JANNAH COMPLETE HAUSA NOVEL

JANNAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Sai lokacin na d’ago daga sunkuyar da kan da nayi, kallon tsakar idona yake kamar yadda nake kallon nasa, ban san bakina yana magana ba nadaiji ina cewa,

“Jibi kenan yallab’ai, kuma zaka dad’e bakazo ba ko?”

Murmushi naga yana yi wanda yake jimawa baiyyi ba, sai sannan na tuna me nake fad’a na sadda kai ina wasa da yatsuna, nai tsittt saboda naji nauyin yadda nai maganar,

“Zan dad’e Jannah, nima kaina ban san yaushe zan dawo ba, kuma ji nake bana son na tafi kefa?”

Uffan na kasa cewa to mekuwa zance masa, bacin zahiri na gama nuna masa ban son tafiyar tasa,

“Ba zakice komi ba kenan”

Ahankali nace, “Allah ya kiyaye hanya ya baka sa’a”

Koma wa yai cikin kujerar ya jingina ya nuna man ledar kayan, “gasunan kije ki goge islamiyyar kuma ta yamma ce asabar da lahadi ne kurin”

“Nagode sosai yallab’ai ubangiji yai maka abunda kai mana, ya kara bud’i na alkairi ya kareka daga sharrin mai sharri”

Lumshe kyawawan idanunsa yayi yanajin matukar dadin adduar, ahankali ya amsa da amin,

Na dora hannuna kan handle din kofar zan fita naji ya sake kirana, dawowa nayi na durk’usa kasa,

Saurarensa nake amman baice komi ba har na gaji nace, “gani yallab’ai”

Iska ya fesar sannan yace, “kiyi nesa da khalid, bana son koda wasa wani kusanci ya shiga tsakanin ki dashi pls”

“Wallahi dazun ma shine………..bance ina son jin komi ba, na dai gaya mikine kiyi nesa dashi shid’in SHU’UMINE kiyi hankali”

Jikina yai mugun sanyi da abunda yake gaya mun, a sanyaye nace “insha Allah zan kiyaye kayakuri”

“It’s ok”

Na dauki jikkar kayan nai gaba karo mukai da Anty Aneesa zata shigo saurin jaa baya nai ina bata hakuri,

“Ke jakar inace bakya gani? Uban me kikazo yi nan?…………karki sake zaginta, Jannah!”

Na juya ina kallonsa yace, “wuce kitafi”

Ina had’e hanya na saka kai na fice jikina na rawa a haka na Isa daki na fada kan gado, wannan gidan akwai damuwa cikinsa, Ya Allah ka bani ikon kiyaye dukkan abunda aka umurceni, ka kareni daga dukkan sharri.

Kudai sake hkr dani pls????????

Mom muhseen✍????
[7/31, 11:33 AM] Mom Muhseen????: ????JANNAH????

{A TRUE LIFE STORY}

E.W.F

By
Mrs Bb
mom muhseen

wattpad name
Humaira3461

    ????️.......12

Kamar yadda nayi ma momy alkawarin zan ringa gyara dakin yallab’ai khalid, gari na wayewa ka sancewar lahadi ce na tafi wajen babaah uwani harta fara kokarin shirya karin safe, na wanke hannuna na kama mata munayi muna fira Irish ne muka fere da doya, duka soya su za’ai da kwai sai nafara kokarin yin hakan, sai ta ce mun “karki manta yallab’ai Asaad baya son dankali da kwai a had’e ki fara soya masa nasa daban, sannan ki soya sauran doyar kuma sai anyi masa yar miya da ita yake had’awa”

Na amsa mata da to, ni nake soye soyen ita kuma tana had’a costand da kunun alkama da kuma kunun gyad’a, ga wanke wanke harya tasu maiyinsa bata zo ba gashi da Momy tafito ta ganshi fad’a zatai,

“Wai nikam babaah uwani meyasa shukra bata kwana ne? Tana makara wajen zuwa kinga kuma aikinta yana bumatar sabko”

“Uhmm murjanatu kenan hakan taga yafiye mata alkairi shiyasa,”

Sai ban sake maganar ba saboda dai daji kasan akwai wani dalili mai karfi a k’asa, ina gama soye soyen tace akwai kaji da za’ai farfesu, a k’age nake na gama na fara share sharena dana tuna zanje dakin yallab’ai khalid hankalin tashi yake, ganin duk a rikice nake ina ta sauri tace “kinga jeki kifara aikin zan idasa”

“Yawwa nagode sosai babaah ta”

Tana dariya na wuce nai cikin gidan falukan na fara gyarawa duk da kuwa babu abunda sukai, kawai dai tsabar tsafta ce irin ta momy, ko na nok’e ince nayi zata gane don har lakutowa take ko zataji kasa kasa, don ma Allah yayi ni mai hanzari dan danan na kammala da falukan, kamar an jefo hindu sai gata ta fito da kayan islamiyyar ta kalar nawa ta wurgo mun,

“Yanzu-yanzu nake son ki goge mun su”

Dauka nayi kurin na wuce d’akina, taga abunda Anty Aneesa ke mun dole itama zata koya ai, na shimfid’a kayan gugar na zauna na gogesu tas daman jiya ban bacci ba saida na goge nawa, addua nake kar Allah yasa a jinmu guda da ita don bazan sake ba sosai.

