BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
9/21/20, 9:58 AM – Ummi Tandama: BAHAGGON RAYUWA, , , , , , , , ,

????????8️⃣3️⃣????

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU

Haka rayuwan mu yaci gaba da tafiya a gidan muna samun kula yadda ya dace daga wurin uncle har yasa yan kanne na wani school mai tsada a nan cikin Abuja.
Sa su makaranta yasa yanzu ina fita in kai su in kuma je hudu in dauko su in sun shirya nakaisu islamiya ranan da ban iya fita kuma sai driver ya dauko su daga school din.
Yau haka na kwana ba lafiya a jikina sai karfin halin da nakeyi ban son asan halin da nake ciki a gidan sai dai jikin ya matsa min har ban iya boyewa mutane halin da nake ciki.
Wanda ya saukar min da zazzabi zuwa rana mai karfi har yakaini da rufuwa da bargo da kyat barci ya dauke ni cikin zafin jiki nake barcin a wahale a lokacin.
Jina shiru ban fito ba tun safe da na sauke yara makaranta yasa mummy lekowa dakina ta duba ni ganina kwance na rufe da bargo har kaina yasa ta shigo tana fadin .
Safiya yau lafiya kike kuwa abinda ya falko dani daga barcin dana dan samu ke nan na bude idona dakyat nace.
Mummy ban jin dadin jikina ne yau tun dare zazzabi ya rufeni sai da nasha magani ya lafa yanzun kuma ya kara dawowa.
Ina gyara kwanci nace karfe nawa yanzu mummy tace uku da rabi ya wuce dan yunkurawa nayi ina son in dauko waya amma na kasa.
Sai mummy ta gane abinda nake son yi tazo da sauri ta dauko min wayan ta mika min neman layin uncle nayi don in fada mai a dauko min su maimu daga school .
Jin murya na yasa shi fadin may ya samay ki safiya ?
Banda lafiya na iya fadi kawai sai naji ya kashe wayan da sauri na gyara kwanciya nayi don ko sallah ban iya yiba a lokacin.
Ba afi wasu mintina ba sai gashi gidan yacewa malam musa yaje ya dauko yaran daga school ya dawo yanzu ya juya ya fita daga gidan kamar yadda ya umurce shi dayi din.
Ciki ya shigo bayan ya sallami malam musa din dakina ya nufo don yafi tsamanin ina can din a lokaci ya turo kofan da sauri.
A kwance ya hangoni kwance na dunkule a wuri daya ina makarkyatan dari duk jikina rawa yake a lokacin .
Bargon dana rufe jikina ya kwarai tare da dan taba jikina a hankali zafi yaji radau a jikin nawa jin hannun shi a jikin nawa yasa na bude ido na hanshi zaune a kusa dani yace .
Safiya baki da lafiya ne har haka baki fada min ba kuma baki kirani ba take ya daga waya ya kira likitan shi yace yana wani wuri amma gashi nan zuwa yanzu.
Yana dakin har likitan ya shigo gida fita yayi sai gasu sun shigo tare da likita dakina ya ce madam sannu yaya jikin ?
Nace da sauki ina takurewa a wuri daya yace yaya nake ji ne ?
Nan na fada mai yau kwana hudu da amai amai ya fara min sai kuma daren jiya ya saukar min da zazzabi .
Yayi min yan tambayo na bashi amsa uncle na zaune ya kafeni da idanuwan shi sai yace bari ya fara saukar min da zazzabin gobe zai dawo akwai awon da zai min.
Wani irin ras ras naji gabana ya bada don ambatan awon da yace na dauka akan maysalan ciwon mu zai mun awo din na yaba allura har biyu tare da magani.
Suka fita da uncle daidai lokacin yan makaranta suka dawo dakina suka shigo don tun a hanya malam musa ya fada masu banda lafiya shiyasa banzo daukan su ba.
Don su fison in tafi dauko su don duk abinda suka gani na marmari a hanya sukan ce min insaya masu ko kuma in tambaye su asai maku abu kaza ne ?
Gaishe ni sukeyi kowa tana kokarin ganin fuskana kamar an fada masu a fuska na ciwo dake damu na yake min.
Dan samun saukin da nayi na rarafa naje ban daki na dauro alwala nazo na tayar da sallah don har da azahar banyi ba ina kwance.
Ina sallah naji shigowan uncle dakin bai fita ba don ina sallah zama yayi har lokacin da na idar da sallah din ya miko min maganin da likita ya rubuta mai ashe shine ya fita sawowa.
