JANNAH COMPLETE HAUSA NOVEL

JANNAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Idanunsa kadai ka kalla zakaga tashin hankali baro baro, nuna kanshi yake yana sonyin magana ya kasa ya dad’e yana kakalo maganar daker ya iya cewa, “ni…….ni……zakima sharri Hafsat? In rasa wanda zanyi ma Fyad’e sai wacce nake kauna nake burin zamowarta uwar yayana,……tirrrr da halinki Allah ya tsine ma mai karya,Jannah ki gaya ma Abba idan har zan iya aikata miki wannan abun, wallahi tallahi Abba ko giya nasha bazan iya aikata fyad’e ba,balle akan Jannah wadda nakeji kamar numfashin…………………..jikake tas tas tas maruka sun sauka akan fuskar Asaad Abbane kuma yasauke masa su,kwallane suke kwarara daga idanun sa yake cewa “ka cuceni Asaad,ka kuma bani mamaki sosai! Ashe duk wannan haukar da kake ashe kasan abunda kayi? Tsakanina dakai Allah ya isa……….wani irin duka naji a zuciyata wace irin magana ce wannan Abba yakeyi? Ni nasan yallab’ai bazai aikata haka ba duk da cewar turarensa ne naji amman hakan bai saka naji cewar shine ba, kuka nake sosai ina rok’on Abba da cewa.

“Wallahi tallahi Abba ba shi bane, Yah Asaad bai aikata abunda kake fada b………..zaki rufe mun baki kosaina karyaki ko kuwa,ashe ke munafukace ban sani ba,ashe ba tun yanxu kuka saba shek’e ayarku ba sai yanzu kice mun wai bashi bane, hotunan su waye wadannan? Nace daku suwaye anan ehy?”

Ya fad’a jikinsa na rawa ya jefoni da wayar momy jikina wata irin rawa yake sosai na dauki wayar ina dubawa, wata kara na saki saboda ganin mummunan abunda ke faruwa acikin wayar, gadai Yah Asaad nan bisa ruwan cikina amman duk da haka wata zuciyar tawa bata yarda ba, wata irin bugawa kirjina yakeyi sosai komawa nai kamar wata zararra yaci gaba da cewa,

“Kingani KO baki gani ba,kun dauka duk abunda kuke bamu sani,zuwanki bangarensa cikin dare da abunda kukeyi a waje in kun fita, da duk iskancin da kuke mun sani daman wannan ranar mukejira asiri da asirinku zai tonu, don haka bake babu gidannan munafuka?”

Momy ke maganar tana mun kallon tsana, yah usy ne jikinsa ke kerma ainun yake kallon Yah Asaad bakinsa rawa yake sosai,yace “ashe dai ka tabbata kaine makaryacin, ga dai gaskiya tayi halinta ashe dai dagaske maha’incine ka kawo yarinya don ka lalatata…………bugun da Asaad yake masa yasaka kowa ya gigice don kamar Asaad ya haukace yake dukansa yana kuka, daker khalid da Abba suka raba su, tsawar da Abban ya daka masu yasa suka natsu yana layi juwa na daukarsa, muryarsa na rawa yake cewa cikin karyar yayyar murya.

“Bansan haka kake ba, bansan zan fuskanci matsala daku ba, ina maka kallon nagartacce kamilallale, ashe daga bayan fage kai d’in ashararine ban sani ba, ka cuceni Asaad amman bazan maka baki ba inaso dai dakai da kannan ka kubar gidan nan yanzu, nagaji da masifar yayan ZUHRA shi wancen dan shaye shaye ne har yana dokar mun mata, kai kuma duk yan aikin gidan nan kakebi kana lalatawa ban sani ba, na tsaneku ku duka bana son sake ganinku a rayuwata, ku dauka bakuda uba kema karna bud’e idona na ganki bakar munafuka ashe ke maha’inciya ceke, karna sauko na sake ganin fuskokin ku……………………

ANAN NA KAWO KARSHEN LITTAFIN JANNAH BOOK ONE, GA DUKKAN MAI SON CIGABAN LABARIN ZAI BIYA DARI UKUNSA KACAL TA WANNAN HANYAR

3150952555
First bank
Aisha Abubakar

Idan ka turo saika turo mun shaidar biyanka ta wannan lambar 09034722970.

Masu turo katin waya kuma zaku iya turo MTN KO AIRTEL na dari ukun ta hanyar wannan lambar
09034722970.

karki bari abarki a baya domin akwai sauran rina akaba,akwai sauran daru sosai ki hanzarta ki mallaki naki.

Ina godiya ga dukkan masoyana na kusa dana nesa????????

Mom muhseen✍????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37

Leave a Reply

Back to top button