JANNAH COMPLETE HAUSA NOVEL

JANNAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Na sadda kai ina murmushi bance komi ba, yayin cikin raina ya fama mun inda ke mun ciwo don har bana son yin tunanin yadda zan kasance bayan tafiyarsa, wani iri nakeji a raina sosai.

“Usman idan ka bari jann tayi kukan rashin gata nida kaine”

Murmushi yayi yana cewa, “bros kanaji da ita ne har haka”

Wani murmushi ya saki wanda zai iya bayyana meke cikin ransa, satar kallona yai kaina kasa ina nan yadda nake,sai yace masa “fiye da haka ma”

“To insha Allah jann bazatai kukan rashin gata ba, usman yana nan kuma zan kasance ina bayanta akodayaushe”

Tattara kayan nafara yi don maganganun su suna rikita mun kaina, miko mun bowl din fruit salad din yayi yana kokarin kallon cikin idona nak’i basa had’inkai,

“Kije kisha kema”

Girgiza kai nayi zan tashi yace, “au ba zakisha kingina ba ko”

Zaro duka idanuna nayi nace, “Aa yallab’ai”

“OK anshi”

Ansa nayi ina masa godiya sannan na fita da kayan, abakin kofa muka had’u da Anty Aneesa tai tsaye tana aika mun da mugun kallo, na rab’ata na wuce kurin.


“Fareeda zoki shirya ko wuce gidanki haka nan,ja gaji da tsogunguman sa keketa faman yi mun tun zuwanki haba,”

Cikin kufula tace, “momy gaskiyar da nake nusar dake itace tsogumi? Yancinki fa muke kokarin ganin mun anso miki, kinagani Abba inba maganar asaad ba bayajin ta kowa,sannan shi kadaine mai kima idonsa sannan shima asaad din bai daukeki bakin komi ba, baki isa ki yanke hukunci yabi ba ko da baki haifai ba aike matar uban sa ce dole ya baki girmanki, kuma akan me zai ringa wulak’anta yaya khalid agirme dai ya girmesa amman duk kin saka ma komi ido momy baki daukar wani mataki, yanzu keda gidanki sai abunda yace zaki yi”

Momyn tai kamar bajinta take ba ta cigaba da danna wayarta tana buga lissafinta, kasancewar tana kasuwar lesses irin na lagos din nan da dubai,

“Kinaji na fa momy”

Aje wayar tayi da biron hannunta tana zubama fareeda idanu na wani lokaci kafin tayi murmushi tace, “inajinki mana”

Kamar tayi ihu tace “shine bazaki ce komi ba, momy ki shigo cikin mu mukwatar miki yancinki”

Girgiza kai tayi tana cewa, “daga ke har khalid d’in babu mai hankali, shekarun banza ne daku baku san komi ba, don haka ki kyale da wannan maganar kizo ki wuce gidanki kafin Abba ya dawo ya sameki”

Daga haka ta cigaba da abunda takeyi, fareeda dai bata gane kalaman momy ba haka ta karaci nazarinta ta dauki jikkarta tace tatafi.


Asubar fari naji wayata nata wannan burrrr burr din alamun vibrating cikin bacci na lalubota na saka ga kunnena,

“Baccin ya isa haka nan atashi ai sallah”

Sai lokacin na dawo hayyacina jin muryarsa ta ratsa kunnena, cikin muryar bacci nace “to yallab’ai”

“Karfe bakwai da rabi zamu fita kiyi komi kan lokaci, saikun rakani airport sannan usman ya saukeki makaranta”

Rufe idona nayi inajin kamar na saka ihu, cikin sanyin murya nace “yaune ko?”

Murmushi yayi yana lumshe idonsa saboda yadda yaji maganar ya tab’a masa rai, jiya bai samu baccin kirki ba saboda jin kwata kwata baya son tafiya,………..”yaune mana”

“Bari nai sallar, akwai abunda za’ai maka na break”

“Aa bazan iya cin komi ba ai”

Cikin sauri nace, “meyasa yallab’ai?”

