JANNAH COMPLETE HAUSA NOVEL

JANNAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Na cire hijabina nace , “ina baba yake zainab”

Tana shimfid’a abun sallah tace, “ai baba yanzu ba zama bakisan kasuwa yake yi ba, yallab’ai ya bud’e masa wani shago a sabon gari, wallahi karkiso kiga dukiya Yaya murja, sannan yazo ya siya mun keken s’ak’a kinga duk unguwar nan ba wanda baisan ina sak’a ba, har daga wani waje zuwa ake siyen kayana, labarin fa da yawa bari nayi sallah”

Bakina kasa rufesa nayi jin wani sabon labarin daga zainab, sai lokacin na lurax da sauye sauyen cikin gidan baki d’aya, anyi tayil ga generator nan harda rizabuwa akai musu, sannan cikin dakin tv ta bango babba ga babbar freezer nan, komi ya sauya sabanin sadda na tafi a cikin wata shidda aka samu wannan cigaban, mezan cewa yallab’ai nikam? Jinake baki yayi kadan wajen yin godiya dame zan saka masa a rayuwata?

Har nayi salla sake sake kurin nake a zuciyata, babu wanda ya kawo cigaba da sauyi a cikin rayuwar mu irinsa, wace irin kauna ce yake mana haka???

Innamu tace, “wannan siyayyar fa murja?”

Na tuna maganarsa kafun ya tafi,
Cikin sanyin jiki nake cewa, “ni na siyo maku innamu ku samun albarka”

Ai kuwa nasha albarka kamar ba zata bari ba da aka zube kayan ni kaina na tsorata ainun, shaddoji kala biyar atamfofi da less biyar biyar, iyayen kayan shafa da mayuka da shampoo burjik, turaruka gasunan na baba daban shida yayanmu saina matan daban, sai takalma da jikka na zainab dana innamu sabida farin ciki innamu harda hawayenta, tace “murja hakika haduwar mu da wannan mutumun alkairice, don Allah kicigaba da yimusu biyayya kina kyautata masu,nasan duk inda kake dole ka samu kalubale murja ki rufe idonki da kunnanki,kiyi abunda ya kaiki karki sab’a masu,shima kuma ki kasance maiyi mashi biyayya don kyautatawar da yake mana baki bazai iya liassafi ba, bayan shago daya bud’e ma babanku kingamu da injin wuta idan an dauke, bamuda matsalar ruwa ga sana’a yabamu nida zainab ni keke napep ya siyamun ake mun haya, duk sati dubun nan goma ake kawo mun, yayanku yana makaranta komi na dawainiyar karatunsa shine ga kudi da yake bashi, sannan ya sakaa zainab ta koma makaranta harda islamiyya, murja meyai saura? Inajin kiris babanku ke jira yace ya bashike,don inhar ba sonki yake ba ai bazai wannan wahalar hidimar damu ba, nikam ina fatan. Ace sonki yake din koda hakan mu biyasa wahalar da yake damu”

Ab’oye nake share kwallar dake zubo mun, nace “innamu bafa sona yake ba kawai dai shidin mai alheri ne, abun hannunsa bai tsole masa ido ba, duk wahalar da yake daku nima cikin yimun yake, bakin rai bakin fama yana kokarin ganin wani bai cutar dani agidan su ba, ina zaune kalau innamu bansan dame zan saka masa ba”

Muryata harta karye saboda raunin da nakeji a zuciyata, kamar na dawo da baya na wanke laifina danai masa,

“Bamu da wani abun da zamu saka masa dashi sai addua, ina fatan watarana yazo da buk’atar aurenki wallahi babuja zan amunce, haka babanku wannan ranar yake burin zuwanta,”

Munsha fira sosai dasu mukaci abinci tare, kowa cikin farin ciki yayanmu ne ban gani ba saboda makaranta hostel yakoma don yafi jin dadin karatun acan, sai isha’i baba ya dawo yadda naga yacanza abun ya mun dad’i kaface kuri baida ita,amman ya samu lafiya jikinsa yai kyau, yanada yan sandunan nan da ake dogarawa dasu.
Shima dai maganar Yah Asaad dince yajeta yimun yana ta fad’ar alkairinsa,yana sake jaddadamun na rik’e amana inyi masu biyayya ba ruwana da abunda ba’a sakani ba, in kauce ma abun wani sanan yace “ina adduar cikin dan lokaci inhar sonki yake yaron nan, yazo ya gaya mun ni kuma nai alk’awarin ko bayan raina yayanku ya aura masa ke, amman baxan gaggawa ba har sai shi yace yana so”

Zuwa yanzu zuciyata tagama yarda da cewar tabbas yana sona d’in, dana zauna na ringa tunano abubuwan da suke faruwa, har kawo yau d’in nan zargina ya tabbata amman ban idasa yarda ba tunda bakinsa bai furta ba, sai na tambayi kaina “shin inya furtan ni ina sonshi kenan???”

