JANNAH COMPLETE HAUSA NOVEL

JANNAH COMPLETE HAUSA NOVEL

“Murjanatu kina jina kuwa? Bud’e mun kofar mana inata kwankwasawa”

Ban kawo ita bace na dauka shine ya biyoni yana buga mun, saurin budewa nai na shige toilet na kunna famfo ina saita muryata nace, “babah gani nan bayi lafiya kuwa?”

“Inkin fito na dawo to”

Ajiyar zuciya nayi na wanke fuskata na bud’e na fito………..cak na tsaya bakin k’ofar ganin sa tsaye rungume da hannuwa yana kallona, cikin wani speed na juya na maido k’ofar zan datse hannu d’aya ya sanya da karfi ya bud’eta, duk kokarin dannewar da nake abanza dole na saki kirjina dagawa kawai yake, daga bakin ‘kofar ya tsaya yana mun magana.

”ki fito nan ko kuma in shigo”

Zai aika shiyasa na fito d’in amman ko saud’aya ban dube shi ba, hijabina ya dauko yana mik’o mun ”saka ki wuce muje”

Idona tab da kwalla nace, “Aa kaje nidai, amman bazan iya zuwa ba aiki zamuyi da babaah uwan………..ki saka kafin na sab’a miki anan wujen!”

Afirgice na na durkushe na saka kuka ina cewa, ” ni bazan bika ba, ai dai aiki zanyi ko kuma in banyi ba momy fad’a zatai mun”

Jiyai har juwa na daukar sa saboda tsananin b’acin rai, watau babu ma wanda ya raina kasa wayau irin wannan yarinyar, duk yadda kukanta ke dukan sa yake sashi sassarfa mazewa yai cikin tsananin kishi da masifa yace, ”kinsan zakiyi aikin da fari meya fiddoki? Usman ne yace karkije ko? Dake nake magana nace usman yace karkije ko??”

Naga rigimar data fi karfina rikicewa nai ina shashshekar kukan hawaye kaca kaca da fuskata, ina haki ina cewa ”ba ruwan sa, ni baice mun komi akan ka ba,nice nace na fasa idan na biku zuciyata bugawa zatai”

Kanshi har jijiya saida ta fito yadda ya nufoni na dauka daukeni da mari zai, don ya fusata sosai cikin wata kalar murya yake cewa ”taki zuciyar kad’ai kika sani, kanki kawai kika sani jannah! Watau ni tawa kota buga ba damuwarki bace shiyasa kikeyin dukkan abunda zaisa na mutu ku huta ko!!!”

Ya fad’a da karfin gaske saida na toshe kunnuwana, Aneesa ce da hindu suka fad’o dakin saboda jin tsawar da yake daka mun, da jajayen idanun sa ya kallesu cikin dakakkar murya yace, ”ku fice anan”
Fittt kamar walkiya suka fita, kerma kurin nakeyi sosai kamar an sakani freezer na kasa fahimtar maganganunsa, wadanda suka dakar mun yar zuciyata da bata da wani k’wari akanshi, muryarsa ta dishe sosai ya sake cewa cikin k’uluwa,

”karkiyi fatan na sake ganinki dashi, Jannah kiyi addua karna sake ganinki dashi komi zai iya faruwa, ki tashi ki saka hijab d’inki ki wuce muje”

Sosai nake kuka jikina har jijjiga yake, tabbas na tsorata da yana yinsa amman bazan iya had’iye maganata ba, saidai ya kasheni jefa nai da hijabin ina haki ina cigaba da kukan, magana nake muryar bata fita sosai.

”bazan daina magana dashi ba saika gaya mun dalili, akan me zaka rabani dashi bacin kai kana can da wata, abunda kuke yi nibana yinsa ba abunda ke tsakanina da yah usy……….fizgar da naji yai min yasa ban idasa ba idonsa kamar jini zai fito, rik’on da yai mun jinake kamar an saka igiya an daureni saboda azabar zafi, idonsa kamar zai fad’o k’asa har wasu ruwa ke taruwa acikinsu, yadda naji kirjinsa na bugawa kadai ya isa yagigita ni sakina yayi yana layi kamar zai kifa yai hanyar kofar fita, baijuyo ba ya sake cewa ”ina mota inajiranki”

Zaman yan bori nayi cikin d’akin ina kuka kamar Allah ya aikoni, kakar bazan je ba ssboda yadda nai banza da maganar dayai mun, ban san meyasa nakejin zafinsa sosai ba idan na tuna yadda na Ganshi da Aneesa da safe da kuma yanzu, kamar ana hura mun wuta haka nakeji a zuciyata naje na wanko fuskar sosai sannan nazo na dauki hijab d’in na fita, a kofa muka had’u da hindu tace “Jannah meyafaru? Duk hankalina ya tashi wallahi, dukan ki yayi?”

