BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
9/21/20, 9:58 AM – Ummi Tandama: BAHAGGON RAYUWA, , , , , , , , ,

????????8️⃣4️⃣????

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU

Fita yayi daga dakin batare da ya kara magana komai ba nima komawa nayi na kwanta ina jin zuciya na yana min zafi maikon in ji farin ciki a raina.
Ba don komai ba sai irin surutun da mutane zasu dinga yi ga haihuwa na a kai akai da nake yi kowa zai fassara min shi da wata manufa ta daban.
Na dade a wurin kwance ban motsa ba shi kuma bai shigo dakin ba har wanan lokacin barci ne ya dauke ni wanda na dade ina yi sai a zahar na tashi don sallah.
Ko da na fito nasamu bai gidan sun fita da yaran zuwa shan ice cream dakina na nufa ban iya yin wani abuba a dakin sai kwanciya da nayi.
Ina nan kwance sai ga hindatu ta shigo da Abba dauke a hannun ta maimu na bayan ta dauke da ledan tsara da ya sayo masu.
Suna zuwa suka fada min a jiki gaba dayan su na dan lumshe idanuwa a hankali ina jin su a jikina kun dawo nace dasu anty kin ga abubuwan da baba Abba ya sayo muna yakai mu mun ga biri da zaki abubuwa da yawa muka gani inji hindu.
Murmushi nayi nace su bude kayan in gani ba komai bane sai tarkacen kayan lashe lashe na yara dasu yought din robobi nace sai kuje wurin mummy kuyi ta sha ai.
Na samu na iza su suna fita na sauke ajiyan zuciya har wani lokaci banji motsin uncle da banyi ba yasa banji dadin haka ba a raina nasan idan na biye mashi fushin nan nashi ne zai wakana a tsakanin mu kwana biyu.
Haka yasa na dan mike jiki ba kwari na nufi dakin shi don bai falo a lokacin dakin shi na nufa na tura da sallama yana ciki zaune ya tasa laptop din shi a gaba yana aiki dashi.
Jin sallama na da yayi ya dago kai ya dan dube ni kadan ya mayar da kan shi ga abinda yake yi a hankali na karaso inda yake zaune nace.
Uncle sannu da aiki kun dawo yau kasha kiriniya da rawan kai wurin su maimu ya ce na kaisu shan iskane da Abba don kin san farin cikin yara shine nawa a yanzu.
Nasan magana ya fada min a fakaice cikin dakewa nace Allah ya raya muna su ta farkin addinin musulunci yace amin kawai ba tare da ya dube ni ba.
Gyara zama nayi da dakyau a kusa dashi na dan dora kaina saman jikin shi ajiyan zuciya naji ya sauke a raina nace su zuciya manya.
An fara sauka ke nan don naji ya sauke ajiyan zuciya karo na farko shiru ba wanda yayi magana a cikin mu har na wani lokaci sai aiki yake yi wanda nake gani sako yake turawa a lokacin.
Gajiya nayi da kwanci haka na na sai na dan juya ina kokarin jawo filo in kwanta sama muryan shi naji yana fadin kin ci abinci kuwa nasha koko nace mashi.
Koko ba abinci bane kin dai ji likita yace ki dinga cin abinda zai gina maki jiki ko yaushe uncle zan ci nace a takaice.
Rufe laptop din yayi ya mike ya fita sai gashi dauke da abinci yazo ya aje a gabana yana fadin oya tashi ga abinci ki ci na kai duban ga abincin .
Sakwara ne da miyan gaye yaji agushi sai manja da tayi amfani dashi da nama manyan yanka da ta saka sai kamshi ke tashi a gabana.
Take naji warin abincin ya nashe ni har amai na son taso min a lokacin amma don dai kawai in farauta mashi rai haka na daure nayi loma biyar da kyat har nayi kusan rabin plate din dake gaba sai dai ban kai ko ina na ba koda ya dawo mayar da kayan abincin ya samay a bayi ina haraswa sosai.
Na galabaita abinda yasani barcin yamma ke nan ranan sai magariba na falka jina na shiru da mommy tayi ta tambaya lafiya nake kuwa ?
Murmushi yayi yace mummy jikin nata yanzu sai a hankali ai don lalurar juna biyu sai a hankali.
Murmushin jin dadi mommy tayi tana fadin masha Allah nikan nayi tunanen haka yadda naga ta koma kwanan amma naji dadi jin haka wallahi .
Maganan mummy wanda yasa shi jin dadi har cikin ranshi yace mummy na gode kwarai don Allah a tayani kulla da ita a gidan idan ban nan.
