JANNAH COMPLETE HAUSA NOVEL

JANNAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Silalewa k’asa Asaad yai yana saka kanshi cikin kafafunsa yana kuka kamar wata mace, abun duk wanda yagani duk taurin ranka saiya tab’a maka zuciya shiyasa har Abba saida ya share kwallah, tare suke da Hindu itama ta isa jikin yayanta tana kukan, doctor dince tace “please kuyi hkr na dubata kuje daga waje”

Fitowa sukai daidai isowar usman ganin kowa na kuka hankalinsa yai mugun tashi, ya dauka mutuwa Jannah tayi jikinsa na rawa yake ma hindu magana, “Hindu meyafaru? Jannah tafarka ne? Don Allah karkice mun mutuwa tayi don Allah kice mun tana nan da ranta…………saidai yaji Asaad kamar daga sama ya kaimasa wata shak’a yana dakashi ga bango yace, “karya kake Jannah ba zata mutu ba, zata cigaba da rayuwarta insha Allahu”

Usman bai wata wata ba shima ya cakumi wuyan Asaad yana haki yace, “kaine kake karya bani ba, pretending kurin kakeyi waya sani ma ko kaine ka jefata wannan hal…….jikake tas tas tas cikin wata kalar zuciya Asaad ya kwasa mashi marika,yana yin jifa dashi gefe yana huci zuciyarsa kamar ta fito, da gudu Abba ya iso yana salati.

“Menake gani haka Asad? Usman kunyi hauka ne? Yau junan ku kuke fada akan Mace? Innalillahi wa inna ilaihir raju’un”

Daidai zuwan su momy da fareeda da Aneesa, Abba kwalla sun cika idonsa yace, “Abunda baku yi kuna yara ba shine kukeyi da girman ku, mace zata had’aku Asaad? Usman akan kace kake cinkwalar yayanka? Hafsat kina ganin abunda hake faruwa kuwa? Fad’a suke da juna akan Jannah hazbunallahu wani imal wakil”

“Abba bakaji me yake fad’a ba, gabanka fa yake kiran mutuwa zatai? Wallahi ina tantama idan ba usman ne yai wannan abun b………..karya kake munafuki kaine babban wanda za’a zarga adaren ranar ina kaje har karfe shabiyu? Ba kana tare da ita b”…………wani kukan kura Asaad yai ya dira saman usman dukan sa kurin yake yana zubda hawaye, yama kasa magana bakin cikine kamar zai kasheshi……..Abba kanshi hankalinsa yai mugun tashi yana kokowar rabasu ya kasa momy na gefe tana kyalkyala dariya ita da fareeda, duk abunda suke Hindu na kallon su da taimakon wasu maza Aka samu aka raba Asaad da Usman, don har bakin usman da hancinsa sun fashe kowa huci yake kamar wasu zakaru, Abba ya zama abun tausayi yake magana.

“Idan Kuka sake wannan fadan ban yafe muku ba Asaad da usman, ni zaku kunyata cikin taron mutane? Mace zata had’aku fad’a ban tab’a ganin ranaku masu munin wad’anan ba”

Momy ta tako cikin makirci tace, “kayi hakuri Abba, harda kuruciya kai Asaad ai babba ne bai kamata kabiye ma kanen ka ba, kuma inhar kasan bakai ba miye na tada jijiyar wuya…………idanunsa kamar zasu fad’o yace “meeee? Mekika kace? Sake maimaitawa”

Kauda kai tayi tana jan hannun Abba tana cewa, “karka biye su hawan jinin ka ya tashi,idan mun koma gida sai ayi wacce za’ai”

Wani irin duka ya kaima bango jiyake zai iya kashe matarcan kowa ya huta,shi zatai ma munafurci so take ta juye laifin kanshi ga dukkan alamu kuwa, amman Ai Abba ba haukacewa yai ba kuma shima da nashi hankalin,itama Jannah tana cikin hankalinta koma miye gaskiya zatai halinta,yayi imanin Khalid zai iya wannan abun inbashi ba kuma tabbas usman ne,don jikinsa na bashi abun baya wuce su biyunan,.

Suna nan tsai tsaye don zaman ma kasa yi sukai Asaad da usman, momy da fareeda firarsu suke afakaice Hindu kallonsu kurin take gaba d’aya bata yarda dasu ba, zuciyarta tana bata cewar 100% suna da hannu aciki,amman bata da shaida bata da hujja ba zata iya yin wani abu ba.

A daidai nan doctor suka fito ita da wasu nurses ta zare glass d’inta tana kallon Abba da Asaad, tace “Daman na gaya maku dole zata shiga cikin firgice da dimaucewa,wannan halin da take ciki tana iya daukar dogon lokaci tana cikinsa yanzu dai tana bacci zuwa yamma allurar zata saketa ina fatan ace ta samu sassauci ko yayane, kuyi mata addua a ruwa idan tatashi sai tasha,don Allah banda hayaniya bisa kanta kubita ahankali ta dawo hayyacinta koma me kukeso kuji daga gareta”

Usman gumi kurin yake yana jin kamar yaje ya goge mata abunda ke ranta daya jefata cikin wannan halin, juyawa yai ya koma yaje ya had’e kanshi da guiwa kurin.

