JANNAH COMPLETE HAUSA NOVEL

JANNAH COMPLETE HAUSA NOVEL

“Yah usee yaushe yallab’ai Asaad zai dawo? Yaufa watansa biyu harda sati uku”

Sai kurin naga ya bud’e mota ya shiga ya ja yai tafiyarsa, idona waje nake bin motar da kallo har ya fice kamar an shukani a wajen saboda kad’uwa da abunda yayi, na dad’e nan kafin na koma cikin gida wayar daya bani na d’auko na tusata gaba ina kallo, iyakar sanina layin da yake kirana dashi kona kira bazai je ba, saboda bazai amfani dashi acan kasar ba shiyasa ban tab’a gwadawa ba, har zuciyata babu daren duniya da bazan dauki dogon lokaci ina tunanin sa ba, yau kam ban sani ba naji kwalla na d’igar mu saurin la kutota nayi ina kallonta kamar zararra, sai na goge fuskata na dauki qur’ani na ina tilawa.

Wannan bai hana shi zuwa washe gari ba don kaini islamiyya da yake weekend ne, nuna wa yayi kamar ma baisan meyafaru ajiyan ba muna hanya ne ba mai magana naji yace,

“Hindu ta isheni akan yaushe zaki dawo, don ban gaya mata inda kike ba tace kema baki gaya mata ba hakane”

Ina kallon waje ta taga nace”uhm”

Bai damuba ya cigaba da magana, “to yaushe zaki koma?”

Nan ma ban kallesa ba nace, “duk sadda ka shirya maidani,”

Burki naji ya taka da karfi ya jiyo cikin fushi, “ni kike ma wannan shariyar ehy? Kin sani sarai bana son wannan abun”

Kadan ya hana ban bushe da dariya ba amman saina sake shan mur na kauda kai naki masa magana, “dake nake magana kika jiyar dakanki ko”

Nan ma nai masa tsitt, ya dad’e mai sake cewa komi ba na dauka ma ya hakura da mun maganar sai naji yace cikin raunin murya kamar zai kuka,

“Ni nake miki magana kina banza dani? Shikenan………….Yah usee ni meka mun jiya fisabilillahi? Tambayarka nayi ko kallona bakai ba kurin ka shige mota kai tafiyarka ka kyaleni, don Allah ni bakai tunanin abun zai mun babu dadi ba”

Na katsesa da fad’ar haka saboda Allah ya sani naji babu dadi sosai, duk yadda nake bashi girma nake gudun abunda zan bata masa shi baya gani.

Cikin sanyin murya yace, “I’m sorry”

Daga haka har ya saukeni bai sake cewa komi ba, ranar duk wanda muke gaisawa yasan bana cikin walwala, hindu ce tazo sit din mu.

“Haba mana yar uwa don Allah kidawo gida hakanan”

Murmushi nayi nace, “waye yace dake bazan dawo ba, zan dawo mana”

“Gidan duk babu dad’i baki nan, ni nake gyaran dakina kullin agajiye zan tafi sch, abinci saidai kashiga ka girka da kanka don baba uwani ma tayi tafiya, wannan yar iskar kuma ko tayi ba dad’i yake ba pls sister ki dawo gida”

Na rik’o hannunta cikin kulawa, “zan dawo insha Allahu, zan matsa ma yaya usee ya maidoni kinjiko yar gidan momy”

B’ata rai tayi tana cewa, “wace momyn kuma? Kedai kawai ki manta gidan nan ya sake rikicewa nida momy yanzu ai saidai gaisuwa”

Ban fahimci maganarta ba sai ban isheta da tambaya ba muka fara wata firar ta daban, har ta sanyo maganar yallab’ai da kanta.

“Jiya ai munyi video call da brother ga computer, sai fad’a yake mun wai principal ya sanar dashi bana maida hankali”

Jinai ta sosa mun inda yake mun k’ai-k’ai na lumshe idona saboda hirar sa kadai tasa naji wani iri araina, nace “Ashe kuna waya dashi?”

Tace”inafa, jiyane kawai shima don yai mun fad’a duk dokin ganinsa danake naji ya fita raina”

Ta fad’a tana b’ata rai, nai dariya nace “Ayya yana son ki maida hankali sosai shiyasa, yanzu yaushe zai dawo?”

Tace”tabdijam! Ai inajin har sai kun kusa weac sannan, daman inya tai Spain yana dadewa bai dawo ba, yaya ne kina kewarsa ne?”

Ta fad’a cikin zolaya tana kanne mun ido, murmushi nayi ina kauda kaina nace, “Allah ya shiryaki daga tambaya?”

