A hankali na share hawayen dake fuskana nace tadawo amma dai har yanzu cikin fitina suke din inna ba barin halinta zatayi ba.
Tace kin ga Safiya ki tsayar da hankalin ki debi kwanaki uku zuwa bakwai duk abin da ya sauwaka daga biyu zuwa uku dare.
Kirinka nafila ko wani raka,a ko wani raka,a ki karanta kulhuwallahu kafa goma sha biyu a bayan fatiha.
Idan ki idar ki zauna ki yi yabo gun mahallicin mu sai ki hada da istigfar duk abin da ya sauwaka kar ya gaza kafa dari, sai ki kara karata kulhuwallahu kafa goma sha biyu ko wani da bisimillah shi safiya muddin kika rike wanan zaki ga abin mamaki idan har ba a fasa auren ba to mukkadarine daga Allah Allah ba zai barki ki tabe haka na ba.
Cike da gansuwa da maganan ta nace nagode mama insha Allahu zandage dayi yau din nan zan fara basai gobe ba.
Amina ta tashi ta debo min ruwa a buta na wanke fuska na dashi bayan na wanke maman ta tayi tayi in ci abinci naki sai da zuciyana ya samu natsuwa.