Koma wa yayi ya kwanta yana sauke ajiyar rai yace, “kiyi sallar lokaci na tafiya”

Jikina yai mugun mutuwa na sauke wayar, sai naji kamar inaso nayi kuka,amman kukan bai zoba raina aa dagule naje nayi alwalla nai sallar, kayan jikina na zuwa masu rufe jiki na fitana fara gyaran falukan inajin motsin babaah uwani ta fito, akasalance nake aikin amman ina maida hankali inyi ingama, dakin hindu na wuce na kwankwasa mata a fusace tataso tana bala’i

“Uban waye zai cire mun kofa”

Tasan nice shiyasa take wannan zagin, tunda tasan ba mai zuwa kamar yanzu ya buga mata kofa saini,

Na kalleta sama da kasa raina ab’ace nakasa yin shiru nace, “please idan bakyason aikin da nake maki kigaya ma momy ba sai kin ringa zagina ba don Allah”

Dogon tsaki taja tana wuce wa ta shige toilet, na hau aikina duk ta jefar da kaya tsakar daki kamar wata jaka, dakin ba babba bane shiyasa ban dad’e ba saida ta fito wanka na shiga na wanke toilet din, na kun na bonner nai ficewata.

Momy na bangaren Abba shiyasa na shiga kaina tsaye kasancewar inda makulli daya hannuna, anan ne na dad’i saboda two bedroom ne da karamin falo, agajiye na koma kitchen na kama ma babaah uwani muka cigaba dayi.

“Murja yau Asaad zai koma kasar da yake aiki duk banji dad’i ba, shi kadai ne akejin dadinsa agidan nan”

Sai naji kamar na saka kuka muryata ta karye nace, “babaah kila na fiki jin babu dad’in, saboda dai ni banda wani mai kaunata agidan ba mai sassauta mun saishi, ji nake kamar wani bangone nawa zai fad’i, da ace banyi alkawarin yin aikin nan ba hakuri zanyi na koma gidanmu, amman iyayena bazasu yafe mun ba idan nayi haka, shima kuma zaiji babu dadi.”

Tace, “hakane murja, saidai hakuri kam don mutanen gidan nan banajin zasu canza, ki dage da addua kawai don injin tsoron wani abu”

Ganin lokaci yayi nace “don Allah babaah ki ida inje inyi wanka”

Tace”babu komi jeki ai munma gama”

Daki na koma na shiga wanka inayi ina jin kamar zuciyata zata tsinke, bantab’a jin irin hakan ba tunda nake koda wasa kuwa, wani irin missing ne nakejin yana nukurkusata arai tamkar naita kuka babu kakkautawa, na fito na fara shafa kenan ya sake kirana jikina har rawa yake naje na dauki wayar,

“Hello Yallab’ai”

Muryarsa tayi slow kwarai yace, “ki kawo mun tea mai zafi”

Sai naji muryar tawa ta koma irin tasa nace, “shikadai”

“Ehy shikadai jann”

Sauke wayar nayi na dora kaina bisa mirrow inajin kwalla na cika mun ido, saurin gogewa nayi na idasa shirin, ko powder ban saka ba na saka riga da siket dina uniform dina siket din yazo guiwa sai doguwar safa da zata rufe maka kwamrinka,da takalma combus blue and maroon, suma kayan haka suke siket din marron rigar fara sai kayi zan zaro sai yar himar d’in da zata rufe maka kirjinka, rigar dogon hannu gareta ban saka kallabiba himar din mai hulace, dana kalli kaina a madubi saida na tsorata na rufe baki da hannuna ina sake kallon kaina,

“Ya subhanallahi, gaskiyar mutane da suke cewa kyauna kamar aljana, Allah ka kiyayena da sharrin dake cikin wannan kyawun nawa”

Nai addua na shafa ga fuskata tunda ba damar in saka nikab dina, turare na saka kadan sannan na fita zuwa kitchen d’in, dining na shirya sannan naje na had’a masa tea d’in,

Babaah uwani tana ganina tace, “masha Allahu murja,hakika kinyi kyau sosai Allah ya tsareki daga sharrin makiya”

Cikin jin dad’in adduar ta nace, “nagode sosai babaah ta Amin Allah ya amsa”

Da khalid muka had’u zan kaima yallab’ai tea d’in daya buk’ata, saboda kallona da yake tayi tunda ya taho saida ya kusan fad’uwa, gabana na duka na risina na gaidasa,

“Ina kwana yallab’ai?”

Baiji abunda nake cewa ba ganin haka nai saurin shigewa ina jan ajiyar zuciya, ban gansa a falon ba don duhu ma falon an rufe ko ina labuleyen duk sauke suke, haske kadan ne.

D’an zama nayi inji ko zai fito na aje cup d’in bisan center table din dake gabana, babu jimawa naji motsinsa haske kuma ya gauraye falon kamar tsakar rana.

Turaren nan nasa ne ya sanar dani isowarsa na sauke kaina k’asa inajin bugawar zuciyata yana hauhawa, cup din ya dauka yana zama bisan table d’in ma’ana ya sani gaba kenan.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Leave a Reply

Back to top button