BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
9/11/20, 7:20 AM – Ummi Tandama: BAHAGGON RAYUWA, , , , , , ,

????????7️⃣6️⃣????

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU KU

Washegari da rana uncle ke fadin gobe zamu koma Abuja maganan tafiyan yazo min a bazata don ban shirya komai ba namu.
Dole haka yasa mu shiri da tanadar duk wani abinda muke bukata a bauchi wanda muke so sai dai ba a cikin dadin rai muke shirin ba don rashin sanar damu da wuri da bai yi ba.
Sai dare na samu shigo gun hajiya baaba tana gani na tace ashe gobe zaku koma nace haka yace muna hajiya nima banda masaniya akan tafiyan.
Babana bai kyauta ba aika fadawa mutane su shirya ko amma haka da rana tsaka kace tafiya zakuyi nace baaba yadda yake so haka yake muna tace sai dai hakkuri shi kuma nasa halin ke nan gadara ga wanda yafi.
Abinda da ta tanadar muna ta nuna min inda nayi godiya tare da nuna mata farin ciki na akan hakan.
Tafiyan safe zamuyi don haka sauran kayan mu hajiyace zata turo min dasu ban samu koyin sallama da yan uwanshi badon ba lokaci.
Washe gari gare goma muna cikin garin Abuja a gajiya don akwai barci a idanun mu mun samu su mummy da gwago lafiya inda suke ta cewa bauchi ya karbe mu sosai.
Ni dai sai murmushi nake masu Uncle bai dade a gidan ba ya fita zuwa wurin aiki muma barcin mukayi don mu huta ranan Samira ta zo ganin mu da yi muna sannu da dawowa.
Motar kayan mu sai washe gari zasu taso don a hada muna kayan mu da kyau koshi sai da hajiya baaba ta roka muna saboda masan da nace mummy tace muzo mata dashi.
Mun dade da Samira a dakina muna hira sai dare yaya yazo ya dauke su suka tafi washe gari motar suka iso wajajen uku na rana da kayan mu ciki.
Sai da na kawar da komai yadda ya dace na dawo falo bayan nayi sallah laasar na zauna tare da mummy da gwago da suka fito falon.
Mummy ke fadin gwago sai kuma shirin gida yanzu ko kafin in magana khadija ta cabe zancen da cewa cabdi gida kan ai ba yanzu ba.
Don dai mai tafiyan yace wai sai yadawo kasan waje zamu tafi gwogo tace wane ni nan ashe ko zan barku anan don yanzu haka munyi suna fada min wai ragona ya kasa shekaran jiya.
Nidai ban yi magana ba tana ta fadin ita gida tayi bata kara lokaci sai mummy ce tace da gwogo din kada kuyi haka don Allah don baku san tsarin shi ba.
Ni dai abinda nake so ku saka mashi ido akan zance musanman ke gwago da kin yi magana zai iya sa ya zaci wani abu don Allah ku sa mai ido kubi sannu.
Tace shine kuma amma gaskiya badon nauyi ba da nayi gaba ni daga baya basai su su iso ba idan ya shirya masu tafiyan.
Nidai jinsu kawai nake yi da khadija ta matsa nace a zafafe aiko yanzu zaki iya tafiya khadija ba sai kin jira zuwa wani lokaci ba.
Sanin baka nayi mata yasa taja bakin ta tayi shiru bata kara magana ba a gaba sai kumbure kumburen da take faman yi ita kadai.
Gwago ma da yake kakace sai cewa tayi kun dai rike mu ke nan ke da mijin ki ai na gane nufin ku damu sai dan ku ya iya tafiya kila zaku bari muje gida.
Dariyan dole tasani nace wai gwago may zaki je gida kiyi ne don Allah baya kina nan hankalin ki kwance.
Da sauri tace ina ne hankali na akwance garin naku da haka ganin kowa kullun gaka gida a kumshe kamar kayan wanki.
Acan din yawo kike zuwa ne ba ko yaushe kina cikin soyan gyada da fitar da mai ba nasan duk wanan aikin ke a ranki.