Kada kaji komai suriki wanan ai farin cikin mu ne mu duka Allah dai ya raba lafiya ya bamu masu albarka rayulayyu masu tarbiya yace amin mummy.
Dana tashi don sallah magariba da yayi na dawo dakina na yi ban fito ba har ishai sai da mayi wanka na fito falon bai shigo gida ba har lokacin.
Mommy tazo ta samay ni a falon zaune wuri ta samu tana fadin ayya safiya ashe abin arziki muka samu da sauri na kalleta tace mun zamu samu karuwa .
Murmushi nayi na sadda kaina kasa don kunya tace wanan abin yayi dadi wallahi da sauri nace haba mummy.
Dudu fa Abba yanzu wata na bakwai yake shiga ko fafiya bai fara ba kuma ace na samu wani ciki a jikina.
To may ye naji ta katsani yo mai shege ma ta goya balle ke naki da ubansu zaki wani ce bai yi ba ai indan ma wata uku uku zakiyi kina haihuwa ba wani matsa bane a hankan yanzu.
Don ko uban su na da halin kula abin shi yanzu ai gara mutum yayi ya gama da wuri wanan haihu mai wahala na yanzu.
Shiru nayi ina nazarin maganan ta sai kuma na tuna a garin mu matar da tai ciki da goyo har waka ake mata da shagube bata da sauran shakat a rayuwan ta kuma.
Ummi tayi haka lokacin goyon hindatu ta samu cikin autar mu har girkin ta inna tace basu ci a gidan wai tayi kazanta tayi abin kunya don bakar jaraba.
Ta shiga wani hali a lokacin sosai a gidan mu duk da banda wayo amma na fahinci halin da mahaifiya na take ciki a lokacin.
Dole kula da hindatu ya dawo kaina sai inda na fita zuwa makaran ta hindatu ke raban ummi a lokacin inna na bin ta da gori tsakar gida.
Muryan mummy ya katse ni tana fadin ai yanzu mata sun waye da ne can ake daukan shi wani abu amma yanzu ai ya zama isa ga mace goyo da ciki ikon Allah.
Ni dai murmushi yake nayi kawai taci gaba da fadin balle ke da ba nono ma diyan ki ke sha ba ai gara kiyi abinki da wuri ki gama ki gyagiji ko taso tare da su.
Dariya ta bani don jin wai in taso tare dasu da tace sai dai banyi magana ba hira take min uncle ya dawo daga wurin sallah.
Muka gaida shi da dawowa daki ya wuce nasan ruwa zai watsa mu kuma mukaci gaba da sha anin mu a falon har lokacin da ya fito mommy ta shige ta bar mu da su maimu dake kallon katun da Abba dake kiriniya ya koyon mikewa tsaye suna ihu su kuma idan ya mike din.
Zama yayi har lokacin fuskan shi babu annuri a ciki sai dai bai daure sosai ba zama yayi yana kallon yaran yana murmushi.
Juyowa yayi gare ni yana fadin maimuna na gaida ke takira wayan ki a kashe sai ta kirani nace ayyah suna lafiya tun da na dawo asibiti ban koma ta wayan nan ba ai zankira mu gaisa idan na tashi.
Abinci ya mike yaje yaci anan ya barni kwance sai da ya gama ya dawo dauke da fruits a plate ya aje a gaba hindatu na bayan shi dauke da cup din koko mai zafi yana tururi.
Kallon shi nayi na yamotsa fuska yace kina nufin haka zaki kwanta da yunwa a cikin ki dauki cup din nan kisha kokon tunda shi kike so in kin gama ga fruits nan ki sha.
Ya koma ya zauna yana facing dina dole na dauka na dan kurba ina yamotsa fuskana ba halin magana ya tsureni da idanuwan shi da kyat na shaye dan cup din kunun ina sauke numfashi.
Gyatsan haraswa nake yi har na samu ya fada min ban fito ba na koma nakai kance alokacin komai ban so don jikina gaba daya ba dadin shi nake jiba.
Ashe barci ya dauke ni har yayi kallon news yaran suka shige sai lokacin daya gama naji yana tayar dani inje in kwanta yace ya rufo min dakina don haka muka wuce dakin shi gaba dayan mu.
Ba laifi na samu na dan warware don kulawan da nake samu gurin uncle da mummy sosai suke bani kulawa yan kaina ma ba a barsu a baya ba suna nasu kokarin dani sosai a gidan har gyaran wuri suke taya mummy da yan sauran aiyukan daba su fi karfin su ba.
Anty tazo daga lagos gani na da yaran ta har da funke mai aikin ta don ita kadai ke gidan yanzu su fati da faiza kowa ya koma gidan su da zama.