Don sai goma muke tafiya islamiyar aida bansan ya zanyi da ayyukan gidan ba, inayi ina tunanin tafiyar yallab’ai a gobe dana tuna sai inji jikina duk yai sanyi,Allah ya sani ban son ya tafi ina kallonsa a matsayin bango majinginata, shine nake dan jin dadi idan ina tare dashi amman bacin shi duka ni tsoro ma suke bani, kayan na dauka na wuce inkai mata sauki na yau shukra ce zatai gyaran dakuna dakin yallab’ai ne zan gyara shi kuma ance sai ten yake tashi, kenan dai saina dawo daga islamiyyata sannan.

Kwakwansa mata kofar nayi tace na shigo, tana ta wayarta na aje kayan zan juya tace, “waye zai gyara dakin?”

“Shukra tana zuwa itace da aikin yau,”

Ina gama fadar haka na juya na fice bazan bari ta rainani har haka ba, idan Anty Aneesa tayi mani ita wannan ta kusan haihuwata ma ita kuwa inma ta girman yan watannine don ko shekara banajin ta bani, shirya dining nayi don in weekend ne su duka sukeyin breakfast a tare sai idan wani bai tashi ba, na kammala komi kan lokaci naje nai wanka nazauna ina shiryawa, hatta kayan shafata na musamman yallab’ai ya siyo mun, duk da iyayen kayan kwalliyar da nakeda su a dakin banayi, bana make-up ko kadan daga mai sai farar powder saboda rage maik’on fuska, sai fa turare shima d’in kadan nake sawa yadda ni kad’ai zanji, doguwar rigace akai min da hijab iyakar guiwa sai safuna da nik’ab, naji dadin nik’ab din sosai yadda zan rufe fuskata ba tare da mutane sun ta yimun surutun kyauna ba.

Kayan sunyi mun kyau ainun murmushi nayi yadda naga ina canza wa ahankali, duk da ba wani dad’ewa nayi ba kalaci naje na dauko nazo nayi anan d’aki na gama nafita da kwani kan, sannan na nufi cikin gidan, duk suna dining har da Abba yallab’ai khalil ya tashi shima yana a wajen, sai kuma yallab’ai Asaad.

Cikin girmamawa na risina nake gaida Abba da Momyn yace mun, “kece jannah kenan”

Ina durk’ushe kaina kasa nace, “ehy Abba nice”

“To sannunki girki yayi dad’i, sai islamiyya ko”

“Ehy Abba”

Kud’i ya ciro aljihunsa yana mik’o mun yace “ki hau abun hawa tunda da nisa”

kasa ansa nayi ina cewa, “Kabarsu Abba zanje a k’afa ma”

Momy ce tace, “ansa mana ana baki”

Na mik’a hannu cikin girmamawa na amsa ina godiya, har na mik’e naji yallab’ai khalid yace “momy baki gaya mata ta ringa gyara mun b’angarena ba?”

Gabana ya fad’i momyn tace, “jannah ya mukai dake jiya?”

Hankalina ya tashi nace, “kuyi hkr don Allah, babaah uwani tace mun sai goma keke tashi shiyasa na bari dana dawo saina gyara……………momy na gaya miki wannan yarinyar ta fara samun gindin zama, har ta isa asata abu tace saita dawo”

Kaina k’asa bance uffan ba, hindu tace “nima ai yau bata gyara mun daki ba wai ai shukra ce zatayi,”

Jikina rawa kurin yake saboda yadda suke ta magana cikin masifa, yallab’ai asaad kamar baya wajen shida usman, Momy ta aje spoon din hannun ta tace,

“Mena gaya miki randa kikazo? Bance miki muddin bakiyi ida aikin ki ba babu inda zaki ba?”

Muryata na rawa nace, “kin gaya mun don Allah kuyi hakuri”

“Maza kije ki idasa aikin sannan kitai makarantar tun kafin ki fara ganin b’acin raina,”

Ina rawar jiki nai hanyar dakin nashi injin kuka na son zuwar mun ina dannewa,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Leave a Reply

Back to top button