JANNAH COMPLETE HAUSA NOVEL

JANNAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Nidai uffan bance ba na maida kaina k’asa facing dina ta dawo kusa dashi ta zauna tana cigaba da magana, “Asaad Ina ka samota don Allah?”

Cike da kosawa yace, “pls Aneesa……..karki samun ciwon kai”

Harararsa tayi tana maido idonta kaina tace, “kar Allah yasa ka fad’a idan momy tazo ai kayi magana, ke ya sunanki?…………JANNAH sunanta”

Ya katse mun magana don harna bud’e baki zanyi magana kenan ya rigani,
“Wow sunan ma kansa mai dad’i……….wata budurwa ce ta fito daga wani corridor ba jimawa saiga momyn da ake magana,
Su duka kowa bakinsa asake yake kallona kamar an hura usur saiga sauran yan gidan suna fitowa daya bayan daya, jikina ya hau tsuma saboda idanun sun mun yawa………….”wow she is so beautiful and cute, mommy is she her friend daughter? don bantab’a ganinta nan gidan b……………..momy itace yar aikin da muke magana akai, Sunanta JANNAH makociyar su sagir ce bayan layinsu take, she is 21 years and she is in ss2 class, tana zuwa makaranta yanzu haka kuma tana zuwa islamiyya, munyi yarjejeniya da mamanta zata ringa zuwa makarantar ta duka, sannan after 3 months zata ringa zuwa ganin gida albashinta kuma ke zaki yanke in kuma ni zan biya saiki fada mun”

Asaad ya tsine maganar khalid dayaketa santina da alama ya girmesa sosai, amman kuma baiyyi kama da mutum uku dana gani a wajen ba,

“Kai! Ni kake katsewa magana?”

Wanda yagama yabona ya fad’a cikin fushi kamar zai hau saman yallab’ai asaad, cikin dakatarwa momyn tace, “please khalid wuce katai aikinka bana son fitina don Allah”

Yana wurgama Asaad din mugun kallo yai kwuta yajuya ya fice daga gidan, yar budurwar wacce bata wuce sa’ata ba inta girman ba dayawa ba cikin natsuwarta irin ta yallab’ai tace, “momy ki zauna pls”

Sai lokacin ta zauna tana janyo hindun jikinta ita kuma ta lafe kamar mage, saida ta gama mulkinta da isarta sannan tace, “usman baka da lectures ne?”

Jinjina kai kurin yayi ya zauna cikin kujerun falon, dawo da dubanta tayi kaina tana cewa, “kalleni nan ke”

Gabana yai bala’i bugawa ahankali na d’ago ina kallonta jinake kamar na zura aguje badai kwarjini ba matar, cikin isa take mun mgana tana cewa,

“Zo nan”

Ahankali na taso na iso gabanta na durk’usa hannu tasa ta zare hijabin dake jikina saida naja ajiyar zuciya, veil din dana daura matsayin kallabi ta zare shi, kitso ya bayyana da gashina daya zubo, ta jinjina kai sannan ta jifo mun veil din,tana cewa “muga yatsunki”

Na mike duka yatsuna na hannuna ta gama kallon su sannan tace “muga kafarki”

Mamaki kamar zai kasheni na dage rigar na fiddo kafafuna waje,ta gama kallon su tsaf na saki rigar tace “bude mun hakoranki”

Ihune kurin banyi ba don tsabar bakinciki na bude bakina ta gama lekenta sannan tace na koma na zauna, ina kerma sosai na maida komi na koma na zauna kowa yaga yadda jikina ke rawa, idona ya cika da kwalla had’a ido mukai da yallab’ai cikin sanyi ya girgiza mun kanshi tare da lumshe mun idonsa, ahankali naji yar natsuwa na shigata na maida hawayen ina had’iyar miyau………….”yana yinki yayi mani kinda tsafta kinci sa’a ta, don bana daukar k’azamai kin ci jarabawar tsafta, abu na biyu shine inhar baki son mu samu matsala duk abunda na saki kiyi,idan gari ya waye abunda kika san aikin kine kiyisa kafin na fito, ki tsaya iya matsahinki na yar aiki in kika ce zakiyi kutse a cikin lamarin gidana zakisha wahalata, dukkan kayan buk’ata zaki samu anan ban son sata bana son munafurci idan na kamaki da d’aya kashinki yabushe, game da makarantarki bazan hanaki ba amman inhar bakiyi mun aikina ba babu inda zaki, dukkan wasu nauyinki hakkinki zamu sauke miki nawa kike buk’atar albashinki?”

