BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
9/24/20, 5:48 AM – Ummi Tandama: BAHAGGON RAYUWA , , , , , , , , , ,
????????????
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
Haka rayuwa ke ci gaba da gudana a gidan uncle watarana mu tashi a farinciki har dare wata rana kuma haka kawai zai daure fuska gare ni ba gaira ba dalili yayi ta fushi dani ga laifin da ban san nayi ba.
Ga dai ci da sha da sutura wadatace a gidan amma banda kwanciya zuciya a
gurin uncle ga fargaban ciwon dake jikin mu yau kaji ance babu wani a cikin masu irin lalaurar mu gobe kaji ance wata ta rasu akan laluran nan.
Ga ciki yayin wani irin girma a jiki saikace cikin tagwaye na dauka wanda bai san halin da nake ciki ba sai ya dauka ai ina cikin daular duniya ne ina cin ta da tsunki ba abinda ke damu na.
Sai dai da zan zauna dake in fada maki ciki na zaki fahinci rayuwan da nake yi a yanzu wanda zan iya kira maki shi da BAHAGGON RAYUWA .
Daga bakin ciki na fito na fada rashin kwanciyan hankali a gidan uncle don kullu a fargaba nake dashi kada yace ga laifin da nayi mai a gidan.
Amma idan yana cikin dadin rai idan ka ganmu saika dauka ba wanda ya kaimu soyewa a duniya a yanda muke daga bakin rayuwa zuwa haske da mai kumshe da magana a zuciya????????????.
Cikin wai a hakan ina jin yan uwan shi na fadin wai ya rage a cikin halin shi na baya sai nakan tuna da maganan da Faiza ta fada lokacin muna gidan anty a lagos.
Dadi na guda shine akwai waddata kuma yana taimakawa yan uwa da nashi da duk wanda yake rabe damu kodan wanan abin dole in yi hakkuri tunda na saba da irin rayuwan shi yanzu.
Su baba da mama sun tafi lagos gaisuwa sun kara tula ma gwangon mu nayi a ka wanda ranan da ta gansu taji kunya sosai ba kadan ba.
Baba yace ai zumunci bai yake ba don Saadu bai yarda zumunci ya lalace ba a tsakanin mu idan ma ke da Amadu bakuje ba ai shi yatafi gurin mu kin ga ko dan shi mazo wanan gaisuwan tunda bai yar damu ba ya dauke mu da muhinmaci sosai a rayuwa.
Mama kuma ta saka gwago a gaba tace yanzu n saboda son kai kika zabi wanan rayuwan a tsakanin kina ganin kin kyautawa kanki ne a hakan da kukayi.
Kun cuci yar mutane badon Allah ya kawo mata mafita ba a rayuwa da anmanta da rayuwan wanan yarinyar a duniya.
Da yake Allah bai barin bawan shi haka ya tabe sai ubagiji yayi mata dubaiya ya saka mata da miji yau itace ke rike damu da yan uwan ta baki daya duk ko da bakin cikin da ta fuskanta da farko a cikin mu bai sa yanzu da ta samu ta watsar damu ba ta jawo mu ta rungumay mu a jikin ta.
Kuka gwago keyi sosai na nadama mama ta gagaya mata magana masu zafi tace kiyi kokarin ganin ta ki roketa gafara zai fi.
Cikin ikon Allah na haifi dana lafiya asibiti don uncle yana gari a lokacin don haka a asibiti na haihu lafiya.
Bai samu gani na ba sai da aka fito dani dakin hutu suka shigo dakin ina kwance shida yaya saadu da mommy dasu samira .
Tunda mommy ta mika mai yaron ya rungumay shi a jikin shi bai yarda ya mikawa wani ba ya dade yanawa yaron addua.
Ya dago kai yace yaya Saadu kaga baiwan da Allah ya karamin kaunaka taso ta min bakin ciki ga hakan da Allah ya azurtani a dan lokaci kankanni ?
Murmushi yaya Saadu yayi yace yallabai ai mata hakkuri ta tuba murmushi yayi kawai ya mikawa yaya Saadu yaron.
Sun dade a dakin ana muhawaran wa yaron yabiyo cikin ni da uncle mommy tace wanan duk fuska gidan su suke daukowa Abba zai koma watarana don da ubansu suke da kama sosai.
