JANNAH COMPLETE HAUSA NOVEL

JANNAH COMPLETE HAUSA NOVEL

“Sannu dai bawan Allah, ince dai lafiya badai wani abun yafaru ba ko?”

Girgiza kai yayi yana sake kallona nai saurin kauda kaina sannan yace, “lafiya sai alkairi mama, naji kuna cikin wani haline na bukatar kud’i gashi baku da halin hakan ko?”

Bakinta na rawa tace, “sosai ma bawan Allah, aikine za’ai ma babansu ance sai mun kawo miliyan biyu, wallahi idan ba daya daga cikinsu zaj siyar ba abani kudin bamuda inda zamu samesu wadannan ma…………..ya isa mama naji komi wajen likitan acan nagansu ai, abunda ya kawoni shine zan taimaka muku zan biya kudin aikin duka zan dauki nauyin wajen zamanku da cinku da shanku da dukkan abunda za’a buk’ata har asallamesa, Amman idan zaki ban wannan yarinyar taki taringa mana aiki agidanmu ni kuma zan muku komi”

Hawaye ne suke zuba afuskar innamu yayin da maganarsa ta karshe ta dakeni, nifa naga ya nuna da hannu abashi ni nai musu aiki agidansu? Kasa cewa komi nai ina kuma tariyo maganarsa akan taimakon da yace zai mana,yayanmu ne ya fara masa godiya kamar zai kwanta mashi,

“Yallab’ai nine madad’in babanmu ayanzu, don haka ga murja nan mun amunce inhar zaka rik’e mana ita da amana”

“Wai wace irin magana kakeyi ne yayanmu? Bamu san shi bafa, yau muka fara ganinsa shine kawai zaka yarda dashi? Idan wani abu ya sameni fa? Innamu kema kin yarda da abunda yayanmu yace?”

Na fad’a inajin tashin hankali yana rufto mun, cikin sanyin murya yace “wannan shine katina address dina no wayata, idan kun gama yanke shawara saiku neman…………..Aa yallab’ai karka tafi mun amince ni na haifeta kuma zatai dukkan abunda na umurceta dashi, indai akan murja ne mun amince saidai kayi mana alk’awarin ba zaku cutar da murja bazaka rik’e mana ita amana”

D’an murmushi yayi yace,
“Ban tab’ajin tausayin wani talaka ba sai yau kuma akanku, karona na farko da zanyi wani abun kirki ga talaka idan hankalin ku bai kwanta ba na hakura daman nayi hakan saboda albashinta na wata zai taimaka maku matuk’a kasancewar shi baban baida kafar fita nemowa shi kuma wannan ya samu ya koma makaranta”

Innamu durk’usawa tayi tana masa godiya kamar me tana yimasa addua haka yayanmu kamar anbiya masa makka,kwata kwata na kasa yin wani dogon tunani tabbas ina son baba ya warke daga wannan ciwon, amman bana son rabuwa da iyayena akan haka banda wani zab’i sai ansar kaddarata ga hannu, domin ceton baba da rayuwar mu.

Tare da yayanmu sukaje aka biya kud’in aikin sannan suka fita cikin gari can wata unguwa wai ita janbulo ya kama mana gidan da zamu zauna, sannan ya damk’a iyayen kud’i hannun yayanmu yace duk abunda ya taso yayi idan sun k’are ga no dinsa nan ya kirasa karyaji komi, abubuwan sai suka ringa zo mun kamar almara yan awanni baya muna cikin tashin hankalin neman kud’in aikin baba,yanzu kuma cikin abunda baifi a wanni uku zuwa hud’u ba dukkanin wasu damuwowin mu sun warware, innamu da zainab da yayanmu ban tab’a ganin farin ciki a fuskokin su ba irin yau, amman ni na kasa farin cikin duk da inajin dadin baba zai warke insha Allahu, Amman a raina mutumin bai kwanta mun ba na kasa natsuwa dashi, bai tafi ba saida aka had’a dukkan abunda ya zama dole acikin gidan sannan yace zai tafi,innamu ta ce masa “yallab’ai munfa gode kwarai da gaske, zuwa yaushe murjar zata fara aikin?”

