JANNAH COMPLETE HAUSA NOVEL

JANNAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Suffing din tea din yake ahankali duk munyi tsit bakina ya rik’e ko gaidasa na kasayi, daker na had’iyi yawu ina sake sauke kaina kasa nace,

“Ina kwana yallab’ai?”

Lumshe idanun sa yayi ahankali sannan ya amsa da cewa, “lapia lau jann ya kika tashi”

Muryata ta mak’ale can ciki daker na amsa masa da “lafiya lau”

“Kinyi kalacin?”

Na girgiza kai nace “Aa yanzu zanje inyi”

Cup din hannunsa ya mik’o mun,sai sannan na dago kaina muka had’a ido, jinai tsigar jikina tatashi sosai idona yai rau rau da sauri na sauke idona k’asa, tunda nake dashi ban tab’a ganin abunda nagani acikin kwayar idonsa ba, sake mik’o mun yayi sai na amsa na rik’e cup din ga hannu na kasa kaiwa bakina, ganin ina b’ata lokaci yasa na fara kurb’a ahankali inajin kaifin idonsa akaina saida na shanye sa sannan yace “kije ki karya to”

Harna fita inajin idonsa akaina, duk yadda naso nayi kalacin sosai kasawa nayi, lokacin dana fito da shirina da school bag dina a rataye duk wanda ke dining din kwalalo mun ido yayi, duk naji na duburce gaba d’aya jikina yana tsuma nake gaida momy kadaran kadahan ta amsa mun, Abba ne kurin ya iyamun magana bayan dana gaidasa.

“Jannah sai makarantar ko”

“Ehy Abba insha Allahu”

“To Allah ya bada sa’a, Asaad muje na taka maka wajen mota”

Momy kad’ai ta iya cewa “Asaad Allah ya tsare yabada sa’a sai munyi waya”

Da kai kurin ya ansa mata hindu tataso tazo ta rungumesa tana hawaye, “Yah Allah ya tsare hanya, don Allah kayi hkr idan kana fushi dani”

Bubbuga bayanta yake yace, “don’t worry Hindu bana fushi dake, fatana dai karnaji karna gani kinajina”

Ta d’aga kai sannan ta cikasa Aneesa na rik’e da jikkarsa akwatinsa tuni ansaka shi a but din mota,shida Abba sun dad’e suna magana daga can gefe driver yana cikin mota shida yaya usman sai ni a baya, Anty aneesa na jikin motar tana jiran yazo.

Glass din tagar danake zaune wurin rabinsa a k’asa yake, so duk abunsa Anty Aneesa ke fad’a ma yallab’ai asaad bayan barinsa wurin Abba, ko kunya bataji ba yana karasowa ta fada jikinsa ta rungumesa sai shagwab’a take masa, saurin cireta daga jikinsa yayi “ki koma cikin gida lokaci yana tafiyar”

“Asaad don Allah ko sau d’aya ka gaya mun kana sona hakan zai saka naji sanyi araina, don Allah karka tafi baka gaya mun magana mai dad’i ba”

Kallon side d’in da nake yayi nai saurin kauda kaina kamar ba jinsu nake ba, yace “please Anees………..Asaad duk haukar son da nake ma ba zaka tausaya mun ba, shekara nawa ina dakon sonsa yaci ka bani waje a zuciyarka koda kadanne”

Lumshe idonsa yayi ganin ba zata barsa ya tai ba, hannunta data rik’e nasa ya sumbata badan yaso ba saidan ta rabu dashi, yace “I miss u Anee”

Lallausan murmushi ta sakar masa tana sumbatar nasa tace, “by by asaad I miss u too”

Daker ya kubce ya shigo motar yace ma mannir yaja motar sutafi, yana duba agogo har eight takusa saura minty goma shabiyar,

Duk yadda naso danne zuciyata da kauda abunda nakeji kasawa nayi, iyakar kunci najisa daga yar firarsa da Aneesar, har bana son tunowa bana son hango hannunta cikin nasa, wani abu ya danne kirjina har nakejin kwalla na son cika idona, wannan wani sabon abune dake shirin faruwa dani yau kuma, wanda bansan dashi ba bankuma tab’a jinsa ba tunda ya shigo ya zauna gefena ni kadai nasan abunda nakeji, turarensa kadai duk ya dagula lissafina na makure jikin k’ofa sai tsifar yatsuna nake ina danne abunda ke kokarin faruwa dani, idaniyata ke shirin tara ruwa ina ganin ban barsu sun tarun ba, baice mun uffan ba kamar yadda na nuna bansan da zaman sa agefena ba har muka iso Airport din, motar na tsayawa zuciyata ta hau dokawa numfashina kansa daker nake jansa saboda danne kukan da nake akirjina, mannir da usman suka fita daga cikin motar suka barmu nidashi, kwallar da bana so ta fito naji tana silalowa ba tare da shirina ba, saurin kauda kaina nayi ina gogewa da hannuna bai hana wasu zubowa ba, ina cikin wannan yana yin naji tattausan tafinsa cikin nawa, runtse idona nayi so nake na fizge kuma bazan iyaba jikina tsuma kurin yake, hanky naga ya mik’o mun ya aje bisa cinyata.