Mummy tace ashe ki gane gwago dai ta juya wurin khadija da ta cika fam tace ta wuri kyale su kinji dole sai yadda sukayi damu yanzu mmutum ko hanyar fita unguwar nan bai sani ba balle ya guda.
Dariya duk muka kwashe dashi nan dai akai ta hira har lokacin sallah magariba yayi muka watse kowa ya nufi wurin sallah.
Yau kwanan mu biyu da dawowa bauchi kowa ya sake a gidan ba zancen zuwa gidan da suke min matsi a kan shi kuma.
Suna zaune falo na fito cikin wani dogo riga green color har kasa sai shape din da aka fitar ma rigan aka dan buda kasan shi sosai cup ne a hannu na na ciko da kindarmo dana dan zuba shikafa a cikin sa kadan ina sha.
Mummy dake zaune tana ba Abba abincin shi tana magana da khadija da ta mimike kafa saman kujera kafin in kai zaune nace ta kwashe kayan da ke saman sauran kujerran don Allah ta kawar dasu.
Tace yanzu nake magana ai don nasan gidan yan tsabta nazo ko tsinke ba a gani a gidan ku zama nayi ina ce mata yanzu wake son kazanta khadija.
Ai ba dadi ne aganka a waje fes azo gidan ka asamay ka ciki kazanta kin ga hakan ai ba dadi a riskeka ta yadda baka so ba.
Ta kawar da komai ta dawo zata zauna sai ga driver shi ya shigo da wasu kwalaye gidan yana gaishe mu da gida mummy ne ke tambayan shi tare kuke da ya bata amsa da eh sai naga sun shiga mikewa suna shigewa dakunan su.
Sai ni da khadija aka bari a wurin muna masu dariya ya shigo yana waya muna mashi sannu da dawowa yana amsa muna da kai kawai.
Dakin shi ya nufa ta kalle ni tace kamar kin san yana zuwa yanzu kika ce in kwashe kayan saman kujerun nan anty khadija nasan zai iya dawowa ko wani lokaci shiyasa ban yarda ya riske mu a hakan ai.
Fitowa yayi daga dakin bayan ya rage kayan jikin shi ya sauya wasu nan yazo falo inda muke zaune ya zauna khadija zata tashi yace No zauna abinki ba komai zanyi ba ai.
Ba ta dai zauna ba ta mike ta shige wurin su gwago tana dariya ya juyo gare ni tare da dan furzar da iska daga bakin shi yace ina son kiyi min list din abinda kike bukata na tafiyan ku.
Da wanda za a saiwa gwago da khadija ko kuma dai ki kira samira ku fita tare kiyo masu sayyaya don banda lokaci gobe ina son zuwa lagos in dawo gobe din kuma.
Don jibi nake son muyi tafiyan nan nakaiku gida kafin in dawo kin dan sha gida kadan, wani irin dadi naji ya ziyarci zuciyana a lokacin wanda ban san lokacin da nayi mai godiya ba.
Daga gwago har khadija duba dari dari ya basu su sayi abinda suke bukata na kasan su da zasu tafi dashi gida.
Sai kuma yace ke kuma ban san irin tsaraban da kike son ki tafi dashi ga dai wanan sai ki shiga kasuwa ki gani zan sa a kawo maki shadda da a tamfofi so ba sai kin saye su ba su.
Har kasa nakai ina mashi godiya tare da nuna farin cikina a gare shi waya aka bugo mai ya mike ya fita waje haka yaba ni daman mikewa zuwa masu bayani a dakin su.
A dakin su na shiga da sallama na nan na samay su suna hira ana dariya na zauna tare da fito da kudin ina mika wa kowa nasa sai kallo na suke yi da mamaki a fuskan su.
Nace Uncle yace na baku wai gobe a shiga kasuwa a sayo wa kowan ku abinda take so na tafiya shiru dakin yayi na dan wani lokaci.
