JANNAH COMPLETE HAUSA NOVEL

JANNAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Girgiza kaina nakeyi hakan bamai yuwuwa bane, yace baida wani buri akaina sai yaga nayi karatu inda yana sona kokari zai yaga yasanar dani,koma yaga ya samu ya mallakeni bazan masa uziri ba shiyasa ma naji na kasa daukar kiran, duk da yadda gabana kuwa yake fad’uwa, inajin kamar banyi daidai ba gatsoron sa daya kamani saboda fad’an daya surfa mun d’azun, cikin yan seconds kamar bashi ba kuma yazo yana lallashina………..murmushi naji inayi saboda abun yaban dariya ni kaina dariyar nake ma kaina yadda na saki baki naita rusa masa kuka kamar wata yar yarinya………….kiran ne ya sake shigowa nasaka wayar gaba ina kallon no din kamar zanga fuskar sa aciki, har cikin raina so nake na d’auka amman bansan meyasa nakeson yaji babu dad’i ba, atakaice saida yai kira biyar inata kallonsu zuciyata bata huta da dokawa ba kawai ina hango rikicin da zamuyi, idanunsa yadda suke juyewa kamar ba nashi ba sunfi komi fizgata, duk da yana cikin mood marar dad’i kyau suke sosai idan suka canza launi, burum naji anshigo saurin tashi nai ina cewa, “haba dai Hindu ba knocking”

“Ashe ma idonki biyu, shine Yah Asaad nata kiranki Jannah baki dauka ba”

Kauda kai nayi nace, “silent takefa niban gani ba……….wayar na gabanki kice mun biki gani ba, kawai dai kice mun wulak’anci zaki masa yace kizo in kuma inkoma ince kince bakizuwa to”

Sai lokacin naji hankalina yai mugun tashi, dirowa nai ina rik’o hannunta kamar zan kuka, “hindu please kice nafara bacci, don Allah karki ce ina gani ban dauka ba”

Hararata tayi tace, “nak’i na fad’a d’in tunda abunda na gaya miki dazun bai shiga kunnan ki ba, har Yah ASAAD yakira Jannah kina kallon kira ba zaki dauka ba? Tabdijam tunda nake da Yah ban tab’a ganin macen da yake bi irinki ba”

Ta juya ta fice ko tsayawa duba sitirara jikina banba na figi hijabin dana dawo da ita nabita a kid’ime, har ta isa sadda naje a bakin k’ofa mukai karo da Yah usy,kallon juna mukai kamar bazai daina kallona ba sadda kai nayi ina ce masa , “Yah usy barka da dar……….wuceni kawai yayi with out said anything, banji dad’i ba saboda ban masa laifin komi ba shiga nayi da sallama duk na rikice, Hindun na iske tsaye shi kuma yana cikin kujera kanshi k’asa, three quarter wando ne fari jikinsa sai sheet mai gajeran hannu coffee brown, duk da bai d’ago ba kayan sun masa kyau sosai, kadan da inda yake na durkusa kan guyawuna Hindu tace ”Yah gata nan”

Banjira yace wani abu ba nahau kare kaina bakina har rawa yake, ba abunda nake gudu irin ya daka mun tsawa irinta d’azun,

“Don Allah Yallab’ai kayi hakuri wayar silent take bacci na fara banji ba, don Allah kayakur…………..dagowar dayai yana kallona yasa nakasa idawa tsoro naji yadda naga fuskarsa idonsa sun lumshe sunyi wani iri, zare ido kawai nake Hindun tace “Yah mezan kawo maka”

“Jeki ki kwanta akwai school gobe”

“Yah tunda ka iso fa bakaci komi ko tea ne naje na had’o maka”

“Banson musu Hindu, kije nace miki ko”

Ta kalleni ta maka mun harara ta fice daga falon, abunda ya tada mun hankali shine jin danai cewar tunda ya sauka yau d’in baici komi ba, innalillahi halan ma kiran da yake mun kenan? Nashiga ukuna nayi haka?jinai kwalla ta cika mun ido zanyi magana kenan ya katseni cikin muryarsa datai sanyi sosai,

“I’m sorry na tadoki ashe bacci kike, kije ki kwanciyarki”

Yana tashi zai shige ciki ban san sadda na ganni gabansa ba, “Aa yallab’ai ai na tashi zan iya yimaka koma me kace, don Allah kayi hakuri”

Idonsa keta lullunshewa gaba d’aya babu kuzari tattarre dashi, idanunsa ya zuba mun kamar zai cinyeni nai saurin sauke idona kasa daga kallon da yake mun, “nace kije ki kwanta ba abunda nake buk’ata”

“Hindu tace bakaci komi ba tunda ka dawo, don Allah kar kayi fushi zanje na dafa maka duk abunda kake so”

Lunshe idonsa yai yana bud’esu kaina taku biyu ya k’ara ya iso daf dani, dole na runtse idona inajan wani irin numfashi cikin yin kasa da murya yace, “kin san a yadda kika shigo nan kuwa?, hakan ya tabbatar mun ba bacci kike ba sadda baketa kiranki”

Idanuna duka na zaro kafin na kalli jikina, riga da wando ne jikina na bacci, wandon iya guiwa yake hajibin kuma bata wuce guiwar ba itama, rud’un dana shiga a sadda hindu tazo yasa ban tsaya dauko dogon hijab din ba, dukan santala santalan kafafuna suna waje wata irin zabura nayi na duk’e k’asa na cusa kaina cikin kafafun, na lullub’e kafafun da hijabin inajin kamar na ringa marin kaina saboda takaici, duk yadda yakejin kanshi dole saida ya sake siririn murmushi durk’usawa yayi gabana yana cigaba da murmushin yace,
“Aikin gama ya gama ai, gaya mun meyasa kika ki daukar kirana?”

