JANNAH COMPLETE HAUSA NOVEL

JANNAH COMPLETE HAUSA NOVEL

“Amman yayanmu duk da haka ai saikace kana son zuwa ka ganni da inda nake din ko”

“Kiyi hakuri murja, ni yanzu bana da ma lokaci sosai kullin ina makaranta course din da aka bani wahala ne dashi dole saina dage, nasan yallab’ai bazai cutar dake ba rayuwarki zatai kyau”

Sai nace masa, “sai anjima ka gaida su innamu”

Raina ya b’aci yadda yake nuna bai damu da inda na tafi ba, dauke kaina nayi daga wayar kurin shi kuma ya kashe yasa aljihu, baice mun komi ba ya wuce dining yana cewa “kizo mu karya”

Har muka gama break din kamar kurame bamai magana, tunda ya sadda kansa bai dago ba saida ya gama kamar bana wajen, ayadda na lura fuskarsa kamar ta canza kamar ransa ya b’aci, to me akai masa? Na tab’e baki na kurin ina daukar tissue kamar yadda naga yayi ya goge bakinsa ya mik’e yace, “ki jirani wajen mota”

Na tashi na wuce wajen motar na jingina da ita ina kallon harabar wurin, ko nan kadai zaka tabbatar gidan yana da kyau, an kawata sa ta ko ina da abubuwan kawata waje, ga flowers nan kala daban daban ruwan da akai yasa sun kara haske, garin da lillami aka atashi yau.

Ina nan tsaye ya fito cikin natsuwa yake tafiya cike da mazantaka yanayin jikinsa kadai zai tabbatar maka shidin dan kwallon kafane, driver ne ya iso cikin sauri gana isowa wajensa ya risina cikin bayar da hakuri,

“Agafarce ni yallab’ai na makara”

Da hannu yai masa nuni da yashiga mota yana jifa masa key din kawai, duk nasha jinin jikina yadda yaketa cin d’acin nan dole akwai abunda yafaru, shigarsa motar yasa nima na bud’e na shiga daga can bangaren sa driver yaja muka dauki hanya hanya kurin yake kallo ta glass din gefen sa, duk banjin dadin wannan abun da yake ko nice nai masa laifin to? Na tambayi kaina sai nasamu kaina da cemasa,

“Yallab’ai nayi wani abunne?”

Yadda ya juyo yana kallona dole na sadda kai kasa, “mikike son ya zarga da kike gaya masa ya kamata yazo ya ganki da inda kike? Idan kinsan baki yarda dani ba meyasa zaki yadda ki biyoni? Ni a tsarina bana son rashin yadda haka bana son zargi, don haka zan maidaki gida shine kawai”

Hankalina tashi yayi cikin duburcewa nake cewa, “Yallab’ai baka fahimceni bane magana ba haka take nufi ba, wallahi ko kusa bana zargin ka da komi, kuma na yarda dakai kayi hakuri don Allah idan ka maidani ban san wani kalami inna da baba zasuyi mun ba, kaji yallab’ai don Allah”

Idona ya cika da kwalla har sun fara zuba, baice mun komi ba hakan ya sake tada mun hankali na saka kaina cikin cinya ina kuka,na dauki lokaci ina kukan sannan naji yace,

“Please………….”

Shashsheka nake tayi ina kokarin daina kukan, saboda yadda ya dauki maganar har raina ba haka nake nufi ba, sake mun magana yayi cikin sassauta murya,

“JANNAH please”

Dagowa nai ina kallon sa hanky ya mik’o mun yana cewa, “ni fa bance kiyi kuka ba”

Yadda yai maganar kamar wani dan yaro ansa nai ina goge fuskata ina shakar kamshin dake jikin hanky d’in, na mik’a masa kin ansa yai yana jingina bayansa sosai da kujera,

“Ka juya yanzu mun fasa gida zamu mannir”

Ya amsa cikin girmamawa sannan ya jiyo yana dubana yatsuna kurin nake ta tsifa, d’an matsowa yai kusa dani har saida gabana ya fad’i murya kasa-kasa yake magana,

“Duk abunda kikaji na fad’a idan mun isa karki sake ki nuna ba gaskiya bane, sannan zaki cigaba da karatu insha Allah Amma lokacin na tafi zan dora nauyin hakan akan usman”

Jinjina kai nayi bance komi ba yaja iska kadan sannan ya dan kallan yace, “fushi kike?”