An sallamay mu mun koma gida bayan dan wani lokaci sai dai ciwon kai da jiri da ke damu na akai akai wanda ya hanani walawa mun koma asibiti washe gari ba abinda likitan mu ya bani sai cewa yayi hutu jikina yake bukata kawai.
Kaina yana rike da hannuna na dafe goshina da hannu daya yana tuka mota muka nufo gida magana yake min amma ban iya bashi amsa a lokacin.
Har muka shigo gida ban tsaya ba na shige daki na kwanta maganin da aka rubuta min ya sayo na sha na samu barci mutane na shigowa amma ban sani ba.
Sai bayan karfe hudu na falka daga barcin da nakeyi kewayawa nayi sai dai daga ban dakin sai da mommy ta kamoni na dawo daki.
Uncle ta kira take fada mai abinda ke faruwa dani yace gashinan zuwa gidan dole ya baro aikin ya nufo gidan da sauri a ranshi yana fadin kardai yar mutane ta mutum dama abinda take gudu ke nan gashi kuma yana shirin faruwa da ita.
Gudun da yakeyi ne yasa shi isowa gida da wuri dakina yayo derict ina mai da numfashi guda guda ina fadin mommy kaina kamar zai fashe min nake jin shi.
Turo kofa yayi da sauri ya shigo dakin yana fadin Safiya har yanzu kan bai bari ba na dago idona da suka kade sukai min ja sosai gaban shi ne ya fadi yadda dan lokavin gadan na sauya nayi wani irin baki sosai.
Gashi na ramay lokaci daya kamar bani ba rike min kan yayi yana addua yana yarfarwa gefe ya dago yana tambayan mommy ko naci abinci tace ban ci komai tashina ke nan na shiga bandaki acan na tashi faduwa sai da ta kamoni muka fito.
Mommy hada mata tea mai kauri sosai ki kawo madarar ruwa da tomotor da gwagwanin maltina in fara bata da sauri mommy ta juya ta dauko abindaya lissafa mata ta shigo dasu take a wurin ya hada ya bani na sha.
Ta kawo tea din nace mata na koshi ba zan iya sha ba suka matsa min nasha rabin cup din nayi getsa sai ga zufa na karyo min lokaci daya na koma na kwanta tare da lumshe idona.
Ya dade a wurin tsaye ganin na samu barci yasa su fita su barni dakin ni daya mommy na goye da jiririn abayanta kallon mommy yayi yace ina ganin jinin da ta dan rasa ne a jikin ta yake haifar mata da ciwon kan haka.
Mommy tace dama shine fargaban ta a kullun wallahi ko haihuwan Abba tayi ciwon kai sai dai bai kai haka din ba gaskiya.
Yaron dake goye a bayan mommy ne yayi kuka ta sauke shi tana dan jijiga shi ajiyan zuciya ya sauke yace ina ganin kamar a kira gida gwago tazo ko khadija su taimaka maki don abin yayi maki yawa ke kadai haka.
Tace don dai abin yazo da akasi ne amma ai bai da matsala don ga yan matan tana suna taimaka min da kula da Abba idan suna gida.
Naji dadin kamun kan da yayi min don shi ya lafa min da ciwon kan da nake ji a baya sosai dana falka cikin dare ni da kai na nemi a bani abinci inci.
Na dauka dare yayi a lokacin sosai ashe wajajen karfe tara na dare muke a lokacin don ganin su maimu da nayi basuyi barci ba na tambaya mummy ke fada min time.
Ganin na tashi ne sukazo kusa dani suka zauna hindu na goye da jariri maimu kuma ta goya Abba.
Ido na lumshe a hankali tare da tunanen yanzu duk yaran nan nawane gasu kamar tagwaye don ba wani tserayan kirki a tsakanin su tunda Abba ma bai wuce goyo ba.
Uncle ne ya shigo dagin ya ganmu shiru sun tasani a gaba ba mai magana cikin mu duk da yawan rakafi su yau sun natsu sanadin rashin lafiyan da suka ganni ciki.
Wuri ya samu ya zauna a kusa dani yana ce masu kune yan jiya naga kunyi cirko cirko a dakin mommy dake zuba min ruwa ina wanke hannu tace dashi ba dole ba.
Sunga yar uwarsu a wani hali da basu saba ganin ta ba yace mommy ina ganin ba zan tsaya ayi suna ba zan fita da ita waje taje can ta samu hutu na dan wani lokaci.
Tace Alhaji kadai yi hakkuri yaron ya karbi sunan shi a nan don kasan mutane akwai tsegumi in anyi suna sai ku tafi.