Godiya Abba yai mata yana dafa kafada Asaad cikin damuwa yace, “zan dawo da yamma din, don Allah ka kwantar da hankalinka kajiko”

Jinjina kanshi yake sannan yace, “zanje wajen baba malam na amso mata rubutu yanzu”

Jinjina masa kai yayi alamun goyon baya, da maganar dayai, (Baba malam kakan su ne daya haifi mahaifiyarsu)

Su momy Abba suka bi akabar usman nan da Babaah uwani, Asaad Mannir ya kira yazo ya daukesa suka wuce Tudun yola daman yana yawan zuwa gaidashi kuma yana aika masa da alkairi, koda ya isa baida shamaki zuwa dakin malam d’in, bayan ya gaisa da tsohuwar gida ya samesa yana rubutu jikin Allo, koda Baba malam ya soma tambayar abunda ya samu Asaad din kuka ya sanya mashi kurin, saboda duk wanda zai ganshi dole zaisan baya cikin natsuwarsa da hankalinsa, saida yasha kukansa sosai sannan yake labarta mashi abunda ke faruwa, shima kanshi Baba malam din ya girgiza sosai hakuri ya bashi yana kuma yi masa nasiha sannan nan take ya hauyin rubutun da kanshi,ya kwashe minty arba’in ina rubutun sannan ya gama yai tofi acikin ruwan bayan ya wanke rubutun, sannan ya daure mashi ga leda yana cewa.

“Insha Allahu Zata samu sassauci daga halin data shiga,ko yayane zata samu natsuwa da dangana sannan bayan kwana biyu ka sake zuwa ka amsar mata wanu rubutun, Allah zai saka mata hakuri dole abun akwai rikitarwa”

Sadda ya dawo anyi la’asar yaje yai salla ya dawo inda yabar usman nan ya iskeshi,ko kallon sa baiba da Babaah uwani kurin yai magana zuwa can mannir ya dawo da take away ya aje gabansa, leda biyu yaba Babaah uwani yace “kici guda dayar idan tatashi sai taci”

Godiya tai masa tana jin tsananin tausayinsa ganin ga usman shima tun sha daya na safe yake nan zaune, tace “ko na bashi nawa idan naje gida sai naci wani aabun”

Nashi ya dauka ya bata yace “ta mik’a mashi”

Inda yake ta isa tana durkusawa tace cikin sanyin rai, “usman tashi kaci abinci kaji ko,sai kayi salla ko azahar bakai ba kana nan tun dazu”

Tabbas yanajin yunwar don haka dole ya ansa yana mata godiya tace, “yayanka ne ya kawo mana”

Yasan kowane yayan take nufi sai baice komi ba,daukar ledar yai yana nufar hanyar waje ko kallinsa Asaad bai ba harya fice, anan wajen Babaah uwani taci abincin sannan take masa nasiha tana kokarin nuna masa yarda da kaddara da kuma hakuri,karya biyewa zuciya itace ke kai mutum ga dana sani karka sake tanka kanenka don Allah”

Lumshe idonsa yai shikad’ai yasan halin da yake ciki, zuciyarsa jiyake kamar ta tsage saboda ciwon da yakeji a cikinta, suna nan zaune nurse ta fito tana cewa,
“Kune masu jinyar Murjanatu?……….ehy mune tafarka ne?”

Cewar Asaad cikin sauri tace, “ehy tatashi kuzo ku bata abinci kitai maka mata tayi wanka da sallah ta canza kayan jikinta”

Jikinsa rawa kurin yake yace, “Babaah ga wannan ta fara shan shi don Allah,bari naje na samo mata kayan sakawar”

Yadda yake b’arin jiki dole ne ya baka tausayi ainun, Babaah uwani tawuce cikin dakin cikin fargaban halin da zata isketa,kaina had’e yake da guiwata ba abunda idona ke tsiyayawar sai hawaye banda karfi ko kadan jikina shiyasa kukan kanshi babu sauti yake fita, ban zaci zan sake bud’e ido na ganni a duniya ba banso ace na farka ba daman sadda zan farka in ganni cikin kabarina,muryar Babaah uwani yasa na dago da kaina kwalla akan fuskarta ta zauna gefena cikin lallashi da ban baki tace, “Murjanatu na kiyi hakuri kinji ko, babu wanda yake tsallake kaddararsa, karkiyi jayayya da Allah ki amshi jarabawarki da hannu biyu ki kuma gode masa, kowa yasan an zalinceki amman ya zamuyi to? MAI AFKUWA ta riga ta faru bamu isa mu gyara ba kuka da iface iface bazai kawo miki komi sai tarin kunci da bakin ciki, don girman Allah murjanatu na kiyi hkr, Allah baya bacci haka kuma baya zalinci kuma baya son maiyinsa,ina mai tabbatar miki watan watarana zakiga sakayya kisa aranki cewar duk inda kike Allah zai nuna miki irin hukuncin da zaiyima wanda ya aikata wannan abun, da wanda yabada goyon baya da wanda yasani kowa zai fuskanci kalar abunda ya shuka,kuka dolene kiyi muma masoyanki munyi maki balle ke,don haka bazan hanaki kuka ba amman ina baki hakuri kiyarda da hukuncin Allah,anshi nan kishanye muje na taimaka miki kiyi wanka sannan kiyi sallah ki kai karar duk wanda keda sakaa hannu acikin wannan ta’addancin, Allah yana gaggawar amsar adduar wanda aka zalinta”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Leave a Reply

Back to top button