JANNAH COMPLETE HAUSA NOVEL

JANNAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Kukan nake sosai saboda abun yazo mun kamar daga sama, wai daman haka soyayyar nan take? Kuncin ta yafi dad’inta yawa, duk yadda baya cikin natsuwarsa bai hana shi lallashina ba, yana duba agogo yace “dare yayi sosai jann ya kamata kishiga ki kwanta, zuwa safe komi kenan zan sanar dake plz kimun alkawarin dakinje bacci zakiyi, karki saka dogon tunani aranki kinji”

Kaina nake d’agawa da kanshi ya ciro hanky yana goge mun fuskata jinake kamar na kwanta kirjinsa nai baccin anan, amman hakan baxai yuwu ba, rik’o hannuna yai yana sakar mun kyakkyawan kiss da najisa har cikin cikina, na lumshe idona bance komi ba, kamar bazai barni na tafi ba sai narkewa yake ni kuma hakan yake sani jin wani iri, yace “ba zakice mun komi ba zaki tafi”

B’oye fuskata nayi ina murmushi yace, “plz jann kice kina sona inji ko a rad’a ne kimin”

Makale kafad’a na nayi zan bud’e infita yai saurin rik’eni, “saikin gaya mun sannan zaki tafi”

Kamar zan kuka nace, “to ba na fad’a ba”

“Wannan cikin magana na ne, plssss don Allah fa”

Gaba d’aya jikina ya saki wata muguwar kasala ke bin jikina, yana yin sai wanda ke cikin giyar kauna zai gane,

Ina ta mimi da baki nace, “to zan fad’a ka matsa daga nan”

Ai kamar zigashi nayi saiya sake matsowa ya had’e gaf din dake tsananin mu, runtse idona nayi saboda hucin numfashinsa dake dukan fuskata, cikin wata lalatacciyar murya yace “oya said”

Numfashi nake jaa kamar mai asthma daker na lalubo abun fad’a din,

“I lov…..love…….I love u Yah Asaad…………saukar tausasan lips d’insa naji akan nawa, wani wahalallan numfashi na sauke jikina har rawa yake, wani namiji bai tab’a koda rik”e hannuna ba sai ta dalilin zazzafar kauna, wani silent kiss ne ya ringa mun saida yaji kamar numfashina zai dauke ya kyaleni, dukan sa nayi a kirjinsa na fice daga motar.

Wata mik’a yayi yana sakin wani kyakkyawan murmushi, har baisan ya furta “wow it’s very sweet”

Ya dad’e sosai sannan ya fito daga motar ya kulle yazare key din yabi ta hanyar bangaren Abba yashige cikin gidan.

Wannan daren k’addarata tasoma

       *********

Bana jin motsin kowa alamun dai kowa ya kwanta, dakina bud’e na iske naita mamaki daga baya kuma nace, “sadda na fita bana hayyacina ko kadan, taya zan iya gane na kulle ko ban kulle ba”

Hijab din na cire inasauke ajiyar zuciya, lips dina na shafa ina lumshe idona, abunda ya faru nidashi kawai yake dawo mun murmushi kwance akan fuskata,yunwa naji kamar inaji don agida ban tsaya naci abincin sosai ba, fita nayi na wuce kitchen d’in indomi na d’ora saboda ban iske abinci ba ancinye, kadan kadan na shafi bakina ina jinjina cewar lallai yallab’ai ogane, ya iya nuna soyayya inbakai wasa ba saika narke inkana tare dashi, fitsari naji ya matseni gashi bata idasa tsanewa ba rage wutar nai na fiddo ruwa don ya huce bana shan mai sanyi sosai, na wuce don nayo fitsarin naga on din ya dauke daman bana wuce kwana biyu uku nake gamawa, kuma bana yarda in dauki kwanaki banyi wanka ba, randa naga yadauke nakeyin kayana ban bar toilet dinba saida nayi wankan tsarkina,.

Fita nai don na kwaso indomin sai naga kamar wulgin wani abu,dan danan gabana ya yanke ya fad’i aguje na isa kitchen d’in na juye na kashe gas d’in, na rugo d’aki na datse k’ofata abun mamaki abun kofar dake rufeta ya lalace bata rufuwa, gabana naji ya sake yankewa ya fad’i kallon k’ofar nake kamar zangano wani abun,banga komi ba saida na turata na jawo bed side drawer na tokare da ita, na zauna kasan kafet ina ajiyar zuciya amman hankalina bai kwanta ba ko kadan, cin indomin na fara inata sake saken to meya kawo lalacewar kofata? Yanzu na tabbatar dazan fita kuwa na rufe akwai dai yadda akai, na cinye idomin na sha ruwana na tashi donyin shafa’i da wutri daker na gama saboda wani mayen bacci da nakeji, idona na rufewa haka nai addua na kwanta kamar matatta.

