JANNAH COMPLETE HAUSA NOVEL

JANNAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Kamar bazamu rabu ba saida aka fara kiransu sannan ya bud’e kofar yana kallona, yace “goodbye jann”

Rausayar da kaina nayi ina cewa, “Allah ya tsare YALLAB’AI ASAAD Allah ya bada sa’a ya maidoka lafiya”

Ya lumshe mun idonsa sannan ya fice daga cikin motar, kaina na saka cikin kafafuna ni kadai zan iya misalta abunda nakeji, nima din wani bazan iya fada ba amman tabbas feeling din yana da girma da fad’i, inaji ina gani muka tai muka barsa.

DAGA WANNAN RANA NA SOMA FUSKANTAR SAUYIN K’ADDARATA, ZAN IYA CEWA TAFIYAR ASAAD ITACE TA JANYO MUN AFKUWA DA FARUWAR KOMI

MOM MUHSEEN✍????
[8/8, 11:14 AM] Mom Muhseen????: ????JANNAH????

{A TRUE LIFE STORY}

E.W.F

By
Mrs Bb
mom muhseen

wattpad name
Humaira3461

    ????️.......15

Dukkan abunda ya kamata aimun yaya usman ya tsayaa anyi mun, wasu littatafai duk ya biya kudi na amsa sannan aka nuna mana class, har sit d’ina yaya usman ya kaini na zauna sannan cikin san cire mun damuwar da nake ciki yai mun murmushi yace, “be a good student jann ta hakane bros zaiyi alfahari a duk sadda ya dawo”

Sai nai masa murmushin nima nace, “insha Allah yaya usy”

Yace, “zan dawo daukarki idan antashi”

Na rausayar da kaina sannan ya fita daga class d’in, bamu da wani yawa bamu wuce 35 ba acikin ajin anyi mixed da maza sit d’inmu ne kad’ai bama da namiji, mu biyu ne nice na fara mata magana tunda nina isketa, hannu na mik’a mata ina murmushin dole saboda har yanzu zuciyata kuntace take.

“Sunana murjanatu ja’afar ana kirana jannah kefa”

Kallona kawai takeyi kamar tv ko keftawa batayi yayin da nabayan mu nakejin suna kus-kus akaina, “kai wannan kamar balarabiya,”

“Ai daker idan bata had’a iri dasu ba, kyau kamar aljana”

Abunda naji suna fad’a kenan, araina nake ta fad’an tubarkallah masha Allah, saida na sake mata magana sannan tai girgigi tace “ohhh sorry don Allah, ni kuma Aslamiyya Nura”

Daga haka sai ban sake ce mata komi ba, bama ita dana bayana ba kowa class din kallona yake sai nakeyin kamar ban gansu ba, a haka mai physic ya shigo aka fara darasi idan nace na gane meya koya nayi karya harya fita, saboda zuciyata bata tare dani kamshin turarensa dake jikina duk sadda na shakesa sai naji sabon abu a zuciyata, ji nake gaba d’aya yallab’ai ua tafi da jin dad’ina da walwalata, har aka tashi babu darasin dazan iya cewa na fahimta kallon malamin kurin nake yi amman ba abunda nake fahimta.

Kamar yadda yayi alkawari karfe biyu yazo ya daukeni, yanata tsonakata duk dan na saki jikina saidai nayi yak’e kurin, daga uhm sai uhm daya gane bana cikin mood mai dad’i saiya rabi dani.

Kamar wasa na cigaba da rayuwa wadda tazo mun da sauyi sosai, na farko kewa da radadin tafiyar yallab’ai asaad sannan ga tsoro da zullumin mutanen gidan nan da suka sake canza salon cingunawar su akaina, tunda akace yallab’ai yasa kafa ya tafi abubuwa suka canza mun acikin gidan nan,aiki nake kamar jaka momy kuma bata sake bud’e baki tayi ma wani fad’a akaina ba, hasali ma agabanta Anee zata daga hannu ta mareni ko nuna ta gani batayi, wanzuwar yaya usy a wuri shine yake sawa ina samun sassauci don shima ba laifi anajin shakkarsa, amma da ance baya wuri shikenan sunana jakkatu, sannan karfi da yaji ansaka ina shiga d’akin khalid gyara masa, haka zanje dakin nasa ina samun sa ayanayin da bana jin dadi, wani lokacin dagashi sai gajeran wando ko singlet babu, ahaka zan masa aikin yana mun wani irin kallo kamar na maita, haka ko aiki nake a kitchen yazo yai tsaye bayana kamar maye yana kallona gabaki d’aya hankalina baya kwance cikin gidan nan, karma ace fareeda tazo ranar ina cikin tsaka mai wuya, Abba baya zaune sai yai sati ma baya gida saboda hidimar siyasar sa, b’angaren yaya usy kuma bakin iyawar sa kulawa yake dani, idan wani assignment ne aka ban shine yake koyar dani har na gane sannan nayi da kaina yana nuna mun, ahankali yauda gobe tasa na fara sabawa da rashin yallab’ai asaad, amman kullin dare sai naita dakon ko zai neman ta waya amman shiru, bakina yana yin nauyi in tambayi yaya usy kasawa nake, sai inji kunya kamar zaiga wani abu shiyasa nake kasa tambayarsa.


