JANNAH COMPLETE HAUSA NOVEL

JANNAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Dariya tayi tace “mekika gani ke?”

“Anty da ba haka yake ba, abu kadan indai akaina ne yanzu karki so kiga yadda yake rawar jiki akansa, sannan yaita yin wasu abubuwan da ni bana ganewa ni bana son hakan”

Kamar zan kuka nake maganar saboda har zuciyata bana son ya canza wannan alak’ar,
Rik’o hannuna tayi cikin lallashi tace,
“Karki tada hankalinki, ke amanace hannunsa kisama ranki babu wani abu tsakaninki dashi face matsayin yayanki ke kuma kanwarsa, da ace baki ansa masa zakije ba zan hana ki zuwa ne amman kin ansa idan kika ce baki zuwa yanzu zaiji babu dadi, ki dai kame kanki kinjiko wannan gown ce da zaki sanya, yace in tambayeki size din takalminki”

A sanyaye na amsa mata da cewa “36 or 37 duk ina sawa”

Saida ta sake kwantar mun da hankali sannan tatafi, na bud’e kayan ina dubawa kyawunta ya dauki hankali ainun red and black GE gown din, tashi nai na kangata ga jikina tsaf kuwa naga tsawon yai daidai dani, nai mamakin yadda ya san size din tsawona haka saina tuna rannan dana rakosa zai tafi gida har na juya ya tsaidani, inda nake ya karaso ya daidaita tsawonsa dani alokacin naji tsoro sosai yadda kusancin namu yai yawa haka, duk tsayina iyakar kirjinsa nake banma karasa ba kadan, yai murmushi yana cewa “Ashe ma ke yar gajerace na zata kinfini tsayi ai”

Ashe daman don ya gane tsayin rigata, harda wani net ajikinta hannun ma net ne ajiki ana ganin fatar jikin, har da veil acikin ledar sai wani dan box na sark’a silver mai dauke da sarka da yan kunne harda zobe,kayan sun burgeni sosai da sosai ainun dagani kuma zasuyi kudi sosai, maido kallona nai ga zoben azurfa ta da yallab’ai ya bani alokacin da muke bankwana, lumshe idona nayi sannan cikin sassanyar murya nake cewa a fili, “yallab’ai ban san iyakar lokacin da zan dauka wajen tunanin ka da kewar ka ba, zuciyata kullin da sabon abu take tashi akanka, har yau na gaza tantancewa na kasa sanin inda zuciyata ta nufa akanka, sannan ga kuma wani sabon abun makamancin irin naka daga d’an uwanka, ina fatan zaka mun uziri banda wata hanyar tserewa lamurransa, amman alk’awari na ne bazan tab’a bujire maka ba”

Zuwa nai na aje kayan saboda la’asar tayi naje nai alwallah nai sallar, su ashraf da sharifa suka dawo school ni nake shiryasu daman, muyita hira dasu muna dariya ba kamar sharifa tafi ashraf sakewa dani sosai, na gama masu suka ci abinci sannan muka zauna dasu study room dinsu na karatu, duk homework dinsu na taimaka masu sukayi Anty najin dadin wannan kulawar da nake masu, saboda wani lokacin bata zaune ma’aikaciyar asibitice in bata nan dagasu sai ramma mai aikinta, tunda nazo kuma sai ni nake hidima dasu kamar dai wata kanwarta hakan yana sata jin dad’i, har rannan tace ita wallahi daman nai zamana anan, saidai nai murmushi kawai bance komi ba, wannan zuwan ma da dalili da kila bazan tab’a zuwan ba.

Misalin karfe takwas na dare lokacin da yah usy yace zaizo ya daukeni, saida nayi sallar isha sannan nashirya shafa nayi daidai misali, ban tsawwala ba don daman ba gwanar kwalliyar bace ni powder da kwalli na saka a fuskar tawa sai dan jan baki red color, wannan kadai yasa naga nai wani irin kyau kamar zara acikin taurari, ni kaina wani lokacin inajin tsoron wannan kyan shiyasa kodayaushe nake cikin addua Allah yatsare ni daga dukkan masu sharri, ai banga nayi kyauba saida na sanya wannan doguwar gown din ko amarya sai haka sharifa ya aiko da takalman kala d’aya da veil din duk red ne, sai wani turare dan mitsili amman sakawa guda naji gaba d’aya ya baibayeni da mugun k’amshi, lumshe ido nai saboda ina masifar son turare karma ace na tuno kamshin turaren yallab’ai asaad, ina da burin mallakar wannan turaren koda zan karar da kudina inhar na samesa, Anty ce ta shigo nace “na daman inason zuwa ince miki bansan yazan daura wannan veil din ba”

Tana murmushi tace “masha Allah Jannah, kin ganki kuwa wannan ko ranar aurenki sai haka kinyi mugun kyau, don Allah kiyita addua kinjiko kodan bakin mutane”

Ina wasa da hannu na nace, “nagode Anty insha Allahu xan keyi”

Ita ta zauna ta gyara mun gashina dake kunce sannan ta daura mun veil din, tace “duk wanda ya ganki koda mace ce saitaji kinyi bala’in daukar hankalinta, to balle cikekken namiji kiyita karanta hazbunallahu wani imal wakil”

Tana sanya mun sarkar da yan kunnen ne mukaji yayi knocking yana cewa, “in shigo?”