Dariya take tace”ehy mana nagama ganoki ai, karki damu inhar kika dawo gida zan kira miki shi”

Daidai malam ya shigo mai yi mana sira da ishmawyi, dole ta koma sit dinsu sannan aka fara karatu, amman gaba daya hankalina akan maganar da mukai yake, sai naji na d’okantu da son komawa gidan kodan ta kira min shi d’in awaya.

Koda aka tashi na dad’e ina jiran sa yazo saida akai azahar sannan sai gashi yazo, yadda yake shigar sa da gayunsa kamar dai na yallab’ai Asaad sai naga yayi kyau sosai, cikin zolaya don in kauda fushin da yake bayan mun fata tafiya nace “yah usee zance zakaje ne haka?”

Wani kallo ya juyo yana mun kafin ya saki murmushi kamar bazai magana ba yace, “nayi kyaune?”

Nace”sosai ma kai baka gani ba”

Girgiza kai kurin yayi yace, “Aa ban gani ba yanzu dai nagani”

Ya mutsa fuska nai alamun rashin fahimta nace, “A ina kagani d’in to?”

“Share kawai, zaki koma gida gobe ne?”

Cikine sauri nace “ehy mana zan koma daman hindu sai complain takeyi”

“Uhm gobe kishirya sai kikoma Abba ma yanata magana wai yai missg tuwanki”

Dariya nayi silent da har saida ya juyo yana kallona nace, “Allah sarki Abba kace masa gobe dana dawo ya shirya cin tuwona”

Zuwa can yace “Jannah”

Juyowa nai ina kallonsa nace, “Naam”

Daidai mun iso gidan maigadi ya bud’e mana get mun shiga, saida yayi parking sannan ya juyo yana kallona saida gabana ya fad’i naga kamar yallab’ai ne gabana, cikin taushin murya yace “yau nakeyin birthday”

Cikin nuna farin cikina nace, “wow masha Allah, happy birthday ya usee”

Murmushi yayi yace, “thank you, na shirya wata yar liyafa ko zaki zo?”

Shiru nayi na dan lokaci saida ya sake cewa, “please………..kallon sa nai na maida kaina kasa sannan nace “shikenan zanje, amman ban san wajen ba”

Cikin jin dadi yace “Ai ni zanzo saina tafi dake, karfe takwas zanzo nama sanar da Anty munirat”

Yadda yake murna abun yaban mamaki fitowa nai muka shiga gidan tare, daki na wuce ina cire kaya amman zuciyata cike da tunani kala-kala……………..

Mom muhseen✍????
[8/15, 4:05 PM] Mom Muhseen????: ????JANNAH????

{A TRUE LIFE STORY}

E.W.F

By
Mrs Bb
mom muhseen

wattpad name
Humaira3461

    ????️.......18

Kafin lokacin da yace zaizo yayi gaba d’aya ja rasa sukunin zuciyata, na kasa samun matsaya akan inje ko kar inje, gashi dai na amsa masa cewar zanje d’in to amman inajin tsoron binsa, bana zargin sa cin amana amman kuma wannan rawar k’afar da yake akaina fa?
Sannan a matsayin wa zan bisa Kanwa? Ko kawarsa? Kome………..rufe idona nai na kwanta kan gadona ina ta tunanin abunda ke faruwa dani, yah usy ya kasance mai kyautata mun da abunda nake so da wanda ma ban nuna inaso ba yimun yake, da karfin sa da kuma aljihunsa duk da nasan yallab’ai yana tura masa dukkan wasu kudi da zai mun hidima dasu, amman nasan wani abun da nashi yakeyi, don ma sun kammala exams dinsu ta final kwanakin baya shiyasa yake samun lokacin kulawa dani, aganina kulawar kamar taso tayi yawa amman idan na tuna kalaman yallab’ai kafin tafiyarsa sai inga yana yin abunda ya dauki alkawarinsa ne,…………..shigowar Anty munirat yasa nai saurin tashi zaune tace,

“Kina son zaman daki Jannah bakijin komi”

Murmushi nayi nace “hutawa dai nake Anty, naga ba abunyi shiyasa”

Zama tayi tana cewa “ramma ta gama komi ai karki damu, yau nake koma wa night duty na usy yace zakuje party birthday dinsa ko?”

Na sadda kaina cikin sanyin murya nace, “dazun yake gaya mun, ni dai bana son zuwa Anty gashi na riga na amsa mashi”

Murmushi tayi tace, “ba wani abu insha Allahu karki damu, na yadda da usy sosai kije d’in idan yazo gashi yace na baki yanzu ya shigo ya fita,”

Jikina a sanyaye na anshi ledar da take bani nace, “Anty yah usy duk ya canza mun wallahi”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Leave a Reply

Back to top button