JANNAH COMPLETE HAUSA NOVEL

JANNAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Wata unguwa muka shiga har kofar wani babban shago wanda akai zane a kofar shagon ana make-up, ana gyaran kai ana wankin k’afa da gyaran jiki, mamaki nake jin motar ta tsaya anan me mukazo yi anan to???

Waya naji yana yi yana cewa, “muna waje fa, karkice baki nan bacin munxo”

Sauke wayar yayi yana kallona kamar yadda na keta kallonsa, saboda ina son karin bayani ganin munata kallon juna baice komi ba dole na kauda kaina wajen taga,can naji yace dani.

“Jannah”

Nikam na kasa sabawa sa wannan sunan wallahi,amman ya zanyi dole na amsa ba tare dana dubesa ba,

“Na’am yallab’ai”

“Za’ai miki saloon anan yanzu da wasu abubuwan, bana son naje dake gida aimiki abunda zai b’ata miki rai, shiyasa na jinkirta tafiyar zuwa gobe idan aka gama zan dawo na daukeki”

Rausayar dakai nayi inajin zuciyata na kerma,meyasa zai anyi mun duk wannan sannan zai kaini? Yar aiki fa zanje dole sai anmun wannan, jin nayi shiru ya sashi cewa.

“Jannah please”

Saurin kallonsa nai idona na son tara ruwa, ni duk ya sakani acikin ko kwanto yana samun zarginsa, yana samun rashin yadda akanshi, cikin rawar murya nace “yallab’ai aikatau fa zanje, meyasa sai anmun wani gyara???”

Lumshe idonsa yayi yana bud’ewa ya shafa kanshi sannan yace, “ba zaki gane ba, amman idan munje zaki fahimta kiyi mun alfarmar wannan wallahi babu cuta araina”

Na sadda kaina k’asa jin yadda yake mun magana cikin tausasawa da marairaicewa, ahankali nace masa “shikenan na amunce”

Fitowa mukai muka shiga shagon babbane sosai don ankillace ko ina da labule, ciki da falo ne ga kayan aikin su nan burjik,wata matashiya ce ta fito daga ciki bakinta a washe take cewa,

“Yah Assad a shagona wace irin sa’a ce yau na taka”

D’an murmushi yai mata kurin yana zama cikin kujerun dake wajen, kallona take tun daga sama zuwa k’asa can naji tace, “Yah Asaad kace mun kanwarka zaka kawo mun?”

Wani duba yai mata kafin yace, “sai kika ga yayata ko kuma momy halan?”

Ya fad’a cikin gatse yak’e tayi tana cewa, “Aa Allah ya baka hakuri ba haka nake nufi ba, to daga ina ka samo mai kyau haka?”

“Jamila kiyi abunda ke gabanki inkuma ba zakiyi zamu kara gaba”

Cikin sauri tace, “Aa kayi hakuri don Allah yanzu kuwa zan fara, bismilla kanwata zauna anan”

Tana nuna mun gaban wani madubi babba da kujera yar doguwa inda customer ke zama ai masa gyaran kan,

“Ina zuwa kanwata, amman ki cire hijabin zaifi”

Gabana ya fad’i a sace na kallesa bama tani yake ba wayarsa yake dannawa, sai na zare wuyan abayar kurin saboda bazan iya cirewa gabansa ba gaskiya, fitowa tayi da wasu kayan aikin ta aje tana cewa,

“Yah Assad relaxer za’a saka mata ko wanke kan kurin za’ai”

Ta fad’a tana zare mun kallabina kitsona manya guda hud’u da innamu taimin wajen wata guda kenan suka bayyana, jinai yace mata “karki b’ata mata gashi please, a wanke ai mata kitso mai kyau”

Tana murmushi tace, “angama yah Asaad”

Saiya mik’e yana cewa “zan dawo karfe shidda”

“OK,Amman sauran abubuwan da kace fa?”

Bai jiyoba yace “duka ayi jamila”

Sannan ya fita, kunce kan ta farayi tana jana da fira tanada kirki matar taita yabon gashina tace, “amman ke fulani neko?”

Ina murmushi nace, “ruwa biyune mu, shuwa da fulani”

Cike da mamaki tace, “hana no wonder, kike da kyau haka ga gashinki mai laushi gashi baki sai tsawo,ki ringa cewa tubarkalla masha Allah duk sadda wani yai magana akan kyanki kinjiko”

Na amsa mata da to, haka mukai ta fira sama sama tana ban labarin cewar yallab’ai Asaad abokin yayanta ne, shine ma ya taimaka mata ta bud’e wannan shagon, a yadda na fahimta so take taji meyake tsakanina dashi, sai na nuna mata ban gane inda ta dosa ba.