Shiru nai kamar xan rusa ihu yace “saboda ki tada mun hankali ko? Idan na sake kiranki kina gani biki dauka ba a ranar zaki san waye ni, watau Usman ya koya miki rashin kunya ko?”

Azabure na dago ina yin kamar zan kuka, “Wallahi aa yalla………inkika sake cemun wannan yallab’ai din saina sab’a miki,”

Na sauke kaina ina turo baki nak’i tashi daga inda nake, jinai kawai yace “kike zagina Jannah”

Bakina da idona duk na bud’e ina zare ido nace, “nashiga uku wlh ban zageka ba don Allaah kayakuri”

Wsni irin kallo yake mun yace, “bazan yi hakurin ba,”

Yak’i tashi daga gabana balle na samu damar guduwa, na sadda kaina ina cewa “to ka rama”

“Ai banji mekika ce balle inrama”

“Wallahi fa bance komi ba, taya zan iya zaginka ni koba kaiba bana zagi ma gaba d’aya”

Ajiyar zuciya ya sauke jiyake kamar su kwana haka da ita, saiyaji duk yunwar ta fece shikadai yasan abunda ke fuzgarsa akaanta, “meyasa? Wani matsayine dani ban sani ba”

Sauke kaina nai inajin murmushi na son kubce mun, nace ahankali “yallab…..ohh kaya kuri don Allah, ina nufin kafi karfin na zageka duk laifin da kai mun,”

Wata irin ajiyar zuciya ya sauke ahankali yana cigaba da kallona kafin cikin lallausan lafazi yace, “shiyasa nace meyasa?”

D’an turo baki nai saboda k’osawa, “karki sake turo min baki tau!”

Na saka hannu na rufee bakin, nace “kaya kuri,”

“Injinki meyasa?”

“Ka zama wani sashe daga gareni, zan iya kiranka dangina inajinka kamar yayanmu”

Jiyai kamar ana shawagi dashi, ya sake sassauta murya yace “danginki kad’ai Jannah, matsayin yayanku kad’ai Jannah? I need more”

Bansan sadda na dago idanuna ina kallonsa ba, saboda furucinsa kasa jure kallon nashi nayi, na sadda kaina nace “nima kaina bansan iyakar adadin matsayin ka ba, ka dauka kana gaba da kowa”

Wannan maganar tayi tsananin tasiri akansa huci ya furzar yana shafa sumarsa, nai saurin cewa “dare yayi Yallab…….wayyo na mance wallahi”

Girgiza kai yayi kurin don yasan ba iya daina cewa xatai ba, “don Allah ji had’a mun oat nasha yunwa nakeji jann kamar zan mutu”

Idona na zaro “ba zaka mutu ba oat tayi kadan Yah, bari na had’o maka da indomi”

Ban jira cewarsa ba naruga nafice daga bangaren nashi, saida na saka doguwar riga na wucena dora mashi wani irin farin ciki nakejin kaina aciki, ban san meyasa ba amman ji nake bana cikin wani bacin rai, cikin kan kanun lokaci na gama naje na kai mashi lokacin har shabiyin dare tayi, tsareni yai wai bazan tafi ba saiya gama dukz spoon din dazai sai mun had’a ido, jinake kamar ina narkewa anan wurin daker yabarni na tafi.


“Yanzu ne lokacin da ya kamata muyi dukkan abunda zamuyi, shiyasa nace maku kudakata tukunna, komi daki daki ake binsa ba karamin abu ke sanya Abban ku yinma Asaad fad’a ba, banajin yadda yake kaunar sa yanajin sauran yaran azuciyarsa haka, rabin kadarar Abba sunan Asaad ne akai, ko duba cewar shima yana da tarin dukiya kamar ta kasheshi baiyyi ba, shiyasa a wannan karon nakeso na rabasu har abadan, ba Asaad ba haka ba usman ba kai bana jin ko hindu zan cigaba da zama da ita acikin gidan nan, Abban ku kissa da kisisina bata sanya shi kuka bata hana shi nayi hakan banga riba ba, wancen karon na had’a da malamai na kori ZUHRA DA HISHAM a wannan karon malamai ba zasu ci kud’ina ba duk da naga nasara, na tuba daga wannan hanyar makirci kad’ai ya isa Asaad da usman Jannah ce kaddarar su don haka ku saurara kuji yadda abun zai kasance………..momy don Allah komj zai faru kifara barina na lashe yarinyar nan, wallahi kullun sai nayi mafarkinta duk sadda idona ya ganta marata har daurewa take”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Leave a Reply

Back to top button