Antyn ce tace”Aa ka koma falo gamu nan fitowa”

Har ban san yadda zan misalta kyan da nayi ba, zan iya cewa tsawon rayuwata ban tab’a ganin nayi kyau irin na yau ba in banda waccen ranar da yallab’ai ya kaini wajen gyaran jiki, wadannan lokutan bazan manta dasu ba.

Tunda muka fito idon yah usy bai dauke daga kallona ba, ko kyafta idonsa ma bayayi kamar ya manta da inda yake, kallona yake tun daga sama har k’asa, shigarsa irin tawa ce suit ne jikinsa bakake sai rigar sa sheet din ta ciki red color idan ka ganmu nidashi zaka dauka cewa wasu sabbin ma’aurata ne,gaba d’aya naji jikina yai sanyi Yah usy yana behaving ba daidai ba, wani miyau na had’iya kakkaura a sadda ya taso ya iso inda nake, idonsa akaina yake amman anty yake ma magana cewa,

“Anty kinyi mu sayar waccen jannah da wata ko? Na kasa yarda itace wannan”

Dariya take tace, “idonka ne kawai ya nuna maka haka, amman ita d’ince dai ba wata ba”

Kin kallonsa nayi saboda nasan wannan kallon da ya fara mun na yan kwanaki shi zan tarar yana yi mun, ni kuma bana son sa ko kadan.

“Jannah da gaske kece?”

Kai kurin na daga mashi alamun bashi ansar shi, yaja ajiyar zuciya yace “Anty mun tafi,”

“Don Allah usyn mama a dawo da wuri nima fita zanyi asibiti zan tafi”

“Insha Allah zamu dawo da wuri”

Kasancewa takalman Hill’s ne dole nake tafiya ahankali wanda inka gani zaka dauka yanga ce, rigar har jan k’asa take daga baya duk da tsinin takalman, sadda muka iso bakin motar sa harya bud’e mun gaban, shiga nayi ya rufe sannan ya zagayo ya tada motar muka fita, banda natsuwa ko kadan zuciyata bugawa take sosai gaba ki d’aya yah usy ya canza duk alak’ar da yafaro da fari, tun sadda ya daukoni zuwa nan gidan komi ya sake canza wa bansan meke ransa ba amman tabbas akwai abunda yake hidden, shiru motar tayi banda kamshi kala biyu dake tashi bakajin komi saifa sautin kid’a dake fita k’asa-k’asa, inata tunane tunane na naji sautin muryar sa cikin kunnuwa na cike da wani a muryar tashi.

“Ban Saba ganin fuskarki a haka ba don Allah ki saketa kozan samu natsuwar fuskantar mutanen dana tara”

Runtse idona nayi kalamansa basa mun dad’i ko kadan, na hadiye abu daker cikin raunanniyar murya kamar zan kuka nace “Yah usy……….shiiiiiit karki ce komi please”

Dole na had’iye maganata har muka karasa wajen daya kama aka shirya shi tamkar wata gagarumar liyafa, abokan sa ne na makaranta maza da mata gasu nan kowa cikin shiga mai kyau, yana tsayawa da motar akazo aka bud’e mana muka fito, abune aka shimfid’a har zuwa cikin wurin wasu bayan mu wasu gaban mu, hayaniyar mutanen har cikin kwalwata, abokan sa ihu kurin suke suna watsa flowers suna kunna abu mai kara yana tats tats ana shewa har muka iso mazauni ga cake nan yasha kwaliya, kowa yazo wurin mu maganarsa akaina nane yayin da naga kishi idanun yan matansa wadanda suketa rawar kai akanshi, yadda suka ga yana wani nan nan dani yasa ransu ya b’aci, saboda hotuna idona har gajiya yayi abokan sa maza kamar zasu fad’o kaina, yah usy yai kokari gaskiya don ko wane table rabin kaza ce ake ajewa da snacks sai lemu da ruwa, tsarin wurin ya had’u sosai ga kid’a dake tashi mai dad’i, saida akaci aka sha sannan aka fara kokarin yanka cake, nidai lemu kurin nasha zuba mun yai a cup d’in ya mik’o mun, sai sannan muka had’a ido dashi daidai kuma sadda mai daukar hoto ya dauke mu, bazan iya fassara kallon da yake mun ba ban ankare ba ya samu cup din ga bakina, dan lumshe idona nayi kafin naji shewar mutane dole na ringa sha har na sha rabin sa, sannan na girgiza kaina cikin sanyin murya nace “na k’oshi fa”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Leave a Reply

Back to top button