JANNAH COMPLETE HAUSA NOVEL

JANNAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Zuwa karfe bakwai da rabi Anty ta dawo drivern dake daukar su shareefa ya iso ya daukesu, inta duba time saboda makara in ka makara wankin toilet ake saka mutum, ni kuma bana so saboda kyankyami nake Antyn tace “lafiya usy baizo ba har yanzu”

Cikin damuwar hakan nace “wallahi kuwa Anty ko zaki kira mun shi pls………..ban ma idasa maganar ba sai gashi yai sallama kananun kaya ne jikinsa ash din sheet sai farin jeans yai kyau ainun, lumshe ido nai ina mik’ewa yace “Anty ina kwana kunjini shiru ko?”

“Da yanzu zan kiraka naji ko lafiya”

Kanshi yake shafawa yana murmushi yace, “makara nayi yau wlh, muje rankiyadad’e”

D’an zaro idona nayi kannemun ido yayi yana cewa “saimun dawo Anty zan dawo na karya banyi break ba”

Ta amsa masa cewar saiya dawo d’ina muka fice ina niye dashi nace, “yah usy babba dakai kana makara”

Wani kallo ya jefoni dashi yana cewa, “ki rantse kema yau baki makara ba”

Yar dariya nake bayan ya bud’e mun motar zan shiga nace, “aini in na makara ba laifi akan ka,”

“Saboda ni ba dan adam bane halan?”

Rufe baki nai ina dariya kadan nace, “Aa wallahi ba haka nake nufi ba, kawai dai shikenan abar zancen”

Fita mukai muka dauki hanyar makaranta kamar ba zamuyi magana ba zuwa can nace,
“Yah usy jiya………..Bros yakira ni jiya har five missed call ban Sani ba, sai yau da safen nan ma naga kiran, nasan duk inda hankalinsa yake yana nan na kirasa ban samu ba”

Lumshe idona nayi ina cewa, “abunda zan gaya maka kenan nima, na dawo na iske kiransa da wayar daya ban, na bi kiran alokacin ta shiga amman har sau uku ba adauka ba, da safen nan nasake kira ance kashe yah usy duk na damu wallahi”

Kauda kai yayi kadan kamar baiji me nace ba, tukinsa kurin yake daker ya amsa mun da cewa, “don’t worry, nasan inhar ya samu kanshi zai sake nemana me zan gaya mashi?”

Ina murmushi nace, “kawai dai kace ina gaida shi……..kuma kinyi kewarsa sosai hakane ko?”

Na zaro idona nace “Aa yah usy ba haka nake nufi ba, ba sosai ba kawai dai da baya nan d’in duk……….bakijin dad’i da baya nan?

Dafe kai nayi ina cewa “Aa yah usy, bansan ma me zance ba kawai dai ka gaidasa sosai shikenan”

Fuskarsa dan danan ta nuna b’acin rai har muka iso makaranta bai ce mun komi ba, hakan dana lura yasa na kifita ina kallonsa,shi kuma yana kallon side din tagar da yake zaune nai gyaran murya don yajuyo nace,”kasan me yah usy?”

Bai waigo ba ya amsa da cewar, “Aa saikin fad’a”

Na b’ata fuska ina cewa, “saika jiyo kozan fad’a”

Jiyowar yayi yana kallona idonsa yai wani kala, nace “fushi kake ko?”

Lumshe idonsa yai yana amsa mun kamar baida lakka,”ehy fushi nake menene?”

Nai kicin kicin da fuska nace, “to menai maka? Daga yin magana shikenan sai fushi,nifa ba ina nufin banjin dadin kulawarka ba”

“Naji kije karki late”

“Korata ma kake yi ko? Shikenan nama fasa yin abotar, ina son nai maka albishir cewar na amunce da friendship din amman kake fushi”

Na bud’e na fice inajinsa yana kirana ko waigowa banyi ba, da yar class dinmu muka had’u sai muka wuce assembly kawai.


Banjira ya zo daukata ba ina da kud’i a hannuna sai kawai na hau napep ina adduar Allah yasa na gane gidan, cikin ikon Allah na gane hanya na sallamesa na shige ciki tun a compound d’in gidan inda asuke parking mota naga alamun kamar anyi bak’i, sabuwar motace da ban saba gani ba nagani a cikin parking space d’in, sai na tsinci zuciyata da mugun bugawa ras ras har naji k’afafuna sun kasa daukata, adaddafe na k’arasa bakin k’ofar falon tun anan naji wannan mayataccen turaren wanda kullin nake burin mallakarsa duk da kasancewarsa na maza,wani irin dokawa kirjina yai na had’iye miyau muk’ut na saka kaina cikin falon tare da sassanyar sallamata abakina, ilai kuwa sai gashi idona yai mun kyakkyawan gani wani irin sanyi naji yana ratsa zuciyata da ruhina, yayinda na kasa dauke idona daga kallon da yake mun, fuskata cike da mamaki da kuma tsananin farin cikin ganinsa saidai abun da ya fadar da gabana yana yin kallon da yake mun shine yasa guiwata sacewa, cikin sand’a nake tafiya ina ta yak’e ga yah usy nan zaune shima wayarsa yake dannawa kamar baiji sallamata ba, Anty ce ta fito daga corridor maganarta ce ta tsinke mun halin da nake ciki

