JANNAH COMPLETE HAUSA NOVEL

JANNAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Atakaice dai nasha bakar wuya nice har wajen karfe uku da rabi a kitchen, ga yunwa ga gajiya ko sallar azahar banyi ba gashi duk bayan mintyna zata shigo ta zageni akan wai ban gamaa ba, don ma akwai blander sai nayi markaden agida.

Ina cikin shirya mata abincin naji kamshin nan da idan najisa nakejin natsuwa da sassauci acikin raina, lumshe idona nayi inajin wasu hawaye sabbi suna zubo mani, bazance ga dalili ba nai saurin sharewa ina juyawa muka had’a ido dashi,
Yana jingine jikin frig yai crossing legs dinsa ya saka hannunsa daya cikin aljihun jeans din dake jikinsa, kansa yasha gyara irin askin yan kwallon nan kuma yai masa kyau sosai,na sauke idona daga kallon da muke ma juna nace,

“Sannu da dawowa yallab’ai”

Cikin cool voice dinsa yace, “sannu da aiki Jann”

Yau kuma wani sabon suna na samu kenan, na fada araina nace “yawwa nagode”

“Mekike yi haka? Abinci kala nawa yau kukai kamar za’ai baki”

“Bakuwar da tazo akai ma wannan tace ba zataci wancen ba………..wai Fareeda kike nufi?”

Yadda yai maganar cikin fusata saida naji tsoro cikin sauri nace, “Aa yallab’ai karkai magana nice nace zan mata”

Hararata yayi ya juya yana cewa ki saman a can falon,
“Innalillahi wa inna ilahir raju’un, yallab’ai zai sake janyo mun fitina na shiga ukuna”

Daukar kayan abincin nayi na dora ruwa da lemun da tace mun, na nufi can babban falon hankalina atashe, khalid,usman,hindu,Anty Aneesa da Anty fareedar sai momy da yallab’ai Asaad, ina rawar dari na risina na aje bisa table din dake gabanta nace, “gashi Angama”

Taja tsaki “wawuya kawai bar nan wajen………….ya zama last warning da zaki zageta! Kinci arziki an gama abincin wallahi da ba zatayi ba, kin son wannan din ki koma gidan mijinki mana kici, momy daga rana irin ta yau kar wanda ya sake had’a masu aiki mai yawa haka, suma fa mutane ne sun buk’atar hutu…………idan hutu suke buk’ata meya kawosu aikatau, aida sai su zauna gidajen uban ninsu su huta dakyau nan kau dole suyi aiki matsayin bayi suke”

Khalid yai maganar cikin gadara da isa cikin kufula Asaad yace, “nidai na gaya maku idan hakan ya sab’a kowa bazaiji dad’i ba”

“Wai Yaya Assad aikin nata dole nan gidan? Ta tarkata ta tafi mana asamu wata, tunda baka son tasha wuy……….fareeda!!!”

Momy ta daka mata tsawar da duk saida kowa yaji ajikinsa jikina rawa yake kamar mazari saboda gigita, cikin fada sosai take cewa, “Asaad shiya kawo Jannah nan gidan tare da yardata, yana da ikon da zai tsawatar akan abunda yaga ansata dayafi karfinta, kowa yana jina anan kar wanda ya sake sanyata aikin da ya wuce wanda takeyi, na fada maku da babbar murya muddin mutum yana son zaman lafiya dani, ke kuma”

Ta watso mun idanunta wanda najisu har cikin yan hanjina ta cigaba da magana idonta akaina tana zarosu, “duk wanda ya saki abu muddin baya cikin aikin ki kuma kikayi nidake ne acikin gidan nan,”

Bakina na rawa nace, “zan kiyaye momy ki gafarceni”

Ta kauda kanta daga gareni harna tafi naji muryarsa data shak’e yace, “zoki dauki wannan”

Na dawo na dauki ledar babbace cike da fruits, “ki raba uku ki saka kashi daya frig ki kawo masu kashi guda nan, gudan ki yi min fruit salad ki kawo mun”

Nace to ina mazari nabar falon, duk yadda yace nayi haka nayi na kawo masu nasu, na koma na had’a masa fruitsalad din na zuba kankara aciki don nasan yanzu zaisha, ta taga na hango fitarsa da mota, saina sanya frig karya huce na wuce naje nai wanka nai sallar azahar da la’asar saboda itace ake kira yanzu.


