BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/31/20, 11:07 PM – Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , ,

????????6️⃣8️⃣????????

Washegari tunda ya shigo ya duba mu da safe ban sake ganin shi ba sai dare ya dawo gidan a lokacin na samu kebewa dashi da yaron dauke a hannu na na shiga wurin shi.
Na samu ya fito wanka yana shirin fitowa falo don cin abinci sai gani na shigo dakin nashi yana goge jiki amma idon shi yana a kan mu har na karaso bakin gado.
Inda na aje yaron saman gado na nufe shi tare da kokarin karban da dan towel dake hannun shi na fara goge mashi kan shi a hankali.
Murmushi naji ya dan sake tare da rike min hannu ya fara fadin duk da gajiyan da kike ciki zaki koma wahal da kanki ga waban kuma ?
Nace gajiya ai yabi jiki yace haba in shirya baki wani baban nawa ko hajiya baaba ke nan da sauri nace kai Uncle sai ana zaune kalau ka dauko maganan da zai firgita mutum.
To be frank ba wasa a magana na sai ki fara shiryawa nan da kwanaki funda naga baki gaji ba kin ga sai mu tara zurian mu hankali kwance ko yaya kikace hararan wasa nayi mai tare da kawar da zancen da ki sa gabana faduwa idan naji.
Nace daddy nazo ne in fada ma ma,aikatan ku sun zo sun kawo muna abin arziki da baka nan yace yana dan duba yaron Saadu ya fada min sun zo sai dai nayi mashi fada may yasa ya bari suka shigo min gida.
Nace uncle ai danka ne ya jawo su da ba a haife shi ba aibasu zo gidan ka ba yace ai sun dade suna son zuwa basu ga fuskan haka bane.
Kila ma sun gama kalle min ke ban sani ba nace ko sun kalle ni nan zasu barni tunda ba kayan su baca ni ina da kishi sosai fa yace min .
Nace ai naga alama amma ai har da budurwan ka akazo ko itace baka son ta gani don yar kauye ce ni da sauri ya kallo ni don jin abinda na fada mai.
Bayi magana ya juya zuwan wurin kayan shi ya dauko wani light brown din jallabiya yana sawa a jikin shi sai da ya gama dakan shi ya dauko yaron dake kwance saman godon shi ya gyara shi da kyau a kafadan shi yana fadin in kin gama fadin maganan ki muje inci abinci.
Tashi nayi nabi bayan su har lokacin bai kara yin magana ba sai da zai zauna cin abincin ya miko min yaro wuce wa nayi wurin su mummy nakai mata yaron.
Ban dawo wurin shi ba sai da ya neme ni na dawo na samu har ya gama cin abincin nace mai na kewa yane bayi,
Tambayana yayi may kuka shirya na maganan suna ne don nasan gobe gidan nan zai cika da baki masu zuwa suna duk da nace su huta aiyi buki acan bauchin .
Amma hajiya tace min dole sai wasu sun zo nan idan sun koma zasuyi bukin su nisawa nayi tare da fadin ni ba wasu mutane nake dasu nan din ba karfin mutanan duk baki ne da zasu zo daga bangaren mu.
Yace ok na dai sa a gyara masu gidajen da zasu sauka a ciki don nan din ba zai ishe mu ba sai abinci naso inji shirin da kukayi akai don zan bada aiki a hotel ne ai muna nace da Aisha da mummy ya kamata kayi maganan don Aishan nan bata wuce ba.
Yace may take yi har yanzu anan nace dashi aiki sukeyi a kitchen shiru yayi sai can yace yimin magana da mummy din da ita Aishan.
Zuwa nayi na kisu sai gasu sun fito daga dakin zuwa gare shi bayan su zaune yayi ma mummy yaya gida ta amsa da Alhamdullahi .
Yake tambayan ta abinda ake shiri akan suna tare da mata bayanin yadda ya tsara abin gaba dayan su sukace hakan yayi dama har Aisha na tunanen yadda zasuyi dahuwa a nan gida .
Yace da sauri a ina zakuyi wanan aiki tace wai da anan mana yaya murmushi yayi kawai tare da kada kafan shi sunci gaba da tsara yadda abin zai kasance da yar uwanshi sai mummy da take a bangare ne.