Mommy ban damu da abinda mutane zasu fada ba kan haka lafiyan ta nake jawa kawai shine muradina, ina gudun kar abinda take gudu ya faru da ita don ta riga da ta nasa hakan gashi yana shirin faruwa da ita kuma.
Haba dai Alhaji bai kamata kayi saurin saka wanan a zuciyar ka ba don Allah ne mai yin komai ga bawan shi dama dai tasan irin kalubalin da hakan ke haifarwa ne tun wuri.
Kaida ayi fatan ta samu lafiya kanfin suna zaifi abar wanan maganan yanzu mu koma na neman lafiyanta kawai.
Ajiyan zuciya ya sauke mai nuna gansuwa da maganar mommy shine amfanin zama kusa da maya din da akeso a hankali nace ya kara min adduan da yayi min dazun don naji dasin shi sosai daya min.
Yaran mommy ta kada kan su zuwa waje dakin ya rage dagani sai shi a lokacin rugumay ni yayi zuwa jikin shi tare da dan shafa min baya yana fadin Allah ya baki lafiya matana ina jin da da halin in karbe ciwon nan a jikin ki.
Murmushi nayi nace Uncle ai ciwo kaffara ne ga bawan shi da yardan Allah zan samu lafiya in koma daidai dama sun fada muna haihuwa akai akai yana haifar da irin matsalan a gare mu rashin daukan matakin da bayi bane bayan haihuwar Abba yasani saurin daukan ciki da wuri.
Yace da rabon wanan yaron kuma yazo a wanan lokacin yasa muka manta da yin plaining a ziciyar mu sai dai yanzu dole a dauki mataki tunda na hango illar yin hakan yanzu.
Kaina ya kama ya fara min adduan da yayi min da rana sai da ya gama yace ki kwanta ki huta kinji abinda likita ya fada muna hutu kike bukata da cin abinda zai gina maki jiki da sauri jinin da kika rasa ya dawo.
Allah ya baki lafiya yace yana kokarin kwantar dani kamar karamar yarinya bakin ba don zaman dama ya isheni na koma na kwanta .
Da safe da ya shigo yake fada ma mommy ya dage sunan sai sarin mai zuwa har na kara jin sauki zai dai yankawa yaro rago idan sunan yazo buki sai wani sati.
Shi ida hali ma bukin ba sai anyi ba don in samu in huta a dakina baison azo a damay ni da hayaniya da yawa don taron suna hayaniyane kawai ba komai ba.
Yadda ya fada hakane ya faru don samira da Aisha sun ta kiran mutane suna fada masu suna sai wani sati idan Allah ya kaimu za ayi.
Sannu a hankali nake jin sauki har na dan bar jin ciwon kan sai dai yawan jiwa dake damuna idan na mike shima yana ragewa a hankali.
Haka dai suna yazo lokacin na samu lafiya sai dai a tsatsaye nake har lokacin akai suna yaro ci sunan uncle din sulaiman.
Na dauka zai min kara ya sa sunan nawa mahaifin sai naji yace wa mommy sunan yaro sulaiman nayiwa kaina takwara don kada a manta baya.
Yan uwana da nashi sunzo akai buki suka koma gida don ba wani hayaniya tunda ba lafiya gare ni ba haka yasa ummi na zuwa ita da su mama da babanmu da mommy mahaifiyar Amina kawata da motan gidan su suka zo.
Suna da kwana uku suka shigo garin da yamma da taimakon yaya Sani wanda yayo masu jagora.
Ba mu san da zuwan su don haka suka shiri da yamma sai ganin su mukayi suna shigowa da sallaman su muna zaune falo a lokacin sisters dina suna min hira mummy kuma na bawa Abba abinci kafin yayi barci.
Matan suka shigo baba sai baba ya tsaya a kofan gida bai shigoba a lokacin munyi mamakin ganin su sosai da tafiya haka babu sanarwa.
Yaran najin ance da baba akazo yana waje nan suka fice da ihun su suna murnan ganin shi yace ho yan nema mutan abuja ke nan.
Watau kuna nan kun shige birni kun manta da kowa ko dariya sukayi gaba daya sun sauya a idon shi sosai yaga sun kara mai girma sosai ba kamar yadda suka bar gida ba.