Tsakanina da hindu yanzu sai mutunta wa abun yaban mamaki yadda naga ada kamar ta hura huta ta jefani aciki, nasan dai abu gudane ya kawo wannan sauyin shine rannan a islamiyya abun ya faru.

Makarantar akwai discipline sosai duk girmanka kuma ko kai dan waye idan baka kawo hadda ba bai hana malami ya dakeka, ko ya baka punishment ga maza suna kallonka a dizgaka gabansu, hakance ta kasance ranar hindu batayi hadda ba gashi malamin baida sauk’i ko k’adan, shine zaizo na karshe daga shi sai a tashi sai wadanda basu iyaba sukai amfani da wannan damar suke zuwa wajena ina sake koya masu, on ready tun a gezawa na gama surar har ma da wadda zamu shiga so banda matsala da hakan, kowa na neman mafita banda hindu girman kai ya hanata zuwa wajena tace na koya mata, har dai yan sit din nasu masu ji da kansu irinta nice naita koya musu harsuka rike sukatai suna nanatawa, karshe har malam ya shigo hindu na kwance bisa sit tayi kamar marar lafiya, tsoro ne karara ya bayyana tattare da ita akafara ansar hadda daya bayan d’aya, wanda yaga yana da gyara yace ya bashi zuwa gobe ya gyara ya kawo ta, da haka har aka kirani naje na bayar cikin jin dad’i yace ma yan class din,

“Ina alfahari da murjanatu kwarai dagaske, don babu mai bada hadda irin tata ga tajwidi tana fiddawa, ina fatan kowa yayi koyi da ita”

Akai mani kabbara, harna mik’e zan tafi na dawo na risina cikin biyayya nace,

“Yag Mu’alleem ina da alfarma don Allah”

Ya maida hankalinsa kaina yace, “wace alfarma kuma murjanatu?”

Na sadda kaina nace, “Hundatu Abdullahi yar uwatace malam tun shekaranjiya bata da lafiya sosai batai haddarta ba, gashi kuma ta riga tazo shine nake rok’a mata ayi mata afuwa zuwa ranar gobe insha Allah zan taimaka mata ta iya”

Jinjina kai yayi yana cewa “ina Hindatu Abdullahi?”

Mik’ewa tayi tana amsawa kallonta yayi sosai yana nazarinta sannan yace, “yar uwarki ta rokar miki alfarma, don haka gobe bazan daga miki kafa ba inhar baki kawo haddar ba”

Wani irin sanyin dad’i taji tace, “nagode yah mu’allem insha Allah zan dage”

Har aka tashi duk sadda na juya sai mun had’a ido da ita, daga yanayin fuskarta kadai na gane cewar taji dadin abunda nai mata matuk’a, koda aka tashi ina hangenta tana nemana ni kuma na kara sauri na fita na samu napep na wuce gida, don aiki na can na jirana har gabana fad’uwa yake idan zan koma gida daga makaranta ko boko ko islamiyya, saboda irin cusgunawar danake fuskanta.

Ranar ban samu kaina ba sai ana kiran magriba nai wanka nai salla kenan sai naji ana knocking, ina budewa naganta tsaye da kayan bacci doguwar riga ga qur’ani ga hannunta ta yane kanta da babban veil cikin mamakin ganinta nace, “kece anan?”

Abunda ban tab’a samu daga gareta ba shine yau tayi mun shine murmushi,
Tace “keda kikace zaki koya mun karatu miye na guje guje to?”

Murmushin nayi nace, “na dauka zaki dauki hakan matsayin laifi shiyasa naketa gujewa”

Ida shigowa tayi tana kallon dakin nawa tana cewa, “ai yau babu bacci har saina iya haddar nan, inba haka ba bani ba islamiyya gobe”

Na rufe na dawo ina cewa, “dako kin saka mu’allem cewa murjanatu bata da alkawari, tunda nice na bashi tabbacin zaki kawo hadda gobe”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Leave a Reply

Back to top button