“Aaa jannah kin dawo, yanzu nakema usy maganar daukoki sai gaki”

Muryata kanta kerma take nace, “ehy ganin inada kudi yasa nace bari na huttasheshi, Anty ashe bak’o mukai”

Na fad’a ina satar kallonsa murmushi tayi mun tana cewa, “gashi kuwa kin gani,muma kawai saidai muka ganshi”

Tana wuce wa kitchen, inda yake na d’an matsa na durk’usa ina cewa, “yallab’ai ina wuni, barka da isowa”

Kamar dai yadda ya saba lumshe idonsa yayi yana amsa mun kasa kasa,
“Thank you ya school din,?”

“Alhamdulillahi yallab’ai komi lafiya……….jeki had’o kayanki mu wuce gida”

Naji maganar kamar daga sama, duk da nasaj cewar yaud’in zan koma amman miye na gaggawa haka? Acikin maganarsa akwai wani abu bansan menene ba, a iyakar tsawon lokacin daya dauka baya nan ban zaci idan ya dawo zan samu wannan tarbar ba, sai na mik’e kurin daker na iya amsa mashi da cewar, “to yallab’ai”

Ganin yah usy kamar bai ganni ba yasa nace masa, “yah usy ba magana”

Murmushi yai mun kurin baice komi ba, duk naji babu dad’i jikina yai mugun sanyi sai na wuce kurin na fara kokarin cire kayana, wanka na shiga anan naga mp dina yazo sai na fasa yin alwallar na fito kurin, gaba daya kasala ta sauko mun banji dadin tarbar dana samu daga wajensa ba, to meyafaru? Ni kam dai bansan ma da zuwansa ba balle nayi masa wani laifin, kila don ya kirani ne ban dauka ba to amman ni kira nawa nayi masa a time din dana gani,haka naita sake saken zuci har na gama shafar na saka auduga na gyare jikina nasaka turaren da yah usy ya siyo mun rannan, doguwar rigace jikina ta kanti pink and golden ce sai zanen flowers da stones ajikinta hijab na saka iyakar guiwata, na hada kayana daman sauran abunda yake nawa na idasa had’awa karnayi mantuwa, ina cikin tattarawa naji vibrate din wayata saurin dauka nayi hannuna har yana rawa nace, “Assalamu alaik………..had’a kayan ne yake da wannan jinkirin?”

Abunda naji yace kenan ko sallamata ban idasa yi ba, na lumshe idona kamar nai ihu nace “kayi hkr yallab’ai gani nan……..naji kitt ya kashe wayar numfashi najaa nai saurin had’a komi na dauki jikkar da school bag d’ina na fito, afalo na iske antyn inata mata yak’e nace “Anty zan tafi, nagode sosai da kulawa Allahu yasaka da alkairi, idan Abban su Shareefa ya dawo ace ina masa godiya sai watarana”

Rungumeni tayi cikin rashin jin dad’in tafiyata tace “ba yadda banyi da asaad yabarki nan ba yakiya, ki kula da kanki jannah kinjiko Ki dage da addua Allah ya kareki, Allah ya sadamu da alkairi”

Kwalla ne suka silalo mun na goge nace, “nagode sosai, mun tafi”

Na zame jikina daga nata nabisu wajen tunda daman tuni sun fice, ni kamar sunyi rigima ma nagani kowa fuska daure babu fara’a ko k’adan nidai shiga baya nayi yah usy ne yaja motar muka d’auki hanyar gida, tunda muka tafi babu abunda bake sai addua don ji nake hankalina yana tashi ainun tsoro yana kamani, mun dad’e a hanya kafin muka k’araso gidan jinai kamar na juya na koma saboda gabaki d’aya tsanar gidan da mutanen cikinsa nake, kwata kwata hankali baya kwance, dole na fito na dauki jakata ina biye dasu har cikin babban falo, kamar anyi shelar dawowata kaf d’insu suna falo don time d’in anyi sallar la’asar, idona cikin na momy duk nabi na tsure mai makon naga ta mako mun harara, sai naga tsananin murmushi akan fuskar ta daidai sadda Abba ya shigo shima, ashe duk basu san da dawowar yallab’ai ba yadda naga Abba na murnan ganinsa ya tabbatar mun irin yadda yake ji da Yallab’ai din, momy sai fara’a take tana nan nan dashi Aneesa kuwa kamar taje ta fad’a jikinsa, hindu da gundun ta fada jikinsa tana masa oyoyo sai yanzu naga murmushin sa da fara’ar sa, har gaban Abba naje na risina ina gaidashi yana cikin annashuwa yace,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Leave a Reply

Back to top button