JANNAH COMPLETE HAUSA NOVEL

JANNAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Lumshe ido yayi yana jin sanyi a ransa, sai yai kamar baiji ba zai rufe k’ofar da karfi na sake cewa,
“Yallab’ai ASAAD

murmushi yake son yayi amman ya danne ya dawo baya idonsa sun lumshe kamar bacci yakeji ya tsira mu idanun sa wanda nakejin suna addabata tun ranar farko,

“gani Rakiyadad’e JANNAH

ban san sadda murmushi ya kubce a fuskata ba, na sadda kai kurin saboda ni dariya ma yabani, nice ma rankishidad’e din nadan jima ina murmushin ina wasa da yatsuna sannan nace ahankali,

“Aa niba ita bace, ban kai haka ba”

Gyara tsayuwar yayi don so yake yajata da magana duk da yaga itama miskilarce irinsa, baisan meyasa yake son suyi fira ba,

“Inji wa?”

Ban sake kallonsa ba kaina kasa na bashi ansa da cewa, “inji ni kuma inji kowa ma”

“Aa injikin dai, don abakin ki akaji”

Daga haka ban sake magana ba tsawon lokaci ban son na dago in kamasa yana kallona,hakan yana samun jin ba dadi kallon yana yin yawa.

da gaske bazai magana ba sai na daure nace masa,
“Yallab’ai idan ka tafi taya zan ringa ganawa dasu baba? Sannan inajin tsoron kasancewa da mutanen da zaka sadani dasu tun kafin naje d’in, bayan nan har yanzu ban san komi a kanka ba”

Ajiyar zuciya ya sauke yana nan a tsayen yace, “tafiyata ba yana nufin mancewa dake ba, duk abunda zanyi inayinsa ne akan tsari koda bana nan indan lokacin zuwanki wajensu yayi zakije, zan sa akaiki”

“Meyasa kikejin tsoron kasancewa dasu bacin baki sansu ba, baki tab’a haduwa dasu ba?”

“Haka nan nakejin fad’uwar gaba, kamar wani abu zai iya samuna”

Ya lumshe idonsa yace, “Insha Allahu muddin ina raye bazan bari wani abu ya cutar dake ba, saidai idan KADDARA wannan kuma ban isa in hana ta faruwa ba”

Jikina yai sanyi sosai na kasa magana, ya cigaba da cewa “tambayarki ta karshe kuma naga baki damu ki sani ba shiyasa, amman tunda kin buk’ata yanzu zakiji kin shirya ko?”

Na jinjina kai,saida ya dan huta sannan yafata cewa, “Sunana Asaad Abdullahi galadima, ba lallai kinsan babana ba tunda ba nan kuke ba amman duk wanda kace ma Audu galadima da yawa zasu gaya maki waye,babana d’an siyayasa ne shiyasa yai suna sosai As ne na governor maici ayanzu, ma’ana mai ba gwammana shawara, momyna sunanta Hafsatu ita yar niger ce babanta commissioner ne, nine babba agidan mu inada kanne maza biyu mata biyu akwai Hisham shine mai bimun yana da matarsa ma harda d’a, sai Farida itama tayi aure sai usman da Hindatu, karatuna duka nayisu a Spain yanzu haka na kammala PhD dina shekara guda kenan, tun ina karami nake sha’awar kwallon k’afa bayan na gama degree dina na farko akaimun cuku cuku na fara shiga harkokin kwallon, yanzu haka shekarata ta biyar kenan cikin sana’ar kwallon k’afa ina daya daga cikin yan wasan spaim a club din arsenal, duk month inasa albashi mai yawan gaske mun samu d’an hutu ne nazo gida mafarin na had’u daku office din abokina ashir, inajin wannan hutun shine silar had’uwata daku,kinji ko waye ni ba d’an shan jini bane”

Murmushi nayi ina cewa, “Ai zuciyata bata tab’a gaya mun haka ba”

Shima yana murmushin yace, “anya zan yarda”

Ina cigaba da murmushin ban dai ce komi ba,

Mun dade ba mai magana har sannan ana ruwa amman ya rage karfi sosai, kafin naji muryarsa yana cewa,

“Abunda Zan gaya miki shine idan munje gida babu ruwanki da shiga harkar wani, abunda aka baki matsayin aikinki shine zaki maida hankali kiyi, ba ruwanki da duk abunda zaki gani akwai abunda saikinje zaki fahimta, don haka please Jannah ki kula da kanki koda bana nan inajin tsoron wannan Kyan naki, please ki tsare kanki kinji”

Ya fad’a da sanyin murya dagowa nai ina kallonsa shima yana kallona mun tsare juna da ido, kamar an bugan akai nai saurin dauke idona inajin sadda ya sauke ajiyar zuciya cikin sanyi yace,

“Zanje na kwanta dare yayi sosai good night”

Daker na amsa masa da cewa “uhum”

Yaja mun k’ofar ni kuma na silale na kwantar da kaina bisa filo, na rufe idanuna ina ta tunanin maganganun da mukai dashi, da alama cikin gidan nasu akwai rud’ani.