Nan ya tsaya sai da na shaye maganin na koma na kwanta fita yayi ya samu Nura mai aiki yace ta hado min tea takai min dakina.
Ina kwance sai ga Nura ta shigo dakin dauke da dan karamin tire a hannun ta da kayan tea ta kawo min tana min sannu.
Ban tashi ba sai ga uncle ya shigo dakin na lura sallah yayi yana fadin kinsha tea din kuwa yana kai idon shi inda kayan suke aje kai kawai na girgiza mai alaman ban sha ba.
Zama yayi ya hada min tea din yana tashi kisha cikin commad yayi maganan shi bawai alaman lalashi ba dole na tashi na sha tea din rabin kofi na koma na kwanta ya mike yana fadin zai dan fita ba dadewa zaiyi ba zai dawo.
Har yakai kofa wani irin amai ya taso min da sauri na yunkura zuwa ban daki kafin in isa na sake amai mai karfi a tsakiyan daki na.
Wani irin kallo ya bini dashi tare da yi min sannu cikin tausayawa a gare ni na karasa zuwa ban daki amai nayi sosai duk da ba komai a cikina.
Fita yayi ya fadawa mummy nayi amai na bata dakina dashi da sauri ta taso da Abba goye a bayan ta ta nufi dakin nawa.
Mummy ta gashe ni ta sauke yaron ta fara gyaran wurin dana bata din da amai sai sannu nake mata ina fadin ai da ta barshi zan gyara wurin ko ta turo su maimu su gyara don suna gida yau ba islamiya.
Tace haba wanan ai ba komai bane aikina ne barin yi ta gama gyara wurin ta dawo tadan zauna sai ga maimu tashi tana saye da wandon tie baki iya gwiwa da yellow din dan riga sannu take min cikin tausayawa.
Nace jeki kitchen ki dauko min lemo guda biyu ki wade min su ki kawo min da sauri ta fita ta dan dauki lokaci ta kawo min na yunkura na tashi dakyat na iya shaye guda na koma na kwanta don sam banjin dadin jiki na.
Ban dade da kwanciya sai barci yau ni dake hana wasu barcin bayan laasar sai gashi ni ina yi fita mummy tayi da yara don kada su ta dani tare da jawo min kofan dakin.
Uncle ya dawo gida kafin magariba ya wuce dakina kai tsaye ya tura kofan ya samu ina barci ga lemon da aka wade min a gefe na aje yadan dade tsaye kaina ban san ya shigo ba.
Ya dan taba ni kadan sai na bude idona yace tashi magariba ya gabato da kyat na samu na tashi zaune yayi min sannu da kara tambaya ko na sake yin aman bayan fitar shi nace banyi Allah ya sauwa yayi min.
Bayan fitan shi daga dakin na daure na tashi na shiga bayi wanka nayi da ruwa masu dumi sosai na dan gasa jikina tare da dauro alwala na fito.
Sai da na zauna na dan huta na mike na gabatar da sallah a inda na idar na sake dunkulewa a cikin hijabi na banyi barci ba ina jiran inyi ishai a wurin mummy ne tashigo duba na.
Ta samu nayi sallah ta yi min yaya jikin nace da sauki mummy murya can kasa kasa na amsa mata tace har yanzu bai fada maki ba ?
Nace na rage jin sanyi yanzu kaina ke ciwo kamar ya tsage nake jin shi sannu tayi min ta dan jima zaune a wuri duk da ba hira muke yi ba a lokacin sallah ya tayar da ita tana idar wa suka dawo tare dasu hindatu suka zauna a dakin.
Uncle ya dawo dauke da ledoji a hannun shi dakin ya nufa dasu su Mommy na ganin shi suka shiga gayar dashi hindatu da maimu suna rige rigen amsan ledojin dake hannun shi din.
Mika masu yayi tare da fadin su aje karamin su tafi da babban suci ya juya wurin mommy data mike tsaye ko tana shirin fita dakin .
Yana tambayan ta bata kara amai ba ko mummy tace bata sakeyi ba sai dai kanta tace yana mata ciwo sosai kamar zai tsage.
Yace kuma again ban san may yasa zata boye min bata da lafiya haka ba har saida abin yayi nisa sosai yanzu ai ba a wasa da ciwo.