Naji dadin wanan zuwan na anty da dare muna dakina da ita tace ashe cikine yake wahalal dake haka amma wanan cikin yazo maki da wahala don kamar bakiyi haka ba cikin Abba ko ?
Idona ya kawo hawaye nace anty sam banyi tsamanin samun ciki yanzu ba duka duka fa Abba wata bakwai yake da haihuwa na takwas yanzu yake bidan shiga.
To shine may safiya ga mijin ki shi yana ta farin ciki da samun cikin shi ke fada min kin samu ciki mai wahala wanan karon cikin yana wahal dake sosai.
Ni gaskiya anty ban son daukan ciki yanzu gaskiya da sauri tace saboda da may nace kinga wata da muke zuwa amsan magani da ita tayi irin haka.
Sai jinta yayi week kamar zata mutu wallahi da kyat ta sha har an debi tsamani a gare ta sai likita ya fada mata masu irin lalurar mu bai dace suna saurin haihuwa ba da wuri haka saboda jinin su dake ragewa suna iya shiga wani hali kan haka.
Shi kuma uncle ya kasa fahinta na gaba daya yama ki bari muyi maganan dashi na fahinta tace toke yanzu yaya kikeso bayan cikin ya riga da ya samu dole zaki kula da kanki sosai yanzu.
Shiru nayi ban fada mata nufina na son in zubar ba don naga tana goyon bayan uncle tace kada ki hada kan ki da waccan don kila ita bata samun kulan da kike samu.
Mun dade muna hira ta tafi ta kwanta nima na shige kwana daya sukayi muna suka juya lagos don dama ganina kawai suka zo yi.
Yau na tashi da son gyara jikina don yanzu shagon matar nan yar uwar wacce tayi min gyara a bauchi na karbi lambata can nake zuwa tayi min gyaran da nake so.
Tare da kanne na na tafi har da mummy amma tace kitso kawai take so nan samira tazo ta samay mu tunda nace mata gamu wurin gyaran jiki tace gata nan zuwa itama ayi da ita.
Angama ma mummy kitso ganin yaran zasu damay yasa sakina ta kaisu gidan ta su zauna ta dawo mukaci gaba da hira.
Nan nake fada mata ina son zubar da cikin jiki na ido ta zaro min tace saboda may madam niko a gani na da kibar abinki kwana nawa kin haife abinki safiya.
Wata mata da ta girmay muna tana jin mu tace mai zai sa ki zubar yar uwa idona yayi kwalkwal ya kawo ruwa nace yanzu fa dana watan shi bakwai da haihuwa hajiya.
Shine suke son in bar cikin kuma inyi yaya da su su biyun don Allah tace ashe ba a yaye shi ba ma lalai wata bakwai kan akwai wahala wallahi.
Yakai wata nawa cikin jikin naki nace yanzu wata biyu da kwanaki bai cika uku ba cif tace ai mai sauki ne barin rubuta maki su kwaya sai ki saya ki sha mu gani idan bai fita ba sai ki hada da alluran shi.
In haka yaki fitar dashi sai kin je an cire maki ke nan ta bude jakkata ta ciro takarda da biro ta rubuta min nayi mata godiya na karba har mukayi musayan lamba da ita a wurin.
Ban je gida ba sai dana biya na sayi maganin a wani babban chemist dake hanyan mu na kwaso mummy da yaran gidan su samira muka dawo gida.
Kai aka wanke min sukayi min kitso sai dai ba kanana ba sai gyaran jiki da sukayi min don jina nake na koma wata irin gaja dani rashin gyaran da ban samu kwana biyu inyi.
Jin jikina nake yau kamar ba nawa ba sai dare Uncle ya dawo don suje site din su dake sulaje yau a can store din su yake babba inda suke tara kaya indan an kawo masu.
Idan yaje can ya dawo yakan gaji sosai don aikin wahala akeyi a wurin har shi yakan taba aikin aje a dawo basu da hutu ranan.
Ko da yadawo ya gaji sosai wanka yayi yaci abinci ya kwanta nima ban dade ba na samay shi a dakin har ya kwanta ko sai dai bayi barci ba.
Na shigo na rufe kofa ido ya tsura min daga inda yake kwance har na iso gare shi yace yau wanan gyara haka sai ya mayar min dake wata irin yar yarinya under age.
Murmushi nayi na karasa hawa godan na kwanta nace under age haka kamar kumama dani yace to be serious yau kin koma yarinya sosai murmushi nayi kawai ina gyara kwanciya na.
Ranan bai barni ba sai da ya dan lalube ni muka gama muka sake wanka na kwanta zuwa asuba sai zazzabi ya rufe ni kuma da kyat na tashi nayi sallah na kara kwantawa.