Kaina k’asa cikin sanyin muryata nace, “banda zab’i duk abunda aka bani nagode”

Kallon yallab’ai tayi tunda ya sa kansa a waya bai d’ago ba saida tayi masa magana sannan,

“Nawa kake ganin za’a ringa bata?”

Adak’ile yace, “inhar zaki biya ki fada mata koma nawane”

“Mekake nufi?”

“Naga ai nina kawota na dauka wannan karon ma nauyin zai hau kaina”

Dajin maganarsa kasan akwai bak’a acikinta, asace na kallesa ya wani sha mur kamar bashi yai maganar ba,bata kulasa ba tace dani.

“Zan ringa biyanki dubu talatin a wata yai miki”

Cikin sauri nace, “ehy yayi hajiya nagode Allah ya kara girma”

“Momy sunana dashi zaki ringa kirana”

Asanyaye nace, “to momy”

“Gaskiya da alama za’aji dadin aiki da ita akwai natsuwa da biyayya”

Cewar Aneesa ba dai wanda yace wani abu momyn ta kalli hindu dake jikinta har sannan tace, “baby makaranta fa?”

Cikin shagwab’a tace, “Bazanje ba banajin dad’i……….”keeeeee!”

Afirgice hindu ta dago tana kallonsa cikin daurewar fuska yace, “tashi ki wuce kishirya kafin na b’allaki”

Kamar an mik’ar da ita atsorace tatashi tai ciki duk aka bita da kallo, watau dai agida mulki yake zubawa son ranshi lallai ne yallab’ai,

“Meyasa kake mata ihu haka? Duk kabi ka tsani yarinya………..”ki gaya mata aikinta yadda idan tatashi zatayi ta gama ta wuce makaranta”

Ya fada ba tare daya kula da waccen maganar da tayi masa ba,

“Momy don Allah dakina ya zama cikin aikinta…………Aa banda shi”

Ya Katseta da fadar haka gaba daya ni mamaki da firgici ya cikani, daman haka yake acikin gidan nasu?

“Kin iya girki?”

Nace”ehy na iya amman ba duka ba”

“Za’a cigaba da koya miki har ki kware girki shine abunda zaki fara dashi amman ranar weekend kawai, sannan ranar working day’s kuma da kin tashi tun daga waiting falo zuwa falukan nan biyu da dakin hindu da dakina sune aikinki, sannan duk sadda mai wanki ya kawo wanki kayana dana hindu dana aneesa zaki goge su, zaki iya”

Cikin sauri nake cewa, “zan iya momy insha Allahu,”

“Good girl,Zan hadaki da shugabar masu aikin mu zata cigaba da koya miki abunda baki iyaba game da sanwa, bayan nan zaki iya yin duk abunda kike so dan gane da cin duk abunda kike ra’ayi, sannan in kina buk’atar abu kanki tsaye kizo ki sanar dani,inhar kika rik’e amana zakiji dadinmu”

Cikin jin dad’i nace, “to momy insha Allahu”

Hindu ce ta shigo cikin shirin makaranta ranta a b’ace, yallab’ai ya kalli usman yace “tashi ka kaita makaranta”

Babu musu ya tashi cikin biyayya yai gaba tana binsa a baya, Aneesa itama ta mik’e “momy zanje saloon daga can zan biya gidansu kamal”

“Ki dai dawo da wuri kinsan yau Abba yake dawowa daga Egypt”

“To Momy bazan dad’e ba”

Aka barmu dagani sai ita da yallab’ai, waya ta sanya ta kira shugabar masu aikin dattijuwa ce amman jikinta bai lalace sosai ba,da karfinta mai fara’a da ita na risina na gaidata,

“Sannunki yan mata tubarkalla kina da kyau”

Nai murmushi nace “nagode babaah”

Momyn tace, “sabuwar mai aiki ce uwani, zata ringa kama miki wajen girki duk ranar karshen sati intana gida,kafin nan zaki fara koya mata abubuwan da mukeci yadda koda baki nan zatayi, na gaya mata sauran aikinta kuje da ita ki kaita dakin da kausar tatashi”

Cike da bin umarni tace, “angama momy Allah yasa azauna lafiya dake yan mata,”

Ta mik’e nima na tashi zan bita momyn ta mik’e tana ansa waya tai ciki, har mun kusa shigewa naji muryarsa calmly yace,

“Jannah”

Waigowa mukai nida babaah uwani, yace “zan danyi magana daita babaah gata nan zuwa”

Tace”to yallab’ai saika rakota bangaren namu”

Juyowa nayi ahankali na dawo inda yake sai lullumshe ido yake kamar bacci bai ishesa ba,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Leave a Reply

Back to top button