JANNAH COMPLETE HAUSA NOVEL

JANNAH COMPLETE HAUSA NOVEL

“Barka da dawowa Jannah yaudai zanci tuwonki kenan”

Ina murmushi nace, “insha Allahu Abba, momy ina wuni barka da gida”

Gani nai kurin ta janyoni jikinta cikin kissa da makirci tace, “barka kadai Jannah kowa yai kewarki sosai, gidan babu dad’i bama kamar wajen girki munfi jin babu dadi”

Yak’e kurin nake nace, “Momy na dawo kenan komi zai daidai insha Allahu, Yah khalid ina wuni”

Tunda na shigo nakejin idonsa akaina mugun tsoronsa nakeji matuk’a, kamar babu abunda ya faru ya saki fuskarsa yana mun murmushi yace, “Jannah yar gudun hijira kin dawo ko, Allah yasa ba zaki sake gudunmu ba”

Na Sadda kaina daga kallon da Yallab’ai ke jifata dashi nace, “ba zan sake guduwa ba”

Na gaida Anty Anee wadda kamar ta cinye yallab’ai da kallo, fareeda ce kurin bata nan saida aka natsuwa sannan Abba ya fara magana cikin natsuwa da jawo hankali,

“Dukkan abunda ya faru naji labarinsa, bana son tado da abunda ya wuce saboda gudun b’acin rai, ina fatan komi ya wuce daga yanzu, Jannah dai aiki tazo yi don Allah ku barta tayi aikinta sannan bance ku maidata baiwa ba saboda itama mutum ce kamar kowa, sannan daga yau albashin ta ya dawo wuyana bana son na sakejin wata rigima ta sake bullowa don Allah, ke uwace Hafsat ki zama mai saka ido akan komi kiyima kowa adalci akan aabunda kikaga yayi wanda ya dace ki dauki mataki, ku kuma nan dukan ku y’ay’an mune dole ku kasance masu yimana biyayya kuma masu bin dukkan umurnin mu,don haka bana son sakejin wani abu ya taso kai usman kaba momyn ku hakuri akan abunda kayi mata yanzu nan”

Yah usy kamar zai bindiga yace, “kiyi hkri bazan sake ba”

Ta na murmushi ta amsa mashi da cewa, “haba my son karka damu ai na huce na yafe maka”

Abban yace, “magana ta k’are Jannah kici gaba dayin ayyukan da kika faro, daga yau ba wanda zai sake takura miki kinji ko, anshi nan wannan katina ne inhar kina da matsaka ki sameni ki gaya mun karkiji komi”

Na amsa cikin girmamawa ina masa godiya yace, “kuna iya tashi kutai na sallameku”

Zuruf na dauki jakata nai cikin gida bangarenmu, ina aje jikkar naji karar wayata yallab’ai nagani ina dauka muryarsa kamar dazun yace,

“Ki sameni bangarena yanzun”

Ya kashe batare da yajira mai zance masa ba.

Mom muhseen✍????
[8/19, 2:31 PM] Mom Muhseen????: ????JANNAH????

{A TRUE LIFE STORY}

E.W.F

By
Mrs Bb
mom muhseen

wattpad name
Humaira3461

    ????️.......21

Kafafuna naji sun mun nauyi na kasa daukar wannan sabon abun da yadawo dashi, menai masa haka da zafi? yadda nake d’okin dawowar sa kullin ban zaci inya dawo za abunda zai zo dashi kenan ba.

Ajiyar rai nayi sannan na kalli fuskata a mudubi bansan me bake kallo akai ba, abu guda na sani shine inajin wani nauyi a kirjina duk akansa tsawon lokacin da yatafi ban huta ba haka zuciyata bata huta da tunanin sa ba, shine ya dawo zai zo mun da haka?……….jin wayar na sake daukar ruri yasa nai firgigi daga dogon tunanin da nake, ashe fa cewa yai naje shaf na mance cikin sauri na dauki kiran bakina na rawa nace, “kayi hak……….ko ni zanzo in sameki?”

Na lumshe idona inajin kamar nai kukaa cikin karyayyar murya nace, “don Allah kayi hakuri yallab’ai gani nan”

Bai kulani ba ya kashe wayar sa, kwalla naji sun cika mun ido duk yadda bake karfafa zuciyata akan kar nayi basuyi shawara dani ba sadda suke layi akan fuskata, gogewa nake ina fita daga dakin amman hakan bai hana wasu sake zubowar ba, har naje bakin k’ofar dakin suna silalowa daker nai karfin halin rik’esu na share fuskar sannan na tura zan shiga naji muryar sa cikin tsananin b’acin rai yana cewa, “saboda ban yarda da kowa ba sai kai yasa na damk’a amanarta hannunka, meyasa zakai mun wasa da hankali usman?”