Tace kila bata dauka sosai bane haka ko irin dan zazzabin da kan zo ya wuce ma mutum ne shaaa .
Fitan mummy ya dan kwanto yana tambayana yadda nake ji nace da sauki yace kan fa ya lafa yanzu nace eh kawai badon ya lafa min ba din.
Ya ce in tashi inci wani abu ga nama na da fresh milk in sha kai na girgiza alaman a a yace to a hado maki tea ki sake sha nacs uncle ko nasha ba zai zauna min ba ne .
Ya mike yana bakuma zaki kwanta da yunwa ba kin sani dole ne kici wani abu sai cewa nayi koko zan sha ka fada wa mommy.
Koko kuma a ina za a samay shu yanzu da daren nan nace muna da abindama shi a fridge mommy ta san inda yake na bashi amsa.
Uhmmm yace kawai ya mike tsaye ya nufi wurin mommy din ya fada mata abinda nace ta tashi da sauri ta shiga kitchen din don Nura ta tafi gida ko dare yayi.
Ta damo min kunun ta kawo min shi na dan samu na sha ya zauna min a cikina har na samu barci ya dauke ni sosai ban farko ba sai cikin dare fitsari ya tayar dani.
Nan dakina naga uncle kwace a kusa dani yana barci jin motsina bayan na fito banda yasa shi falkawa yace yaya ne kuma ?
Nace ban daki na fito da sauri yace haras wan ne kuma nacs fitsari nayi yaya jikin yanzu nace da sauki cikin gundura da magana na haye gadon na kwanta a bayan shi.
Haka barci ya kara daukan mu sallah asuba ya fita yi don jin jikina yadda ya gashe kuma ina rawan sanyi yasa shi fita bai tayar dani ba.
Har yaje massalaci ya dawo ina kwance sai kaduwa jikina keyi ina wani irin sam bato hakorana suna kadawa da yan uwan su na kasa.
Hawowa yayi saman gadon tare da dan tallabo ni yana fadin tashi muje asibiti hakana .
Kasa tashi nayi dakyat ya samu na tashi nace kuma zanyi sallah kina iyawa yace dani kai kawai na gyada mai na shiga ban dakin ya biyoni ciki har nayi alwala na gama na fito ya miko min hijjab dina.
Da kyat na sallamay bai saya jiran komai ba ya dagani muka fita daga dakin da kanshi ya toka motar muka fice a gidan bayan ya buga ma mommy zamu tafi asibiti tace jikin ne har yanzu ?
Eh kawai yace ya fice bamu dawo gida ba sai da suka bani gado suka kwantar dani likitan shi ne a kaina sai wasu dakan dan shigo sun debi fitsarina da jini zasu auna su gani.
Alluran da akai min yasa ni barci sosai fita yayi ya kira yaya Saadu ya fada mai anbani gado ya kashe ya kira Aisha tace gata nan zuwa da ta sauke yara makaranta.
Gida ya kira mommy ya fada mata don hankalin ta ya kwanta shigowan yaya Saadune da samira na dan falka ban dade ba na koma barcin don karfin alluran da akai min din.
Zuwan su samira yasa shi komawa gida don anan suka barsu a tare dani sai barci nakeyi hankali kwance ga ruwa daure a hannu na .
Aisha ta zo nan suka hade wurin suna dan hira mummy da zai dawo bayan yara sun tafi makarantane yazo da ita don ance sai sha biyu result zai fito na test din da akayi.
Bai shigo dakin ba amso result din yayi suka hade da likita bayan ya karba yafita sai ya dawo dakin da nake kwance din sun gaisa dashi ya nufi wurin gadon yana tambaya ban falka ba har yanzu ?
Samira tace na dan falka dazu ban dade ba kuma na koma barci ya dade tsaye a kaina ya juya ya fita sai suka hade da likitan.
Hannu likitan ya mika mai yana fadin congratulation sir madam.cikine gare ta har five week shine ya jawo mata ciwo haka kuma kasan yanayin jikin nata gashi kuma bata dade da haihuwa ba strees yayi mata yawa ne.
Wani irin lumshe ido uncle yayi tare da dan rike hannun likitan yana fadin ya gode kamar shi ya bani cikin.
Takardan magani ya mika mai yace asamo wanan maganin idan ta tashi zata samu sauki sai tasha don jikin nata ya samu dan karfi don yanayin ta.
Bai dawo dakin ba don mata sunyi yawa a ciki yake gani wurin sayen magani ya tafi daga can ya wuce office ya duba wasu bakin da yayi sai bayan la,asar sosai ya shigo asibitin.