Sai mummy ne tace Allah ya umfana ya saka da alheri yayiwa dukiya yawalta nace amin mummy gwago ta bude baki da kyat tace ni na rasa abinda zance wallahi.
Shi baya gajiya da dawainiya ne kullun kazo da alherin da za a bika dashi haka ba kadan ba kuma ?
Haihuwa ne tayi ranan ta inji mummy hakurin yar ku ne yaja maku haka da Safiya bata da hakkuri a rayuwa da ba acin ma hakan ba.
Biyayyan aure ba abinda baisa miji yayi ma mace da yan uwan ta sai aga kaman wani asiri take wa mijin yake sakar mata hannu haka.
Nan ko mutane basu san iya hakkuri da diya mace ke hadewa a dakin auren ta ba sai idan dadi yazo ne zakaji ana fadin ta mallakeshi ne musanman dangin miji.
Sun fi jin zafin macen da mijin ta ke yawan kyautata mata da yan uwanta koda yana ma nashi yan uwan sai suga ai yafi kyautatawa matarshi da yan uwanta.
Gwago tace haka abin yake a ko wani gida wallahi mu dai bamu da abin da zamu ce wa wanan yaron sai dai muyi mashi fatan alheri da gamawa da duniya lafiya.
Duk muka ce amin dakin nan khadija ta shiga rawan kai tana lissafo abubuwan da take bukata na rayuwan ta.
Gwago tace ke arr wawiyar banza baki lissafin kayan daki ba sai shirmay kike faman lissafa muna kawai ko kwabo bazaki taba ba cikin kudin nan.
Uwarki za a kaiwa su gida idan mun koma lafiya take ta turo baki gaba tana magaba kasa kasa.
Rankwashe gwago takai mata akai nace gwago rabu da ita don Allah kudin tane fa yaba ta ne don bukatunta mana.
Tace kaiyya yaro mankaza yanzu har dake kike bata shawara ta kashe kudin nan ga banza ba zata kai ma uwar ta tasai mata abin kwarai ba.
Nace haba gwago ayi fatan a samu wadata mana kafin auren anci gaba ai gaba gaba muke fata a rayuwan mu shiru tayi nace khadija barin buga ma Samira waya ta shigo gobe sai mu fita kasuwan.
Khadija ta fara murna ji zan barta tasai abinda ranta ke so gwago tace miko min kudin nan baza ki kashe su duka ba mara hankali kawai.
Tace anty wai may yasa kika bani nawane a gaban gwago yanzu zata sakani gaba da tsegumi wallahi bayan itama an bata nata ta kulle a lalitan ta.
Gwago zata taso tabar dakin da gudu tana dariya ta juya gare ni tana fadin Allah dai ya shirya ku mummy tace ai idan zaki kara mata da naki indai yaran yanzu ne tas zata kashe su wallahi.
Ban zauna ba nabi yar uwana muka zuwa daki nan muka zauna muna hiran da ita har na kira samira tace zata shigo goben mu fita.
Washe gari Uncle yayi asubancin barin gida kamar yadda yace bayan yaja min kune akan kada mu dade idan mun fita ya kama hanyan airport.
Sai misalin sha biyun rana samira ta shigo gidan bamu jima ba muka tafi bayan mungama zolayan gwago ta kawo kudin ta a kaso mata.
Tace Allah ya tsari kakanta kande da tashi fatalwa ai idan mun anshi kudin nan a hannun ta kashe ta mukayi.
Bamu dawo gida ba sai da muka cika bayan hilux din da muka shiga kasuwa dashi fan na hado tsaraba mai himilin yawa muka dawo gida karfe biyar da wani abu na yamma.
Mun shigo a gajiye mummy tana muna sannu da zuwa gwago dake daki tafito tana daura dankwali a kanta tana fadin .
Yau kan akuyan daure ta samu saki naso ace mijin nan naki yana gari inga karshen yawon ku sai da aka fara shigo muna da kayan ne ta kama fadin dan kari.
Ban tsaya ba na shige daki wanka nayi na rage kayan jikina n tare da jero sallah da ake bina na fito falon.
