JANNAH COMPLETE HAUSA NOVEL

JANNAH COMPLETE HAUSA NOVEL

“Abba Jannah ba zata ringa gyara masa daki ba, ai yana da mai masa aiki miye zai saka ace sai ita? Kuma a daidai lokacin tafiyarta makaranta a tilasta saitayi, duka awa biyuce sun tashi idan ta dawo ba sai tayi ba, to na hanata gyara dakin daga wannan ba zata kuma ba, wallahi idan aka sake sakata gyaran dakin wannan gardin duk abunda nayima mutum shiyaso”

Abba baice komi ba saida Asaad yakai aya sannan yace, “Momy ayi hakuri a kyale jannah da gyaran dakin khalid, tunda John yana yi masa ya cigaba dayi kawai”

Uffan bata ce masa ba hakan ya nuna ranta yai kololuwar b’aci, ba wanda ya sake magana a wurin har Hindu ta gama usman ma ya tashi,

Ba wata tsiya ke cikin dakin ba tsabar takurawa ce kawai, ban dad’e ba na gama na fito sannan momy ce da Aneesa a falon, gabana yana fad’uwa nace, “momy na gama zan tafi saina dawo”

Kallona kurin tayi sannan ta jinjina kai,nai waje ina ajiyar zuciya tsaye suke jikin mota suna magana shida usman, na rab’asu zan wuce naji ya kira sunana.

“Jannah”

Dawowa nayi ina sake gaidashi yace, “shiga mota mu saukeki”

Banyi musuba na shiga baya su suna gaba, usman yake jan motar suna cigaba da maganarsu wadda bansan akan me sukeyi ba, har cikin makarantar muka shiga muka nufi office d’in malaman, dukkan littatafan da sukeyin amfani dasu aka siya mun sannan ya had’ani da class master dinmu, bayan mun fito zan tafi aji ne ya tsayar dani.

“Usman gobe zan tafi, kuma zan bar amanar Jannah a hannun ka kai ne kake zaune kullin,kasanya ido akanta abunda ya kamata ka tanka akanshi idan anyi mata kayi magana, idan kina bukatar wani abu ke kuma ki samesa karki ji komi ki masa magana, kai ne nasan baza’a samu matsala daga wajenka ba”

Yace”ok broth insha Allah”

“Sannan duk sadda zaka fita lectures inhar bata tafi makaranta ba ka tafi da ita, randa kuma bakaz fita saika bata kudin hawa napep”

“To broth noted insha Allah”

Ahankali na risina nai masa godiya sannan nan na tafix class, akai daidaitoni ajinmu guda da hindu ban nuna na ganta ba,na samu second sit na zauna ranar qur’an akai mana da hadith surar da muke tuni na gamata ni tuntuni, hadith din ma na gama shi duka banda wata damuwa anan, shabiyu da kwata aka tashi na hau abun hawa daker na gano unguwar.

Mom muhseen✍????
[8/1, 1:05 PM] Mom Muhseen????: ????JANNAH????

{A TRUE LIFE STORY}

E.W.F

By
Mrs Bb
mom muhseen

wattpad name
Humaira3461

    ????️.......13

Inayin sallama da shukra naci karo anty Aneesa tana ta balbala masifa ta inda ta shiga ba tanan take fita ba, akan rashin zuwanta da wuri da batai ba gefe guda kuma naga bakuwar fuska da alama itama yar gidance don naga fuskar momy jikin tata, sunyi kama sosai kwabo da kwabo.

“Zaki tashi daga gabana ko sai nayi kwallo dake, kidahuma kawai”

Tana shashshekar kuka ta mik’e sauri-sauri tabar wurin, kasa shiga nayi saboda gaba d’aya na tsorata sai lab’e nake bakin k’ofa jikina na tsuma, su duka banga alamun sassauci daga garesu ba basuda tausayi da rangwame…………..”momy idan kina son ki zauna lafiya mu zauna lafiya muma dole ki bamu had’inkai, agaban kowa fa kika ce yai miki warning akan yar aiki, yar talakawa wadda bata kai darajar takalminki ba, shi yaya khalid d’in yana wajen kuma baice komi ba”

Aneesa tace, “Anty fareeda don Allah kibar maganar nan, ya riga ya wuce gobe ma zai bar kasar ba shikenan ba, nifa duk abunda xai cutar dashi bana so…………zaki rufen baki ko saina ci ubanki Aneesa? Shegiya da bata kishin uwarta,kodayake dan wani daman bai zama naka”

Cike da rashin kunya tace, “Niba shegiya bace Anty fareeda, kuma ni da kike gani nafiki kishin momy duk da bata haifan ba”

Fitowa nai daga karamin falon nayo waje, nama rasa ina hankalina yake kaina ya kulle ban fahimci duk abunda suke cewa ba, bazan iya bi ta gabansu ba tabbas in suka ganni akaina zasu huce, tunda nice silar komi.