Kallona yake da wadannan idanun nasa kamar na yan indiya saboda zuwa lokacin ya cire glass din, fuskarsa cike da annuri ko na miye oho ya shafa kanshi da ya cire hular tare da babbar rigar, sai yai kyau sosai cikin natsuwa yake cewa,

“Nafi son ayi aikin baban sannan komi yai daidai sai tashirya mu tafi”

Kawar dakai nayi inajin wani d’aci azuciyata,inhar taimakon tsakani da Allah ne meyasa dole sai nayi aiki gidansu? Meyasa innamu da yayanmu zasuyi saurin yadda dashi? Duk zafin talaucin da muke ciki bai dace kwatsam su anshi bukatarsa ba, Amman innamu ba zata fahimta ba idonsu ya rufe kan neman kudin aikin baba,

Bayan mun dawo cikin gidan na buga tagumi ina jinsu sunata magana akan gidan da kayan da aka sanya, gaba d’aya basuga wani rashin dacewa anan ba……………”yaya murja ban ganin kina murna”

Cewar zainab dake mik’e cikin kujera kauda kai nayi bance mata komi ba, inajin babu dadi sosai cikin raina basu damu da rabuwa dani ba, burin su dai ya cika na samun kudin aikin baba da kuma cigaban rayuwar da suka samu,

“Na lura hankalinki bai kwanta da wannan abun ba murja ko? Kiyi hkr ki kwantar da hankalin ki inaji araina alkairine zai kaiki gidansu aiki, kudin aikin ki zasuyi mana rana kema kuma zaki samu ci gaba sosai”

Cewar yayanmu har sannan bance komi ba, to mekuwa zance idan nayi magana suka ba akan daidai nake ba.

“Murjanatu”

Innamu ta kirani cikin natsuwa, dagowa nai ahankali ina kallonta sannan nace, “Na’am innamu”

“Kina ganin bamu kyauta maki ba akan hukuncin da muka yanke akanki ko? Kina kallon munso dukiya fiye dake ko?”

Girgiza kai nai inajin kwalla na son zubo mun bata saurareni ba tacigaba da cewa, “lafiyar mahaifinku ta fiye mun komi,kuma koda cewa yai in bashike duka ki zauna gidansu kina masu aikatau zanyi hakan inhar mahaifinku zai warke ya samu lafiya, saboda ida kece kike acikin halin da yake ciki zai iyayin komi don ganin kin tashi, kenan ke bazaki iya wannan domin sa ba? Kina ganin kamar mun zalinceki ko?”

Kuka na sanya mai sanyi inajin haushin kaina akan abunda nake ganin nayi matsayin laifi, baba ya cancanci nayi sadaukarwa dominsa saboda shidin ubane na gari, mai tsayuwa akan hidimar mu da dadi da babu dadi, da lafiya da babu lafiya amman shine ni bazan iya masa wannan sadaukarwar ba?

“Innamu kigafarce ni wallahi zan iya bada rayuwata kaf akan baba, kiyi hakuri bazan sake abunda nayi ba, kawai dai inajin dacin rabuwa daku ne inje inda ban saba dasu ba, wata kila su kyamaceni su ringa hantara ta kamar yadda ake mun acan garinmu, inajin tsoron shiga cikin wani ahalin bayan ku innamu”

Sassauta muryarta tayi jin ina kuka tace, “ki natsu ki kwantar da hankalin ki, ki tsarkake zuciyarki muddin babu wani mummunan kudiri a ranki Allah bazai bari a wulakantaki ba, abunda kawai zance dake shine ki iya talaucinki murja, ki kuma tsaya iya inda Allah ya ajeki, don wannan hidimar da yai mana ya tabbatar mana shidin dan gidan masu hannu da shuni ne, ki kauda kanki akan abunsu nasanki nasan halinki keba mai kwadayi bace, duk cikin ku ba wanda keda kwadayi da son abun duniya, ina gode ma Allah akan hakan don haka ki wanke ranki insha Allahu babu abunda zai faru sai alkairi, kedai ki tsare mutuncin ki aduk halin da kika tsinci kanki”

Nasihar innamu tayi matukar shigata na kuma yi na’am da maganganunta, naji na natsu da tafiyar da zanyi din………………..

Mom muhseen✍????
[7/20, 9:04 PM] Mom Muhseen????: ????JANNAH????

{A TRUE LIFE STORY}

E.W.F

By
Mrs Bb
mom muhseen

wattpad name
Humaira3461

    ????️.......5

Cikin kan kanin lokaci akai aikin baba ranar mun shiga cikin tashin hankali ainun, saboda dai aikin kila wa k’ala ne ai nasara ko akasin hakan, Yallab’ai Asaad bai samu damar zuwa ba saida aka fito da baba, munsha kuka ganin lokacin da akace baba zai farka bai barko d’in ba, duk mun dauka ya mutune sai can bayan wasu awanni masu tsawo ya farka, fadar irin farin cikin da muka shiga bata bakine don kuwa farin ciki ne harda kuka, shima baban kwallace ke bin gefen idonsa badai magana tunda yaji jiki ba kadan ba, yayanmu muka bari tare dashi mu kuma muka fito driver yallab’ai dashi yallab’an suka kaimu gida.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Leave a Reply

Back to top button