JANNAH COMPLETE HAUSA NOVEL

JANNAH COMPLETE HAUSA NOVEL

“Amman dai yah khalid baka da hankali momyn kake fad’a ma wannan maganar? Kayi asara…….zanci ubanki inkika sake mun magana ina ruwanki dani ne ehy,taya ina ganin abunda raina yabiya zaki nemi hanani”

Ya katse fareeda da fad’ar haka yana huci, fareeda tun isha’i tazo gida bata yadda wani ya ganta ba ta b’oye dakin momy, sai lokacin da kowa ya kwanta sannan tafito.

“Ku refan baki dalla can,zaku saurareni ko kuwa fad’a zaku cigaba dayi?”

Hakuri suka bata sannan suka maida hankalin su kanta wajen sauraren abunda take shirya masu………..


Asuba nayi naji wayata na motsi kasan filo, kamar na rushe da kuka saboda baccin bai isan ba, jiya sai kusan daya baccin ya saceni idona rufe na saka ga kunne ina cewa cikin muryar bacci,

“Uhmm inaji”

Bashiri ya lumshe idanun sa daker yace, “ki tashi kiyi sallah karki makara”

Saida naji muryar sa sannan na bud’e idona cikin bacci-bacci nace, “Sallah kuma?”

Murmushi kurin yake yace, “ehy sallah, ko bakiyi”

Tabbas banayi ina period ne amman hauka nake nagaya mashi, sai nace “Aa zanyi yanzu”

“OK tashi yanzu, sai naji shigarki toilet sannan zan kashe”

Doriwo nayi daman kuma fitsari nakeji na bud’e kofar toilet d’in na shiga na kunna famfo ina cewa, “to na shiga fa,”

“Ok by, don’t forget me acikin adduar ki”

Kasa- k’asa na amsa masa “uhmmm”

Na kashe na aje wayar nai fitsari nai tsarki sai kawai nace bari nai wankan yanzu, wanka nayi na fito na shirya na canza auduga na saka hijab na fita don fara aikina, sai lokacin muka had’u da babaah uwani taji dad’in dawowata tana ta ban labarin lokacin da bana nan yadda aiki yai mata yawa, “yusra kuma yanzu ta giga Murja,ban sani ba ko daurin gindi ta samu cikin gidan,yanzu kanta tsaye takeyin abu ga wata sabuwar alak’a da suka k’ulla ita da khalid”

Nai mamaki sosai nace “Amman babah uwani khalid bana masa kallon mutumin arziki,meyasa yusra zata ringa biye masa, ni kam tsoron ma had’a ido nake dashi wallahi”

“Taji zata iyane, nidai nayi mata nasiha danaga bataji ba sai na kawo ido na sanya mata, don haka kema ba ruwanki komi kika ga zatayi”

Da haka muka bar maganar naje nafara aikina yanzu anyi timetable din girki, sai muka samu sauki cikin lokaci mukai duk abunda zamuyi muka gama,na wuce don gyara dakin momy,

Da sallama na shiga sai lokacin take sallar asuba wajen karfe bakwai da minty biyar, tirr da wannan d’abia risinawa nai ina gaidata.

“Lafiya lau Jannah antashi kenan, yau zan huta da gyaran dakin nan ai ba kadan naji dadin dawowarki ba”

Murmushi kurin nayi sannan na fara aikin, na dad’e saboda saida na gyara mata wadrope dinta, dazan taho ne ta bani turare mai kamshi naita godiya,

“Laaa kibar gode mun, kema yata ce ai ki saki jikinki dani kinji ko,”

Da haka na fito na isa kitchen na fara shirya table, ina cikin shiryawar Yah Asaad ya fito kamshin sa kad’ai ya sanar dani wanzu warsa, da sauri na d’ago ina kallonsa, shima nidin yake kallo yai mun masifar kyau ainun, kananan kaya yasanya masu kala d’aya rigar ciki kadai ce fara ta saman da wandon sune kala d’aya dark blue, rigar saman bai saka mab’allan ba hakan yasa ana ganin ta cikin, kashi yasha gyara bansan na dad’i ina kallon sa ba saida naji ya d’an buga cokali bisa table sannan na dawo hayyacina, kunya cema ta kamani na juya nabar wajen cikin sauri, sadda na kawo sauran kayan Aneesa ta fito da Yah usy gaidata nayi ta amsa mun a dak’ile nazuba mata nata sannan na isa ga Yah usy ina gaida shi,

“Ina kwana yah usman”

Dan har usy yazo mun nai saurin canza wa, cikin natsuwa ya amsa yana cewa “kina kallon time kuwa?”

Ina zuba masa nashi break d’in nace, “yanzu zanje na idasa shiryawa”

Yah Asaad naje na xuba mawa sannan na wuce ciki don sauran basu fito ba, dana tuna yadda Aneesa ta kama hannun Yah Asaad ta makale sai wani narkewa take tana masa magana k’asa k’asa, wani abu ya tsaya mun ga mak’oshi saboda haushi.