Wajen maigadi na nufa na sake gaidasa cikin sanyin jiki nace, “baba mudi akwai wata hanya da zata kaini bangaren mu banda waccen”

Yace”zo muje na nuna maki, ai don kina bakuwa amman waccen kofar ai ba hanyar fitowarki bace”

Binsa nayi zarai zarai har muka zaga baya sai gamu kofar kitchen ta baya, kadan muka kara matsawa sai na samu shukra tana ta kuka ga wanke wanken tana tayi har taci rabinsa, baba mudi ya koma bakin get ni kuma nai tsaye bayanta naji duk ta bani tausayi,
Muryar baba uwani naji tana isowa wajen tana cewa,
“Ki hanzarta ki gama tunda ba shikadai zakiyi ba, duk ke kika jawoma kanki bakijin magana shukra ko kadan………Aa aha ke kuma yaushe kika shigo?”

Sai lokacin shukra ta waiwayo nai ajiyar zuciya nace, “yanzu na dawo, sannu da gida babaah uwani”

“Yawwa kema sannu, kije kicire kayan kizo mu dora sanwa”

Na amsa mata da to ja wuce ta kofar na isa har dakina ba tare da na had’u da wani acikin su ba, kaya nake cirewa ina sake tariyo maganganun su da naji a falo, Anty Aneesa ba yar gidan bace kenan? To shi yallab’ai khalid d’in fa? Wannan dai Anty fareedar da alama itace kebin yallab’ai hisham duk da har yau bamu had’u dashi ba, wane hadin kai take son momyn ta basu? Duk bai wuce akan abunda ya faru dazun da safe ba,

“Ya Allah ga murjanatu! Ka taimakeni ka kawo mun dauki, ka kareni daga wadannan mutanen”

Har ga Allah tsoron su nake matuk’a,momy kanta abun tsoroce shirun da take baya nufin alkairi, haka dai naita zancen zuci har na wuce muka fara aikin nida babaah uwani, saukin mu akwai time table na abincin da akeyi duk rana, sannan ba kullin mukeyin na dare ba nida babaah akwai babah azumi itace keyi akin yamma har wanke wanke da gyaran kitchen da sanwa, daman sai bayan laasar take zuwa ita.

Weekend ne muke yin girkin safe dana rana,sai idan za’ai ma Abba tuwo ni nakeyi masa, sauran gyare gyaren kuma working day’s nake yinsu weekend kuma shukrace, ba laifi ina dan samu hutu matsalar mutanen gidan ne basuyi ba.

Muna cikin aikin ne naji an shigo kitchen din, juyawa nayi mukai ido biyu da bakuwar ta yau na risina ina gaidata,

“Ina wuni, anzo lafiya”

Wani kidahumin kallo take wurgamun kafin cikin izgili tace, “kece jannah?”

Gabana na fad’uwa nace, “eh nice”

Taja wani dogon tsaki ta bud’e frij ta dauki lemu tana cewa, “babaah me kuke girkawa yau”

Ba tare da babaah ta kalleta ba tace, “pride rice ce da nama, sai tuwon shinkafa da miyar agushi da naman kaza”

“Ohhh duk ciki banada abunci, kee!”

Na jiyo ina kallonta tace, “maza ki jik’a wake alale nakeso da kwai aciki, asanya mata alayyahu da sannan ai mata miyar kifin gwangwani”

Wani rugugin tashin hankali naji ya rufto mani, na had’iye miyau daker………..bakijina ina magama jakar banza”

Ina kerma nace, “to…to zanyi yanzu”

Tana jan tsaki tace “kidahuma”

Tana ficewa hawaye na zubo mun, na aje wukar hannuna ina sharewa babaah tace “kiyi hakuri murja, mutanen gidan nan abunda suka iya kenan yana daya daga cikin abunda yasa yan aiki basa zama da sun fata kwana kadan suke guduwa, ki kara hakuri abunda kawai zance maki kenan, sai kuma ince ki ringa addua kina rokon Allah ya tsareki daga dukkan mai sharri”

Naji dadin lallashinta saboda da ciwo aimaka cin mutunci bakada wanda zai lallasheka ya baka hakuri, waken na jika sannan na tuka tuwon na barsa ya silala sannan na hau kullashi, babaah ta dora mun naman kafin in gama kulla tuwon.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Leave a Reply

Back to top button