JANNAH COMPLETE HAUSA NOVEL

JANNAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Zaman me zanyi to? Kawai nima na bud’e zan fitan kenan naji ya rik’e hannuna sosai, saida na runtse ido saboda damkar da yai masa kamar zai karyani,

“Wayyo Allah na, hannuna zaka balla mun plz”

Na fad’a cikin jin zafin rik’on dayai mun,

“Rufe mun kofar motana”

Dole na jawo murfin na rufe na zauna inda nake, yana nan yadda yake tsawon lokaci baice komi ba, da kamar nai magana na fasa saida ya mulmule yace,

“Maimata abunda kika fad’a dazun”

Bai saki hannuna ba amman ya sassauta rikon da yaimun, gabana bugawa kawai yake sosai sai motsa baki nake na kasa cewa komi, saida ya sake cewa “kin zama kurma ne?”

Bansan manayi maganar cikin shagwab’a ba, “to Aidai kaji me na fad’a ko?kuma saina sake maimaitawa”

Ajiyar zuciya yayi yana yin kasa da murya, “kidaina mun shagwab’a please”

Yadda yayi maganar saida tsikar jikina tatashi,kunya ta kamani wallahi ban san nayi ba,

“hum inajinki maimaita mun”

Runtse idona nai sannan nace “nasan na maka laifi don Allah ka yafe mun, bansan mekake tunani akaina ba amman har cikin zuciyata ba ina nufin nai maka rashin kunya ba, Yah Asaad ka fahimceni please!”

“Abunda nace kenan fa”

Wata ajiyar zuciyar ya sake saki yace, “baki kai karshe ba ai,ba kince baki cikin hayyacinki duk kikayi ba? Meya jawo fita hayyacin???,”

Duburcewa nayi saboda sai yanzu naji nayi hauka amaganata dazun, ina in ina nace “Aa….dama…….daman ba haka zan…..zance ba”

Gyara zamansa yayi duk da d’an duhun dake wurin akwai dan haske kadan dayasa muka had’a ido dashi, saurin daukewa nai saboda kalar kallon da yake mun.

“Kina so mu kwana cikin motar nan?……..Aa don Allah wallahi bana so kayakuri”

Cizon lips dinsa yayi yana cewa, “ok kiban amsar tambayar danai miki yanzu nan”

Shashshekar kukan karya na fara ina cewa, “nifa ban sani ba, don Allah kayakuri Yah Asaad………….”ya salam! Jannah nace kibar yimun shagwab’a ko”

Tsitt nayi saboda ni nama mance, kuma ban sanin inayi na rasa meke damuna jinake kamar zan zare anan inda nake, cire F-cap din yayi yana cusa hannuwan sa cikin gashin kanshi,ya fesar da huci duk na tsorata cikin karma nace,

“Ka……kayakuri don Allah”

Muryarsa ta shak’e yace, “kiban amsar tambayata, meya kawo fitar hayyacin dazu? Tunda kince bakya cikin hayyacinki”

Jujjuya hannuna nake bansan me zance ba, duk abunda zan fad’a zai fallasani, zai tona mun asiri bacin ban shirya ba bana son ya fahimci cewar ina cikin wani hali akansa,

“Ohh my god, ba zakiyi magana bako?”

Yafad’a yana juyowa yana fuskantata idonsa sun wani juye, kusancin mu yasa kamshinsa kamar zai zautani, na matse jikin k’ofa ina turo baki nace,

“Nidai ka matsa to zan fad’a maka”

“Nak’i na matsa din, inbaki bud’e baki kin mun magana ba wallahi nan zaki dawo”

Ya nuna cinyarsa zaro idanuna nayi ina rufe bakina da hannu, gabana duka kurin yake ina rawar murya na b’oye fuskata cikin abaya nake cewa,

“To ba……bakai bane ba, ni….ni….natsani ganin ku tare, saita ta wani shige maka ko? Da safe ma ba haka ta ringa kama maka han…..hannu ba kuma ko hanata bakai ba, dazun kuma amota akan shoulder dinka fa…….na…..naganta…….sai kuka ya kubce mun,ina tuna yadda naji kamar zan tashi sama don bakin ciki, dunkulewa nai wurin ina kukana kasa kasa…………cikin wata voice dinsa mai gigita mace yace, “to kibar kukan please”

Makale kafad’a nayi murmushi ya saki yana sake cusa hannunsa acikin kanshi, jiyake kamar yana shawagi ne asama shikad’ai, kasa-kasa yake cewa “in bakiyi shiru ba nan zan doraki wallahi”

Wani abu na had’iye muk’ut dole na tsayar da kukan, inata jan ajiyar zuciya ga wata irin kunya dake shawagi dani, kamar na b’oye nakeji jinai ya kira sunana…………

“Jann”

Lumshe idona nayi na kasa amsawa, ya sake kirana still,

“Jann”

Daker na amsa can kasan makoshi, “uhmm”

Magana ya cigaba dayi cikin natsuwa da tausasawa, “yadda kika fita hayyacinkin nan dazu nima nafita nawa fiye da naki, yadda kike ji dakika ganmu da Aneesa jannah inajin fiye da haka idan na gankis da usman, taya kike tunanin zuciyata zata huta???”