Tambayar da tasani cikin wani sabon tunanin, ban samo amsar ba abunda kawai na sani shine ina tsananin kishinsa, idan naganshi da wata zafin da nakeji kamar zai sumar dani, bansan yaushe na fara jin hakan ba amman halin da nake tsintar kaina kenan, sannan idan ina kusa dashi jinake tamkar wurin yaimun kadan, kwarjini yake mun muryar sa har tayar mun da tsikar jikina take, komi ya saka kyau yake ga idona ba abunda ke fizgata irin sassanyen murmushinsa da kallonsa,

“Yaya murja kiketa murmushi bama jina kike ba”

Dafe kai nayi ashe tunanin sa ma danake murmushi nakeyi ban sani ba, dole na bata hankalina tana ta ban labarin makarantar su, da costumer dinta.

Sai wajen karfe goma ya dawo na dauka ma kwana zanyi, saida ya shigo ya gaida su baba da innamu ya aje masu katuwar takaddar nama da kud’i bandir din dari biyu.

Har waje suka rakoni jinake kamar na koma amman ya zanyi dole na tafi, muka shiga bayan mu duka mannir yaja muka dauki hanya, ga garin in dare yayi go slow ake tarawa sosai.

Yanzun ma tunda muka taho uffan baice mun ba, f-cap dinsa ya jawo ya rufe fuskar sa daita,da yake kayan da yazo dasu d’azun basune jikinsa ba alamun yayi wanka kenan, suma din kananu ne bai cika saka manyan kaya ba sai juma’a da litinin, ganin cewar dama ce dazan yi amfani da ita in bashi hakuri saboda in mun isa gida ba lallai ya sake bi takaina ba,bai tab’a yin fushi dani irin wannan ba ada idan muna tareshine yake kokarin ganin nai masa magana yana jana da fira, amman yau kamar muna tare da gunki haka ya nuna.

Kwalla ta cika idona ban san meyasa yanzu kuka baya mun wahala ba,kodan hada kari da cewar zuciyata tayi matukar rauni akansa, zoben daya tab’a bani naketa jujjuyawa ina wasa dashi, ina tuna ranar daya saka mun shi ranar da zai tafi yabarni, na tuna saddana kama hannunsa na rik’e yana mun murmushin dake lumar dani, yake cewa

Kona bar miki shi

Alokaci guda murmushi da kwalla suke fita a fuskata, ban damu na goge su ba ban dubi inda yake ba nake magana, don nasan ba bacci yake ba duk motsin da zan yana jina,shiyasa ban damu saiya dubeni ba cikin muryata da ta karye ta zama so cool nake cewa ahankali duk da nasan mannir zai iyaji,amman ban damu ba burina ya fahimceni ya kuma daina wannan fushin dani.

”Yah Asaad I’m sorry”

Na fad’a inajin kamar naita masa kuka, na danne kukan shiyasa muryata ta fito like kamar inayin kukan, nasan yajini sarai magana ce bazai mun ba……….

“Bakina yayi kadan wajen yimaka godiya amman duk da hakan dole na gode maka akan dawainiya da kake da ahalina, Allah ya saka da alkairi”

Sai lokacin naji yai magana inba dan ina gefensa ba da kila bazanji ba,saboda yadda muryar tai silent sosai.

“Ba danke nayi ba, ban kuma yi donki gode mun ba”

Hawayena suka silalo tabbas zafina yakeji, ya zanyi naja majina ina saka kallabina ina goge fuskata, duk da wasu na sake zuba nace masa.

“nasan ba danni kayi ba, amman ya zama dole na gode maka koda baka so, nasan na maka laifi don Allah ka yafe mun, bansan mekake tunani akaina ba amman har cikin zuciyata ba ina nufin nai maka rashin kunya ba, Yah Asaad ka fahimceni please! Bana cikin hayya….ya….cina duk nai……nayi abunda nayi……….”

Na karashe ina yar shashsheka kasa kasa don ko karfin yin kukan ma bana dashi, ko tari bai sake yi ba hakan ya sake tun zira kukana na saka fuskata cikin hijabina nayi tayi harna gode Allah, har muka iso gida bace mun ba nima ban sake cewa komi ba, wurin parking mannir ya isa yai parking, saiya fita kurin ya barmu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Leave a Reply

Back to top button