Nikan mikewa nayi na shige na barsu a wurin don na fara jin barci na damuna sai da na falko ne naga har mummy tashigo ta kashe muna wutan dakin ko na gyara kwanciya na da kyau.
Washe gari zuwa karfe ukun rana baki sun fara isowa duk na matsu inga masu zuwa daga bangare na alokacin sai hudu na yamma suka shigo garin inda yaya Saadu yaje ya taro su a hanya.
Shigowan su yayi daidai da fitowa na daga bayi don tsarkake kaina da nake yawan yi lokaci lokaci saboda in samu walwala a jikina.
Samira naji tana masu oyoyo yasa nasan sun iso ke nan don haka na fito taron su falo da shafiu kanina na fara arba da sauri yayo wuri rungumay shi nayi cikin murna da jin dadin ganin shi.
Don Allah ya hada jina da yaron sosai duk da bashi ke bin mun amma shine abokin shawara na a dakin mu mama na gani na sake shi na rungumay ta.
Abin mamaki shi har da Inna yau a gidan aure na da kannen ummi na da suka zo mutum hudu da gwago nan dai gida ya cika alokaci guda.
Zama sukayi aka fara gaisuwa tare da gabatar masu da abinci da na sha wanda har uncle ya fara odan su a gidan don bakin mu da suka zo.
Yan bauchima sun iso mota biyu suka zo dashi bus cike da mutane gidan sai ya koma min kamar ba gidan mu ba duk girman gidan inda ka duba jama, a ne tako ina.
Inna ta koma can hanya coridor din shiga part din uncle tayi zaune tana raba ido tana kallon ikon Allah tana anyanawa a ranta.
Wai yau gidan Safiya ne haka safiyan da taso agida ita da uwarta ko na sabulu wuya yake masu gaskiya nake ganin kowa na rawan kafa da ita yanzu ashe sun san abinda suka gani ne.
Tasa hannu ta shafo ties din kasan da ta zauna tana kallo wanda aka malalashi kamar ruwa da kifaye suna yawo acikin sa.
Mummy ne ta katse ta da cewa aa Rakiya nan kika zo kika zauna hanyan dakin surukin ki kuma tashi mana ki shiga dakin diyar taki tana can ciki ai.
Tace ummm, ummm aiko nan ma yayi min tace a a taso dai ki shiga wurin ta sauran jamma, an da kuka zo ai suna can tare da ita.
Janta tayi har zuwa daki inda nake tsakiyan su mamana suna min bayani kan abinda suka shirya akazo min dashi wanda ummi tabar kudi da zata tafi sai su kuma su kara tasu a wurin dawai niyar.
Nayi mamakin abunda suka zo min dashi don ba karamin kashe kudi akayi ba kamar lokacin aure wanan karon ma haka suka hado mi gara mai yawa akazo dashi.
Sai hango inna nayi can daga kofa ta rakube wuri guda tana bin dakin da kallo har tana dagen kai wurin kallon dakin nawa.
Nace a a inna karaso mana shigo daga ciki ki zauna na mike ina fadin kinci abinci kuwa na juya wurin khadija kauna ta ina cewa khadiza debo ma inna abinci don Allah tana fadin anbata abinci ai taci.
Nace jeki debo mata nama ki kawo masu ta karaso ciki ta samu wuri ta zauna nace a mika mata jaririn dake goye a bayan gwago dake zaune a kasa.
Aka kawo mata nama cike a plate ta karba tana washe baki ina kallon ta ta fakaici idon mutane ta juye a wani tsohon jakka dake rataye a kafadan ta.
Murmushi nayi don bata ganni ba mama ma tashigo nan suka zauna nace su shiga bayi suyi alwala a dakina suka fito na mike da kaina na dauko masu abin sallah.
Karshe wasu waje suka koma suka zauna saman fararen kujeron roban da aka baza a wurin sai ci ake da sha ga ma aikata wuri su Nura sai raba abinci sukewa mutane.
Fitowa nayi zuwa wurin yan bauchi muna gaisawa dasu gungu gungu tare da masu ban gajiyan tafiya.