Lokacin ina zaune ina tauna Apple din da nace yaya Saadu yazo min dashi idan zai zo gaishe sukayi ya amsa a duduke ba tare da ya kalle su ba.
Bakin gadon ya karaso yana tambayana yaya jiki da sauki kawai na iya bashi amsa ya kalle ni duk na ramay na fada a lokaci guda kamar na dade ina ciwo .
Fita suka fariyi a dakin kamar wa yan da ya kora bansan may sa suke shakkan shi idan yana wuri har samira bata sakewa takan ce dani mijin nan naki kamar ustazu yake baya kallon mutane ko kana gaida shi sai ya dinga yi kamar yana tsoron mata.
Muryan shi naji yana ce min cin fruits din ya tashi ko da sauri na kalle shi sai kuma na sadda kaina nayi kasa .
Sai kuma na dago nace dashi ciwo yasani ci idan bashi na dan ci ba banjin dadin baki na yace aifa yanzu banda sauran wasa da saye fruits .
Haba uncle daga ciwo kuma sai in buge da shan fruits ko yaushe murmishi yayi yana gyara zama da kyau yace yanzu yaya kike ji naji sauki na fadi a hankali kamar banson magana.
Ga magani likita ya rubuta yace a sayo dazun sai kin ci wani abu zaki sha don haka barin fita in kira Aisha ta zuba maki kici sai ki sha ido na lumshe a hankali tare da fadin bazan ci abinci ba zan dai sha koko da mummy ta damo min.
Yace ok kisha din sai ki sha maganin ya mike ya fita ya kira Aisha tazo ta zuba min ya dawo ya zauna inda ya tashi yana zaune har na gama sha ya bare maganin ya bani na hadiye na koma na kwanta.
Kwana daya nayi aka sallamay muka koma gida ba laifi don na samu lafiya sosai sai dai jikin nawa ba karfi har lokacin su Maimu da hindatu keyi wa Abba wasa ina zaune na kura masu ido kawai banjin dadin hayaniyar nasu amma kuma ban iya tsawata masu su bari.
Mummy ne ta fito tana masu fada daga dakin ta lokacin uncle ya shigo gidan zama yayi nan falo inda muke mommy ta gaida da dawowa.
Bayan ya tambayeni jikin yana yi ma abba dan wasa ya leke mai wai ya dauke shi yace tafi wurin uwar ka maimu zan dan watsa ruwane a jikina.
Ya mike ya shiga dakin shi ya jima a ciki na tashi na bishi dakin nashi don ban iya jure hayaniyan da yaran ke yi haka kawai nake jin haushi komai ba gaira ba dalili.
Shiga nayi na kwanta saman gado har ya fito ya samay ni a nan nan kika dawo kuma nace haniyan yaran nake jin shi har cikin raina wallahi.
Sai da ya gama shirin shi yasa jallabiya ya fesa turare a jikin shi haka yasa nasan bazai fita ba ke nan yau kuma don baya fita hakana.
Takowa yayi inda nake din yazo ya zauna safiya naji ya kira sunana a hankali na dan bude idona da suke lumshe na sauke akan shi tare da dan kakaro murmushi a fuskana kadan.
Kin san kina dauke da ciki a jikin ki na wata daya da kwanaki da sauri na daga daga kwanciyan da nake ina fadin na shiga uku.
Kin sha uku akan may safiya ban taba zaton jin wanan furucin daga bakin ki ba domin ko abin farin cikine ya samay mu bana shiga uku ba.
Uncle abi fari ciki fa kace yaro na yana da wata bakwai uncle zakace wai abin farin ciki ya samay mu ?
Kallon da yake min ne yasani natsuwa na farga da katobaran da nake shirin yi a gaban shi a yadda na san shi da son haihuwa yanzu.
Yana yawan fada min shi haihuwa yake so yayi yanzu yana son ganin yara sun cika mai gida kamar sauran gidajen yan uwan shi da abokai.
Sai gashi ina shirin yin baranbarama da albishir din da yake min na dan cikin da ke jikina wanda ashe shiyani zazzabin nan da nake yi duk dare.
A hankali na koma na kwanta tare da lumshe idona ina mai jin zafi a raina da samun wanan cikin na jikina a wanan lokacin da ban tsamace shi ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92Next page

Leave a Reply

Back to top button