JANNAH COMPLETE HAUSA NOVEL

JANNAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Tajuya ta cigaba da tafiyarta kallon kaina nayi inga abunda take yamutsa ma fuska,kila kod’ad’d’un kayana take kallo,ko kuma kod’ad’d’sr fuskata data kod’e da kuka,na juya na dawo wajen yayanmu na gaya mashi yace,

“Ai ba zamu koma ba murja jiransa zamuyi, in muka tafi bamu san ya dawo ba ko bai dawo ba”

Zama mukai kowa da irin kalar tunanin da yakeyi, ni kuma na tafi wata duniyar ganin yadda rayuwa take juyawa damu, araina inajin ya dace ace mun samu wani canji da cigaba haka nan, wannan rayuwar k’uncin ta isa haka nan to amman tayaya? Na girgiza kai kurin saboda banga ta inda zamu kama ba, munfi karfin awa guda anan ni har bacci ya fara figata kamar cikin mafarkin naji wani hamshak’in k’amshi kamar na yan aljanna ya surbud’a cikin hancina, a firgice na bud’e kyawawan idanuna ina duba ta ina naji wannan k’amshi, idona ya sauka kan wasu mutane maza guda biyu daidai bakin k’ofar ofishin likitan,

“Kinga murja ya dawo, Alhamdulillah”

Inji yayanmu kallonsu nake tayi saboda ba ko musu cikin su wani keda wannan kamshin kamar na yan gidan aljanna,inata tunanina har suka shige suka barmu nan.

“Ke kina Lafiya kuwa?”

Nai saurin juyowa ina kallonsa nace, “yayanmu wani kamshi naji kai bakajiba?”

Dogon tsaki yaja yana figar hannuna muka doshi ofis din likitan, kwankwasawa mukai yayin da nidai gabana yake fad’uwa,addua naci gaba dayi inajin wani irin fad’uwar gaba bansan ma ambamu iznin shigaba saida naji yayanmu yajani mun shiga.

Wayyo Allah na sanyin naji mai dankaren kamshi yana ratsani, da alama suna cikin na’ura mai sanyaya jiki,kamar daga sama naji likitan yace,

“Malamai lafiyarku? Mekuke nema?”

Jikina yai sanyin bala’i yayinda gudan dake zaune kujerar dake kallon likitan ya kafeni da ido ta cikin bakin glass d’insa, duk da banganin kwayar idonsa nai imanin kallona yake, shiyasa gabaki d’aya naji ina kerma yayanmu ne yai karfin halin cewa,

“Likita mune muka kawo babanmu mai ciwon daji jiya, wanda kace aiki za’ai mashi sai mun kawo miliyan biyu………..ok ok ok na gane kun samu kudin ne?”
Ya katse sa da fadar hakan yayanmu yana rausayar dakai cike da halin fargaba yace,”ehy mun samu d’an abun……………to ai banan zaku kawo ba can wajen biyan kud’in zakuje da katin dana baka jiya ku biya sai mu sanya lokacin aikin”

Tsaye mukai nidai sai rab’e rab’e nake saboda har sannan kallona wannan mutumin keyi, cikin in ina yayanmu yace masa “lik…..likita dama…..dam…..daman kud’in ne bas…….basu kai b…………..what!!! basu kai ba shine kuka dawo? To uban me zan maku da kuka dawo mun? Kaga malam please work out, daga nan zuwa gobe indan baku kawo su complete ba zamu tattaraku da tsohonku kuyi gaba”

Wannan abun yasani sakin rigar yaya kuka ya kubce mun, ban san sadda na isa garesa ba na duka na rik’e kafarsa ina kuka sosai ina rok’onsa cikin rauni,

“Likita kar kayi mana haka, kaji kanmu ka tausaya mana wallahi tallahi gonakin mu aka siyar har biyu daker muka samu wadannan, bamu da kowa ba muda wanda zai taimake mu sai ku,ka rufa mana asiri ka anshi kudin haka wallahi bamu dasu bamu san inda zamu samu su ba kataimake…………..keeeeee!!!”
Ya runtuma mun wata tsawa data saka na zabura na mik’e ina kerma,ruwan hawaye yana layi akan fuskata kamar an kunna famfo,

Cikin fusata da fushi ya nuna hanyar fita yace,
“Ku fice mun anan kafin na kira afidda ku, karki sake tab’ani inba so kike na b’alla ki ba, oya get out of my office”

Yayanmu yai saurin kamoni muka fice daga cikin ofishin, kasa isa wajen su innamu mukai na yanke hanya na zauna na cigaba da kuka iyakar iyawata, shi kanshi yayanmu zama yai ya saka kanshi cikin guiwa nasan kukan yake don dai karna ganine kawai.