Mom muhseen✍????
[8/23, 5:23 PM] Mom Muhseen????: ????JANNAH????

{A TRUE LIFE STORY}

E.W.F

By
Mrs Bb
mom muhseen

wattpad name
Humaira3461

    ????️.......24

  *MAI AFKUWA!*

Bakina yayi mun nauyi balle har na iya bud’esa nace wani abu, yaud’in tazo mun amugun bazata meke faruwa damu? Duk kauce kauce na wannan ita ake kira SOYAYYA yah salam! Daman haka soyayyar take, tabbas babu abunda yakaita zak’i, hakan kuma ba abunda yakaita d’aci da k’unci saboda murzar yatsuna da nake har sun fara mun zafi sosai…………..hannunwan sa kurin naga yasa ya rik’esu duka yana cewa cikin tausasawa, “karki jima kanki ciwo fa”

Tilas na kallesa shima yana kallon cikin idona duk yadda naso hana kwayar idona cigaba da kallonsa kasawa nayi, jinake kamar idan na daina kallonsa suma zanyi, yadda ya rungume hannun nawa kamar sune rayuwarsa numfashina kansa bana shakarsa yadda ya kamata, kamar wata maganad’isu ce take fizgata zuwa ga idonsa.

Tabbas idan bai amayar da abunda ke cikinsa ba zai iya ajalinsa, yana jin labarin soyayya kala daban daban amman bai san haka akeji ba saida ya d’ora idonsa akanta ranar farko, tunda zucuyarsa ta doka a lokacin har yanzu bata dawo masa yadda take ba, jin alamun zan anshe hannuwana yasa yaja wata ajiyar zuciya cikin disasshiyar murya yace,

“Please jann ki kasance dani har karshen rayuwata, duk randa na rasaki zan iya rasa rayuwata ganinki da wani namiji koba usman ba zuciyata ce take bugawa fiye da kima, inaji kamar na had’iyi raina! Yau d’in nan da ace bana tare dake bayan abunda ya faru zan iya zaucewa, please jann kice mun ba zaki sake sauraren sa ba”

Da fari kamar gizo idona keyi danaga kamar kwallace kwance cikin idonsa,sai danaji d’igarsu bisa hannuwan mu dake sarke yasa naji wani iri na runtse idona, har wani haki nake nace ina shafo ruwan daya d’iga kan hannuna,

“Yah Asaad minene wannan? Yah Asaad kamar kwalla kake fitar wa, don Allah kace mun ba hawaye bane ba karka saka na zargi kaina akan haka, Yah asaad ban cancanci haka ba nifa bakowa bace bakuma yar gidan kowa bace, meyasa zaka zubda hawaye akaina?………..nai idasa maganar inajin nima hawayen suna cika idona, makale d’ayan hannun nawa yai yana cewa.

“Ke kike ganin cewar ke ba kowa bace, sannan kin wuce duk yadda kike tunani azuciyana jann, tsoro nakeji ban tab’ajin tsoro irin wanda nakeji ayau ba,jinake kamar za’a rabani dake hankalina ya kasa kwanciya idan har ban amayar da abunda nake ta dakonsa ba yau bazan iya runtsawa ba kamar zai iya ajalina, ada ban shirya sanar dake halin da bake ciki akanki ba saboda burina kiyi karatu sosai zuwa lokacin zuciyarki zata iya daukar wannan nauyin da nakejin zuciyata dashi, sai naga ashe bazan iya hakuri ba,ashe kaunar da bake miki tafi karfin na iya sarrafata saidai ita ya sarrafani, inaso ki rik’e a ranki cewar duk runtsi bazan tab’a daina Sonki ba, don had’e yake da jinin jikina saidai idan nine na mutu…………..zuwa lokacin hawaye har bisa hijabina sosai nake shashshekar kukan, girgiza kaina nake cikin tsananin firgicin sauraren kalamansa, ina cewa “kadaina ambatar mutuwa bana sonta, bana kaunar ta dauke ka saidai ni ta daukeni, bana fatan ganin ranar har abadan, Yah Asaad bana ji araina zamu kasance tare bana jin cewar SOYAYYAR DA MUKE MA JUNA zatai kai mu ga nasara tsoro nakeji, Yah Asaad tsoron nakeji sosai araina akan zan iya rasaka akowane lokaci, bansan meyasa nakejin haka ayau d’in nan ba amman ina fatan koma menene karya rabani dakai, ayau na tabbatar ma kaina dacewar da kaunarka numfashina yake fita, duk bugawar zuciyata tare da Sunanka take bugawa a yanxu danasan matsayin da nake dashi a zuciyarka sai nakejin kamar nafi kowa sa’a arayuwata, ina rok’on alfarma agareka karkayi jinkiri wajen cikar burinmu, kaje ga baba ka nemi aurena hakan shine zai katangemu daga nesantar juna……….”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Leave a Reply

Back to top button