“Yaya kanaganin abunda momy tayi ko? Wai momy tana cikin hankalinta kuwa? Nifa na gaji da wannan abun wallahi”

Khalid daya kafe waje guda da kallo baice mata komi ba, suna cikin dakinsa lokacin kallo daya zakai masa kasan cewar akwai wutar dake ci cikin ransa………..yaya kayi shiru bakace komi ba”

“Fareeda ki bani lokaci dole hakarmu zata cimma ruwa, nayi alk’awarin muddin ni d’an babana ne inhar na cika dan halak saina wulak’anta rayuwar Asaad, ke gabar taki yar mitsilace akansa kiyayyar da kike masa batakai ta kawo ba, inda zaki laluba raina kiga abu da ke ciki akansa,sai kin kasa bacci don haka kar hankalinki ya tashi kina dani koda sanin momy ko babu saninta saina saka Abba yai masa korar kare cikin gidan da yake tak’ama dashi, yake tutiyar gidan ubansa ne yana mana kallon mu y’ancin arziki”

Ajiyar zuciya tayi tace, “naji dadi, har hankalina ya kwanta zan saurareka amman komi ake ciki karka saka wannan jakar Aneesa, shegiya haukar son da take masa bazai barta ta goya mana baya ba”

Jinjina mata kai kurin yayi sannan ta fita daga dakin.

muje zuwa yanzu aka fara bamu saka ko yatsa ba

Mom muhseen✍????
[8/3, 1:13 PM] Mom Muhseen????: ????JANNAH????

{A TRUE LIFE STORY}

E.W.F

By
Mrs Bb
mom muhseen

wattpad name
Humaira3461

FAUZARH ORGANIC SKINCARE
PRESENT

               *5️⃣ DAY'S SKINCARE ONLINE TRAINING*

????ABUBUWAN DA ZAN KOYAR????

da farko zanyi bayani akan ƙurajen fuska da abun da ke kawosu, da hanyar da za a bi wajen magance su

WHITENING BLACK SOAP
LIGHTENING BLACK SOAP
NATURAL BLACK SOAP
FACE AND BODY SOAP
BODY CREAM
SABULUN GYARAN AMARYA

Wannan training ɗin tamkar gara6asa ne???? da naira ɗari ukun ki kacal za ki koyi sana’a.????
Zamu fara training din 5 ga wannan watan ne insha Allah

DUK GARIN DA KI KE ZAN SANAR DAKE INDA ZA KI SAMU KAYAN HADIN

Domin neman karin bayani a tuntu????????http://wa.me/+2347065012071

    ????️.......14

Tilawar karin da akai mana na qur’ani nakeyi amman zuciyata duk ta kasu kashi-kashi, yar mitsilar wayar da yallab’ai ya ban tun randa nazo naji tana ta burrrr burrrr karkashin filona da nake sata, saurin tashi nayi na daukota bani da mai kirana sai shi kuma shima tunda ya ban ita yaune ya kirani.

“Assalamu alaikum”

Nai masa sallama da siririyar muryata,

“Yunwa zata lahantani Jann, ki kawo mun abincina, da abunda nace ki had’a mani”

“To yallab’ai gani nan”

Na aje wayar da hanzari na rufe qur’anin hijabin danai salla na saka da yake ba babba bace iya guiwa take, na had’a masa abincin sa da komi a cikin wani kyakkyawan dogon tire,bakin k’ofa mukaci karo da hindu ta dalla mun harara tanajan tsaki, uffan bance mata ba nai kamar banji ba na wuce wata kurin.

Allah yasoni falon babu kowa nai zuruf na shige bangaren nashi na kwankwasa kofar falon, kamar yana bakin kofar naji ya bud’e,usman ne mukai four eyes dashi ya sakar mun murmushi, wanda tunda nazo bamu ma tab’a had’a ido dashi ba.

“Shigo mana”

Ya tsinke man mamakina da na shiga, ahankali na rab’ashi na shigo falon yana kwance cikin doguwar kujera kamar marar lafiya, na aje tiren k’asa sannan na durk’usa ina gaidasa.

“Yallab’ai ina wuni? Ga abinci”

Bude kyawawan idanunsa yai akaina sun lumshe sosai sun rage girma, kasa dauke idona nai daga kallonsa yace calmly,

“Toki zuba mun pls”

Cikin sauri na zuba masa tuwon shinkafar don cikin kwanakin nan na lura yana son sa, miyar ina bud’eta tafara kamshi na zuba masa komi sannan nace,

“Na zuba yallab’ai”

Usman yana falon wayarsa kurin yake faman dannawa, saukowa yai k’asa kusada inda nake durk’ushe, duk yai wani kala dashi kamar na tambayesa meke damunsa amman sai nai tsit,
Tuwansa yafara ci cikin natsuwa lokaci zuwa lokaci muna had’a ido dashi, saidai in sunkuyar dakai kasa kawai kulli biyu yaci anan na tabbatar da yunwa yakeji sosai, ruwa ya dauka yasha sannan ya dauki bowl din fruit salad din yana sha ahankali, sannan ya dubeni cikin sassanyen kallo………”zanyi missing abincin ki”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Leave a Reply

Back to top button