“Doctor Ashir meyasa kake treating mutane irin haka? Kodan ka gansu cike da talauci? Ban san sai yaushe zaka canza halinka ba don inhar ka cigaba da haka watarana zakai dana sani……………….dakata mun ASAAD! wai kaine kake ma wani nasiha? Tabdijam to ka fara ta kanka kafin kazo kaina, idan ma ana neman me wulakanta mutane irin wadannan aikai kafi kowa suna,sannan kace zakai mun fad’a akan me”

Cikin b’acin rai Asaad ya kauda kai yana shanyewa ya mik’e kurin yana cewa, “ni na biyoka har office dinka shiyasa kake da right din da zaka wulakantani, sai anjima”

Ya fice kurin ba tare da yasake tankawa ba ko ya kallesa,cikin takunsa na kasaita da natsuwa ya fito daga hanyar office din ashir anan yaci karo damu kuka kurin nake har muryar bata fita sosai ba abunda nake cewa sai surutu barkatai,

“Allah karka barmu a haka,kaga halin da muke ciki bamu da wani karfi sai naka,ya Allah ka taimakemu ka kawo mana mafita, bayinke ne masu bauta ma ba dare ha rana ya Allah karka bari a wulakanta mu,ka taimaki bawan ka dake kwance baisan inda kanshi yake ba……………tsitt nayi saboda wanan kamshin da naji dazun ya dawo mun, jinsa nake akusa dani kamar ni na sanya shi ajikina yayin da naji kamar an tsaya gabana inajin kamar wani ne yake bisa kaina,fuskata tai kaca kaca da hawaye ja dago ina kallon gefena, tabbas kuwa mutum ne kafafu na gani sanyi cikin sawu ci bakake, hadaddu irin na yangayu saurin daga kaina nai sama yayin da mukai cikekken ido hud’u da wannan mutumin na ofis din likita,zabura nai na tashi zan ruga yayanmu ya dago yana mun magana,

“Menene murja?”

Hannuna kurin nake nunawa inda mutumin yake tsaye ya rungume hannuwa ga kirjinsa, jikinsa manyan kayane farare harda babbar riga kanshi da hula k’ube, inka gansa zakace balarabe ne akwai da haske da kyau, yayanmu ne yace “yallab’ai lafiya dai ko? Tayi maka wani abunne? Kayi hakuri bata cikin natsuwarta ne, kanwata bata da neman rigima”

Murmushi yaga yana yi kafin ya gaji da shan k’amshin yace, “ko zaku biyoni muyi magana”

Kallon juna mukai nida yayanmu kafin muka maida akanshi ya jinjina kai ya sake cewa, “Bismillah, karku damu ba dan yankan kai bane”

Sai sannan yayanmu ya rik’o hannuna muka bisa kamar jela.

Mom muhseen✍????
[7/19, 7:40 PM] Mom Muhseen????: ????JANNAH????

{A TRUE LIFE STORY}

E.W.F

By
Mrs Bb
mom muhseen

wattpad name
Humaira3461

    ????️.........4

Bayan mun fito wajen da ake ajiye motoci driver ne aciki yana jiran fitowarsa isarmu kenan cikin azama direban ya fito ya bud’e masa motar yana risinawa,

“No ba tafiya zanba”

Ya maida kofar ya rufe da kanshi ya zagaya can wajen zaman driver ya dauko wani d’an littafi siriri dogo ya ciro biro daga cikin aljihun sa yana kallon yayanmu, har sannan da glass a idonsa kuma duk sadda ya kallan sai naji zuciyata ta dage ta buga bansan dalili ba,

“Ya sunanka malam?”

Ya tambayi yayanmu wanda shima sai kallonsa yake kamar yadda bakeyi, cikin sauri yace “sunana sulaiman amman sale ake cemun”

Jinjina kai yayi sannan yace mun,”kefa?”

Kamar wata doluwa na nuna kaina da hannu nace, “ni?”

D’an guntun murmushi yayi sannan ya daina ya sake cewa, “ehy ke”

Na rausayar dakai nace cikin sanyin murya, “Sunana Murjanatu”

“MURJANATUU”

ya fad’a ahankali iska ya fesar sannan yaci gaba da magana wadda na lura tana masa wahala yace,

“Kunzo da wani babba ko ku kad’ai kukazo?”

Yayanmu yace, “harda mahaifiyarmu muke suna daga can baya da dayar kanwar mu”

Maida dan littafin yai aljihu yana cewa, “ok muje wajenta sai muyi maganar acan”

Cikin yan mintuna muka iso inda su innamu suke tana ganin mu ta mik’e cikin mamaki, bai bata damar magana ba ya gaidata,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Leave a Reply

Back to top button