Har ya gama shirin shi ban sani ba sai da zai fitane yake tayar dani zai fita indan jikin ya matsa ki kirani mu koma asibiti tau kawai na iya ce mai na koma na kwanta.
Yafita ya sauke yara makaranta ban fito ba sai kusan shabiyu koshi na fito in samu dan ruwan liptop ne in sha.
Anan falo na zube na umarci Nura ta hado min ruwan liptop jin muryana yasa mummy fitowa tana min yaya jikin , ?
Fuska a yamutse nace mummy da sauki take cewa ko jigilar gyaran jikin da nayi jiya ne ya saukar min da zazzabi ciwon ne kawai ya dawo mummy.
Litop din ya taimaka min naji bakina ya koma min dan daidai har na sha lemu anebi wanka na naje nayi dakina koda na fito wayana yana ruri a lokacin.
Na dauka da dan sauri kada ya katse uncle ne yake kirana a lokacin ina dauka nace uncle yaya aiki shiku bai tsaya bani amsa ba sai tambayana yayi da yaya jikin naki ?
Nace da sauki uncle kin ci abinci ya tambaya nace mai naci alhalin banci din ba bani mummy yacd nace mommy tana dakin ta nima dakina nake kwance.
Ok sai ki sha magani kafin in dawo Allah ya sauka nace dashi amin ya kashe wayan na wurga wayan saman godo naci gaba da shirina.
Bayan yadawo gida da yaran ya samu naji sauki sosai zaune ma nake da Aisha data kwaso yara tabiyo tanan dubani da jiki mun da ita kafin ta wuce gidan ta.
A gida yayi magariba duk banda wani matsala komai zuwa tara kaina ta fara ciwo kamar zai tsage min haka yasa dole ya fita ya samu min magani nasha.
Zazzabi sosai nayi da dare dole da safe muka nufi asibiti ban so zuwa ba amma ba yanda zanyi dole naje aka dubani muka dawo gida.
A hanya ya matsa min may nake so ya saya min nace ban son komai sai masa mai zafi idan zan samu dariya yayi yace aiki ko ya samay ni ni madam wani irin ciki kika dauko wanan karon kuma ?
Haka mukayi ta yawo gidajen abincin hausawa ana muna kwantace sai da kyat muka samu masa yayo min take away leda biyu muka juyu gida ina ji a mota yana ma hajitan shi waya ta sa a turo muna da masa bana ya samu dan gargajiya a gidan shi.
Dariya tayi tace insha Allahu goben zata sa ai min za a samu wanda zai kawo min in Allah ya yarda tace ya bani waya idan ina kusa muka gaisa tayi min yaya jiki har muka iso ina magana dasu.
Ban tsaya falo ba dakina na nufa na aje jaka da maganin da aka bamu asibitin irin ta masu lalurar mun ta masu ciki sai na saka a jakkana.
Ruwa na watsa ma jikina don in ji dadi nafito nayi sallah sai na dawo falo na zauna masan naci shi sosai kusan na kusa cinye take away din.
Na sha ruwa nan muka zauna hira da mummy shiya dawo gida da yaran yau ma ya zauna kusa dani yana wasa da Abba kamshin turare shi ya haddasa min wani irin ciwon kai.
Gudu nayi na shige daki na kwanta sai kuma amai yazo min nan na amaye dan masan danaci koda zai saura a cikina sai kadan.
Shine ya shigo yana tambayana a harasawan ya dawo ne kuma yanzu kai yace har ya juya yace kin sha maganin ki kuwa nace ban kai gasha da na bari idan zan kwantane tunda sunce yana da karfi.
Ina kika a je maganin yace min tare da kafe ni da idanuwan shi bako kiftawa nace gayan nan cikin hand bag dina ina fadi ina mikewa zaune don nasan shan maganin zanyi.
Sai damay yana cikin tona jakkan ya jawo wanan maganin da na sawo a chemist wanda matar nan ta banj na zubar da ciki.
Jin shi shiru danayi yasani juyowa inga may yake yi a lokacin maganin na ganshi rike dashi a hannun shi yana karanta wa.
Take naji gabana ya fadi a wurin juyowa yayi yana tambaya na wanan maganin may Safiya ?
Magani na ne nace mashi yace ai nasan maganin ki ne na may ye na tambaya ?
Kaina na dukar kasa ban ce dashi uffan ba Safiya naji yace na dago kaina yace cutana zaki yi komay ?
Shiru nayi na kasa magana sai naga ya fita da maganin a hannun shi take fuskan shi ya juye ya koma wani irin zaki a gabana.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92Next page

Leave a Reply

Back to top button