Girgiza kai nayi ina cewa “idan na dawo munyi maganar Hindu,kice ma babaah uwani naje indawo don Allah”

Cikin rashin jin dadi tace, “Ai yama sanar da ita, kije kawai ba komi amman don Allah jannah kibar kukan”

Share kwallar nayi nace a sanyaye “to hindu nagode sai nadawo”

Ban bita falo ba nabi ta can baya saboda kauce ma idon momy, inda motar take dazun yanzun ma tana nan,kofar baya bud’e take na isa wajen motar na shiga ina kilewa can jikin k’ofar na jingina kaina jikin kofar yatsuna kurin nake tsifa kamar zan cizgesu, haka mannir yaja motar muka fita mu uku babu aneesa bana son ko kadan na tuna abunda ya faru cikin yan mintuna da suka wuce, har tsikar jikina tashi take idan ina tuna rikicin, tunda muka dauki hanya kamar baya cikin motar lamo yai cikin kujerar ga wayarsa anata faman kira kamar bayaji, kuma nasan sarai idonsa biyu, nidai ko tari banyi ba wata babbar plazer naga mun tsaya kamar bazai fita ba haka ya fito ya shiga, tafiyar ma kamar zai fad’i.

Mun dauki minty talatin muna jiransa sai gashi ya fito ma’aikata wajen dauke da manyan ledoji sai kuma wasu matasa daketa daukar hoto dashi, murmushin karfin hali nake gani akan fuskar sa badan yana so yakeyi ba, har aka gama saka kayan aBut bai taho ba zuwan can wasu yan mata suna ganinsa suka hau washe baki, suma saida sukai hotunan dashi sannan ya taho.

Ayanzu na gane cewar ba Aneesa kad’ai na tsani ta rab’esa ba ko wacce mace inajin kamar nai aman zuciyata, rufe idona nayi inajin yadda har yanzu take buga man.

Shigowarsa yasa naja ajiyar zuciya can kasa a duk sadda yake gefena numfashina kansa yana mun wahalar shak’a, wani yana yi ne da nikadai nake jin yadda nakeji, tafiya muka cigaba dayi kamar kurame har shidda ta kusa na yamma, wata unguwa muka shigo inata kallon wurin kamar nagane sa ban ida tantancewa ba naga mun tsaya akofar gidanmu, wannan shine bazata yau nice nazo gida? Wayyo dad’i karka kasheni dan danan fuskata ta washe da murmushi da farin ciki duk da ga alamun kuka nan, still har sannan kishingid’e yake idonsa rufe kamar yana bacci, naji yamun magana da muryarsa data zama so cool,

“Zan dawo bayan sallar isha’i mutafi, ga kaya nan kice kekika kawo musu”

Wani abu ya sokeni na kasa fitar, godiya nake so nai mashi bakina yayi nauyi, saboda nasan na zuba rashin kunyata d’azun sai naji nauyinsa ya kamani, inajin ban kyauta ba duk da kuwa shima yana da laifinsa, uffan bai sake ce mun ba kuma yasan zaman danai magana nake son yi masa amman ya shareni, dole na bud’e na fita zuwa lokacin duk kayan da ya siya a shago dazun mannir ya gama shida dasu cikin gidanmu, siyayyace mai tarin yawan gaske har zuciyata nadamar abunda nayi ta kamani, meya shiga kaina danai masa haka?
Saidai naga har sun bar kofar gidan, kamar kwai ya fashe mun aciki haka na lallab’a na shiga gidan, da zainab mukaci karo wata kara ta saki tana sakin butar da take alwalla da ita, aguje tazo ta makalkaleni tana murna ihunta ya fiddo innamu, ai tana ganin nice itama kamar ta taka rawa saigani ina kuka na rungume innamu, saboda ba kadan nai kewarsu ba kasa sakinta nayi inata kukan,farin ciki kamar yai mata me tace “haba murja minene na kukan to, muma munyi kewarki sosai agidan nan”

Ina kukan nace, “Amman arasa wanda zai neman yaje inda nake innamu? Kamar kun siyar dani fisabilillahi, ko yayanmu ai yaci ace yaje yaganni tunda suna waya dashi Yah Asaad d’in”

“Yanzu dai kiyi hakuri zamu samu lokaci duk muje muganki da inda kike, tashi muyi sallah tukunna”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Leave a Reply

Back to top button