Dare yayi yaya Saadu yashigo gidan yana fadin yan bauchi su fito akaisu masaukin da zasu sauka suka fara fito fogayen mota wurin aikin su Uncle suna waje ciki suka shiga aka tafi dasu.
Suka dawo aka kwashi yan garin mu aka tafi dasu zuwa wirin da suma akai masu masaukin su gidan ya rage daga mummy sai gwago da yayan samira da muke zaune sai Rukaiya da na hana wucewa da Khadija na.
Hira mukai tayi da rukaiya a daki tana bani labarin auren ta da Ado mai mai da yadda zaman ta da kishiyoyin ta yake yanzu a gida.
Rukaiya tace dani na shigo dakin dada sai kika ga Inna ta biyo mu nace wallahi ai nayi mamakin zuwan su duka su biyu tace.
Ita fa akace ta zauna gida da yara taki wai sai tazo yaya Sani kuma dama yaja mata kunne sosai kafin ya tafi.
Nace kai Inna ho har yanzu dai tana nan da halin tace ai dole ta rage yanzu da kika ganta nan bata dako lafiya tafiyan karfin hali ne kawai tayi inji khadija na dake gyara ma yaro jiki a hannun ta ya gama shan madara zata kai ma gwago ta goya shi.
Washe gari kafin wani lokaci aka fara shaanin buki baki da yan gari sun fara cika gida don haka kowa ya koma busy cikin mu maigidan tunda ya shigo da safe yace zai tafi unguwa bai dawo gidan ba.
Kowa yasan sunan yaro Abdulrahaman nan yan bauchi suka fara kiran Abbamu ya dawo yaro yaci sunan tsoho ke nan.
Anci ansha an raba kyaututuka masu ma,ana dake dauke da photo jariri da sunan shi a jikin kyauntan sai ga wasu mata sun shigo wai mata yan kasuwa ne suka zu taya mu murna har da yan wurin aikin su uncle wasu sun turo matan su wasu kuma ma,aikatan su mata ne masu aure suka zo.
Alhamdullahi har dare babu wanin hayaniyar da akayi sai faman ci da sha mata keyi koma anyi ba mai yawa bane abinda ba a rasawa ne kawai na taron mata.
Na shiga na fita walima mukayi inda wata malama da tazo daga bauchi tayi mu nasiha akan “ya”ya da hankin uwa akan dan ta.
Nashiga na fita daga suturun da Uncle ya waddatani dasu don fitan buki wanda daga Dubai wanda duk wanda nasa sai an kalle ni daga ni har yaron.
Ban da abin cewa sai hamdala ga ubangiji subbahanahu wata,ala da ya wadatani daga cikin ni,imomin shi nake rayuwa kamar banda wani tabo na tashin hankali a jikina.
Har kishiyar Aisha da abokan aikin ta sunzo mata karan suna da makwabtan Samira da suke zamar arziki dasu suma sunzo mata kara.
Sadiya kaunan su yaya saadu yasa tazo daga lagos don halartan sunan kawai naji mamakin ganin ta kwarai da gaske don yaya bai fada min cewa zata zo ba sai ganin ta nayi kawai da safe da suka shigo.
Mun rage daga mu sai bakin mu suma da dare aka maidasu masauki don a gajiye kowa yake yana son hutu.
Khadija ne dakin da samira suna nade min kayan da nayi amfani dashi da rana ni kuma ina zaune bakin gado rike da wayana a hannu.
Ina kokarin neman layin anty mu gaisa Uncle ne ya shigo dakin suka shiga gaida shi da gajiya dago kai nayi ina kallon shi yana wasa da khadija na.
Yace ke budurwan kauye kin boye kawai abinki a kauye baki ko tuna mutane ta turo baki gaba tana cewa ai mu yanzu garin mu ba a kiran shi kauye don mun waye.
Yace amma dai zaki dan zauna kwana biyu nan ko don ki kara wayewa dakyau dariya tayi nayi saurin cewa a a kan tace nima bance zan zauna ba ai.