Da murna muka tare su sai fadin lalai Safiya ba lafiya jiki duk ya zube haka a lokaci daya murmushi nayi ina fadin ai naji sauki mama yanzun gashi ina iya mikewa kai tsaye ban taba komai ba.
Waya na dauka bayan mun gama gabatar masu da abinsha na kira uncle da bai dade da fita ba a lokacin ganin kirana yasa gaban shi faduwa sosai ya dauka cikin murya na yanayin mai ciwo nace su ummi na sun zo uncle har da baba.
Nan Abuja suka zo ko ina nace nan suka zo uncle yanzu suka iso garin da sauri yace gani nan tafe na kashe wayan na dago kai na kalli mummyn su Amina nace.
Mommy yaya hanya yaya wajen su Amina da yaranta tace suna lafiya naji tana fadin ai zats zo idan an kwana biyu tace yaya jikin naki yanzu ?
Naji sauki sosai mommy yanzu tace amma dai kan kinji jiki wallahi duk kin zube haka kamar kin dade kina jinya.
Mama tace yanzun kin ji sauki ke nan a haka gaskiya hankalin yan uwan ki ya kasa kwance sun koma suna fada muna ba dadi wallahi.
Sai da uncle ya iso ya matsa ma baba su shigo da dan uwan mommy daya jawo mota da yaya sani matan suka mike suka bi mommy zuwa ciki.
Har kasa muka zube muna gaida baba sai yaya jikin yake mun tare da jajantawa sun dade suna magana da uncle bai yarda yasha ko ruwa a gidan ba munyi munyi dashi yaki shan komai .
Gab da magariba yaya Saadu ya iso suka fice tare baba na fadin gidan dan shi zai tafi sai gobe idan sun shigo.
Mukai mai sallama ya tafi Allah ya taimake ni nura bata tafi ba a lokacin ta dora girki da sauri saboda bakin da tagani a gidan sun zo.
Gaskiya ina jin dadin zama da ita don tasan ya kamata sosai koda nace mummy taje asan abinda za a ayi masu sai ta samu har ta kusa gamawa a lokacin .
Ranan ban san irin farin cikin da nake ciki ba yau ummi ce da kanta a gidan aure na wani abu sai ciwo wallahi da ban san ranan zuwa mommy gidana ba.
Muna dakina dasu tunda akayi sallah suka shigo dakin lokacin ina ciki na dan kwanta anan suka samay ni mommy ce tayo masu jagora zuwa dakin.
A nan aka kawo masu abinci mama sai bin su maimu sukeyi da kallo wai yaran sun girma sosai yanzu..
Ranan dai kwanan farin ciki mukayi ga iyayye na a gidan uncle ya rasa ina zai saka su ya kwaso wanan ya sayo wanan yace a ba baki su ci.
Da safe suka tashi da shirin haraman komawa don wai kwana daya zasuyi muna anan uncle ya dago da maki da na samay shi a daki ina fada mai shirin tafiya sukeyi.
Take ya kira yaya Saadu yace mai yayi magana da baba ba zancen tafiya yau gare su sai gobe ko jibi idan an duba masu motar su.
Dole badon baba ya so ba ya hakkuri suka kara kwana yaya Saadu yazo ya dauke su suka tafi gidan shi ya kaisu kuma gidan Aisha.
Uncle ya shigo ya samay ni da rana yana fada min cewa ummi fa ba zata koma ba dasu don zata kwana muna biyu ina son muyi tafiyan nan da ita.
Yaya Saadu nace yayi wa magana don nasan ko baba ya yarda ita tana iya kin yarda tace bata zama gidan suruki komawa zatayi gida.
Hakan ko akayi shima baba bai so yarda ba da farko sai da yaya saadu yayi mai magana akan yara yake son a tafi da ita ya yarda.
Ita ko da aikai mata magana kafewa tayi bazata zauna ba su mommy suka ke be da ita a idon mama suka ce kada tayi haka.
Ko wace uwa tana fatan haka a wanan zamani Allah yayi mata baiwa don may zata guje ma haka dole bataso ba ta yarda ta zauna tana kallon washe gari suka kama hanya zuwa gida.
Kwana biyar muka kara wani yammaci sai gashi ya shigo har dakina yace an gama komai a shirin tafiyan mu don haka ranan monday zamu tashi har da yara zamu tafi don zamu kwana biyu a can.
Ban dauka har mommy su samira zamu tafi ba don ganin dawainiyar yayi yawa sai gashi da yaba pasphot na ga har da ita a tafiyan.