Sannu a hankali muke bude kayan da ba ayi packeding din su ba muna gyawa dani da samira da mummy muka hade komai gwago na kallon mu.
Sai dare uncle ya iso gida don tafiyan yini yayi ranan tunda ya shige bai fito ba sai washe gari nan yake fadawa gwago washe gari zamu tafi in Allah ya kaimu.
Murna wurin gwago ba a cewa komai do haka ban samu kaina ba ranan sai faman shirin tafiya nake yi sai yamma na samu kaina na huta.
Kayan da uncle yaga na dauka yasa shi yin magana wai yaushe ne zaki dawo wanan uban kayan da kika dauka haka ?
Nace ko kwana nawa ka bani ai shi zanyi bakari cikin sa murmushi ya gyara zama yana fadin kwana hudu yayi maki ko da kallon fuska na don son jin amsan da zan bashi a lokacin.
Nace na gode Uncle ya ce ki kwanta don sammako nike son muyi don inje in dawo gobe din don jibi zamu daga zuwa Egypt.
Mun raya daren mu cikin dadin rai inda nayi asubancin tashi tare da tayar da su gwago muka shiga shirin tafiya kafin shida duk mun shirya ko .
Ban san da yaya Saadu za ai tafiyan ba sai da yazo da safe yake fada muna ai dashi zamu tafi inda mummy zata je fatakwal kafin mu dawo ta duba yaran ta nacan amma ba ranan zata tafi ba gidan yaya Saadu zata dan zauna tukun.
An gama saka kaya a motocin da zamuyi tafiya dashi mu uku baya su biyu da yaya Saadu a gaba sai dayan motan driver da wani mutum ke ciki da kayan mu wanda ban san mutumin ba ko gaisuwan kirki bamuyi dashi uncle ya tsare ni da ido.
Ban son yawan gaisawa da mazan da ban sani ba duk da wurin shi suke zuwa amma da naga bai so sai nima nake share su kawai.
Don ko zuwa da ma aikatan su sukayi da na haihu ba karamin fada yayi ba daya dawo wai na zauna wasu kattan baza suna kallo na dama suma abinda ya kawo su ke na don su ganni saboda sun ga bai gari.
Wanan abin tun yana bata min rai har nagaji na bari don halin shi kishin maza irin na haukan nan har ba a san abin fadi ba.
Shida yaya saadu ke fira sai jefi jefi nake saka masu baki daga inda muke zaune a bayan motan don gudun zurewa ya kuma samu abinda yace nayi mai abinda ba dadi don ba freedom yadda ya dace.
Tunda zamu taso na buga ma ummi na waya cewa zamu taso don haka ayiwa su uncle abinci kafin mu iso don yau zasu juyo su.
Mun sauka mi salin kare biyu saura na rana don ba karamin gudu yaya yake yi ba shiyasa muka sauka da wuri wani iri nake ji a raina yau zanga yan uwana da iyayyena dana dade ban gani da sauran abokan arzikin mu.
Tunda aka ce gamu mun iso yan uwana sukayo waje da gudu don taron mu abin gwanin ban shaawa kaina sukayo ni da khadija.
Da murna muka rungumay juna kowa yazo kokari yake ya rungumay ni kamar bani bace safiyan da suke gudu da karna shafa masu cutan dake jikina a baya.
Sai gashi yau sanadin auren mai kudi da samun gata an manta da komai da ya faru a baya an koma kamar ba a yi ba muryan shi naji a bayan mu yana fadin.
Watau yar uwarku kawai kuka sani baku san kowa ba ko nan suka shiga mashi sannu da zuwa wasu suna fadin ashe da mijin ki kuka zo yaya saadu yace ai kauyawa ne wa yan nan.
Nan muka shiga gida suka dinga kwaso kayan da yaya saadu ke dora masu yana masu sheri irin na tobasai uncle sai murmushi yake yi kawai .

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92Next page

Leave a Reply

Back to top button