Nace dama shafiu ne da ko wata nawa zaiyi ban damuwa amma wanan wataran zaka dawo ka samu tamin dan karen duka a gidan nan.
Tace kai anty Safiya ai dane muna kanana ko tun da muka girma ai muka bar fada dariya su samira suka kwashe dashi.
Yace au ashe da gaske da kina dukan min mata tace wallahi yaya sherin anty Safiya ne itace dai mai dukan mu din.
Nace ke khadija ni yaushe nake dukan ku ina kafa kafa kada inna ta cuta maku a lokacin tace ai kin yi kokari wallahi.
Nan Samira ke fadin munafuka sai gata tazo tana simi simi da ita Uncle yace tazo ne ita ma khadija tayi saurin fadin tazo gulma bata da ko lafiya.
Shirin fita dakin sukayi su sai ya dakatar dasu da fadi No ku zauna abinku ni fita zanyi nazo duba madam dina ne.
Samira tace gako madam nan ta sauke gajiya yaron ya tambaya khadija tayi saurin fadi yana gurin gwago ai kun samu maigadi yau gwago bata bari kowa ya dauke shi ba yau ita da mummy.
Yace amma sun kyauta min ina can ina tunanen wanan taron dana gani za ai ta jagulamin yaro da kuma na tuna mummy na nan sai ban damu sosai ba.
Khadija tace oho ita anty nawa fa dariya kawai yayi ya fita dakin har ya kai kofa ya juyo yace khadija ba fa dake za a koma ba kinji na fada maki.
Samira ce tace bayan ya fita daga dakin ashe uncle yana magana haka mai tsawo nace yan maganan dai ke kusa yau.
Washegari baki basu shigo da wuri ba don gajiyan da suka tara sun fita zuwa kasuwa masu shiga gari ma sun shiga ziyaran yan uwa sai iyayyena da suka ce gidan yaya Saadu zasu tafi suga gida.
Dare anan sukaci abincin dare aka kwashe su zuwa masauki sai washe gari zasuyi asubancin komawa gida.
Zaune muke daki suna ta faman saka kaya a leda wanda yaya Saadu ya shigo dashi gidan da za a bawa baki sallama matsayin kyautar bukin su.
Na kalli Rukaiya nace yanzu haka kike zaune a gidan baki sanaan komai Rukaiya ga yaro ta dago kai tace to yaya zanyi Safiya.
Ni dai zaman yafi min zama gida wurin inna don yanzu sai ta ganin zatai fitinan ta ranan da ya samu ya kawa muci randa bai samu ba muyi hakkuri hakana.
Nace yanzun dai zan baki wasu dan kudi sai ki dinga juyawa shima zan baki kikai mai amma don Allah ki bashi don zaman magidanci ba sana,a ba dadi wallahi.
Don ina tuna lokacin da muke kanana baba baida wani sana,a irin wahalan da iyayyen mu mata suka dinga yi a gida.
Tace bari kedai lokacin ai ba a magana amma yanzu ga baba nan kamar ba ayi ba ya gyagije ya zama kamar yaro dashi.
Nace wanan leda ta saka mai turmi uku takai wa kishiyoyin ta komai ta saka ma nan na shiga lissafa masu duk muka cire ma wa yanda suka zo sai mahaifiyar Amina don Amina nada tsohon ciki bata samu zuwa ba.
Kudi na mike na dauko na bata nace ta cire dubu hamsim taba mijin nata dubu hamsim Khadija ne ta katse ni da fadin itafa ba a cire mata leda ba.
Nace ba kinji uncle yace ba tare dake zasu koma ba nasan kuma da gaske yake yi tunda kikaji ya fada.
Tace ita dai a cire mata nace zabi wanda kike so ba shike nan ba Rukaiya na ta min godiya nace tadai samu sana,a da zatayi dasu nasan zasu isheki ai.
Washe gari ko wani mota ya basu na shan ruwa hanya kusanna lokaci daya suka tashi sai gidan ya koma saura mu kadai a ciki.
Sai yan wirin aikin su Nura dake ta faman gyaran gida don tsabatace wuri uncle badai tsabta ba kan don bai son kazanta ko kada shi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92Next page

Leave a Reply

Back to top button