Dauka nayi na saka fuskata cikinsa ina kukan ahankali wanda sautinsa ke fita silently gently yana saukar masa cikin birnin zuciyarsa da bargonsa, dunk’ule hannunsa yayi idonsa yai jaaa sosai lips d’insa yake ta cizawa gaba d’aya yana neman rasa kanshi lokaci guda, har wata shashsheka nake yi tun daga zuciyata kukan yake fita shine kadai zanyi inji nauyin dake kan kirjina yai sauk’i, amman inaaa banji ba banji yayi saukin ba………..jinsa kurin nayi akusadani sosai yayin da ya saka hannunsa biyu ya tallabo fuskata dake cikin hanky din daya bani, dan dole na d’ago rinannun idanuna na sauke acikin nasa shi kansa da zai samu dama zai iyayin kukan, saboda yadda fuskarsa tayi jawur idon nan ya canza launi, muryarsa ta zama wata iri yake cewa,

“Don Allah kibar kukan hakanan, nima zan iya yi inhar kika cigaba saboda sautinsa anan yake mun illah”

Ya dora hannuna akan kirjinsa da naji zuciyarsa tana bugawa sosai, idona a warwaje nake kallonsa, ban iya cewa komi ba kwallata bata tsaya ba kuma shine ya cigaba da magana,

“Da ace zanji irin haka a lokacin da zan tafi tuni dana soke tafiyar, ayanzun nakejin zan iya hakuri da komi na zauna inda kike, domin anan ne kurin zan samu natsuwa,farin ciki da annashuwa amman inba nan ba duk inda zanje zan kasance cikin kunci da damuwa, jann zuciyata cike take fargaban tafiyar nan jinake zaki manta dani, tsoro nakeji kamar akwai abunda zai faru dake”

Bansan sadda na cigaba da kukan ba saurin rik’e fuskar tawa yayi yana girgiza mun kai,

“Yallab’ai tsoron da kakeji nawa ya linka naka sau dubu, ka kawoni cikin mutanen da kwata kwata basa kaunata, a tunanina zaka zauna ka cigaba da zame mun kariya, gashi zaka tafi kabarni dasu bansan halin da zan fuskanci kaina aciki ba, inaji araina akwai abu marar kyau dazai faru dani, ji nake inama zaka fasa tafiyar nan”

Ban ankare ba ya dora goshinsa bisa nawa zuciyata kamar zata fito waje saboda bugawa, wani abu yake ratsani da bantab’a ji ba jinake inama mu kasance tare har gaban abadan, lumshe idanuna nayi saboda hucin numfashin sa dake dukan nawa numfashin, yakesa wa inajin kamar zan narke a wajen,magana yakeyi wadda saboda sanyin da muryar sa tayi ni kadai zan iyajinta.

“I’m sorry jann, bazan iya fasa tafiyar nan ba dole nayita, amman nai miki alk’awari daga can ma bazan kasa kulawa dake ba, abunda nake so dake shine kiyi karatu iya iyawarki, abunda ya dameki ki gaya ma usman zai kula da duk abunda kike buk’ata, zai taimaka miki kuma zamu ringa gaisawa time to time, don Allah jann ba ruwanki da khalid koda wasa bance ki kadaice dashi ba, ya wuce dukkan tunanin ki zan tafi jann”

Yadda na rik’e hannunsa kai kace bazan cika shi ba, wani murmushi ya saki wanda ya sake narkar da zuciyata yace mun yana mun wani sassanyen kallo, “ko in bar mikishi”

Ahankali na saki hannun ina kauda fuskata nima murmushin yana saukar mun ban shirya ba, kunya na kamani kuma riko hannun damata yayi ya zira mun wani kyakkyawan zoben azurfa, kallon hannun mukai nidashi sannan muka kalli juna nace “nagode sosai”

Ya lumshe idonsa sannan yace, “no need jann, duk hidimar makarantar ki na damk’a komi hannun usman, lokaci nayi zai biya miki kudin makaranta kawai”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Leave a Reply

Back to top button