Cikin sanyin murya yace, “kayi hkr Bros bazan sake ba”

Sallama nayi na shiga saboda rashin shigar kuma zai sake janyo mun wata damuwar,

Da yah usy muka fara had’a ido yai saurin sadda kanshi k’asa, yallab’ai yana cikin kujera ya dage kanshi sama ya rufe idonsa na sakeyin sallamar, yah usy ya amsa mun na samu gefe guda daga k’asa na durk’usa na soke kaina k’asa kurin ina tsifar yatsuna.

Zuwa can daya mula ya mulmule yace, “kana iya tafiya,”

Tashi yai cikin b’acin rai ya fita daga falon yabarni dashi, shakar kamshin turarensa kad’ai da nake ni kadai nasan illar da yake mun acikin raina ganin kamar bai san nazo ba yasa cikin rawar murya da nasha kuka nace,

“Gani yallab’………na ganki Jannah! na ganki!! Saida kika gama raina mun wayau sannan zakizo ko? Yar tafiyar danai har yasa kin waye haka ban sani ba, usman ya bud’e miki ido ko?”

Yadda yake zuba fad’a da masifa yai masifar tayar mun da hankali, dan danan na rikice ina shashshekar numfashi girgiza kai kurin nake, ina jan yatsuna idona kuwa tuni ya cika tab da ruwa bakina har rawa yake nace,

“Yallab’ai ka…..kayi hak…..hakuri wallahi ba haka ba….bane don girman Allah………..will u keep quiet?”

Runtse idona nayi yayin da ruwan hawayen dake ciki suka samu damar zuba, na sauke kaina kasa ina shashsheka ina jan numfashi jikina sai rawa yake, tunda na had’u dashi bai tab’a daga mun murya ba sai yau,sannan kuma gani mai tsananin tsoron shouting bana son fad’a gigicewa nake,

Shiru yayi yana jin kirjinsa yana wani irin zafi, a mugun tun zure yake da ita duk da yasan ba itace ummul aba’isin faruwar komi ba, amman ta bada goyon bayanta duk dokinsa da zalk’insa na son dawowa don ya ganta ashe abunda zai tadda kenan, ya dauka tsawon wannan lokacin zatai mugun kewarsa zai ga wani canji sosai tattare da ita,amman shine zai tadda kusancin ta da kanensa har yafi wanda take dashi, babu abunda yake tun zirashi irin pics d’in da yagani hauka ne kawai bai ba, wani irin zafi yakeji aransa, shashshekar kukanta dake shigar masa zuciya yakejin wani iri tsikar jikinsa ke wani irin tashi, had’iyar abu yai ga mak’oshin sa yana sassauta zafin daya d’auka muryasa ta shak’e yace,

“Kimun shiru”

Goge hawayen nake ina kerma shashshekar ce na kasa tsayar da ita, haka hawayen ma sun kasa tsayawa, wani abu nakeji ga kirjina ya kasa wucewa……….”meke tsakanin ki da usman?”

Wani mugun bugawa kirjina yayi sai wasu sabbin hawayen suka fara zuba, “yallab’ai Yah usy……..idan na sake jin wannan sunan saina sab’a miki, ki kirasa da usman d’insa”

Ina shashsheka ga ruwan hawaye kamar an bud’e famfo nake cewa, “kamar yayanmu na daukesa bacin matsayinsa na kanen ka da yayana babu abunda ke tsakanin mu, dukkan kulawar da kace yaban ya bani bai tab’a cutar dani ba, wallahi yallab’ai Yah usman bai canza matsayina a wajensa ba”

“Wad’annan hotunan kuma fa???”

Ya jefo mun wayarsa batai masauki ko inaba saiga kirjina, azabar da naji ce tasa nace da dan karfi “wayyo Allahna!!!” Ina dafe kirjin……….saida kurin na jishi gabana “innalillahi ta dokeki ko? Sannu ban san zata dokeki ba I’m sorry please bana sane,”

Tattare kafafuna nayi na saka kaina cikin guiwata kurin na fara rera masa kuka mai cike da kunan rai, ba kadan wayar ta dokar mun na fulanina ba wani irin zogi naji sukeyi,jinai inba kukan nai ba zan iyarasa numfashina bacin zafin da nakeji turarensa yazo yaimun k’ak’agida ga zuciyata, ni kaina nasan kukan da nake ya isa ya rud’a duk mai saurarensa, tabbas ya rud’en ba abunda yake yace fad’a face,

“Jannah, Jannah please stop crying, Im very sorry I don’t mean to hurt u, please kinji”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Leave a Reply

Back to top button