Drivern sa mannir shiya kaimu makaranta nida hindu, sai masifa take mun wai ina wulak’anta mata d’an uwa, abun ma sai ya ringa ban dariya yadda duk tabi ta rikice sai masifa take daker na shawo kanta da lallashi,

Muna tasowa karfe biyu nai wanka na ci abinci sai bacci, saboda gajiya na kwana biyu banyi aiki irin na yau ba, ban tashi ba sai karfe hud’u harda rabi gyara jikina nayi saboda kamar nayi stain, wayata na dauko da naji tana vibrate na saka ga kunne tunda on ready na san ko waye,

“Kishirya yanzu ki sameni compound,”

“Turo baki nayi saboda har yanzu in natuna yadda Aneesa take masa dazun, haushi kamani yake shi kuma ko wani anshewa bai ba can kasa na bashi amsa,

“Aikin yamma fa zanyi”

“Aikin yamma yaci k’aniya Jannah, karki bari na sameki a dakin nan”

Cikin haushi ma na kashe wayar.

Ayi hkr faa da rashin yawan pages????????

Mom muhseen✍????
[8/22, 3:13 PM] Mom Muhseen????: ????JANNAH????

{A TRUE LIFE STORY}

E.W.F

By
Mrs Bb
mom muhseen

wattpad name
Humaira3461

    ????️.......23

Kaya na canza sai tuttura baki nake kamar yana ganina na saka turare sannan na dauko wata hijab din shigen kalar kayan jikina yau harda jikka na dauka, inajin araina inama ace gidanmu zai kaini rabona dasu wata cikin na shidda kenan, ina kewarsu kuma suduka ba wanda yake tunanin yazo inda nake,

Ina fitowa compound din na hangoshi shida Aneesa tsaye jikin motar kamar zata shige jikinsa, da karfin gaske kirjina ya buga yadda kuka san na juya na koma ince ban zuwa, hango yah usy danai yasa ban koma d’in ba daina kallon su nai na bada duka hankalina kanshi,ganin zai yanke hanya yasa na d’aga murya nakirashi.

“Yah usy kaji”

Duk wanda ke area saiyaji muryata nasan kuma sunjini, nai kamar ban gansu ba na taka har gabansa ina murmushi hanuwansa duka cikin aljihu yake kallona, kamar marar lafiya yace “Ya akai yine?”

Na b’ata rai ina cewa, “wai menai maka ne? Kwana biyu kenan kanata fushi nayi ma laifine?”

Kallon da yake mun na kasa fassarashi ya lumshe idonsa ya bud’e yana cigaba da kallona kafin cikin sanyin murya yace, “inason na kaurace makine?”

Zaro idona nayi nace, “ni kuma? Danai maka mekenan?”

Yar hararata yayi yajuya indasu Yah Asaad suke yace, “gashi can yana kallonki kin tsaya kina mun magana”

D’an murgud’a baki nai nace, “to saime? Wai meyasa kake haka aibani nai maka ba ko”

“Amman dalilin wa akai mun? Kije yana jiranki”

Kamarna rusa ihu “nafasa ba zanje ba…….na juya zan tafi kuma har raina dagasken tafiyata zan nakoma ciki, saurin rik’o hijabina yayi baiko motsa daga inda yake ba, juyowa nai ina kallinsa shima ni yake kallo yace “inhar bakya tsoron yaganmu tare yau da daddare bayan isha’i kizo muyi karatu”

Jinjina kai nayi nace, “zanzo, a ina zan sameka”

Da hannunsa yanuna mun,”guiden, ai yayiko?”

Rausayar dakaina nayi kurin sannan yai mun murmushi ya shige ciki ya barni nan, kafafuna naji na kasa d’agasu daga wajen duk da inajin yadaina kallona yanzu, tambayar kaina nake inje ko kawai na koma ciki abuna, watau da Aneesar ma zamuje inda zamu d’in? To indai da itane na fasa bazanje ba duk tsoron fad’ansa da nake na danne na nufi inda motar take, a tun zure nake na bud’e bayan kenan na ganta zaune gefensa ta d’ofa kanta jikin shoulder d’insa, ai saidai naji na maida kofar da karfi sannan na wuce fuuuuu nai cikin gida, dakina nai burki na cire hijabin nai wurgi dashi na zauna bakin gado jagwab, huci kurin nake fiddawa duk kokarin na kauda abunda nagani na kasa, na fad’a kan gadon na dora filo bisa kaina ina cikin wannan halin kawai akafara knocking kofata, bansan ko waye ba amman bazan b’ud’e ba ko Abba ne kuwa a yadda nakejin wani irin abu ga kirjina da mak’oshina, ko kadan ba abar bugun k’ofar ba zuwacan kuma saiga kira a wayata filon na dauka na ringa bugunta dashi kamar ita tai mun laifin, muryar Babaah uwani naji tana mun magana.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Leave a Reply

Back to top button