Ban tab’a ganin kyan gashina irin na yau ba, tayi matukar kokari wajen gyara mun kaina kitso ta rairaya mun masu kyan gaske, kasancewar tsawon gashin yasa muka dau lokaci, muna cikin kitson daya daga cikin yaranta take wanke mun k’afata, naga abun mamaki irin dattin da ya ringa fita a kafar tawa, aka sa wani abu ake murzar tafin kafar wani daud’a na fita kan kace me kafata ta zama sumul sumul, an gyara mun farata na sunyi gwanin sha’awa har wani mai aka shafa masu daya kara masu shalk’i, haka ma yatsun hannuna sadda aka gama kitson da gyaran kafafun da hannun, tace na bita aciki na tashi inata kallon kaina a madubi kamar bani ba, mamaki duk ya cikani kowa na wajen saidai yace “kai masha Allah, kin k’ara kyau yan mata”

Murmushi nake masu araina ince tubarkallah,acikin akwai bayi tare muka shiga naga ta zuzzuba wasu abubuwa cikin ruwan dake cikin wani bahon wanka, sannan tace na shiga nayi wankan in saka soso na dirje jikina sosai,saida nai wanka sau uku sannan taban tawul na daura na fito,da kanta ta taimaka mun wajen shafa, mayukan kansu kamshi suke na daban na gama shafa man sannan ta dan gyara mun fuskata kwalli ne da yar powder da man baki,dai dai nan wadda tai min gyaran farce ta shigo tace, “Anty yace gashi”

Ledace take mik’a mata ta ansa tana dubawa tace, “ok kayan da zata canza ne”

Gaba d’aya na shiga wani yanayi, har kayan nau ma bazanje dasu ba? To wai wannan wane irin gidane zanje kamar gidan Annabi, nida zanje yar aiki ina ruwana da wannan gyaran?

“Yah Assad Bai son araina masa kanwa shiyasa yake duk bakin kokarinsa”

Kallonta nayi kamar ince wani abu amman sai na kasa tace “saidai kuma under ways d’in kamar zasuyi maki kad’an fa”

Zaro idona nayi kamar zasu fado nace, “harda su?”

Dariya ta kamayi mani tana cewa, “to bakiga naki sunyi datti ba, ba zai yuwu ki maida ba kuma inkikaje can komi zaki samai na yanzu kawai aka nema”

Kamar zan kuka nace, “Anty meyasa zai siyo su don Allah”

Dariya take tayi tace, “saboda kina buk’atarsu ai”

Bakin ciki kamar yai mun me, na rasa meyake nufi dayin duk wannan abubuwan, idona har kwalla ya tara nai kokarin maidata,haka na sanya kayan atakure saboda bra din ta matsene ba laifi, doguwar rigace ready-made ta atamfa anyi mata sassaukan dinki sai kamshi takeyi, harda turare ya sanyo da takalma yan fashion masu kyau, dana gama shiryawa ni kaina sadda na ganni gaban madubi saida na girgiza saboda dai zahir ba zakace murjar inna nace, wannan itace JANNAH Antyn tace mun,

“Ga no Dina duk sadda kike bukatar taimakona ko wata shawara ki nemeni, naji araina kin kwanta mun sosai kuma har zuciyata bazan so duk abunda zai illata rayuwarki ba, kina da kyau wanda duk wanda yai miki kallo guda saiyaji kin dauki hankalinsa nesa ba kusa ba, don haka ki rik’e addua wannan kyan da kike dashi zai iya jefaki acikin matsala, ina maki fatan alkairi in zaki shiga gidan kiyi addua kinji ko”

Kwallane suka zubo mani sharrr nace, “Anty kinsan wani abune game da inda zani? Ki fad’a mun idaan kin sani don Allah, maganarki tabani tsoro daman kuna acikin tsoron nake”

Murrmushin kwantar mun da hankali tayi tace, “karki tashi hankalinki Jannah, ba abunda na sani akan inda zaki nadai baki shawara ce matsayin yayarki”

Ta share min hawayen sannan ta kamo hannuna muka fito yana waje jikin mota yana ta sana’ar tashi ta danna waya, kasancewar darene sai hasken fitilun wajen suka haskesa sosai,ya canza kaya zuwa wasu kananu sunyi masa kyau sosai fitowarmu yasa shi kallonmu, tunda ya kafeni da ido har muka isa inda yake bai daina kallona ba, kamar ma baiga Anty jamilar awajen ba saida tayi magana………….”Yah Asaad baka ganni ba halan”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Leave a Reply

Back to top button