“Ya Rabbil’alamin ka kareni don ikonka, karka ba wani mahaluki damar cutar dani nayi tawassuli dakai da alqur’ani maigirma nayi tawassuli da sunayenka tsarkaka guda casa’in da tara, ka tsareni daga dukkan sharri”

Na fad’a a sarari sannan na cire hijabin najawo bargo nai addua na shafa na kwanta, daker bacci b’arawo yazo ya saceni cike da mafarkai………….

Mom muhseen✍????
[7/27, 4:50 PM] Mom Muhseen????: ????JANNAH????

{A TRUE LIFE STORY}

E.W.F

By
Mrs Bb
mom muhseen

wattpad name
Humaira3461

    ????️.......9

Saboda cewar da yai da wuri zamu fita yasa tunda nai sallar asuba sai ban koma ba, naita tazbihi ina gyangyad’i har sadda takwas da rabi tayi sannan na tashi ja shiga wanka.

Ban dad’e ba na fito ina duba kayan doguwar rigace irin wadanda ake sawa tare veil din nan irin ta yan gayu amman ba kwalliya jikinta ko kadan, kalar blue black ce mai dogon hannu iyakar wuyan hannun, tun asuba daman na wanke pant din dana saka jiya na shanya sa inda zai bushe,sadda na dauko sa yabushe don fanka na kunna masa duk da sanyin da aka tashi dashi saboda ruwan jiya,rigar tayi mun kyau sosai ni kaina na shaida hakan, nagama kintsawa sannan na fito zuwa falon lokacin tara daidai tayi, kamshi ta ko ina ya baibaye gidan na turaren wuta mamaki ya kamani ba dai shike da wannan aikin ba, ina cikin wannan tunanin naji motsi daga hanyar da zata kai kai kitchen waigawa nai naga wannan kukun nashi yana shirya dining, ga boner a jone jikin socket risinawa yai yana gaidani,

“Good morning madam”

Sai na jinjina masa kai kurin na samu waje na zauna ina kallon tv dake kunne, tunanin su innamu kurin nake ko yasu? Sunyi kewata kamar yadda nake cikin tasu kuwa? Bazan iya ganewa ba ahaka banda waya balle na kirasu wanda ya daukoni har yau bai had’ani dasu ba, wannan kamshin dake shigar mun har zuciya naji ya bakunci hancina nai saurin dago kaina ina dubar hanyar danasan tanan zai b’ullo, saman labbana nake furta “Tabarakallah masha Allah”

Don kuwa yai kyau ainun suit ne dai yasaka amman navy blue rigar cikin fara sai yar falmaran din da coat din da wandonsa sune navy blue din, kafafunsa sanye cikin bakaken sawu ciki hannunsa daure da dankareriyar agogo wanda daka kalla kasan akwai tsada, kunsan yan ball suna son aje suma shid’inma gata nan ya tara gwanin kyau datasha gyara, waya yake yana isowa inda nake zaune ai sai dan danan naji xuciyar zata fito waje, ban yaudari kaina ba duk sadda na gansa gefena gudun zuciyata karuwa yake, bansan dalili ba nasan dai yana mun kwarjini ainun, yana da cikar haiba sosai idanun sa kamar wani mai mai ne aciki idan muka had’a ido jinake idona yana tara ruwa,wani irin kwayar idone Allah yai masa mai daukar hankali, bansan ni shashasha bace saida naji wayarsa bisa kunnena yana cewa, “kibar kallona kiyi magana yayankune”

Wata yar ajiyar zuciya na sauke ina sadda kaina k’asa wayar na hannunsa yasamun ga kunne naji yayanmu na magana, cikin sanyi da doki nace “yayanmu kaine? Ashe zaku tuna dani”

Dariya yayi yana cewa, “kullin yallab’ai yana gaya mana kina lafiya shiyasa bamu tada hankalin mu ba”

Mamakin sa nake don yana gaya masu ina lafiya hakan na nufin sun yarda koda ace ba hannu na gari nake ba, meyasa kudi sun rufe ma yan gidanmu idanu har haka?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Leave a Reply

Back to top button