        ***********

Karfe takwas na safe kowa ya hallara dining ranar kamar an hura usur kowa yana nan har da Abba, Yusra ce take serving din kowa daidai Asaad ya fito cikin shirin sa na suit blue sunyi masifar yi masa kyau, kujera yaja ya zauna yana gaida Abba saida suka gama gaisawar sannan ya gaida momy, wani killer smile ta Sakar mashi tana amsawa a gadarance, kallon yusra yayi sannan ya juya wajen Hindu yace cikin ya mutsa fuska.

“Ina jannah?”

Gaba d’aya kamar ya tuna masu da wani abu kowa ya aje spoon d’insa, momy tace “nidai yau banga taje gyaran dakina ba, tunanina ko tana kitchen aiki ya rik’eta”

Abba ya amshe da cewa, “Aahh, ke Yusra ina Jannah ne?”

Yamutsa fuska tayi tace, “tunda nazo banganta ba Abba, nida baba uwani ma muka had’a abun kari…………a zabure Asaad ya mik’e sai kuma ya dakata dan danan hankalinsa yai kololuwar tashi,yana rawar murya yace “Hindu maza jeki duba dakinta kigani”
Ai bai idasa maganar ba ta ruga da gudu hanyar dakin jannah, ita kanta hankalinta ya tashi abunda bai tab’a faruwa ba kenan tun zuwanta, itace mutum ta farko dake rigan kowa fitowa bayan asuba, wannan shirun ta yau na nufin babu lafiya.

Kofar tafara kwan kwasawa taita bugawa tana kiran sunanta amman babu alamun za’a ansa mata,jikin hindu har rawa yake take buga k’ofar taga ba datse take ba amman kuma ta kasa bud’ewa, koma wa tayi wajensu jikinta na rawa tace, “Yah Asaad kofar bud’e take amman kamar daga ciki an saka abu an datse dashi,nakasa bud’ewa kuma inata bugawa ina kiran sunanta banji alamun ko motsi b…………da mugun speed Asaad yai hanyar dakin, ai suduka ba wanda ya tsaya suka rufa masa baya har Abban, usman jikinsa karkawa yake kamar an saka shi cikin ruwan kankara,shi kan shi yasan babu lafiya wannan shirun nata, momy kamar gaske yadda take rawar jiki tana salati, da duka karfinsa ya sanya ya tura k’ofar ya shiga jikinsa yan wata irin kerma, binsa sukai har cikin dakin me zasu gani……….

Kwanta take tana kallon sama kanga babu dankwali gashinnan ya watse kamar mahaukaciya, bargo ne ya rufe ta daga kafafuhar wuyanta fuskarta tayi jajawur kofar hancinta guda jini ya bushe jiki, cikin mutuwar jiki momy ta isa bakin gadon tana yaye bargon……………..da mugun karfi sukaji karar Asad yana cewa “No!!!……………….saida kowa ya dad’e kunnensa saboda duka gidan saida ya d’auki sauti, babu komi jikin Jannah tsirara take ga jini nan har ya bushe jikinta har kan fafunta, babu alamar numfashi tattare da ita, usman zubewa yai k’asa dafe da kanshi, cikin sauri momy ta maida bargon jikinta, salati kurin take tana karawa Hindu kuka take kamar ranta zai fita,a haukace babaah uwani ta fad’o dakin ganin abunda ke faruwa yasa tafasa kara tana cewa, “lahaula wala quwwata illabillah,” ba abunda ke fita daga bakin Abb face,
“Innalillahi wa inna ilahir raju’un”

SAURA PAGE GUDA MU GAMA BOOK ONE.

WANNAN SHINE TUSHEN K’ADDARATA, DAGA NAN KOMI YA LALACE ????????????????

Mom muhseen✍????
[8/24, 6:41 PM] Mom Muhseen????: ????JANNAH????

{A TRUE LIFE STORY}

E.W.F

By
Mrs Bb
mom muhseen

wattpad name
Humaira3461

END OF BOOK ONE

    ????️.......25

Gaba d’ayan su suna zaune reception acikin wani private hospital da aka kawo Jannah, Asaad ne d’urk’ushe k’asa ya had’e kai da guiwa ba abunda ke tsiyaya a idonsa sai ruwan hawaye, zuciyarsa kuwa karma atona don hayak’i take saboda wutar dake ci acikinta, usman yana daga can baya shima ya had’e kanshi da guiwar Hindu har yanzu kuka take saboda ta girgiza da abunda akaima Jannah, kadan kadan tace “Allah ka tona asirin ko waye, Allah karka barshi ka saka ma wannan baiwar Allah”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Leave a Reply

Back to top button