Saurin kallon sa nai nace, “Aa fa”

Lumshe idonsa yai daga nan har Allah ya iso damu nasarawa bamu sake magana ba,
Girman gidansu yallab’ai kadai dole ya baka mamaki, babbane katon gaske harda bene asama saidana kilga get uku ne garesu, gidan fa ba karya duniya kenan bed’e mana akai muka shiga cikin harabar gidan, anan na fahimci bangare bangare garesa gidan, ga motocinan sai numfashi suke dirma dirma babu wadda tasha jiki acikin su, jinai gabana yana fad’uwa sosai sai na tuna maganar anty jamila da tace nayi addua, dan danan na kamayi inajan ajiyar zuciya.

“Are u OK?”

Ya tambayeni firgicin daya gani tare dani yasa bai fita ba yace mun, “ki natsu pls babu abunda zai sameki insha Allahu kinjiko”

Na d’aga kaina kurin sannan ya bud’e yafita na bisa abaya adduar nake tayi ina biye dashi har zuwa babbar kofar da zata sadaka da cikin gidan, gaba daya bangwayen tayils ne mai dan karen sulb’i, kofar ma da maddanni ake bud’eta muka shiga saida muka wuce wani karamin falo da kujeru guda uku harda tv a wurin, sannan muka sauka daga wani dan bene hawa shidda sannan muka shigo katafaren falon mai dauke da set din kujeru guda biyu, ga faskekiyar tv nan da kayan kallo, kai idan na tsaya fayyace gidan bazan gama ba gidansu yallab’ai karshene………..”zauna anan ina zuwa”

Yace dani, zama nai cikin daya daga cikin kujerar mai laushi inata cigaba da kallon falon, shi kuma yabi wata hanya ya b’ace ma gani na……………..

Sai kunyi hkr dani akan posting, banda lafiya isassa ba kullin zan ringa typing ba ina fatan zaku mun uziri, na yau ma karfin haline ngd da kaunarku

Mom muhseen✍????
[7/28, 12:58 PM] Mom Muhseen????: ????JANNAH????

{A TRUE LIFE STORY}

E.W.F

By
Mrs Bb
mom muhseen

wattpad name
Humaira3461

    ????️.......10

“Ka dauke ta kubar gidan nan tun kafin na fito ma na sameta, na gaji da kwaso yara agidan nan kazamai dasu sai sunci sunyi girma sun gyagije sannan suyi mana butulci, bazan sake daukar yar aiki inba tsohuwa ba ai na gaya maka tun wancen karon ko?”

Momyn ce take ta fad’a tun sadda ya shiga b’angarenta sanar da ita zuwan jannah, kasa cewa komi yayi saboda shi baison fad’a ko kadan, dagula masa lissafi yake.

“Momy Mai zai hana kiganta idan ta miki ba shikenan ba, kawai dai k
Matsalar a samu yar gidan talakawa kazamai suyita mana kazanta agida, bayan haka kuma waccen matsalar kuma sai adauki mataki”

Kallonta momyn tayi tana cewa, “watau don Asaad ne yasa kike wani lauye baki kina tayasa begin ko?”

Cikin shagwab’a tace, “no momy babu dad’i kazo da mutu kuma ace ka maidasa”

Tashi yayi zai fita bai ce uffan ba harya bud’e k’ofar momyn tace, “yar inace? Inma daga kauye take tashin farko bazan dauketa ba gaskiya”

Atakaice yace, “kizo ki ganta saiki ida yanke hukunci”

Ya fice rai b’ace yana banko kofar, “jarabebben banza da wofi, ke kuma saina ci ubanki in kina samun baki idan ina magana”

“Momy duk kinsaka ransa ya b’aci don Allah, kefa kiketa complain akan yan aiki sun miki kadan, yanzu yaje ya samo miki ko ganinta bikiyi ba kinhau kushewa, taya zaiji dad’i”

Afusace ta dauki abu zata maka mata tatashi aguje ta fice daga d’akin.

Ina nan zaune zuciyata nata bugawa naga fitowarsa hada ido mukai cikin sigar kwantar da hankali ya lumshe mun idonsa, na rausayar dakai kurin wuri ya samu ya zauna yana dora d’aya kan d’aya ya cigaba da danna wayarsa, babu jimawa kamar daga sama saiga wata matashiya ta fad’o falon kamar anbiyota, tunda muka had’a ido da ita ta kafeni da ido kamar zata cinyeni, mamaki da rud’ani ya bayyana akan fuskarta araina kuwa addua kurin nakeyi, cikin rudewa take cewa “Asaad ina yar aikin? Wannan kuma bakuwa momy tayi ko kawar hindu ce?”

Batare daya kalleta ba yace, “itace wadda zatai aikin ai………..wannan kyakkyawar? Tabdijam ke kinganki a madubi kuwa? Ki rasa abun yi sai aikatau?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Leave a Reply

Back to top button